Showing 3001 words to 6000 words out of 58121 words
sosai.
Maryam ta mik'e tsaye tayi hanyar zuwa d'aki domin tayi wanka,,, sannan taci abincinta..
Alokacin ne Mubarak ya k'ara cewa "Mama ayita hak'uri k'urciya ne wata rana zata daina,,,
sannan nima zan k'ara saka mata idanu sosai ".
"hmmm haka ne Mubarak amma zamanin nan abin tsoro ne,,, ya zama dole mutum ya k'ara
lura da d'iyansa. Saboda mayyu sunyi yawa a cikin mutane sosai kowa ka gani yaci magani ne
domin yayi kud'i,, ko ya cimma wani buri nashi wurin bid'ar abin duniya sai mutum ya zama
maye kowa ya kama gudunsa,,, kuma ba ko'ina ake amso maganin ba illa wurin bokaye da 'yan
bori. Mutane sun manta da cewa babu mai talautawa da azurtawa idan ba Allah kad'ai ba. Sun
manta da cewa babu mai iya ba mutum abinda Allah bai bashi,,, da ace wani bawa yana iya
azurtar da d'an uwansa da ya fara azurtar da kanshi kafin kuzo neman taimako wurinsa.
Ba'aganshi walak'ance cikin k'azanta da datti ba ".Inji Mama Sa'ima.
Mubarak yace "haka ne gaskiya Mama Allah ubangiji ya bamu ikon bin gaskiya da kuma
gyarawa,, wad'anda suka b'ace Allah ya daidaitasu akan hanyar gaskiya ".
Mama tace "Amin summa amin Mubarak ".
Suka cigaba da firarsu cike da tsananin jin dad'i da nishad'i sosai,, sunyi nisa cikin fira ne saiga
sallamar Alhaji Suleiman ya shigo cikin gidan. Suka amsa masa Mubarak ya gaidashi tare da yi
mishi sannu da zuwa,,, ya amsa mishi fuskarshi cikeda fara'a da murna sosai. Mama Sa'ima
itama tayi masa sannu da zuwa ya amsa mata,, ta amshi kayan da ke hannunsa suka shige
cikin parlourn d'akinsu.
Mubarak ya jima sosai yana tunani akan al'amarin rayuwa,, sannan daga baya shima ya shige
cikin d'akinsa. Ya shiga cikin toilet yayi wanka sannan ya sanya singlet da guntun wando domin
shan iska,, ya kunna vedio ya sanya American film ya fara kallonshi cikeda natsuwa da
kwanciyar hankali....
*Ku biyoni sannu domin jin ko wa cece Iya Gwamma,,, da kuma jin tushen labarin*.
_Share&Comments_
~Muje zuwa~
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 3*
**Yaya Mubarak yayi nisa sosai a cikin kallon American film d'in da yakeyi,, ko k'wakk'waran
motsi bayayi sosai saboda yadda ya mayar da hankalinshi kacokam a wurin kallon vedio. Da
gani babu tambaya kasan yanajin dad'in kallonshi,,, hankali kwance yake gudanar da komai
nashi..
Ab'angarensu Mama sa'ima kuwa suna shiga cikin d'akin,,, ta taya Alhaji cire kayan jikinsa.
Bayan ta gama cire masa kayan tas ta barshi da singlet da guntun wando,, sannan ta ja
hannunsa kamar yaro k'arami ta kaishi cikin toilet tareda had'a mishi ruwan wanka,, bayan ta
gama duk abinda ya kamata ta fito ta bar Alhaji domin yayi wankansa. Tana fitowa ta k'ara
gyare bedroom d'in tareda sa ma d'akin room freshner mai k'amshin dad'i matuk'a,,,, sannan ta
fitoma Alhaji jalabiya fara da zai saka a cikin gida tareda da feshe jalabiyar da perform mai
k'amshi,, sannan ta samu wuri ta zauna a cikin d'akin tana jiran fitowar uban 'ya'yanta..
Bayan minti goma sha biyar saiga Alhaji ya fito daga wanka,, yazo kusaga Mama Sa'ima. Tana
ganinshi tayi murmushi sannan ta d'auko lotion mai k'amshi ta fara shafa masasannu sannu
cikeda nuna matuk'ar kulawa ga mijinta. Babu abinda Alhaji yakeyi sai lumshe idanu ma'ana
yana jin dad'in yadda take bashi kulawa,, bayan ta kamalla shafa mishi mai neta d'auko
jalabiyarsa ta sa mishi,, tana gama sa mishi suka zauna a tare suna fuskantar junansu. Alhaji
Suleiman ya dubeta duba mai cikeda k'auna da son matarsa yace "Ummu Maryam Allah
ubangiji yayi miki albarka hak'ik'a ke mace ce ta gari mai biyayya ga mijinta,, ina alfahari da
kasancewarki matata uwar 'ya'yana,,,nasan nayi dace da farin cikin rayuwata mai sona kuma
mai son farin cikina,, da gudun b'acin raina banda tamkarki a cikin zuciyata ".
Alal hak'ik'a kalaman Alhaji Suleiman sunyi matuk'ar sanya Mama Sa'ima cikin tsananin nishad'i
da farin ciki sosai,,, sunbi jini da jijiyoyin jikinta suna shawagi a cikin zuciyarta. Ta dubi Alhaji
cikeda matuk'ar nishad'i sosai tace "Amin ya Alhajina kasani biyayya ya zama wajibi agareni
nayi maka muddin ina numfashi a doron k'asa,,, kaine silar farin cikina hasken idaniyata,,, idan
ban faranta maka ba waye zan farantawa aljannata tana k'ark'ashin tafin k'afarka fa mijina,,,
idan ka d'aga k'afa in shiga idan ka take shikenan! Taya zanyi sakaci har na tab'e Abban
Mubarak,, ina matuk'ar alfahari da kai Alhajina ".
Alhaji ya rik'o hannunta yana murmushin jin dad'i,, sannan yace "haka ne matata idan har miji
ke d'agama matarsa k'afa ta shiga aljanna,, to ni tawa k'afar a d'age take matata kuma insha
Allahu zaki shigeta ".
"Ina godiya Alhajina,, to ya kasuwar? ina fatar ana samun ciniki sosai ".Inji Mama Sa'ima..
Alhaji Suleiman yace "lafiya k'alau Alhmdlilah,, agaskiya ana samu ciniki sosai ".
Mama Sa'ima tace "masha Allah komai yayi k'yau matuk'a,,, dama haka ake son ji Allah ubangiji
ya k'ara taimakawa ya bada sa'a da nasara "..
Alhaji yace "Amin amin Ummu Maryam,, ina yaran nan suke ne Mubarak da Maryam d'in? ".
"hmm Mubarak yana d'akinsa Maryam kuma na barota ta gama cin abinci zata kwanta,,, kasan
yaran idan suna gida kodayaushe suna cikin d'aki shiyasa ba'a sanin suna nan ko basa nan
".Cewar Mama Sa'ima..
Alhaji yace "haka ne musamman Mubarak akwai shi da son zama cikin d'aki kamar mace,,,
shiyasa ma bai fiye son zaman shago ba,,, Maryam ko taso zaman d'aki ai ita mace ce gidan
wani zataje ".
Mama Sa'ima tace "ai zai saba da zaman shago saboda namiji dole ya fita ya nemo,, Maryam
kuma ai lamarinta sai addu'a saboda akwaita da rashin ji wallahi ".
Alhaji ya harareta da wasa cikin tsokana yace "a'aaa kada ki sanyama 'yata ido barta tayi rashin
jinta,,, ai komai yanada lokacinsa addu'a dai zamu dinga yi akan Allah ubangiji ya shirya mana
yaranmu "..
"kunfi kusa kodayake bakason a ce ga laifin Maryam,, addu'a takobin mumini ce Allah ya shirya
mana zuri'armu ".Inji Mama Sa'ima.
Alhaji yace "Amin yanzu dai naji magana ba'a dinga takurawa 'yata ba,, ana cewa tayi kaza
kaza ba "..
Mama tace "kaidai ka sani da dad'in bakinka ".
Yace "harda ke kinsan inada mana "..
Mama tace "nasan mi? ".
Alhaji yace "inada dad'in baki mana,, kuma har kin yaba ".
Mama tace "rashin aikin yi dai ".Tana murmushi sosai..
"da ni dake bamuda aiki yi ba ".Fad'ar Alhaji yana dariya sosai..
Mama kauda kanta tayi gefe guda,, tana ta dariya sosai mai cikeda matuk'ar farin ciki da
walwala,, Alhaji shi ma yana tayata dariya tareda da jifanta da kallon soyayya da k'auna...
*********************
***Agidansu Fatima kuwa suna isa cikin gidan sukayi sallama,, aka amsa musu suka samu
uwayensu zaune wuri d'aya suna fira cikin farin ciki da nishad'i. Su Fatima suka samu wuri
kusaga iyayensu saman tabarma suka zauna,, bayan sun zauna ne sukayi shiru basu ce komai
ba saboda sunsan sunyi laifi...
Iyayen nasu sai firarsu sukeyi kamar basu gansu ba,, can dai Fatima da yake batada hak'urin
yunwa ta bud'i baki da k'yar tace "Umma yunwa nakeji fa,, tun safe rabon dana koma saka wani
abu cikin bakina ".
Mahaifiyar Fatima mai suna Nusaiba ta banka mata wata uwar harara,, sannan ta bud'i baki
tace "to sabon salo inda kukaje ne baku ci abinci ba,, na aikeki yawon gantali da sakarci ne ?
Da zaki zo kina damuna yunwa kikeji yau naga bak'ar munafuka,,, salon ubanki yaji yace ina
miki horon yunwa ko,, Fatima Fatima! Ki fita daga cikin idona mai yawon sakarci da wawanci ".
Mama Nafisa mahaifiyar Fadila ta harari su Fadila,, tace "k'yaleta Nusaiba ai gara ita tayi
magana,, wannan mai taurin kunne _(ta nuna Fadila)_ ko magana batayi ba saboda tasan
batada gaskiya,,,gameda shegen yawon nan saina saka ki cikin turmi nayi miki dakan tankwan
d'an bashirwa! Munafuka 'yar iskar yarinya ".
"Ni banga dalilin yawon banza ba miye kuka nema kuka rasa ne? Saboda Allah salon ku jawo
ma kanku wani mugun abu! Ga mayyu a garin nan kamar tsaki,,, saboda haka zamu d'auki
mataki akanku tunda bakujin magana ".Inji Umma Nusaiba.
Mommy Nafisa tace "mataki ya wuce musa Fadil ya basu matsiyacin kashi idan suka koma,,
saboda naga sun raina Nabila basajin tsoronta kwata kwata,,,ni wlh idan rayuwata ta b'aci ina
iya yi muku mugun bugun walak'anci da halaka,, saboda naga lalama batayi muku musamman
ke Fadila mai kunne roba ".
Umma Nusaiba tace "ba wani Fadila aiko ba ita kad'ai zakiyima fad'a ba,,, ko Fatima ba baya ba
wurin rashin jin magana ba,,,mu samesu rana d'aya mu basu kashin k'warai ko zasuyi hankali
"..
Mommy Nafisa tace "naji amma ai tafita rashin jin magana,, amma nasan maganinsu ".
"babu wani ta fi ta duk d'aya suke ".Inji Ummu Nusaiba.
Fatima ce ta tattaro dauriya,, tareda marairaice fuskarta tace "Mommy,, Umma dan girman Allah
kuyi hak'uri Insha Allahu bazamu sake ba,, dama gidansu Hassana ne mukaje shiyasa muka
jima sosai bamu dawo ba ".
"munsan munyi kuskure ayi mana afuwa,,, bazamu k'ara aikata kwatankwacin haka ba ".Inji
Fadila..
Mommy Nafisa taja mugun tsoki mtssss! Saboda ita akwaita da saurin d'aukar zafi da wuri,, ta
juyar da kanta wani gefe domin kada suga fuskarta. Umma Nusaiba ce taja dogon numfashi
tace "komai ya wuce yarana ubangiji Allah ya k'ara shiryaku,, Nafisa baki ce komai ba ".
Mommy Nafisa tace "ai kin riga kin gama magana Nusaiba,,, nima na hak'ura Allah ubangiji yayi
musu albarka ".
Su Fadila sukace "amin mun gode sosai Iyayenmu ".Suka mik'e tsaye atare suka nufi cikin d'aki
domin suyi wanka suci abincin rana,, iyayen mata suka cigaba da firarsu cike da walwala da
annashuwa mara misaltuwa..
*ASALIN LABARI*
Maryam 'ya ce ga Alhaji Suleiman da Hajiya Sa'ima,, asalinsu 'yan nijar ne kasuwanci ne ya
kawosu Nigeria acikin garin Gumi Zamfara state. Suleiman da Sa'ima 'yan uwan juna ne domin
kuwa auren zumunci akayi,, sun taso ne tun suna yara suna matuk'ar k'aunar junansu fiye da
yadda kuke tunani. Sun taso gidan mutunci masu nagarta da son zumunci,,,a familynsu sun
kasance sunada had'in kai da kuma k'aunar juna babu gulma ko hassada da nuna k'yashi.
Komai nasu a had'e yake abin burgewa da sha'awa matuk'a,, idan ka shiga cikin gidan da yake
babban gida ne ba zaka iya gane wani banbamci ba,, saboda ba zaka iya gane wannan d'an wa
ne ba ko d'an wance ce ba saboda had'in kai da zumunta,,, hak'ik'a famili ne mai matuk'ar
k'aunar juna da yarda da 'yan uwa...
Sun had'a auren Suleiman da Sa'ima domin zumuncinsu ya k'ara k'arko,, masha Allah akayi
dace ko su yara ne masu biyayya da k'aunar juna. Sun bada had'in kai cikin tafiyar da rayuwar
aurensu cike da aminta da juna da zaman lafiya na hak'ik'a,, kowanensu yana k'ok'ari wurin
ganin ya farantama d'an uwansa tareda k'yautatawa juna domin samun farin ciki da annashuwa
mai d'orewa har abada ....
_Share &Comments_
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 4*
Domin samun farin ciki da annashuwa mai d'orewa har abada,,, zamansu zama ne na fahimtar
juna da amana,, tausayi da tsananin shak'uwa a tsakaninsu. Dukansu suna k'ok'ari wajen ganin
sun sauke hak'k'in dake bisa kansu na auratayya,, Suleiman ya kasance mutum ne mai sauk'in
kai da tausayin na k'asa dashi bayada rowa ko k'yashi ko kad'an. Yanada son bayarda k'yauta
da taimako gashi kuma mai tsananin biyayya da ladabi ga mahaifansa,, haka itama Sa'ima
mace ce wadda batada matsala a rayuwarta,, tanada kirki da k'yakk'yawan d'abi'u tanada son
mutane da yawan fara'a. Haka take kowa nata ne babu ruwanta da shiga sabgar daba ta
taba,,,, shiyasa lamarin aurensu yazo da sauk'i matuk'a saboda shi bayada matsala hakama
Sa'ima batada wata matsala..
Haka suka cigaba da gudanar da rayuwar aurensu cike da jin dad'i da farin ciki mara
misaltuwa,,, kowanensu yasan abinda ya dace ya kamata zaman lafiya ya wanzu a cikin gidan
aurensu. Babu abinda sukeyi sai sunyi shawara tare su kashe tare su binne tare babu mai jin
sirrinsu,, Alhaji Suleiman kasuwanci yakeyi tun anan nijar kafin harakar ta bunk'asa sosai .Itama
Sa'ima tana saisuwa su kayan miya cikin gida irinsu,, maggi star racco,, daddawa,, maggi ajino
motto,, gishiri,, kanwa,, sabulun wanka da wanki,, k'uli -k'uli,, tankwa da dai sauran kayayyakin
miya..
Sunyi wata biyu da yin aurensu saiga ciki ya bayyana a jikin Sa'ima,, sunje asibiti an auna wata
d'aya da satittikka zo kuga murna da farin ciki a fuskokin wad'annan bayin Allah. Bayan sunje
gida suka sanarda 'yan uwa da abokan arzik'i duk wanda suka fad'ama sai yayi murna da farin
ciki sosai,,, zo kuga farin ciki da nishad'i a cikin zuciyar iyayensu Alhaji Suleiman. Haka dai
Sa'ima ta cigaba da samun kulawa ta musamman ta b'angare biyu iyayenta dana mijinta,, duk
abinda take so shi akeyi mata na daga abubuwan ci da abinci mai gina garkuwar jiki,, haka
abubuwan ke tafiya cikeda matuk'ar kulawa da tarairaiyarta. Shima kanshi uban gayya wata
kulawa ya k'ara bata yana shagwab'ata da tarairaiyarta hundred percent,,, haka dai Sa'ima ta
cigaba da rainon cikinta da bashi kulawa fiye da tunanin mai karatu,,, kwanaki suka cigaba da
tafiya suna zama watanni..
Watanni takwas sukazo alokacin ne bayan sallar asuba,, ciwon nak'uda ya kama Sa'ima tun
tana nishi hmhmhmhm hmhmhmhm hmhmhmhm babu wanda yaji,, har tazo ta fara kiran sunan
mahaifiyar Suleiman. Inna ta shek'o da gudu ta taimaka mata tana mata addu'a harta santalo
santalelen d'anta,, k'yakk'yawa son kowa k'in wanda ya rasa. Bayan Innar Suleiman ta gyarata
ta kuma gyara ko'ina sai k'amshi yake tashi ,, can ta shiga cikin gida ta sanarwa kowa da kowa.
Zo kuga yadda ake tururuwa zuwa ganin sabon jariri sabon jini,, haka dai mutanen unguwa
suka cigaba da zuwa ganin jariri tareda yi mata barka da haihuwa,,, haka dai suka cigaba da
zuwa dubiyar Sa'ima...
Sati yana zagayowa ranar suna yaro yaci suna Mubarak,, hak'ik'a 'yan uwa da abokan arzik'i
sunyi matuk'ar k'ok'ari wurin ganin sun fitar da Sa'ima kunya,, anyi mata abin arzik'i k'warai da
wadata raguna biyu manya -manya aka yanka da tinkiya d'aya. Haka dai akayi bikin cikin rufin
asiri da wadatar zuci,, bayan maraice tayi kowa ya kama gabansa ya wuce zuwa gida..
*********************
Bayan shekaru biyar da haihuwar Mubarak,, Alhaji Suleiman ya kwaso iyalinsa daga mahaifarsa
nijar ya dawo Nigeria zamfara state cikin garin Gumi. Ya cigaba da kasuwancinsa cikeda
kwanciyar hankali,, itama matarsa ya bata jari domin ta cigaba da sana'arta da takeyi acan
nijar..
Garin Gumi gari ne mai tarihi da d'umbin albarka,, sunayin kasuwanci da kiwo amma ba sosai
ba babbar sana'arsu shine noman k'warya. Itace sana'ar da mafi akasari da 'yan garin keyi da
kiwo amma ba sosai ba,, garin ba za'a kirashi k'auye sosai ba kuma ba za'a kirashi birni ba
yana dai tsaka tsakiya. Mutanen garin mutane ne masu addini da tsoron Allah,, komai nasu zad
sha'awa suke gudanar dashi...
**Anan garin ne Mama Sa'ima ta haifi Maryam atsakaninsu da Mubarak akwai tazarar shekaru
shida,,, zo kuga murna alokacin da Mubarak yaga ya samu k'anwa fara tass k'yakk'yawar gaske
ta bugawa a mujalla,,, hak'ik'a Allah yayi halitta a nan domin kuwa kallo d'aya zakayima jaririya
ka gano sai anyi k'yakk'yawar mace abar kwatance da kallo cikin mutane. Haka dai Mama
Sa'ima ta cigaba da rainon Maryam itada Mubarak,, shima Alhaji Suleiman Allah ya d'ora masa
tsananin k'aunar iyalinsa wato yaranshi,, komai yi musu yakeyi gwargwadon iyawarsa domin
samun farin cikinsu da walwalarsu....
Fatima 'ya ce ga Malam Nura da Nusaiba,, kuma yaya ne ga Nazifi mahaifin Fadila da
mahaifiyarta Nafisa. Nura da Nazifi sun kasance 'yan uwan juna uwarsu d'aya ubansu d'aya,,,
sun kasance 'yan asalin jahar kebbi amma sun dad'e cikin garin Gumi sosai tun kafin su fara
tara iyali sosai,,, babbar sana'ar da suka dogara da ita shine noman k'warya da ita suke ci suna
rufama junansu asiri. Ahaka suke d'aukar nauyin iyalinsu cikeda zafin nema da wadatar zuci,,,
shiyasa ake son mutum mai zuciyar neman na kanshi domin kada mutum ya dogara ga wani.
Zuri'arsu zuri'a ce mai had'in kai da zumunta,, tareda da matuk'ar kulawa da kuma soyayya da
juna. Kan mazan a had'e yake babu wani munafurci ko gulma,,, hakama matansu sunada had'in
kai matuk'a d'aya batayin abu saida shawarwarin junansu. Duk abinda suka yanke shawara shi
sukeyi tare shiyasa ko yaransu Fatima,, Fadila,, Nabila da Fadil kansu yake