Showing 30001 words to 33000 words out of 58121 words

Chapter 11 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

Advertisement

12 Jul 2025

3003

abu ko da yayi masa rauni sosai agaskiya koma miye bayada imani ko
kad'an,, Allah ubangiji dai yasa shi farfad'o daga suman da yayi ".Inji baba Labaran,, Ummaru
yace "amin baba ai komai yayi zafi maganinsa Allah,,, Allah ubangiji ya bashi lafiya ".Baba
Labaran yace "amin yanzu abinda za'a yi shine mu kamashi mu ida shigardashi cikin gida,,
kada mutane su fara taruwa suna yad'a maganganun gulma da jita jita ".Ummaru yace "to baba
maganarka haka take mutane lamarinsu sai Allah "."ai shine saboda kasan mutanen garin nan
akwai shegen munafurci da gulma ce gulma ce ".Cewar baba Labaran.
Ummaru ya kama hannuwa baba Labaran ya kama k'afafuwansa,,, suka ciccib'esa dak'yar suka
shigardashi cikin gida suna nishi mai d'aukeda wahala,, suna shigowa baba Labaran ya kira

Innar Ummaru da sauri ta fito daga cikin d'akinta,,, ya umurceta ta kawo tabarma a shimfid'a ma
Sala mafarauci akwantar dashi,, jikinta yana rawa zuciyarta tana fad'uwa rasss saboda ganin
halin da mijinta yake ciki na ciwo sosai,,, yasa tayi sauri ta d'auko tabarma da filo aka kwantar
da Sala mafarauci samanta,, sannan aka aza kansa saman filo. Inna Ummaru mai suna Yashe ta bud'i baki dak'yar cikin rashin kwanciyar hankali tace "yaya
Labaran mi ya sami Sala,, a ina kuka tsintoshi? ".Baba Labaran ya dubeta duba na fahimta
yace "kwantar da hankalinki Yashe anan muka tsinceshi bakin k'ofar gidan nan,, kwance a k'asa
cikin ciwo ".Ummaru ya dubi mahaifiyarsa ganin irin tashin hankalin da ya bayyana a fuskarta,,
dole yasa ya tausasa halshensa yace "eh ba wani babban abu bane Inna,,, rauni ne kawai
yakeda ajikinsa kuma Insha Allahu zai warke ".Inna Yashe tace "Allah ya bashi lafiya ".Baba
Labaran yace "amin Ummaru tashi ka shigar masa da jikkarsa cikin d'akin,, sannan kafin ka
shigarda da ita fito da namun daji daya kamo saboda kada su lalace a banza,, wanda ya
kamata asaisuwa sai asaisuwa wanda ya dace aci sai a ci".Inna Yashe tace "haka ne gaskiya
".To baba ".Cewar Ummaru alokacin ne ya mik'e tsaye yana fito da duk naman da Sala
mafarauci ya kamo,, bayan ya gama fissuwa hmmmm yaji akwai abinda ya rage mai nauyi
dunk'ulalle kamar k'wallo,, yana tab'awa yaji kamar kan wata dabba haka ne yasa ya fitar dakan
Inna Talatu batare da yasan ko miye ba,,, yana fitarwa dukkansu idanunsu ya sauka ga kan
Inna Talatu MAYYA,, ai saida suka zabura da k'arfi! Hankalinsu ya d'unguma sosai ita Inna
Yashe fitsari ta saki a tsaye tareda rik'e bangon d'akinta ��,,,su baba Labaran kuwa jikinsu
sai rawa yakeyi da makarkatar tsoro,,, saboda shi yasan har abada bazai tab'a mantawa da
Inna Talatu MAYYA ba domin jikinsa da zuciyarsa sun bashi itace sanadiyyar mutuwar Lado da
sauran mutanen da ake kashewa! Ummaru ne yayi saurin mayarda kan Inna Talatu acikin jikka
sannan yasa acikin d'akin Babansa ya kullesa aciki.
Sannan Ummaru ya dubesu yace "ina ganin kamar wannan abin bana damuwa bane,,, karku
damu idan baba ya farfad'o zai sanardamu duk abinda ake ciki ko mike faruwa ".Baba Labaran
ya dubesu yace "wannan abin haka yake amma akwai ban mamaki da al'ajabi acikinsa ".Inna
Yashe dake wuru wuru da idanu alamar tsoro tace "muyi dai hak'uri har lokacin da Sala ya
farfad'o zamuji duk abinda mukeson ji ".








"tabbas haka ne amma indai shi ya kashe Talatu MAYYA da kansa dole ne yaji jiki sosai,,, kuma
Sala ya cika babban jarumi ".Inji baba Labaran.

Ummaru yace "babu shakka baba ne ya kashe Talatu mayya,,, shikenan mun rabuda azzaluma
macuciya mai cin naman mutane ".









Inna Yashe tace "haka ne gaskiya maganarka Ummaru ".






Baba Labaran ne ya umurci Ummaru daya d'ebo ruwa a cikin randa masu sanyi,,, Ummaru yaje
ya d'ebo ruwan ya kawo masa,,, yana kawon ruwan baba Labaran yayi doguwar addu'a acikin
ruwan sannan ya watsawa Sala mafarauci ruwan ajikinsa.











Bayan jimawa kad'an sai naga Sala mafarauci yaja numfashi mai tsawo ya farfad'o daga suman
da yayi,,, farin ciki da murna ya bayyana a zuk'atansu,,, shima kallonsu kawai yakeyi ya kasa
magana akan rad'ad'i da zafin ciwo..

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤







**Tsuntsuwar da Gwamma ta zama ta kama falfala gudu bata sauka a ko'ina ba sai cikin
k'usurgumin dajin da aka kashe Inna Talatu,,, tana sauka ak'asa cikin dajin ta girgiza sannan ta
rikid'a ta koma Gwamma,,, tana shiga cikin dajin lungu da sak'o gabas da yamma kudu da
arewa tana neman Talatu MAYYA. Ta jima sosai tana nemanta harta galabaita akan yawo cikin
dajin gashi hankalinta duk ya k'ara tashi,,, jikinta yayi matuk'ar sanyi da fargaba akan neman
mahaifiyarta,, saida ta sake dawowa baya sannan taci karo da gawa kwance ak'asa duk naman
jikinta tsutsotsi ne da tsuntsaye da namun daji sun yakuce naman,,, sunyi guntu guntu dashi
wani mugun wari da d'oyi kawai ke fita daga cikin naman Inna Talatu.
Gwamma bata gane Innarta bace Talatu ba saida ta tsaya tana nazari da kallon gawar da
k'yau,,, cikin natsuwa da yawan kallon gawar can taga guntun zanen Inna Talatu ak'asa
yasshe,, ta duk'a har k'asa ta d'auko guntun zanen Inna Talatu sannan ta d'ebi jinin da yake ga
naman tana karanta wasu d'alamisai na tsafi da sihiri ,,,,tana tayin wasu surutai marasa dad'in
saurare da ji,,, ta jima tanayi saiga rugugin tsawa da hayak'i sun bayyana dajin gaba d'aya ya
kama girgiza da tsawace tsawace mai muni! Jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye zago zago,,,
idanunta sunyi jawur kamar barkono can dai duk abinda ya faru a tsakanin Inna Talatu MAYYA
da Sala mafarauci ya bayyana tana ganin komai,,, daga farkon fad'ansu har K'arshensa inda ya
kashe mata mahaifiya..









Tana ganin abinda ya samu mahaifiyarta ta fasa gigitacciyar k'ara da kuwwa! Dajin gaba d'aya
ya amsa kuwwarta wani irin mahaukacin kuka ne takeyi mai cikeda tashin hankali da bak'in cikin
rayuwa,,, jikinta gaba d'aya bak'in hayak'i ne ke fita bakinta da kunnenta kumfa suke fitowa
saboda b'acin rai k'arara dake cikin fuskarta,,, kammaninta gaba d'aya ta rikid'e zuwa babbar
dodanniya! Ta bud'i baki dak'yar tace "na rantse da rayuwar mahaifiyata na rantse da boka
LOK'ORO,, kuma na rantse da gadon maita da tsafi! Sala mafarauci kajama kanka masifa da
bala'i,,, kajama kanka mutuwa wlh saina kasheka na kashe duk zuri'arka!Saina d'auki fansar
jinin mahaifiyata duk mutane garin Gumi kaja musu bala'i da tashin hankali !Saina kashe duka

mutanen gari baki d'aya ".








Haka dai ta kama kururuwa da kuwwa mai cikeda tashin hankali da k'uncin rayuwa! Sannan
daga baya ta dawo tsuntsuwa ta tashi sama cikin sararin samaniya tana masifar gudu harna
tashin hankali,,,,, ta kamayin masifaffen gudu mai cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa!.







**********************






**Ab'angaren Lawwali bayan ya gudu ya koma gidan baba Labbo da kuma matarsa Inna Tani,,,
bayan ya koma gidan baba Labbo ya had'ashi da d'iyansa Ila da Sagiru yana koya musu aikin
noma da kasuwanci,,, komai na gidan cikin kwanciyar hankali da natsuwa suke yinsa basu
nunawa Lawwali banbanci ko kad'an,, hankalin Lawwali ya kwanta sosai har haske da k'iba ya
k'ara yi,,, duk abinda suke buk'ata shi sukeci iyaka gwargwado suna cin mai k'yau susha mai
k'yau cikin rufin asiri da wadatar zuci ,,,komai tare sukeyi shida su Sagiru suna tsananin k'aunar
Lawwali da tausaya masa saboda irin muguwar uwa da Allah ya bashi mara tsoron Allah da
mugunta iri iri daban daban.








**Wata rana ne Inna Tani tana zaune da baba Labbo suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da

fahimta sosai ,,,,Inna Tani ce ta dubi baba Labbo tace "agaskiya maigida ina matuk'ar
tausayawa rayuwar Lawwali,, yanada halayyar k'warai da sanyin zuciya sannan gashi Allah ya
had'asu da muguwar uwa MAYYA ".








"hmm Allah ya dai karemu daga shairin mugayen mutane,, amma lamarin Talatu kam sai a
hankali duk ta rikita mutanen gari sai kashesu takeyi,, harda d'an uwana mijinta ta kashe
saboda kada yayi mata kishiya! ".Inji baba Labbo cikeda matuk'ar bak'in ciki da jimamin
mutuwar Malam Mamman.







Inna Tani ta nisa sannan tace "ai ganin akan irin abubuwan da Inna Talatu keyi ne yasa
Lawwali ya gudu ya barta itada Gwamma su kad'ai aciki gida,,, Talatu kam tayi nisa bata jin kira
saidai kayi hak'uri na kashe yaya Mamman da tayi,,, amma agaskiya ba zata tab'a k'arshe mai
k'yau ba saitayi mutuwar walak'anci da tozarci! ".......














_Share&Comments_

*ku cigaba da bina fans*
[6/28, 4:35 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 18*

Malam Labbo ya dubi Inna Tani yace mata "idan banyi hak'uri ba mi zanyi mata Tani,, ni kaina
idan nayi mata wata maganar banza tana iya kasheni a banza da yofi! Ni wallahi tsoronta nakeji
kamar ciwon ajali,,, saboda nasan wadda rashin imani da rashin tausayi yasa ta kashe mijinta
akan *KISHIN JAHILCI* da hauka,,, to babu shakka uban kowa tana iya kashewa batare da
wani fargaba ko tsoro ba,,, domin mayyu da kike ganinsu basuda d'igon imani da tausayi ko
kad'an a cikin zuciyarsu ".






Inna Tani ta bushe da dariya sosai sannan tace "ashe dai maigida kana tsoron mutuwa wallahi!
Nida so nayi ka tareta kace mata miyasa ta kashe maka d'an uwa,,, ka dai gane ka irin tsorata
ta d'in nan kace zaka had'ata da hukuma ".��







"wa! Ni idan kikaga an kaini cikin kabari kaini akayi bani nakai kaina ba,,, so kike ina zuwa ta
dubeni da shegunan idanunta jawur kamar wuta ta kame mini kurwa ta lak'umeni aini duk
abinda tayi alhakin mutane na nan bisan wuyanta,,, saboda haka ki rufamin asiri babu ruwana
duk abinda zatayi taje tayi tayi duniya ce wanda baizo bama jiransa take ".Inji Labbo cikeda
matuk'ar tsoron al'amarin Inna Talatu MAYYA.








Inna Talatu ta sake fashewa da dariyar k'eta harda rik'e ciki takeyi akan dariya,,, sai ta dubi
Labbo sannan ta fashe da wata dariyar mugunta.

Can dai ta daure ta tsayar da dariyar ta karkace baki tace "kaini wasa nakeyi maka taya zance
kaje mahalaka da hankalina,, halan so nake in zama bazawara ai nasan ko maza masu tashe
da k'arfi da mazantaka tsoron tunkarar mayyu sukeyi,, balantana kaida ka kwana biyu Allah ya
sawwak'a in tura uban 'ya'yana wurin annobar gari mai cin naman mutane ".





Labbo yace "aike bakisan wani abu ba,,, idan kikaga yadda maza da mata yara da manya suke
gudu in suka hango mayyu yadda zasu cikama buje ko wandonsu iska da gudu,, to sai cikinki
yayi ciwo akan dariya wlh ai ni abin na d'aure min kai yadda suke rikid'a su koma kowace irin
halittar suka gadama ".






"ina ni ina tsayawa dariya kowa yanata kansa,, to kai maigida miye abin mamaki bayan kowa
yasan tsafi da sihiri ne sukeyi suna komawa kowace irin halitta,, inda ma Gwamma kaje ka
dawo da ita nan kada uwar ta koya mata mummunan dabi'a da halinta ".Inji Inna Tani tana
dariyar mugunta k'asa k'asa kada Labbo ya jiyota.





Labbo ya harareta yace "ina ni ina raba uwa da d'iyarta babu ruwana wlh,, ai tasan da zamana
tayi zamanta wurin mahaifiyarta amma ke na baki iznin ki fita kije ki dawo da ita wannan gida ".







Inna Tani tace "hmmmm wai mutuwa kenan! Ni ko uwatace ke maita gudunta zanyi saboda in

tsira da raina da lafiyata,,aini saboda tsorana ko muryar mayya naji saina saki fitsari a cikin
wando �balantana har nakai kaina mahalaka ".






"to shine saboda kin mayardani wawa kike cewa inje ina ruwanki,, ai d'an uwana ne ta kashe ba
naki ba to nabarta ga Allah ubangijin talikkai shi zaiyi mana hisabi a tsakaninmu ".Cewar Labbo
ya muzurai da idanu alamar tsoro..







Inna Tani tace "kaini wasa nakeyi maka ai duk abinda zai cutar dakai sai inda k'arfina ya k'are,,
bawai ince kaje gidan mutuwa ba ".






Labbo yayi murmushi yace "ai nasan wasa kike yimin matata,, uwar yarana banda tamkarki a
cikin zuciyata ".Yana wani kashe mata idanu alamar soyayya. �







Inna Tani tayi masa kallon so tace "su Labbo kenan an tunada tsohuwar soyayyar da mukayi
tunda dad'ewa sosai ".




"na tuna uwargida ran gida ".Inji Labbo.

Suka fashe da dariya tareda kallon juna suna murmushi,, daga ganin yadda suke gudanar da
rayuwar aurensu akwai soyayya da k'auna mai k'arfi a tsakaninsu,,, firarsu kawai sukeyi cikeda
matuk'ar farin ciki da kwanciyar hankali.








¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤






**Abangaren Sala mafarauci yana farfa'dowa daga suman da yayi,, Inna Yashe ta kawo masa
ruwa da abinci da magani ya fara cin abinci sannu a hankali,, cikin yanayi na ciwo sosai baba
Labaran da Ummaru suna zaune gefe suna kallonsa cikeda matuk'ar tausayawa sosai.








Ya cigaba da cin abinci bayan ya d'anci mai dama sannan yasha ruwa tareda maganin,, ya aje
kofin gefe yana jan numfashi dak'yar,, su duka sukayi masa sannu ya amsa,, baba Labaran yaje
ya d'auko garin magani na gargajiya Inna Yashe ta shafe duka jikin Sala mafarauci dashi
maganin,, da maganin ya fara yi masa rad'ad'i da zafi sai naga Sala mafarauci yana runtse
idanu tareda cije baki yana nishi sannu sannu.

Zuwa wani lokaci sai naga maganin duk ya game jikinsa gaba d'aya yana ratsa sassan jikinsa,,
ga wani irin zufa dake tsiyaya cikin jikinsa can yaja doguwar ajiyar zuciya sannan yace "hmmm
yau naga mutuwa ga filin wuri naga tashin hankalin da ban tab'a ganin irinsa a rayuwata ba,,
nasha azaba da bak'ar wuyar da ban tab'a shan taba a cikin rayuwata,, lallai mayyu annoba ne
kuma guba ne cikin al'ummarmu saboda suna kashemu a banza sannan su cinye namanmu a
yofi,,, ban tab'a zaton rashin imani da rashin tausayin mayyu yakai haka ba sai yanzu da naga
mutuwa a filin wuri k'iri k'iri ".





Baba Labaran yaja doguwar ajiyar zuciya sannan yace "hak'ik'a yau k'anena kaga tashin
hankali,, kuma Allah yasa kanada tsawon rai domin Talatu ko cikin mayyu ba k'aramar mayya
bace ba,,, sannan duk ta zamo shahararriyar *MAYYA CE* wadda ta gagari mutane da dama
acikin wannan gari namu mai tarin albarka ".






Ummaru yace "abin ba'a cewa komai amma gaskiya sharrin mayyu da muguntarsu ya wuce
tunanin duk wani d'an Adam,,, sabodasu sun riga sun fita daga cikin mutane sun zama mayyu
haka suke ganin komai na jikin mutane,, kamar dai yadda kukasan k'warangwal (skeleton),,
wasu ma idan suka kama mutum idan ya gagaresu aljannu suke mik'awa kurwarsa su kashesa!
Saboda haka baba ka auna babban arzik'i da ka dawo da ranka ".








"mun godewa Allah ubangiji da ya bashi ikon kasheta da kuma dawowa da rai,, duk da yake
shegiyar annobar duk ta jimasa raunika da yawa ga jini sai zuba yakeyi a d'azu ajikinsa ".Inji
Inna Tani cikeda matuk'ar sanyin jiki da farin cikin mutuwar Talatu k'usurgumar mayya.

Baba Labaran yace "haka ne gaskiya maganarki mun gode Allah da farin cikin dawowarsa a
raye gida,, amma muna son ka bamu labarin irin gwagwarmayar da kasha wurin kashe wannan
mayyar Talatu ".









Sala mafarauci ya gyad'a kansa yace "yanzu kuwa zan baku labarin yadda abin ya kasance
"......Ya kawo labarin komai duk abinda ya faru daga farko har k'arshe ya gaya musu,,, bai b'oye
musu komai ba na irin abubuwan da suka faru a tsakaninsu da Inna Talatu,,, da kuma irin tsafe
tsafen da ta kamayi tana rikid'a ta koma mutum,,, haka dai ya sanardasu komi bai b'oye ba..






Suka had'a baki wurin cewa "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! "...






Haka dai suka cigaba da tattaunawa akan lamarin mayyu,,, da kuma irin cutarwar da sukeyi
acikin al'ummar musulmai baki d'aya..





*Allah ubangiji ya kiyayemu*..

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤





*BAYAN KWANA BIYU*



Bayan faruwar mutuwar Inna Talatu MAYYA duk labarin komai,,, da irin kisan walak'anci da Sala
mafarauci yayi mata ya bazu ko'ina a cikin garin Gumi,,, ko'ina lungu da sak'o acikin garin kowa
ka gani fuskarsa tana bayyanar da tsananin farin ciki da nishad'i mara misaltuwa.
Majalisar samari da ta dattijawa sai murna sukeyi suna mayarda labarin abinda ya faru ,,,
saboda farin ciki da murna ji sukeyi kamar su goya Sala mafarauci abayansu,, sarki da
dogaransa da kansu sukaje har gidan Sala mafarauci sukayi masa godiya tareda da bashi
babbar k'yauta,, ya amsa yana cikin farin ciki da nishad'i sosai domin yanzu kam yaji sauk'i
sosai a jikinsa,, sukayi masa sallama tareda musabaha da junansu cikin girmamawa,,, suka
wuce zuwa gida..






Tsuntsuwar bata sauka a ko'ina ba sai a cikin k'usurgumin dajin da boka LOK'ORO yake
zaune,,, tana sauka ak'asa ta koma ainahin siffarta Gwamma,,,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login