Showing 39001 words to 42000 words out of 58121 words

Chapter 14 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

Advertisement

12 Jul 2025

3007


*PAGE 22*




"Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un Allahumma ajirni fi musibati wa'akhalufni khari minha!!!".Suka
fad'a atare cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa! Bayan sunje wurin Ummaru da sauri
d'aya daga cikinsu yaje ya d'ebo ruwan sanyi a cikin randa,, ya kawo akayima ruwan addu'a mai
tsawo sannan aka juye masa ruwan gaba d'aya ajikinsa saida ko'ina a jikinsa ya jik'e da
ruwan,,, ganin da sukayi zasu gaji da tsayuwa yasa dole aka d'auko tabarmi guda biyu
kowanensu ya zauna akai,,, sukayi jugum duk jikinsu yayi matuk'ar sanyi da fargaba akan
abinda idanunsu suka gani,, sannan kuma ga k'asusuwansu Sala mafarauci nan yayyasshe
ko'ina a cikin d'akin k'arnin jini kawai yake tashi,, ,,babu dad'in ji balantana gani sunyi shiru na
tsawon lokaci da tagumi gabansu sai fad'uwa yakeyi da sauri da sauri,,, can dai sukaji Ummaru
yaja dogon numfashi tareda yin tari yana farfad'owa ya tashi zaune yana kallonsu d'aya bayan
d'aya,,,,, ganin ya farfad'o ne zuk'atansu suka cika da farin ciki da murna sosai sannan
kowanensu ya matso kusaga Ummaru suna yi masa sannu,,, yana amsawa bayan d'an wani
lokaci ne maigari Garba ya k'ara matsowa kusa ga Ummaru yace "Ummaru munzo wurin
iyayenka da yayan babanka Labaran,, saboda in sanardasu abinda yake faruwa acikin garin
Gumi na mutuwar mutane ishirin,,,,, biyu daga cikinsu 'yan uwanku ne,, amma sai muka tarar da
kai ka suma sannan bamuga mahaifanka ba da yayan babanka,,,,sanardamu mi yake faruwa
yakai Ummaru? ".Alokacin ne Ummaru yaji wani irin turirin bak'in ciki ya tokare masa gaba,,,
wani abu ne ke yawo a cikin jinin jikinsa idanunsa sukayi jawur hawaye kawai ke fita daga cikin
idanunsa,,, zuciyarsa sai tafasa takeyi da k'una sosai babu abinda kake hangowa sai tsananin
b'acin rai da bak'in ciki acikin idanunsa,,, maigari ne ya sake cewa"kayi hak'uri ka sanardamu
duk abinda yake faruwa,,, komai yayi zafi maganinsa Allah kuma komai yayi farko yanada
k'arshe zaizo ya wuce kamar ba'a tab'a yinsa ba ".Wani dake gefen maigari mai suna Tukur,,, ya
karkace baki yace "haka ne maganarka maigari Allah yaja zamaninka,,, hak'uri zakayi Ummaru
ka gaya mana abinda yake faruwa saboda kaga anan babu wanda yasan abinda ke faruwa
".Madu yace "mu kanmu jikinmu duk yayi sanyi hankalinmu duk ya tashi! Saboda bamuga
alamarsu Sala mafarauci da matarsa da yayansa a cikin wannan d'akin ba,,, kuma matar
Labaran ta tabbatar mana yana nan yazo gurin Sala mafarauci domin ya k'ara diba yadda
jikinsa yayi sauk'i sosai ".
"k'warai da gaske haka maganar take Ummaru,,, ba kai tsaye mukayo nan ba saida muka biya
gidan babanka Labaran ".Inji maigari cikeda matuk'ar sanyin jiki da lallashi. Ummaru ya d'ago
ya kallesu idanunsa sunyi matuk'ar ja,,, ya bud'i baki dak'yar yace "kuyi hak'uri bawai na
k'yaleku bane saboda baku isa gareni ba,,, na k'yaleku ne saboda zuciyata k'una da tafasa

takeyi alokacin amma yanzu zan sanardaku irin mummunan k'addarar data sameni nida
iyayena da baba Labaran,,, k'addarar da ban tab'a zaton ko a mafarki zata afku gareni ba,,,
mugun al'amarin da har abada bazan tab'a mantawa dashi ba ko bayan raina....... ".Ummaru ya
kwashe labarin irin ta'adancin da tsutsar tayima iyayensa da baba Labaran harta kashesu,,, ya
sanardasu yadda tayi masa mugunta har ya some baisan inda kansa yake ba,,, yana kawo
k'arshen maganarsa ya fashe da wani rikitaccen kuka mai ban tausayi da tarin bak'in cikin
rayuwa.
Gaba d'ayansu suka k'ara saka salallami "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un Allah ubangiji ya
jik'ansu Sala mafarauci! Yasa sun huta acikin kabarinsu ".









Maigari yace cikeda matuk'ar tashin hankali da rikicewa! "kayi hak'uri Ummaru Allah yana
tareda masu hak'uri,,, amma wannan abin ya zamo d'aukar fansa ne ga Inna Talatu MAYYA
saboda kasan babanka shine ya zamo ajalinta,,, kaga kuwa kenan tanada 'yan uwa ko abokiya
wadda ta d'aukar mata fansar jinin Talatu harta kashe mutane ishirin da uku gamida iyayenka! ".





Madu yace "wannan abin babu shakka haka yake,, saboda kashe rayuka da akeyi acikin garin
Gumi yayi yawa sosai wlh,,, ada muna ganin abin da sauk'i ayanzu yazo yaci uban na da ".








"ai wannan mayyar da ta kashe mutane ishirin da uku to ta wuce Talatu MAYYA,,, awurin
hatsibibanci da zalunci! Saboda Talatu bata tab'a kashe rai kusan ishirin lokaci guda ba ".Cewar
Tukur cikeda matuk'ar bak'in ciki da takaicin abinda ke faruwa..

Maigari yace "haka ne gaskiya amma zamu d'auki babban mataki acikin garin Gumi,,, na duk
inda aka kama MAYYA akasheta saboda abin yayi yawa sosai idan ba haka harmu zasu shiga
cikin gidajenmu suna kashemu da iyalenmu,,, kunga kenan muma bamu tsira ba akodayaushe
akowane lokaci mutum za'a iya kame masa kurwa a cinye ,,,yanzu dai Madu tashi ka tattara
k'asusuwan nan muje ayi musu sallah arufesu mak'abarta "..









"to maigari ".Cewar Madu ya tashi tsaye ya samo buhu ya tsince k'asusuwan baki d'aya,,, ya
sanya cikin buhu ya dawo ya zauna.








Tukur ya dubi Madu yace "ba zama zamuyi ba tashi zamuyi yanzu nan muje can cikin gari,,
akaisu tareda da sauran gawarwakin dake can ana jiranmu ".







Dogarawan sukace"maganarka haka take Tukur angaisheka".

Suka mik'e tsaye gaba d'ayansu harda Ummaru,,, suka fito daga cikin gidan cike da matuk'ar
bak'in ciki da jimamin mutuwarsu Sala mafarauci da mutane ishirin,,, suka d'unguma zuwa inda
aketa yima gawarwakin mutane wanka.


Koda sukaje har angama musu wanka da sallah,,, za'a kaisu gidansu na gaskiya maigari ne ya
umurci mutane da su tsaya,,, suna tsayawa ya umurci Ummaru ya basu labarin da ya basu na
mutuwarsu baba Labaran da Sala mafarauci sannan aka gwada musu yadda mayya ta cinye
musu nama har ya dawo k'asusuwa,,,, ai kuwa mutane suka k'ara rikicewa da d'imaucewa!
Akan mummunar annobar mayya data zarce Inna Talatu akan rashin imani da shahara a cikin
maita! Haka dai sukayiwa k'asusuwan sallah sannan suka d'unguma zuwa mak'abarta domin
akaisu makwancinsu na gaskiya.







Mutane kowa ka diba hawaye ne ke gangaroya daga idanunsu,,, tsoro da tsananin tashin
hankali ne bayyane afuskokinsu saboda kowa yasan zai iya fad'awa cikin tarkon k'ursugumar
mayya gagararriya acikin mutane da aljannu! K'arin takaici da haushi basusan ko wa ce ce
sabuwar mayyar dake kashesu abanza tareda jaddada fitina a tsakaninsu ba..






**********************

Bayan sun dawo daga kaisu Sala mafarauci gidansu na gaskiya,, to alokacin ne maigari yayi
sanarwa akan mutanen gari su taru bakin k'ofar gidansa,,, bayan mutane sun gama taruwa ne
ciki kuwa harda baba Labbo,,, sannan maigari yayi bayanin cewa duk inda aka kama mayyu
acikin garinsa to akashesu,,, sannan ya juyo ya dubi baba Labbo ya tambayesa rannan miye ya
sanyashi gudu har ya kawo wurinsu da matsiyacin gudun ceton ransa,,, baba Labbo ya duk'ar
da kansa ya kwashe labarin irin yadda macijiyar ta bashi tsoro da kuma gargad'insa akan kada
ya sake dawowa gidan yayansa marigayi Malam Mamman.







Mutane sunka k'ara tsoracewa da rikicewa akan wannan labari da baba Labbo ya sanardasu,,,
maigari yayi magana ya nuna musu za'a saka matakan tsaro acikin garin baki d'aya sannan
za'a sanyawa Gwamma ido matuk'a,, saboda yadda take rayuwar cikin gidan batare da tsoro ko
wani shakku ba.







Su kansu mutunen gari zuciyarsu ta basu akwai wani abu ab'oye ko lauje cikin nad'i,,, saboda
sunsan babu mai iyawa zama cikin gida shi kad'ai idan ba hatsabibi ba,, aka umurci Malamai
gaba d'ayansu dasu k'ara dagewa akan Allah ubangiji ya tonama mayyu asiri,,, mutane sukace
amin sannan sukayi addu'o'i kowa ya kama gabansa cikeda matuk'ar zullumi da rad'ad'in ciwon
mutuwar mutane ishirin da uku..








Musamman yafi kowa jin zafi da rad'ad'in ciwo har cikin zuciya ,,,,,yasha alwashin kowaye ya
kashe masa iyayensa da yayan babansa sai ya d'auki fansar jininsu,,,, ab'angaren Innar Lado
wato matar baba Labaran tanajin labarin mutuwar mijinta dana Sala mafarauci da matarsa ta

fad'i k'asa ta some,,,,mata mak'wabtanta sukazo kawo mata agajin gaggawa kafin ace wani abu
zuciyarta ta buga ta rasu! Haka dai itama akayi mata wanka aka kaita gidanta na gaskiya..







Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!!.







**Ab'angarensu Sule da Gwamma haka suka cigaba da mu'amalarsu kamar mata da mijinta,,,
akodayaushe yana manne da ita,,, ita kuma ta cigaba da cin naman mutane dana aljannu komai
cikin sirri da b'oye takeyinsa,,, shi kansa Sule baisan wa ce ce ainahin Gwamma ba kawai yana
tare da ita ne........



















_Share&Comments_
[7/3, 2:53 PM] Mugiratmusa66:






*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_


*Hak'ik'a ban tab'a zaton zan samu tarin masoya a rayuwata ba,,, ban tab'a zaton novel d'ina
yanada farin jini da masoya masu yawa sai yanzu,,, nagode da soyayyarku masoyana aduk
inda kuke a fad'in duniya,, inasonku ina k'aunarku kamar yadda kuke k'aunata*.



*PAGE 23*





Shi kansa Sule baisan wa ce ce ainahin Gwamma ba kawai yana tare da ita ne,,, ita kuma bata

yarda ya gano ita mayya ce ba saboda batason ya baza ta acikin gari,,, kowa yasan
mummunan dabi'ar da take aikatawa na kashe rayukan mutane....








*BAYAN KWANA BIYU*




Bayan kwana biyu da faruwar wannan mummunan al'amari,,,mutanen gari gaba d'aya kowa ya
k'ara tsoracewa akan lamarin mayyu gashi sunga ankashe musu babban mafarauci,,,, wanda
ya shahara a wurin kamun namun daji da kuma maganin mayyu,,, sun riga sunsan cewa Inna
Talatu MAYYA tabar mai d'aukar mata fansa amma basu gano ainahin wa ce ce ko wa ye yake
d'aukar ran mutane,,, kamar ran dabba shiyasa maigari bayan yasa matakan tsaro ya kuma
samu amintattun mutanensa asirrance,,,, su dinga lura sosai da shige da ficen Gwamma,,,,
babu wanda ya sani daga maigari sai wad'annan amintattunsa,,, ita kanta Gwamma bata sani
ba balantana sauran mutanen gari...





Ab'angaren Ummaru kuwa bayan rasuwarsu Sala mafarauci ya shiga cikin matsanancin hali
na bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, kullum kullum idan kaga Ummaru sai ya baka tausayi yayi
bak'i sosai ya rame,,,, saboda damuwa da yawan tunani gashi yanxu shi kad'ai yake kwana
acikin gidansu,,,, domin bayason yaje wani wurin ya kwana saboda kada yabar gidan babu
kowa acikin gidan nan....
Wata rana Ummaru yana zaune shi kad'ai acikin gidan yayi tagumi,,, zaune yake saman
tabarma ya fad'a duniyar tunani,,, kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin wani hali domin yayi
babban rashi na har abada! Ya rasa iyayensa da yayan babansa da kuma matarsa alokaci
guda,,, duk wani farin ciki ko walwala nasa ya tsaya cak sai dai ya zauna shiru shiru babu
magana,,, ganin haka ne yasa Kabiru abokinsa yana yawan zuwa wurinsa domin ya d'ebe masa
kewa da kuma bashi kalamai masu dad'i...

Can dai bada jimawa ba saiga sallamar Kabiru ya shigo cikin gidan,,,, yaji shiru ba'a amsa ba ya
sake sallama ya shigo har kusaga Ummaru yasa hannunsa ya jaye hannun Ummaru daga yin
tagumi,,, sannan ya zauna alokacin ne Ummaru ya dubi Kabiru yace "mutumena yaushe ka
shigo cikin gidan nan ban sani ba? ".




"ya za'ayi ka sani inata sallama kanacan kana tunani Ummaru,,, wai miyasa ba zakayi hak'uri ka
fallamawa Allah komai ba,,,, ka daina yawan tunani domin kada ka kamu da wani ciwon ".Inji
Kabiru cikeda tausayin abokinsa.





Ummaru ya bud'i baki yace cikeda matuk'ar bak'in ciki da takaici "idan Allah ya yarda zan rage
tunani Kabiru,,, amma har abada bazan tab'a mantawa da iyayena ba dasu baba Labaran
domin sune jigon rayuwata,,, na zama maraya gaba da baya ba wanda zan kalla inji sanyi a
raina Yaya Lado shima ita ta fara kashesa ".







"addu'a zakayi musu akan Allah ubangiji yasa sun huta kuma yakai haske kabarinsu,,,, sannan
maigari Garba ya aikoni wurinka Ummaru ".Cewar Kabiru.







Ummaru yace "wa ne sak'o ne ya baka ka gayamin?,,, sanardani inajinka Kabiru ".

Kabiru yaja dogon numfashi yace "Maigari ne ganin halin da kake ciki na bak'in ciki da
damuwa,,, gashi kuma kai kad'ai kake rayuwa acikin gidan nan kaga kuwa dole damuwa ta
k'ara maka yawa,,,, sannan nayi nayi dakai kazo mu dinga kwana tare ka nunamin bakayi
saboda inada mata,,, to maigari ya baka auren 'yarsa Ummu Salma wani sati idan ya zagayo
za'a d'aura muku aure idan har ka yarda,,, saboda haka yace kaje ka samesa idan ka amince
kanason 'yarsa ".








Ummaru yayi shiru na tsawon lokaci yana nazari da tunanin maganar Kabiru,,, ya lula duniyar
nazari da tunani...








Babu jimawa ya d'ago kansa ya kalli Kabiru yace "hmmm to kai mi ka gani akan wannan
maganar,,, na amince ko yaya abokina ?".







"ka amince mana Ummaru maigari yana sonka da alkhairi sannan ta haka ne idan kayi aure
zaka rage damuwa da yawan tunani,,, domin sadaki kawai zaka biya ad'aura aure sannan kaga
idan kayi aure sai mu fara shirin d'aukar fansar rayukan iyayenka da sauran mutanen gari,,,
saboda ni jikina ya bani idan ba macijiyar da ake labari acikin gari wadda Talatu MAYYA tabar
fakon Gwamma ta kashe maka iyayenka ba da sauran mutane,,, to mi Gwamma take tink'aho

dashi dahar zata zauna ita kad'ai a cikin wannan gida mai cikeda sihiri? ".Inji Kabiru cikeda
matuk'ar nazari da tunani.









Ummaru yace "na amince da auren Ummu Salma d'in zanje in samu maigari ,,, domin mu
tattauna sannan inyi magana da yarinyar,,, kuma maganarka akwai alamun k'amshin gaskiya
acikinta amma ba komai kowaye ma zan kamasa da hannuna saina kashe duk wanda yakeda
sa hannun acikin mutuwar iyayena! ".









Kabiru yace "haka ne gaskiya ai da sannu koma waye Allah zai tona masa asiri,,, kowa ya gano
mai aikata wannan mummun d'abi'a ta maita! ".








Ummaru yace "ai bawai haka na k'yale ba ina nan ina saka idanu akan shige da ficenta ita
Gwamma,,, sannan idan ma itace wlh bazanyi mata sassauci ba ".

"sassauci kuma? Ai mayyu babu su babu sassauci har abada acikin rayuwarsu,,, saboda basu
aikata alkhairi ba taya za'a yi musu da k'yau idan aka kamasu ".








Ummaru yace "haka take maganarka Kabiru ".








Haka suka cigaba da tattaunawa akan yadda zasu b'ullowa al'amarin mayyu,,,da kuma
maganar aurensa da Ummu Salma d'iyar maigari....








¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤






Bayan gari ya waye Ummaru ya tashi yayi wanka ya shirya,,, sannan yaje gidan Kabiru suka
d'unguma zuwa gidan maigari.

Suna zuwa sukayi sallama a k'ofar gidan ,,,,Zubairu k'anen Ummu Salma,,, shine yayi musu
jagora har cikin gidan zuwa wurin maigari,,, suna shiga cikin gidan suka iske maigari Garba
zaune saman kujera ga tabarma shimfid'e gaba garesa,,, suna zuwa suka duk'a har k'asa suka
gaida maigari,,,, ya amsa musu fuskarsa asake cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai..







Maigari ya bud'i baki yace "Ummaru ina fatar sak'ona ya isa zuwa gareka,,, da fatar zaka bani
had'in kai akan auren da nakeson in had'a ku kaida Ummu ".









Ummaru ya duk'ar da kansa cikeda matuk'ar ladabi da girmamawa yace "eh baba sak'onka ya
iso gareni ".








"kayi hak'uri Ummaru komai ya samu bawa muk'addari ne daga Allah,,,, sannan bawa bai isa ya
gujewa k'addararsa ba kuma komai nufin Allah ne shine masanin gaibu,,, saboda haka na baka
auren 'yata Ummu Salma wani sati za'a d'aura aurenku ".Cewar Garba maigari.

Sai asannan Kabiru ya d'ago kansa yace "hak'ik'a baba babu abinda zamuce maka Allah
ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairi,,, sannan mun amshi auren 'yarka hannu bibbiyu kayi
mana abinda bazamu daina yi maka addu'ar gamawa lafiya ba,,, mun gode sosai Allah ubangiji
ya k'ara nisan kwana ".








Ummaru yace "amin ya rabbi na yarda na amince da auren Ummu Salma baba,,, kayimin
abinda har abada bazan tab'a mantawa da halaccinka agareni ba,,, sannan ka nunamin nima
d'an gata ne a wurinka duk da yake banida iyaye,,, ka nunamin k'auna azahiri da bad'ini Allah
ubangiji ya k'ara girma da d'aukaka ".












"karku damu duk abinda nayi maka nayi maka ne domin Allah mad'aukakin sarki,,, sannan ba
fad'uwa bane komai mutum yayi ladarsa tanaga Allah,,,, saboda haka ku daina yimin godiya
kunfi k'arfin haka a wajena sai dai ku jira har lokacin biki ".Inji Garba maigari cikeda matuk'ar
farin ciki sosai.

"tabbas haka ne gaskiya baba ".Cewar Kabiru.







Haka dai ya cigaba da yi musu nasihohi masu ratsa zuciya,,,, sannan ya nuna musu
muhimmanci hak'uri da juriya da kuma zamantakewar rayuwa.







Bayan maigari ya gama yi musu nasiha mai ratsa jiki,,, sannan ya tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login