Showing 57001 words to 58121 words out of 58121 words
Chapter 20 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf
wayyo
Allah ni Gwamma na shiga uku na lalace! ".....haka dai wuta ya cigaba da cin jikinta bal bal bal
sosai sai kuwwa da kururuwar neman agajin gaggawa takeyi,, mutane sai kuwwace-kuwwace
sukeyi na tsananin farin ciki da murna sosai,, kowanensu ka kalli fuskarsa farin ciki da murna ne
bayyane afuskokinsu saboda ganin k'arshen Iya Gwamma,, Hassan ne na hango wani wuri
zaune.......
[7/12, 1:46 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Ina godiya sosai matuk'a da soyayyarku da kuma k'aunarku gareni,, hak'ik'a ina matuk'ar farin
ciki da kasancewarku acikin group d'ina saboda kuna sanyani cikin nishad'i da farin ciki mara
misaltuwa.*
*Maman Haneef*
*Suwaiba Danabu*
*Maman twince*
*Ummu Shaheeda*
*Maman Hanifa*
*Ummu Usman*
*Maman baffa*
*Aishat Salisu*
*Ummeen Amatullah*
*His priceless jewel*
*Mom Hauwee*
*Khadijat Lookman*
*Hajja Saki*
*Ayshat*
*Firdausi Muhammad da duk sauran wad'anda ban ambata ba ina godiya sosai matuk'a
sister's.*
*LAST PAGE*
*PAGE 32*
Hassan ne na tsinkayo yayi zaune yana tagumi,,, hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa sai
shatata yakeyi daga cikin fuskarsa,,, jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u idanunsa sunyi jawur
kamar barkono,,, baba Labbo ma kwallar takaici da bak'in cikin rayuwa ne ke zuba daga cikin
idanunsa,,, tausayin Iya Gwamma ne da takaici ya mamaye zuciyarsa ga wani abu ya tokare
masa acikin k'irjinsa,, Suhaila tana ganin irin kisan gillah da walak'ancin da akayiwa
mahaifiyarta ta fasa gigitacciyar k'ara da razananniyar kururuwa da kuwwa da k'arfi! Wani irin
kukan bak'in ciki da k'uncin rayuwa takeyi da k'arfi nan da nan ta kama fisge fisge kamar
mahaukaciya sabon kamu,, 'yan uwanta mata sukazo zasu rik'eta cak numfashinta ya d'auke ta
fad'i k'asa d'immmmm ta some,,,, ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Kawai mutanen wurin suke
fad'a tana fad'uwa mata 'yan uwanta suka d'auketa sukayi gidan mijinta da ita!..
Tokar gawar tana gama k'onewa,, wata irin mahaukaciyar guguwa da razananniyar tsawa suka
bayyana k'arara atare,,, mutane da suketa kuwwace-kuwwace da yin farin ciki da murna akan
mutuwar Gwamma mayya,,, guguwar ta fara d'iban mutane tana yassuwa k'asa rikcham da
majinjiwa dasu,,, mutane suna ganin irin abinda ke faruwa kowa yace k'afa mi naci ban baki ba
suka ranci na kare dimm dimm dimm,,, kawai ke tashi k'arar gudunsu!. Guguwar ta daina bin
mutane ta tashi sama ta lulluk'a a cikin sararin samaniya ta nufi hanyar zuwa gidan boka
LOK'ORO da saurinta!.
Boka LOK'ORO yana zaune kwatsam tokar gawar Iya Gwamma,,,tazo ta shige cikin jikinsa da
sauri boka ya buga wata irin gigitacciyar k'ara da mahaukaciyar kuwwa! Yana cewa "ni boka
LOK'ORO na shiga uku na lalace! Banyi kaina adalci ba saboda arayuwata ban aikata alkhairi
ba,,, gashin tokar shegiyar nan Gwamma mayya tazo xata kasheni,, domin Ummaru ya k'oneta
da ranta wayyo Allah wayyo Allah na tuba kiyimin rai! Baxan sake aikata mummunan dabi'a da
kashe mutane ba,, yau ni boka LOK'ORO naga takaina yau nayi mugun gan..... ".Bai k'arasa
maganar ba jini da mugun tari ne ya sark'esa ya fad'i kwance k'asa yana shure shuren mutuwa
da kakarin fitar rai! Sai da jini gunduwa gunduwa ya zuba sosai acikin bakinsa sannan ya fad'i
k'asa d'immmmm ya mutu,,, aikuwa nan da nan batare da b'ata lokaci ba gawarsa ta kama wuta
bal bal bal tana ci! Sai da wutar ta k'onesa k'urumumus ya zama toka,,, acikin tokar kana hango
macijizai da kunamai suna yawo wurin ya gameda wani irin mahaukacin wari da d'oyin masifa
da bala'i!.
Wa iyazubillah ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Allah ubangiji ya rabamu da aikata shirka ya
kuma sa muyi k'yakk'yawan k'arshe.
********************
Bayan wani lokaci ne su Maryam da Fatima sun warke garau kamar basu tab'a yin irin wannan
ciwo ba,,, suka cigaba da zuwa makaranta da kuma rage yawon banza,,, da sukaji cewa Fadila
ta mutu ta barsu suka kama yin kuka babu mai kama wani,,, aranar sunyi kuka fiye da tunanin
mai tunani idanunsu sukayi jawur akan bak'in ciki da rashin Fadila,, iyayensu ne suke
lallashinsu tareda basu kalamai masu dad'i har suka dangana suka barwa Allah komai.
Mama Nafisa da baba Nazifi,, Fadil sun hak'ura da dangana akan rashin Fadila saboda sunsan
Allah da yabasu ita yafisu sonta ya amshi ran abarsa,,, saboda haka ne suka cigaba da binta da
addu'o'i da yawan karatun qur'ani domin ta samu rahamar ubangiji Allah..
Bayan mutuwar Iya Gwamma mutane suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikeda matuk'ar
farin ciki da kwanciyar hankali,,, komai zasuyi cikin natsuwa sukeyinsa saboda sunsan an riga
an kashe Gwamma mayya wadda ta addabi rayuwar mutane da aljannu! Sai godiya da addu'a
sukayiwa Ummaru d'an Sala mafarauci akan irin k'ok'arin da yayi wurin kamata da hannunsa da
kuma nuna matuk'ar jarumta,,, garin ya dawo dai dai farin ciki,, annashuwa,, jin dad'i,, walwala,,
nishad'i,, da dai sauransu duk sun dawo cikin garin Gumi..
*ALHAMDULILLAHI.*
Duka anan ne na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai suna *MAYYA CE*,,, da fatar mutane
zasu d'auki darasin dake cikinsa su watsar da abinda nayi kuskure,,, sannan alal hak'ik'a
maganar mayyu gaskiya ce bawai k'age ne nayi ba,, naman mutane sukeci dana aljannu babu
k'arya.
Ina rok'on Allah ubangiji ya yafe mini kurakurren da nayi acikin wannan littafi,,, abinda nayi dai
dai Allah ubangiji ya bani sakamako mai k'yau.
Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki wanda ya bani ikon gama wannan littafi lafiya,, ina
mai numfashi da cikakkiyar lafiya sannan ina godiya ga dukkan masoyana masu bibiyar
labarina da k'aunar wannan novel nawa.
*Ina godiya sosai da mik'a dubun gaisuwa ta ga wannan k'ungiya tamu mai tarin albarka,,
INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION kungiya d'aya tamkar dubu wadda ta tara
shahararrun marubuta masu matuk'ar ilmi,, hazak'a,, fasaha da kuma iya tsara labari mai
fad'akarwa da nishad'antarwa,, ilimantarwa Allah ubangiji ya k'ara d'aukakaku yasa kufi haka
shahara da d'aukaka har k'arshen rayuwarku,, ya kareku daga sharrin mahassada da mak'iya..*
_Ni Mugirat ina muku fatar alkhairi a rayuwa masoyana,,, sai kun jini asabon novel d'ina mai
suna *SOYAYYAR GASKIYA* nan ba dad'ewa ba...._
Mugirat ce