Showing 45001 words to 48000 words out of 58121 words
yaya Gwamma aikata
alkhairi komai k'arancinsa arayuwarki ta duniya ki guji aikata masha'a komai k'arancinsa,,,
amatsayina na d'an uwanki kuma k'ane agareki ya zamo dole in sanardake gaskiya koda zakiji
haushina ki tsaneni,,, koda hakan zai zamo silar b'acin ranki abinda kike aikatawa acikin garin
nan dai bai kamata ba,,, sana'ar maita bata dace dake ba !Ko'ina acikin gari maganarki kawai
akeyi ana cewa ke *MAYYA CE* sannan abin takaici da bak'in cikin rayuwa gashi yanxu na gani
da idona har namiji kike kawowa acikin gidan nan kuna aikata abinda kuka gadama,, ansha
kawomin gulma da jita jita amma ban yarda ba gaskiya sai yanzu ,,,,ki ji tsoron Allah domin ina
guje miki yin mummunan k'arshe! Duniya bakiji wani dad'i ba hakama lahira ba zakiji dad'i ba ".
Gwamma ta hararesa tareda jan mugun tsoki mtsssss! Sannan tace "ka gama tsohon munafiki
wato an turoka ne domin kazo ka cimin mutunci ko,, wallahi kam baka isa ba kayi d'an k'arami
da kai Lawwali maita kuma bazan daina ba! Duk ubanda zaka gayawa jeka gaya masa bana
tsoron uban kowa ciki kuwa harda kai! Shege wanda baisan d'an uwa ba ".
Lawwali yayi hucin mai cikeda takaici da bak'in cikin Gwamma,,,sannan yace "Alal hak'ik'a na
k'ara tabbatarwa da wanda yayi nisa bayajin kira acikin aikata masha'a da mummunan dabi'a,,,
daga fad'in gaskiya ayau shine zaki cimin mutunci ki nunamin ni ban isa in gaya maki gaskiya
ba,,, Allah ubangiji ya shiryeki yasa ki gane gaskiya gaskiya ce kuma k'arya k'arya ce ".
"aini ashirye nake kuma kowa shiriyar Allah yake nema bata mutum ba,,, ehehhh maita ce da
kuma yin zina bazan daina ba koda kuwa mutum zai fad'i k'asa ya mutu har lahira! ".Cewar
Gwamma cikeda jin haushin maganarsa da bala'i..
Lawwali yace "to yayi miki k'yau matuk'a duk dai abinda kikeyi marasa k'yawo,,, Allah yana
sama yana kallonki kuma shi zai musu sakayya tun anan duniya ina k'ara tabbatar miki muddin
baki daina aikata miyagun ayyuka ba,,, karshenki bazaiyi k'yawo ba !".
"kar yayi k'yau d'in ina ruwanka idan har nayi mummunan k'arshe? To idan aljanna taka ce ka
hana in shigeta,,, kuma tun yanzu kazo kasa inyi mummunan k'arshe mara mutunci wawan
banza dolo wanda babu tunani da nazari acikin kansa ".Inji Gwamma cikin takaici da haushi..
Lawwali ya tashi tsaye yana cewa "to tunda bak'yajin nasiha na k'yaleki,,, kije kiyita aikata duk
abinda kika gadama babu abinda ya shafeni! ".Yana k'arasa maganar yayi tafiyarsa batare da
ya tsaya ya saurarin irin martanin da zata mayar masa ba.
"aikin banza yima karen mak'wabta wanka mtssssssss kai har ka isa kace zakayimin wa'azi ko
nasiha,,,, to wallahi ka kiyayeni idan ba haka ba barin ganin uwarmu d'aya ubanmu d'aya ina iya
kasheka in cinye namanka d'anye! Kuma ba'a komai babu maija dani Gwamma mayya ".Inji
Gwamma ta kama sambatu tana zage zage na cin mutunci da tozarci.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Baba Labbo ne zaune da Inna Tani suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai,,,
saboda su yanzu Alhmdlilah babu abinda suka nema suka rasa komai su Sagiru kawo musu
sukeyi,,,, na dangane kayan masarufi da mak'ulashe abinci kala kala sukeyi wani buhun
shinkafa,,, masara,,,wake da dai sauran kayayyakin abinci wani saiya tadda wani,,, nama sai
sun ture da kuma kayan marmari..
Inna Tani ta karkace baki tace "Hhmmm maigida ashe dai Gwamma ta zama k'usurgumar
mayya,,, shiyasa rannan ta zama macijiya ta koraka daga cikin gidan yayanka ".
Baba Labbo yace "aike wallahi lamarin akwai ban mamaki da al'ajabi da maigari yana gaya
mana,,, ba kiga irin yadda mutane suka rikice suna hawaye ba!Wai ashe ta zama babbar mayya
tafima uwarta shahara ".
"ai Allah yasa kanada k'arar kwana agaba da yanzu Gwamma macijiya ta lak'umeka zama
guda,,, ni wallahi abin har mamaki yake bani wai cin naman mutane takeyi ".Inji Inna Tani tana
kallon baba Labbo tana masa dariyar k'eta.
Baba Labbo yace "haka ne gaskiya da yanzu ina can cikin kabari kwance,,, aini yanzu ko bakin
k'ofar gidan nan bazan iya k'ara giftawa ba saboda in tsira da rayuwata ".
Inna Tani ta bushe da dariya sosai tace "maigida akwai ka da tsoron bala'i,,, ai b'oye b'oye baya
maganin mayyu saboda ko'ina kake suna ganinka,,, addu'a itace maganin mayyu kuma takobin
mumini ce "............
_Share&Comments_
[7/6, 5:42 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 26*
"Addu'a itace maganin mayyu kuma takobin mumini ce,,,, sannan mace mai yara k'anana da
basu iya yin addu'a ba,,,, ya zama dole ta dinga yi musu addu'o'in neman tsari tana shafe musu
jiki akodayaushe,,,, ba wai mace ta nuna son jiki ko k'yuya ba ".Inji Inna Tani,,, "tabbas
maganarki gaskiya ce Tani,,, babu yadda zaka saki baki bakason yin addu'a sannan kace wani
abin cutarwa bazai tab'a cutarka ba ".Cewar baba Labbo yana murmushi,,, Inna Tani ta dubesa
tace "aini yanzu lamarin duniyar nan tsoro yake bani sosai,,, yanzu kaga mutum lafiya k'alau jibi
ace maka ya zama mayye cin naman mutane yakeyi ko takeyi ".Baba Labbo yace "kwarai da
gaske ma ai kinga yanzu idan da ace Gwamma lafiyarta k'alau,,,, bai dace ace na barta zaune
ita kad'ai tana aikata abinda ta gadama ba ,,,,saboda naji ance yanzu har namiji yake shigowa
cikin gidan nan yana tayata kwana,,, to daga barcin tare da k'ato saimi zai faru? Sai iskanci da
abinda ba'a so shine zai iya biyowa baya "."Af ai iskanci da yin maita yanzu ya zama ruwan
dare,,,,, saboda yanzu yanada wuya kaga wanda baya aikata d'aya daga cikin wad'annan
abubuwan dana ambata,,,,, kaga kuwa saidai mu dage da yawan yin addu'a akan Allah ubangiji
ya karemu daga muyagun k'addarori muda iyalanmu ".Inji Inna Tani cikeda matuk'ar sanyin jiki
da natsuwa,,, baba Labbo yace "amin ya rabbi Tani lamarin mutanen yanzu sai a hankali,,,, ai
Gwamma ta koyar dani darasin rayuwa idan kace ka faye shiga cikin abinda bai shafeka ba,,,,
matsalolin rayuwa mutum zai jefa kansa ciki kuwa "."Hmmm maigida kenan wata rana kana
bani mamaki sosai,,,, ai duk abinda ya shafi Gwamma ya shafeka saboda koba komai 'yar
yayanka ce uwa d'aya uba d'aya ba lafiya bane,,, sannan kuma ko kwatance za'ayi sai dai ace
yanzu d'iyar Mamman da Talatu,,, Mamman yayan Labbo mijin Tani mai wake kaga kuwa anan
hannunka bai tab'a rub'ewa ka yanke kayar ,,,,ka dai k'yaleta ne saboda kaima tafi k'arfinka
ne,,,, amma ako'ina akaje kaine ya kamata ka rik'eta amatsayinta na marainiya domin kaine
dolenta ".Baba Labbo yayi dariya yace "babu k'arya a cikin maganarki Tani shiyasa nake k'ara
sonki,,, saboda kinada natsuwa da hangen nesa Allah ubangiji yayi miki albarka kuma ya barmu
tare "..
Inna Tani taji dad'in addu'arsa k'warai da gaske,,,, wani farin ciki da nishad'i ne ke wanzuwa
acikin sassan jikinta gaba d'aya,,, tayi murmushi tace "amin amin maigidana ".
Firarsu suka cigaba da yi mai dad'i da ma'ana sosai,,, daga ganin yadda suke gudanar da
rayuwar aurensu babu abinda suka nema suka rasa a cikin zamantakewarsu...
*********************
***Aliya ce matar Lawwali zaune tana tankad'ar garin tuwo,,, ga d'iyarta nan mai suna Hajara
tana wasar k'asa agefe,,,, ita kuma uwar ta mayarda hankalinta kacokam wurin aikinta,,, can
bada jimawa ba saiga sallamar Lawwali ya shigo cikin gidan,,, fuskarsa murtuk'e babu alamun
fara'a ko walwala ana hango b'acin rai acikin k'wayar idanunsa ,,,,Aliya dai ta amsa masa
sallamarsa cikin sanyin jiki ta kawo tabarma ta shimfid'a masa cikeda ladabi da girmamawa,,,,
bayan ya zauna ne ta kawo masa ruwa masu sanyi cikin kofi ya d'auki ruwan yasha,,,, sannan
yayi ajiyar zuciya yace "Alhmdlilah Allah ubangiji yayi miki albarka ".
Aliya tayi murmushi tace "amin baban Hajara amma mi ye yasa ka shigo cikin gida da b'acin
rai?Har baka iya b'oye b'acin ranka kafin ka shigo cikin gida ".
Lawwali yaja dogon numfashi sannan yace "kede bari Aliya abin ne akwai matuk'ar b'acin rai da
ban takaici,,,, wai nine zanje wurin yaya Gwamma in bata shawara akan abinda take aikatawa
bai dace ba,, shine ta kama yimin fad'a da cin mutunci abin babu dad'in ji balantana saurare ".
"ayyah baban Hajara hak'uri zakayi domin koba komai itace sama da kai,,, kuma yayarkace
kaine ya zama dole kayi mata biyayya kuma shiriya tana hannun Allah,,, da kad'an kad'an sai
kaga ta daina yin duk abubuwan da takeyi ".Inji Aliya cikeda matuk'ar lallashi da ladabi..
Lawwali ya nisa yace "Aliya kenan bakisan ainahin halayyar yaya Gwamma ba,,, mace ce mai
matuk'ar taurin kai da tsattsauran ra'ayi kuma duk abinda ta sama gaba komai rashin
k'yawonsa,,,, ba zata daina ba yanzu ma bari in sanardake gaskiyar lamari maigari yace idan
aka kama mayyu akashesu! Sannan Ummaru d'an Sala mafarauci yawon nemanta yakeyi ruwa
a jallo saboda itace ta kashe masa iyayensa da yayan babansa,,,, ta cinye namansu ni kuwa ina
jiye mata mummunan k'arshe da mugun hukunci ".
Aliya tace"hmmmm amma kam wannan hukuncin yayi tsauri da yawa gaskiya,,,, ana kama
mutum kenan ana kashesa! To ka cigaba da hak'uri kana zuwa kana lallashin yaya Gwamma
har ta daina maita,,, kafin hukuncin maigari ya hau kanta akasheta abar mana abin gori da
fad'a,,, surutu,,, gulmace gulmace ko munafurci ".
"abin gori da surutu na nawa kuma saboda ni idan na fita waje,,, har nunani akeyi ana zund'ena
da nunena da cewa ga k'anen Gwamma mayya can tafe,,, wasu ma har guduna sukeyi wai
saboda basu yarda niba mayye bane domin Innarmu wai gadon maita tabar mana! ".Cewar
Lawwali cikeda matuk'ar takaicin yadda rayuwar Gwamma ke tafiya tana cin naman mutane da
aljannu!.
Aliya tace "hak'uri zaka k'ara yi ai mutane iyawa dasu sai Allah,,, sannan ya zama dole ka toshe
kunnuwanka daga jita jitar mutane da tseguminsu,,,,,,saboda haka ka daina damuwa akan anyi
ance da surutun mutane ".
"idan banyi hak'uri ba mi zanyi musu? Kedai Allah ubangiji ya sawwak'a yasa mu dace ".Inji
Lawwali..
Aliya tace "amin baban Hajara Allah ubangiji ya sanyaya maka zuciyarka ".
Aliya ta cigaba da yi masa kalamai masu dad'i,,, sannan kuma ta k'ara nuna masa muhimmanci
hak'uri da juriya akan zamantakewar rayuwar duniya,,,,, ta dinga lurar dashi ya dinga toshe
kunnuwansa daga jita jitar mutane......
Allah ubangiji yaba kowa abokin rayuwa nagari..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARU HUD'U*
Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kama sauran mayyu,,, da suka addabi rayuwar
mutane ana kashewa,,, Ummaru ya kama mayyu kusan ishirin yana kashewa acikin wad'annan
shekarun da suka wuce,,, yayi yayi ya kama Gwamma shahararriyar mayya amma ya kasa
saboda ita yanzu ta k'ara shahara da gunguma akan harakar maita! Duk wanda takeso take
kwad'ayin namansa kamesa kawai takeyi,, duk da yake Lawwali yayi zuwa kusan goma yana yi
mata nasiha akan ta daina maita! Amma wanda yayi nisa bayajin kira sai dai taci masa mutunci
tana zaginsa,,, zuwa na goma da yayi tayi masa kashedi da inya k'ara takowa gidanta da sunan
wa'azi saita kashesa ta cinye namansa! Yabar ganin uwarsu d'aya ubansu d'aya,,, jin ta fad'i
haka dole yasa Lawwali yajawa k'afafunsa linzami ya daina zuwa kwata kwata saboda yasan
duk abinda Gwamma tace tanayi,,, to tabbas zata iya aikatawa domin yasan halinta batada
tsoro tanada dakakkiyar zuciya.
To acikin wad'annan shekarun ne Gwamma ta haifi 'yan biyu mace da namiji da Sule
saurayinta,,, namijin sunansa Hassan macen sunanta Suhaila,,, bayan yaran sun fara girma da
tasawa taga ai amfanin Sule ya k'are koba komai tagama morarsa,,, gashi taga yanzu shima
har nasiha da wa'azi yakeyi mata akan ta daina maita! To ita kuma da mutum ya dameta akan
tabar maita gara yahau risho da wandon leda,, ganin da tayi Sule yana neman takurawa
rayuwarta yasa dole ta kame masa kurwa ta mayar ita zakara,,, arannan ne ta yanke zakaran
ta cinye abinta tasha ruwa tayi gyatsa.
_Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Allah ubangiji ya rabamu da aikata masha'a da kuma biyewa
*SON ZUCIYA*..._
Aka wayi gari Sule ya mutu abin kamar almara,,, akayi masa wanka aka kaisa makwancinsa na
gaskiya,,, Allahu Akbar duniya ba matabbata bace duniya mai cikeda bak'in ciki da k'uncin
rayuwa,,, Gwamma ta cigaba da gudanar da rayuwarta cikeda kwanciyar hankali da jin
dad'i,,,tareda da kula da yaranta cikeda matuk'ar k'aunarsu batason ko k'uda ya tab'asu idan da
son ranta ne,,, babu abinda take so da k'auna fiyeda yaranta.
Ita dai cigaba da cin naman mutane dana aljannu kawai takeyi wata rana ta mayarda kurwar
mutane zakara ko rago taje can kasuwar wani gari,,, inda ba'a santa ba tana samun kud'inta
cikeda wayo da 'yan dabaru ta haka ne take samun kud'ad'e tana ciyarda yaranta da kashewa
kud'i .......
_Share &Comments_
[7/6, 6:05 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 27*
**Ta haka ne take samun 'yan kud'ad'e tana kashewa da kuma kula dasu Hassan,,, haka dai
take gudanar da rayuwar gidan da maitarta,,,, Lawwali kuma ganin irin walak'anci da korar kare
da Gwamma tayi masa ya watsar da ita gaba d'aya ya fita harakarta,,, saboda yasan tunda ta
bud'i baki tace zata kashesa to tana iya kashesa abanza da yofi yabar yaransa da matarsa cikin
k'unci da tsananin maraici,,,, baba Labbo ne dama ya tsorace gameda lamarin Gwamma
mayya,,, domin tun lokacin da yaje domin ya dawo da ita gidansa ta rikid'a ta koma macijiya ta
koresa,,,,,to tun daga lokacin nan bai sake giftawa ko bakin k'ofar gidan nan ba,,,, balantana
yaje ya shiga cikin gidan kunsan yadda baba Labbo yakeda masifar tsoron mutuwa da mayyu!.
Ummaru mafarauci dai yana nan yana cigaba da bibiyar duk wani motsi na Gwamma,,, sannan
duk inda taje yana hankalce da ita yana kallonta babu inda zataje ko tayi wani motsi ba'a kan
idon Ummaru ba,,, ya damu sosai ta yadda take azabtar da mutane da cin namansu amma ya
gagara kamata! Shiyasa dole wata rana yayi zaune yana tagumi da bak'in cikin rashin kama
Gwamma mayya,,, domin zaluncinta da cin amanar mutane sai k'aruwa yakeyi,,, bata tunanin
abinda zaije ya dawo a rayuwa bata tunanin ai wata rana dubunta zai iya cika,,, bata tunanin
wata rana zata bar duniya baki d'aya taje can ta girbi abinda ta shuka? Ita dai Gwamma
gatanan dai kamar ba mutum ba zuciyar nan babu d'igon imani da tausayi,,, ta k'ek'eshe
zuciyarta daga barin tsoron kowa bata gudun abinda zai faru,,, bata tunanin kamar yadda aka
kama sauran mayyu 'yan uwanta to ita ana iya kamata!.
Mutanen gari kuma kowa ya shiga taitayinsa,,, saboda kada su afka cikin tarkon Gwamma
mayya,,,, kowane daga cikinsu ya tashi tsaye tareda dagewa da yawan addu'ar Allah ubangiji
ya kawo musu k'arshen zaluncin Gwamma,,, domin susan Ummaru yana iya bakin k'ok'arinsa
na ganin ya kamata amma abin yaci tura! Ya kasa kamata saboda yadda takeda k'arfin sihiri da
gunguma acikin harakar maita,,, kunsan ta zarce mahaifiyarta Inna Talatu awurin shahara da
bunk'asa domin ita har aljannu tsoronta sukeji balantana bil Adama,,,, bata shakkun tunkarar
kamun kurwar kowa acikin garin Gumi,,, Ummaru kawai ne take d'an tsoronsa domin kada wata
rana dubunta ya cika ya chafketa!.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ummaru ne zaune yayi tagumi cikeda matuk'ar bak'in ciki da damuwar rashin kama Gwamma,,,
ya rasa yadda zaiyi ya kamata.
Salma ce ta jaye hannun Ummaru daga yin tagumin da yakeyi,,, sannan ta dubesa tace "lafiya
baban Husna kana tagumi?Babu k'yawo ka daina sama kanka damuwa ".
Ummaru ya d'ago idanunsa da sukayi jawur akan damuwa,,, yace "Salma ina cikin damuwa wai
ace wadda tayi sanadin mutuwar iyayena da baba Labaran,,, na kasa kamata sai yawo da
hankali takeyimin ta mayardani mahaukaci ko mara sa'a a rayuwa ".
Salma ta kallesa cikeda matuk'ar tausayawa da k'auna matuk'a,,, tace "haba farin cikin
rayuwata miyasa zaka damar da kanka,,,akan abinda akodayaushe akowane lokaci kana iya
kamata,,,kai bakasan komai yanada lokaci da k'addara ba? Idan Gwamma ce zaka kamata duk
ta gama guje gujenta da b'oye b'oyenta sai dubunta