Showing 9001 words to 12000 words out of 58121 words
gamawa ta d'ebo ruwa a famfo ta shige toilet domin tayi wanka,, bata jima da shiga wanka
ba saiga Malam Mamman ya fito daga cikin d'aki yana gugar bakinsa da asuwaki,, shi ma yaje
famfo ya d'ebi ruwa a bokiti domin yayi wanka ya tsaya yana jiran fitowar Inna Talatu..
Ta jima sosai tana yin wanka sannan ta fito daga cikin toilet,, Malam Mamman ya dubeta yace
"har kin fito daga wanka Talatu? ".
"Eh mana na fito har na gama had'a karin safe ".Inji Inna Talatu MAYYA.
Malam Mamman yace "to yayi k'yau gaskiya kinyi sauri sosai,, dan Allah kafin in fito ki tabbata
kin had'amin komai nawa karin kumallo ".
Inna Talatu tace "to Mamman karka damu yanzu nan zan had'a maka komai ".
"na ko gode miki sosai ".Cewar Malam Mamman tareda shigewa cikin toilet,, domin ya tsabtace
jikinsa yaje wurin sana'arsa..
Inna Talatu kuwa wucewa tayi cikin d'akinta tana shafa man shafi,, bayan ta gama komi ne ta
sanya tufafinta masu dama dama ,,,sai alokacin ne Inna Talatu ta lura da bata tayar da
Gwamma ba daga barci,, ta je ta tasheta daga barci sannan ta juya ta nufi hanyar d'akin da
Lawwali yake kwance,, ta tayar dashi daga barci tana zaginsa saboda haushinshi da takeji
sosai ,,Lawwali ya tashi yana wuru wuru da idanu ya duk'ar da kanshi k'asa yana sauraren irin
zagin da Inna Talatu ke masa akan rashin so..
Bayan ta gama zaginsa ta fito daga cikin d'akin tayi cikin d'akinta,, ta iske har Gwamma ta
gama karin kumallo,, shi ma Malam Mamman har yasha kunun da k'osai ya shirya yayi wurin
neman na kansa,, Inna Talatu ta samu wuri ta zauna saman kujera ta fara cin k'osai tana shan
kunu cikin natsuwa da nishad'i,, bayan ta kamalla cin abinci ne ta dubi Gwamma cikeda
matuk'ar k'aunar d'iyarta tace "Gwamma babanku ya fita ne,,, ina fatar kin k'oshi sosai babu
abinda kikeso? ".
Gwamma tace "Eh ya fita Inna kuma ni a k'oshe na ke,, babu abinda nake buk'ata ".
"babu damuwa d'iyar Inna ".Inji Inna Talatu.
Lawwali ne naga ya shiga cikin kitchen ya d'ebo kunu da k'osai cikeda fargaba da matuk'ar
tsoron Innarsa,, zullumi da fargaba ne suka bayyana k'arara a saman fuskarsa,, duk abinda
yakeyi Inna Talatu tana lura dashi sai dai bata ce dashi ci kanka ba yaja k'afafunsa ya yi cikin
d'akin da ya kwanta barci..
Su kuma Inna Talatu da Gwamma suka cigaba da firarsu cike da tsananin k'aunar juna da wasa
da dariya,, babu abinda suke yi sai shewarsu da kuma yin muguwar dariya ta yadda ko wanda
yake waje zai iya jiyo dariyarsu da surutunsu..
Shi dai Lawwali yana nan lab'e cikin d'aki bayan ya gama cin abinci,, ya kwanta yayi shiru yana
tunani can naga yana zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa kamar marayan da
bayada uwa ko uba,, ayadda na fahimta Inna Talatu ta tsaneshi bata sonshi hmmm wai kamar
ba ita ta haifeshi da cikinta ba,, ko da yake ba abin mamaki ba ne sau da yawa iyaye su kan
tsani 'ya'yansu akan *SON ZUCIYA* da hujjar banza..
**********************
Ab'angaren Lado kuwa kafin gari ya waye sosai ya farfad'o daga dogon suman da yayi,,,, ya
tashi tsaye yana kakkab'e jikinsa Sannan ya nufi cikin gidansa,, ya shiga da sallama matarsa
Hassi ta amsa mashi tareda yi masa sannu da zuwa,, domin ita azatonta daga masallaci ya fito
tana surfen hatsi ta ga Lado ya nufi randar ruwa ya d'iba a cikin buta yana arwala,, bayan ya
gama ne ya shiga cikin d'aki ya shimfid'a sallaya yana sallah..
Hassi ta daina surfen da takeyi tayi tsaye sakatoto kamar wawuya,, tana ta mamaki da al'ajabi
akan mijinta,, tana ta addu'ar Allah yasa ba wani abu na cutarwa ba ya gigita mata miji ba ya fita
cikin hayyacinsa..
Bayan Lado ya gama sallah ne ya fito waje wurin matarsa,, Hassi ta kalleshi cikeda matuk'ar
tsoro da gigicewa tace "Lado lafiya naga ka sakeyin wata sallar asuba bayan wadda kayi a
masallaci? ".
Lado ya d'ago jajayen idanunsa yaja wani dogon numfashi,, sannan yace mata "aike yau na
auna arzik'i da tuni sai dai a kawo miki gawa ta na mutu,, sai dai kiyi takaba ki sake sabon aure
Hassi ".
"Subahanillah!!! Ta ya hakan ya faru? Inji abin da sauk'i Lado ".Tace cikeda matuk'ar tashin
hankali da zullumi..
Lado ya kwashe labarin komai gameda karyar daya had'u da ita,, da irin azabobin da aka gana
masa da kuma sihirin da tsafin da ya gani karyar ta aikata,, babu abinda ya b'oye mata na
dangance abinda ya faru.
Hassi ta buga k'irjinta da k'arfi! Tace "karya fa kace daga zuwa wurin yin fitsari ".
Yace "Eh mana karya ce na gani ".
Tace "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! In dai har karya ka gani to babu shakka *MAYYA CE* ka
had'u da ita Lado,, wayyo Allah Allah yasa kada ta cutar da kai na shiga uku na lalace ni Hassi!
".
Lado yace "mayya kuma ni ina ni ina mayya Hassi,, ki rabani da shirmenku na mata kunfi kowa
shegen tsoro da koke koke ".
Hassi ta fashe da kuka mai cin rai tace "ba wani koke koke sai gaskiya,, mijina ka yarda da
maganata wallahi *MAYYA CE* ta tare ka kan hanya ".Tana k'ara gunjin kuka sosai..
"ni kinga tafiyata idan kika daina kuka zuwa anjima zan dawo,, kinzo kinata cika ni da surutun
banza mtsssss! ".Inji Lado yaja k'afafunsa yayi wucewarsa yana ji nini..
Ya bar Hassi zaune tana ta kukan damuwa da fargab akan yadda abin zai iya kasancewa,,
saboda har cikin zuciyarta da jikinta ya bata abinda ya had'u dashi ba alkhairi ba ne.....
_Share &Comments_
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 7*
***Saboda har cikin zuciyarta da jikinta ya bata abinda Lado ya had'u da shi ba alkhairi ba ne,,
kuka kawai takeyi mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro,, ta jima tana hawaye harta
gaji da yin kuka sannan ta shige cikin d'akinta domin har kanta ya fara ciwo akan damuwa..
Lado kuwa yana fita bai zarce ko'ina ba sai cikin kasuwa rumfar da abokinsa yake zama,, yana
zuwa yayi sallama Idi ya amsa masa sannan sukayi musabaha da juna,, Lado ya zauna saman
benchi kusa ga Idi sannan yace "Abokina ya kasuwar? Ina fatar dai komai yana tafiya dai-dai ".
Idi yaja dogon numfashi yayi ajiyar zuciya yace "Alhmdlilah Lado komai dai-dai,, ina ka fito ne
yanzu? ".
"gida na fito kai dai na baro Hassi can tanata koke koken banza,, ganin nayi ta dameni da kukan
banza shiyasa na fito nabar mata gidan ".Inji Lado.
Idi yace "kai kuwa abokina baka k'yauta ba taya zaka baro iyalinka cikin damuwa,, baka tsaya
ka saurari abinda ya sanyata kuka ba,, kai wa ne irin mutum ne kai Lado ".
Lado yace "ba haka ba ne Idi akan wata 'yar magana ce dana gaya mata,, maganar bata taka
ka ra ta karya ba shi ne ta ke kuka ".
"to wannan wa ce irin magana ce da ta sanyata kuka nan da nan? ".Cewar Idi yana jimamin
maganar..
Lado yace "yanzu kuwa zan baka labarin abinda ya faru dani jiya abokina ".Ya kwashe labarin
komai abinda ya faru da shi,, da kuma irin abubuwan da karyar tayi masa na mugunta iri iri
daban daban ya gaya masa ..
Bayan ya gama gaya masa labarin sai Idi ya dubeshi cikin jimami da tausayawa,,, yace
"Abokina hak'ik'a ka ga tashin hankali da bala'i a daren jiya,, ina rok'on Allah ubangiji ya tsayar
nan yasa abin ba mai cutarwa ne ba,,, amma fa Hassi tana da gaskiyarta saboda mayyu suna
iya komawa kowace irin halitta na dabbobi irinsu karya,, ma ge,, rago,, jaki da dai sauransu,,,
saboda haka ka daina ganin laifinta ".
Lado yace "haka ne gaskiya amma duk abinda Allah ya tsara zai samu bawa ,,babu mahani sai
ya same shi ni na yarda da k'addarata duk abinda ya sameni daga Allah ne ba daga wani ba ".
"tabbas maganarka haka ta ke Lado,,, Allah ubangiji ya tsare mu daga shairin mugayen mutane
da aljannu,,, yasa kuma mu dace baki d'ayanmu ".Inji Idi cikin sanyin jiki da damuwa.
Lado yace "Amin abokina ".
Suka bar firar nan suka fad'a firar kasuwanci da kuma abubuwan da ke faruwa a cikin
duniyarmu,,,, babu abinda ke tashi sai muryarsu da dariyarsu cikeda matuk'ar k'aunar juna da
amintaka da junansu..
***** ***** ***** ***
***Washe gari da safe misalin k'arfe 11:00am na safe,, bayan Malam Mamman ya fita zuwa
kasuwa wurin sana'arsa,,,, Inna Talatu ce ta aiki su Gwamma da Lawwali su sayo mata kayan
miya kasuwa,,, daga nan zuwa kasuwa da k'afa akwai nisa sosai,,, bayan sun wuce ne Inna
Talatu ta fissuwa fa rar da ta saka cikin jakarta jiya da dare,, tana cirowa ta je ta aje fa ra wurin
tulun ruwa masu sanyi da ya ke gefen filin gidan,, tana aje fa ra (grasshopper) sai naga fa ru
(grasshoppers )masu yawa sosai. Ta aje su kusan wuri guda ashe dai duk kurwar mutanen da
Inna Talatu ta kama ne domin ta cinyesu,, ta samu wuri ta zauna tana ta sambatun sihiri da tsafi
idanunta sunyi matuk'ar ja kamar garwashi,, gashin jikinta ya fito yayi zago zago kamar
dodanniya,,, gashin kanta ya koma fari fat kamar tsohuwa..
Hak'oranta suka yi zago zago kamar gatari,, nan da nan naga ta d'aga hannunta sama tana ta
tsafi ta jima tana yi sai naga anyi wata irin mahaukaciyar tsawa! Ta bayyana ratsatsatsa
ratsatsatsa fasss fasss fasss !!!Gidan ya kama girgiza komai na gidan ya kama rawa da girgiza
da sauri da sauri,,, wani bak'in hayak'i ne yazo wurin Inna Talatu yana ta zagayarta har tsawon
minti talati,, sannan ya daina Inna Talatu tasa hannunta fartuna zagal zagal,,, ta yi amfani da
wutar da ke fitowa daga cikin bakinta ta d'auko fa ru(grasshoppers) guda biyar tana gasa su da
wutar bakinta ..
Kuwwa da kururuwa kawai kurwar sukeyi da k'arfi! Har ma kana jin kukan mutane sosai kawai
ke tashi ya cika gidan gaba d'aya,,, hayak'i duk ya gauraye gidan!. Inna Talatu tana gamawa ta
sa fa run cikin bakinta ta lak'umesu ba tare da b'ata lokaci ba,, har wani gurnani da nishi takeyi
cikeda matuk'ar jin dad'in naman da ta keci na mutane,, tana gama ci ta nufi wurin murhun wuta
sai naga wasu fa ru masu yawa ta ajesu nan..
Wai ashe mayyu idan suka kama kurwar mutune,, zasu mayar da ita fa ra ko kaza ko k'aton
rago da dai sauran dabbobi iri iri daban daban da suke mayar da mutane..
Idan mayyu suka kama mutum suka mayarda kurwarshi fa ra ko kaza,, za suyi ma fa rar tsafi
domin kada ta tashi ta je ko'ina ma'ana ta tsaya a inda anka ajiyeta,, sai mayyar ta ajeta wurin
tulun ruwa masu sanyi sai kaga jikin wanda aka kama yanada matuk'ar sanyi sosai,, idan kuma
aka aje fa rar wurin murhun wuta zaka samu jikin wanda mayya ta kama yayi zafi sosai kamar
garwashin wuta. Wasu kuma suna aje kurwar saman gidan tururuwa,, shi kuma zai ji kamar ana
sukar jikinsa da allura.
Wasu kuma kaza suke mayar da kurwar mutum su je su saisuwa,,, su samu kud'i to fa ana
yanka kazar nan shikenan mutum zai mutu har lahira,, wasu kuma rago suke mayar da kurwar
mutum su je can kasuwa su sai suwa musamman ga sallar layya,, xa'a ga mutane suna ta
mutuwa to akwai mutuwar Allah akwai wadda sanadiyyar mayya ta maida shi rago ta sai suwa
idan aka yanka ragon sai mutum ya mutu,, batare da ansan *MAYYA CE* ta kamashi ta cinye
ba..
Akwai abubuwa da dama da mayyu sukeyi fiye da wad'anda na ambata,, addu'a ce kawai
mafita agaremu 'yan uwana musulmai,, amma maganar gaskiya mayyu sunyi yawa a k'asarmu
ta hausa ba yaran ba,,,ba manya ba tsofaffi,, budare,, samari maza da mata kowa a cikin
wannan zamanin zaka iya samunshi maye _(Allah ubangiji yayi mana mafita da kuma maganin
abinda bamu iya yima kanmu )_..
Bayan Inna Talatu ta gama cin naman mutanen da ta kama,,, ta samu ruwa masu sanyi ta sha
ta yi gatsa..
Sannan ta samu kujera k'arama ta zauna tana dama fura cikin roba,, sai wani gyad'a kai takeyi
kamar ba ita ba ce ta gama cin naman mutane ba!.
Babu jimawa sai ga su Gwamma sun dawo daga inda ta aikesu,, suna isowa suka d'auko
tabarma suka zauna tare da aje kayan miyan gefe cikin bak'ar leda.
Alokacin ne Gwamma ta dubi Inna Talatu MAYYA tace "Inna mun dawo ga aiken da ki kayi
mana fa ".
Inna Talatu tace "na ga ne ku d'iyar albarka,, Allah dai yayi muku albarka Gwamma ".Tana
cigaba da dama furarta cikeda matuk'ar kwanciyar hankali da jin dad'i.
"Amin Inna ".Inji Lawwali.
"ku tashi ku shiga cikin d'aki ku ci abinci idan na gama dama furar zan sha,, in rage muku
sauran amma kuyi wanka kafin ku ci abincin ".Cewar Inna Talatu.
Suka ce atare "to Inna ".Suka tashi tsaye suka shige cikin d'aki suna ta dariyar murna da farin
ciki..
**** *** **** **** ***
Acan cikin kasuwa kuwa Malam Mamman ne zaune da Mande suna fira cikin farin ciki da
nishad'i sosai ..
Malam Mamman ya dubi Aliyu Mande yace masa "kasan wani abu kuwa Mande ?".
"sai ka fad'a Mamman ina jinka ".Inji Mande mai shago..
Malam Mamman yayi doguwar ajiyar zuciya sannan yace "kwata kwata al'amarin Talatu yana
bani mamaki da tsoro,, duk ta chanza kwanakin nan ta zama kamar ba itace mu ka shafe
tsawon shekaru muna soyayya ba,, sannan kuma bayan munyi aure muna zaune zaman lafiya
babu mai jin kanmu,,, amma yanzu ta tsiro da wani hali mara k'yawo bata ganin girmana ko
mutuncina,, zagina tareda rashin kunya kawai takeyi min,, ni yanzu na rasa yadda zanyi da ita
wlh sai na ke ganin kamar maganar mutane ta fara tabbata Talatu ta zama abin k'yama wato
mayya ce ".
Mande yace "Subahanillah!! Zato zunubi ne koda ya zamo gaskiya ne kada ka zamo mai
d'aukar gulma da jita jitar mutane,, kuma ka ga duk k'azantar da ba ka gani da idonka ba tsabta
ce,,, ni dai shawarar da zan ba ka amatsayina na amininka kuma abokinka kayi hak'uri kayi
hak'uri domin Allah yana tare da masu hak'uri,, komai da kake gani a rayuwa sai mutum yayi
hak'uri sannan ya ke zamowa wani abu a rayuwa,, Annabinmu Muhammad (S. A. W) wanda
yafi kowa daraja a duniya an zagesa an dukesa an jefeshi da duwatsu wanda sanadiyyar haka
nan saida kanshi ya fashe da jini amma yayi hak'uri,, balantana mu da bamu kowa fa ce bayin
Allah,, kaje ka cigaba da hak'uri da ita komai na duniya yana da farko yana da k'arshe zaizo ya
wuce kamar ba'a yi sa ba ".
Malam Mamman yace "nagode sosai da shawararka abokina hak'ik'a kai mutum ne na gari,,
wanda ya san abinda ya kamata insha Allahu zanyi amfani da shawararka".
"yauwa Mamman ka k'ara hak'uri akan hak'uri duniyar yanzu guda nawa ta ke,, lamarin duniya
d'an hak'uri ne wata rana sai labari,, Allah ubangiji yasa mufi k'arfin zuciyarmu ".
Malam Mamman yace "tabbas haka ne gaskiya,, amin amin ubangiji Allah ya amshi bakinka ".
"amin amin ".Inji Mande.
Haka dai suka cigaba da firarsu cike da tsananin yarda da juna da shak'uwa,,, abotakarsu zad
sha'awa da burgewa ta yadda suke ba ma juna shawarar k'warai batare da wani munafurci ba
ko hassada ba.. ....
_Share &Comments_
[6/21, 9:55 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 8*
***Bayan Malam Mamman da Mande sun gama firarsu ne,, sai kowa ya maida hankali kan
sana'arshi suka cigaba da lura da jama'ar da ke zuwa wurinsu da kuma masu kai