Showing 21001 words to 24000 words out of 58121 words
cikinsa harda saka sabon
panting,,, yayi mata kayan lefe kala shida,, takalmi biyu,, hijabi biyu,, sark'a biyu da dai
sauransu duk abinda kukasan ake sakawa a cikin lefe ya sanya mata bibbiyu,,, sannan ya aje a
cikin d'akin dazai sakata Malam Mamman ya d'auki turmi biyu na daban yaba Inna Talatu ,,, tak'i
amsa masa tareda wurga masa kayansa a saman fuska cikeda matuk'ar son tashin hankali!
Tace "amshi tsiyarka Mamman! Saboda niba matsiyace ba inada suturata,,, kuma ba gidan
matsiyata ka d'aukoni ba da suturata kaje ka aureni alokacin kuma kana fak'irinka! ".
Malam Mamman yace "sannu mai arzik'i har abada Talatu ba zaki tab'a yin hankali ba da
karatun ta natsu ba,,, kibi duniya a sannu domin zata koya miki hankali wata rana kuma nasan
zakiyi nadama anan gaba alokacin da nadamar da batada amfani,,, aure dai babu fashi sai nayi
duk abinda zakiyi kiyi mahaukaciya! ".
Inna Talatu tace "hmmm kaidai akeji Mamman wannan maganartaka baya tayar mini da
hankali,, aurenka auren banza bai shafeni ba kana bari dai har a d'aura auren tukun kafin ka
cikani da kurin banza ".
"aure ne kamar anyi an d'aura kina ji kina gani,, babu abinda zaki iya yi na maji dad'i sosai da
kika k'i amsa saina k'ara ma Lawiza amaryarta matata farin cikin rayuwata ".Cewar Malam
Mamman cikeda lalama..
Inna Talatu taja mugun tsoki mtsssss sannan tace "kodai bak'in cikin rayuwarka ce babu abinda
ya dameni,,, da ran mai toka da mutuwarsa duk d'aya ne ga hankaka! Saboda haka kaga
tafiyata inada aikin yi ".Inna Talatu tayi shigewarta cikin d'akinta batare data tsaya sakejin
abinda zai fito daga cikin bakinsa.
"gara da kikayi wucewarki cikin d'akinki,, jahila wanda batasan muhimmancin miji ba da
darajarsa ko kad'an ba ".Inji Mal. Mamman..
Allah ubangiji yaba mata mazaje nagari,, mazan kuma yabasu mataye nagari masu tsoron Allah
da iya d'aukar dukkan lalurorinmu..
Ana saura kwana biyu a d'aura auren Lawiza da Malam Mamman,,, sai Lawiza ta tashi da wani
mugun ciwon ciki sosai kuka kawai takeyi da murje murjen ciwo,, babu abinda takeyi sai danna
cikinta tana kukan ciwo da nadamar rayuwa.
Lawiza ta kamayin shure shure da k'afarta sai birgima takeyi,, idanunta har wani k'ak'k'afewa
da juyewa sukeyi akan rad'ad'i da zafin ciwo can naga ta fasa ihu da wani gigitaccen k'ara tayi
kuwwa da k'arfi! Wani irin jini ne ke fita a cikin bakinta da hancinta gunduwa -gunduwa.
Innar Lawiza ce ta shek'o da gudu da saurinta,, tana shigowa cikin d'akin gabanta ya fad'i
rasssss! Da taga abinda d'iyarta ke fissuwa hmmmm,,
tace "Lawiza mi ya sameki? Ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!.....
_Share&Comments_
[6/25, 6:20 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 13*
Innar Lawiza tace" Lawiza mi ya sameki ?Ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Na shiga uku na
lalace ".Cikin kid'emewa da matuk'ar tashin hankali,, tana kuka mai cikeda bak'in ciki da k'uncin
rayuwa..
Dak'yar Lawiza ta bud'i baki tace cikin matuk'ar zafi da rad'ad'in ciwo,, idanunta suna rufewa
suna bud'ewa "kuyafemin Innata hak'ik'a nasan bayan mutuwata zaku kasance cikin bak'in ciki
da k'uncin rayuwa,,, kuyi hak'uri wannan itace k'addarata kuma haka Allah yaso sannan na baki
amanar Audu ki kulamin dashi ko bayan raina,,, ina son kisan cewa ashe matar Malam
Mamman Talatu k'usurgumar mayya ce itace sanadin ciwona saboda haka ku kiyaye kanku
Inn..... ".Ai bata k'arasa maganar ba idanunta suka k'ak'k'afe nan ta rasu ga jini duk ya b'ata
jikinta,,, Innar Lawiza ta fasa gigitacciyar k'ara tayi kuwwa da k'arfi! Ta fashe da kukan tausayin
kansu tana jijjigar gawar Lawiza tana cewa "dan Allah Lawiza ki tashi karki tafi ki barmu! Wallahi
na yafe miki duniya da lahira,,,,babanki nasan shima zai yafe miki yau naga ta kaina wannan wa
ce irin k'addara ce,, wannan wa ne irin rashin imani ne? 'yar tawa guda da nake kallo inyi farin
ciki an kashemin ita,, Allah ya isa Talatu Allah ya isa Talatu!Bamu yafe miki ba duniya da lahira
sai kinyi mummunan k'arshe a rayuwarki! Baban Lawiza baban Lawiza ".Ta sake fashewa da
wani rikitaccen kuka tana ihu tana ifface iffacen kamar mahaukaciya sabon kamu,,, baban
Lawiza da yanzu ya shigo cikin gidan ya shek'o da gudunsa,,, domin yaji kuka da kuwwa yana
shiga cikin d'akin yaga Lawiza kwance cikin jini bata motsi,,, hankalinsa yayi matuk'ar tashi
sosai gabansa sai fad'uwa yakeyi dummmmm! Yana ganin yadda duk Innar Lawiza ta yatsume
da gigicewa yasan kila mai faruwa ta faru,,, yazo kusaga gawar Lawiza yana kallonta na wani
lokaci can ya d'aga hannun Lawiza yana saki hannun ya fad'i alamar babu rai kenan,,, yasa
hannunsa ya shafe mata idanu tareda furta "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un Allahumma ajirni fi
musibati wa'akhalufni khari minha! Allah ubangiji ya jik'anki Lawiza da rahama ".
Yasa hannunsa ya jawota a jikinsa ya rungume Innar Lawiza yana lallashinta,,,, yana shafar
mata baya alamar lallashi cikeda matuk'ar tausayin kansu,, sannan ya dubeta cikin raunin
zuciya yace "kiyi hak'uri Innar Lawiza ubangijin da ya bamu Lawiza ya amshi abarsa,,, saboda
haka muyi hak'uri Allah ubangiji ya jik'anta da rahama yasa ta huta ".
Innar Lawiza ta d'ago rinannu idanunta da suka rikid'e sukayi ja,,, ta saki wani sabon kuka tace
"ya zamuyi baban Lawiza,,,shikenan ta tafi ta barmu ba zata dawo ba,,, shikenan bazan sake
ganinta ba har abada,,, shikenan Audu ya zama bayada uwa,,, wannan wa ce irin rayuwa ce
mai cikeda bak'in ciki da k'uncin rayuwa? ".
"kiyi hak'uri domin Allah mad'aukakin sarki da ya bamu Lawiza a matsayin d'iya yafimu sonta,,
kuma komai na duniya sai mutum yayi hak'uri mutuwa dole ce dukkan mai rai saiya d'and'ani
zafin mutuwa,,, to ya zamuyi idan ba hak'uri ba muma lokaci ne kawai muke jira Allah ubangiji
yasa muyi k'yakk'yawan k'arshe,,, bari inje in sanarda mutane abinda yake faruwa ".Cewar
baban Lawiza cikeda sanyin jiki da tsananin damuwa.
Ita dai Innar Lawiza babu abinda takeyi sai kukan bak'in ciki da mutuwar Lawiza,,, fuskarta tayi
jawur majina da hawaye sun b'ata mata fuska yab'e yab'e zad tausayi,, baban Lawiza ya fita
daga cikin gidan saboda ya sanar da mutane da 'yan uwa..
*********************
***Agidan Malam Mamman kuwa shi ne ya shiga cikin d'akin dazai saka Lawiza ya share
tasss,,,,sannan ya gyara ko'ina cikin d'akin ya k'ulle d'akin ya fito ya zauna.
Yana zaune ne ya kira Gwamma ya aiketa domin ta siyo masa fura da nono,,,,tazo ya bata d'ari
biyar ta siyo masa furar d'ari nonon d'ari,, ta amsa mashi ta wuce domin ta siyo masa furar.
Bayan wucewar Gwamma ne Inna Talatu ta fito daga cikin d'akinta itada Lawwali,,, ta dubi
Malam Mamman tana wani yi masa rikitaccen murmushi cikin zuciyarta wani nishad'i ne da farin
ciki ke wanzuwa a cikin zuciyarta,,, saboda tasan ta riga ta kashe Lawiza har abada! Sai dai
Mamman ya nemi wata matar badai Lawiza ba kuma muddin tana raye babushi babu k'ara
aure,,, sannan tayi masa walak'antaccen kallo tace "Mamman angon Lawiza saura kwana biyu
ka angwance ko? Ya kamata ka k'ara kawo kayayyakin miya wad'annan da ka kawo baya isa fa
".
Malam Mamman yace "hmmm lallai duniya akwai makirar mace,,, har kin sauko Talatu ko kuwa
wani sabon salon munafurci ne kika b'ullo min dashi? ".
Inna Talatu ta banka mishi uwar harara tace "ban gane ba Mamman daga magana sai kace
wani sabon salon munafurci na b'ullo dashi,,, ada fa aurenka ya dameni ayanzu ko matan duka
garin nan zaka aure babu abinda ya dameni,, saboda haka kaje kayita harakarka ".
"aiko bakice babu ruwanki ba bashi zai hana in fasa abinda nayi niya ba,, saboda haka naji zan
k'aro kayan miyan ko banason abin tashin hankali kada ki b'atamin ranar farin cikina ".Fad'ar
Malam Mamman fuskarsa tana bayyanar da farin ciki sosai..
Inna Talatu tace "kaidai akeji anyima akuya wanka wannan kuma ba damuwata bace ".
Malam Mamman yace "ai naga alama Talatu kishiyar Lawiza,,, Lawiza amarya a gidan Malam
Mamman kwana biyu kawai ya rage in zama ango,, mijin Talatu da Lawiza ".
Da yake Inna Talatu tasan abinda ta aikatawa Lawiza,, ta kasheta har abada bazai ganta ba
tace "tabbas haka ne mijin mace biyu Talatu da Lawiza takawarka lafiya ango mijin amarya
gaba haske baya k'amshi ".
Malam Mamman har cikin zuciyarsa yayi matuk'ar mamakin yadda Inna Talatu bata wani nuna
damuwa ba ko tashin hankali ba,,, a fuskarta wani annuri ne ke bayyana a cikin fuskar Talatu
babu abinda takeyi sai murmushi da dariya sosai..
Malam Mamman yayi murmushi yace "tabbas haka ne gaskiya zan baki goron kirarin da
kikayimin nida amarya ".Yana rufe bakinsa saiga sallamar wani yaro tareda Gwamma domin
kunsan ita batayin sallama,,, suna shigowa Mlam. Mamman ya amsa masa suka iso kusaga
Malam Mamman,,,, Gwamma ta bashi sak'on ya amsa tayi tafiyarta wurin mahaifiyarta,,,,
sannan yaro ya dubi Mal. Mamman yace "ana kiransa can gidansu Lawiza ".
Malam Mamman yace "lafiya dai mi yake faruwa ne yaro? "..
"lafiya k'alau baban Lawiza ke nemanka ".Cewar Yaron..
Malam Mamman yace "to yaro ".Sannan ya tashi tsaye ya bud'e d'akin daya gyara domin
amaryarsa,,, ya aje furarsa da nonon aciki ya jawo d'akin ya kulle d'akin sannan ya juyo ya
dubesa yace "muje zuwa ko to Talatu na fita zuwa can gidansu Lawiza ".
"lafiya dai Mamman mike faruwa? ".Cewar Inna Talatu MAYYA..
Malam Mamman yace "nima ban sani ba Talatu zanje can injiyo ko mike faruwa ".
Inna Talatu tace "saika dawo Mamman Allah yasa muji alkhairin Allah ".(Kamar da gaske har
cikin zuciyarta alhali kuwa ran nan nata da zuciyarta fari fas akan murna da farin ciki sosai,,,
saboda tasan mugun labari na mutuwar Lawiza za'a sanardashi).
Yace "Amin ya rabbi ".Suka sa kai sukayi wucewarsu ayayinda gaban Malam Mamman sai
bugawa yakeyi da k'arfi! Rassssss,,, yaji duk jikinsa yayi matuk'ar sanyi wani k'ololon bak'in ciki
ya tokare masa zuciya,,, shi kansa jikinsa ya bashi akwai mummunan al'amarin da yake
faruwa...
Yana wucewa ne Inna Talatu ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai! Sannan tace
"Hhhhhhhhhhh haukar banza da yofi ni za'a kawowa iskanci da rainin wayo! Harda cemin shine
mijin Talatu da Lawiza _(ta karkace baki tana kwaikwayon maganarsa cikeda matuk'ar raini)_ to
yanzu zaka samu mummunan labarin da zai gigita rayuwarka da tunaninka,,, nasan saika kusa
haukacewa da d'imaucewa kuma wlh ko ya nemi wata mata itama kasheta zanyi,,,saboda ni
bazan tab'a zaunawa da kishiya ba niba wawuyar mace bace kamar sauran mata,,, ko waye
yace zaija dani rabonsa wahala!".
Lawwali da Gwamma wasarsu kawai sukeyi,,, suna kuwwace-kuwwace suna dariya sosai..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
¤¤¤Koda su Malam Mamman suka isa gidansu Lawiza har anyima gawar Lawiza wanka da
sallah,,,,suna isa aka fito da gawar Lawiza za'a kaita makwancinta .
Suna zuwa Malam Mamman yaji gabansa ya k'ara bugawa da k'arfi dummmmm!Ya dubi baban
Lawiza yace masa "Sani wa ye ya rasu? Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un ".Gabansa yana fad'uwa
da sauri da sauri zuciyarsa tana bugawa!.
Sani yace "saidai muyi hak'uri Allah ya amshi ran Lawiza ayau da rana Malam Mamman ".
Gaban Mamman ya bada dummmmm zuciyarsa ta girgiza hankalinsa yayi k'ololuwar tashi
sosai! Har wani duhu duhu ya fara gani akan tashin hankali da rikicewa,,, ai kuwa nan da nan
ya fad'i k'asa ya some mutanen dake wurin suka saka salati atare! Mutane hud'u suka kamashi
suka shigardashi cikin gidan Malam Sani mahaifin Lawiza.
Sauran mutanen dake rik'e da gawar Lawiza cikin makara suka wuce da gawarta zuwa gidanta
na gaskiya..
*Allahu Akbar! Duniya kenan wata rana za'a wayi gari duk babu mu a cikinta...*
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
***Suna dawowa daga wurin kai Lawiza gidanta na gaskiya mutane suka taru suna zaman
makoki,,, 'yan uwan Sani dana matarsa suke karb'ar gaisuwa kowa ka gani ya zauna jugum yayi
shiru yana jimami da damuwa.
Acan cikin gidan Mal. Sani kuma bayan an watsawa Malam Mamman ruwa ya farfad'o daga
suman da yayi,, cikin mutuwar jiki da damuwa Malam Sani yace "kayi hak'uri Mamman Allah ya
k'addara Lawiza ba matarka bace tun farko,,, sannan ubangijin da ya bamu Lawiza ya amshi
abarsa alokacin da yaso ya kuma gadama saidai muyi hak'uri mu bita da addu'a,,, shi kad'ai
take buk'ata ".
Innar Lawiza tace "tabbas haka ne gaskiya babu yadda zamuyi haka Allah ya k'addara,,,
lokacinta ne yayi kuma bawa bai isa ya gujewa mutuwa ba,,, saboda haka hak'uri zamuyi muma
ba zamu wuce lokacinmu ba ".
Malam Mamman ya juyo ya kallesu idanunsa sunyi jawur,,, jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u
sannan yace "haka ne Sani nagode sosai da kulawarku akaina,, Allah ubangiji ya jik'anta yasa
ta huta mu kuma idn tamu tazo yasa mu cika da imani ".
Suka ce "Amin ".Atare da juna.
Malam Mamman ya tashi tsaye yana musu kallon tausayi da jimami sosai,, yace musu shi zai
wuce gida,, Malam Sani ya tashi domin yayi masa rakiya zuwa waje tare da bashi hak'uri da
maganganu masu sanyi,,, shidai Mamman jijjiga kansa kawai yakeyi yana saurarensa.......
_Share&Comments_
[6/25, 7:51 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 14*
Shidai Malam Mamman jijjiga kansa kawai yakeyi yana saurarensa cikeda matuk'ar sanyin jiki,,,
can dai bayan Malam Sani ya gama yi masa nasiha mai ratsa jiki,,,, bayan ya gama ne sukayi
sallama da juna cikeda rashin jin dad'i da jimamin mutuwar Lawiza....
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Malam Mamman ya shigo cikin gidan da sallama cikin sanyin jiki,,, Inna Talatu tana cikin
d'akinta amma tanajin muryar Malam Mamman ne ta fito da saurinta tana kallonsa..
Malam Mamman ya zauna ak'ofar d'akinsa yayi tagumi cikeda sanyin jiki,,, yanayinsa ya nuna
yana cikin damuwa da bak'in ciki Inna Talatu ta matso kusa gareshi cikin munafurci da
k'ulle-k'ullen makirci,,, ta canza yanayin fuskarta daga farin ciki xuwa zullumi kamar ta damu da
damuwarsa,,, tagumi yayi yayi shiru kamar ba Malam Mamman ba sarkin kiza-kiza,,, Inna Talatu
tasa hannunta ta jaye hannun Malam Mamman domin son taji gulma kuma ta tabbatar ta kashe
Lawiza ko kuwa da sauran aiki agabanta,, kunsan mace duk munin halinta ta iya munafurci da
makirci idan tanason taji tsegumi ko gulma.
Ta dubi Malam Mamman zuciyar nan tata fara fass amma afuskarta kamar tana tausayinsa,,,
tace "haba Mamman ka daina tagumi babu k'yawo,,,, sannan naga yanayin fuskarka ya canza
mi yake damunka,,, mi yake faruwa? ".
Malam Mamman ya d'ago idanunsa wad'anda suka fara canzawa daga launin fari zuwa ja,,,, ya
bud'i baki muryarsa tana rawa yace "Talatu dole in shiga cikin bak'in ciki da k'uncin rayuwa
saboda mummunan k'addarar da ta sameni,,, ya zanyi da rayuwata,,, wannan wa ce irin
k'addara ce mai cikeda bak'in ciki da takaici? ".
"ban gane ba Mamman abinda yake faruwa,,, ya kamata ka sanardani mi ke faruwa? Kayimin
bayani dallah dallah yadda zan gane bawai kazo kayi tagumi ba ".Inji Talatu MAYYA cikeda
matuk'ar makirci da munafurcinta..
Malam Mamman ya daure yace "Talatu Allah yayima Lawiza rasuwa a yau da rana,,,, kiran da
kikaga akayimin d'azu alokacin ne koda na isa za'a kaita makwancinta na gaskiya,,,, ina cikin
matuk'ar damuwa Talatu ina son Lawiza domin ta nunamin k'auna amma ubangijin da ya fimu
sonta ya karb'i abarsa,,, ya zanyi ne yanzu? ".
Hak'ik'a maganar Malam Mamman ta k'ona ran Inna Talatu,,, amma da yake ta iya kissa da
kisisina da munafurci bata nuna masa ba,,, kuma tasan burinta ya cika saboda ta k'ara
tabbatarwa Lawiza ta mutu tabar duniya har abada!.
Ta dubeshi cikin munafurci tace "Ayyah Allah sarki duniya kenan! Allah ubangiji ya jik'anta da
rahama yasa ta huta mu kuma yasa muyi k'yakk'yawan k'arshe,,,, amma agaskiya Mamman
banji dad'in faruwar wannan mummunan al'amarin ba,,, amma ya muka iya lokacinta ne yayi,,,,
kayi hak'uri Mamman Allah yana tareda masu hak'uri sannan zaka samu wata matar ka