Showing 54001 words to 57000 words out of 58121 words

Chapter 19 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2977

"."dan Allah
Fadila ki daina cewa zaki tafi ki barmu zaki warke da yardar Allah,, bakiyimin laifin komai Allah
ubangiji ya tashi kafad'unki ".Cewar Mama Nafisa tana kuka sosai mai tarin yawa,, Fatima dake
kwance tana kuka ta amsa ak'asan mak'oshinta "amin".Fadila ce ta juyo ta kalli Fatima tana
murmushi sannan tace"ina sonki Fatima keda Maryam har abada kuna cikin zuciyata da
ruhina,,, ku kasance masu biyayya da ladabi ga manyanku kada ku kasance masu rashin kunya
da tsiwa nasan rashin kunyata ne yaja muku silar wannan ciwon,,, ku gafarceni ya k'awayena
na tub......."Bata k'arasa maganarta ba tari ne ya sark'eta idanunta suka k'ak'k'afe suna rufewa
da juyawa,,, can ta kama fisge fisgen fitar rai harta mutu Mama Nafisa tana ganin abinda ya faru
ta fasa razananniyar k'ara da gigitacciyar kuwwa da k'arfi! Ta fad'i k'asa ta some Fatima dake
cikin ciwo numfashinta ya d'auke da sauri akan tashin hankali da magagin ciwo!.

Umma Nusaiba ta saki gigitaccen kuka mai cike da rikicewa da d'imaucewa akan rashin
kwanciyar hankali da masifa! Ta kama fad'ar kalmar "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!! Na shiga
uku ni Nusaiba wannan bala'in dami yayi kama?,,,, dan Allah ku tashi karku tafi ku barni cikin
bak'in cikin rayuwa da k'unci ".Ta shek'a da gudu ta d'auko wayarta ta dialling numbar baba
Nura cikin tashin hankali da rikicewa! Tana kuka ta sanardashi abinda yake faruwa cikin gidan
yace mata gashi nan zuwa shida su baba Nazifi,, ya katse wayar ita kuma ta dawo wurinsu
Mama Nafisa tana wani irin rikitaccen kuka jikinta sai rawa da makarkata yakeyi akan tsoro da
fargaba!.







Babu jimawa sosai sai gasu baba Nura sun shigo cikin gidan cikeda matuk'ar sanyin jiki da
tashin hankali,,, damuwa ce da bak'in cikin rayuwa da ya bayyana akan fuskokinsu suna zuwa
wurin gawar Fadila sukace "ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un Allahumma ajirni fi musibati
wa'akhalufni khari minha!!.





Baba Nura ne yayi k'arfin halin d'ebo ruwa ya yayyafawa Mama Nafisa da Fatima,,, sannan ya
umurci Fadil da yaje ya sanarda mutane da kuma maigari abinda yake faruwa,,, Fadil ya fice da
saurinsa cikeda k'unar zuciya da tashin hankali!.







Baba Nazifi ya shiga cikin wani yanayi mai cikeda tashin hankali da rikicewa! Ya kasa koda
k'wakk'waran motsi akan ya shiga cikin yanayi mai ban tsoro da tausayi,,, baba Nura yaja
hannunsa ya zaunar dashi sannan su Mama Nafisa suka farfad'o daga suman da sukayi,,, babu
abinda yake tashi sai shasshekar kukansu cikeda matuk'ar damuwa da bak'in ciki!.

Bada jimawa ba saiga Fadil ya dawo da mutane akayiwa Fadila wanka,,, sannan baba Nura da
baba Nazifi sukayiwa gawar addu'a suna zubar da hawayen tausayin kansu,, Umma Nusaiba
ma tayi mata addu'a itadasu Nabila amma Mama Nafisa kasawa tayi sai kuka takeyi mai cikeda
bak'in ciki da k'uncin rayuwa,, haka dai aka sallaci gawar Fadila bayan angama sallar ne aka
kaita makwancinta na gaskiya!.









Aranar nan iyalan gidansu Fadila sun kwana suna zubarda hawayen rashinta da bak'in ciki
mara misaltuwa,,, ita kanta Fatima da batada lafiya sai kuka takeyi cikin k'unci da bak'in cikin
rayuwa.







_Duniyar kenan Allah ubangiji yasa muyi k'yakk'yawan k'arshe yasa aljanna ce makomarmu_..





*********************





Duk abinda yake faruwa Iya Gwamma tana gani acikin madubin tsafinta,,, babu abinda takeyi

sai k'yalk'yalar dariyar mugunta harda fad'uwa k'asa akan makirci da k'eta,,, saboda murnar ta
kashe Fadila burinta ya cika wani irin farin ruwa ke fitowa daga cikin jikinta sosai ga wata
sansanyar iska mai dad'i da take buso mata,,, babu abinda takeyi sai surutai da tsafe tsafenta
can ta bud'i baki tace "dama na gaya maki ba'a ja da mayyu akwana lafiya,,, saboda haka
yanzu na kasheki na kashe banza sauran k'awayenki suma na gama dasu saboda ni arayuwata
babu tausayi ko sassauci acikinta !".





"amma bari yanzu inje insha iska in dawo sai inzo in d'ora daga inda na tsaya! In kashesu
Fatima Hhhhhh hhhhhh".Inji Iya Gwamma tana gama fad'ar wannan maganar,,, ta b'ace b'at
kamar bata tab'a wanzuwa awannan wurin ba......
[7/12, 1:17 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_

*Maman Ummi ina godiya sosai da soyayyarki gareni matuk'a da kuma halaccinki,,, hak'ik'a ke
masoyiyata ce ta gaskiya kin nunamin k'auna a zahiri,, Allah ubangiji ya saka miki da mafificin
alkhairi kuma ya biya miki buk'atunki na alkhairi.*


*PAGE 31*




Tana b'acewa b'at bata sauka a ko'ina ba sai a can bayan gari cikin d'an daji,,, tana bayyana a
cikin dajin tayita yawonta da shawagi tana d'ebo wasu itacen da zata had'a tayi wani maganin
sihiri,,, bayan ta kamalla d'iban duk abinda takeso daga cikin dajin,,, saita juyo ta fara tafiya
domin komawa gidanta,,, tayi tafiya mai nisa harta kusa shiga cikin gari kwatsam! Babu zato
babu tsammani taga Ummaru d'an Sala mafarauci agabanta kamar an jefosa,,, ta murza
idanunta domin tabbatarwa idan ba mafarki takeyi ba,,, gabanta ya buga da k'arfi rassssss!
Hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai amma ko a fuskarta bata nuna masa ba,,, tayi tsaye tana
jiran taga irin abinda zai faru atsakaninsu. Ummaru ya dubeta yayi murmushin mugunta da jin
dad'i,,, sannan yayi mata walak'antaccen kallo yace "kin gama b'oye b'oyenki da guje gujenki
Gwamma mayya,,, dama na gaya miki idan kere yana yawo zabo ma yana yawo wata rana dole
su had'u,,, saboda haka yanzu nan zan gana miki azaba sannan in shiga dake cikin gari kowa
ya ganki a walak'ance! Sannan in kasheki kamar yadda kike kashe wasu ".Iya Gwamma ta
bushe da mahaukaciyar dariya sosai sannan tace "Ummaru kenan ka d'auka kasheni abu ne
mai sauk'i awurinka,,,ko ubanka Sala mafarauci na kashesa cikin sauk'i bale kai! Saboda haka
k'aryarka tasha k'arya ka kaini a walak'ance cikin mutane,,, saina gana maka azabar da baka
tab'a shanta ba a rayuwarka! "."yimin shiru bak'ar annoba dangin tsiya,,,, idan kin saba kashe
mutane acikin sauk'i,, toni naci dubu sai ceto ba zaki iya jadani ba Gwamma azzaluma
macuciya mai cin naman mutane da aljannu! ".Cewar Ummaru d'an Sala mafarauci cikeda
matuk'ar hasala,,, Iya Gwamma ta dubesa da idanunta jawur kamar barkono,, jijiyoyin kanta
suka tashi tsaye rud'u rud'u akan b'acin rai k'arara tace "hak'ik'a ka tafka babban kuskure daka
tunkareni gaba da gaba,, yau zan shayar dakai d'acin mutuwa ayau sai dai uwarka ta haifi wani
amma ba kai ba! ".Ummaru ya harareta yace "sai an gwada akan san na k'warai,, saboda haka
yau zan gabatar dake durk'ushe agaban mutane domin kowa yasan Gwamma mayya,,
shahararra azzaluma mara imani azuciyarta ".Kai! Ya isheka ayau zakasan ka zageni saikabi
ubanka acan lahira! In yaso ka iskosa acan barzahu! "Cewar Iya Gwamma cikeda hasala da jin
haushi,,, Ummaru yace "karki kuskura ki gayamin maganar banza shegiyar karuwa! Annobar
gari k'are dangi,,, wadda tayi abin kunya acikin gari ".

"yanzu kuwa zan nuna maka ainahin wa ce ce Gwamma ".Ta rufe bakinta ta afka masa suka
rungutsume da azababban fad'a mai cikeda tashin hankali da bala'i! Naushin juna da bugun
juna kawai sukeyi cikeda matuk'ar dauriya da zafin nama,,, Ummaru yana amfani da takobinsa
domin ya kare kansa yayinda Gwamma ke jifarsa da ababen tsafi irinsu wuk'a,, mashi,, wuta,,
kibiyoyi da dai sauran abubuwan mugunta iri iri daban daban,,, da bala'i yayi bala'i ta dinga feso
masa wuta jawur yana kaucewa,, ta k'ara karanta d'alamisai na tsafi wata irin bak'ar guguwa ta
bayyana,, ta d'auki Ummaru tana hajijiya dashi asama yasha wuya sosai sannan yayi wata
addu'a,,, guguwar ta b'ace b'at kamar k'iftawa da bismillah,, ganin haka ne yasa ta k'ara yin
wani sihirin k'aton rami da macizai ya bayyana a tsakiyarsu! Yana bayyana igiyar tsafi ta fito
daga cikin ramin ta d'aure k'afafun Ummaru tana jansa da k'arfi,, yasha bak'ar wuya sosai
sannan yayi wata addu'ar ramin ya b'ace b'at kamar bai tab'a wanzuwa ba! Iya Gwamma ganin
ya tsira ne yasa ta k'ara harzuk'a da hasala ta feso masa ruwa tafasasshi suka zuba ajikinsa!
Ummaru yayi kuwwa da kururuwar da k'arfi akan zafi da rad'ad'in ciwon ruwan zafi,, fatarsa
jikinsa ta fara kwayewa akan masifa ganin ya fad'i d'immmmm ak'asa yasa Iya Gwamma ta
bushe da mahaukaciyar dariya sosai tace "bazaka iya ja dani ba Ummaru,,, ubanka ma baisha
d'a dad'i ba a wajena! ".Tana gama yin magana ya taso cikeda matuk'ar zafin nama ya naushi
fuskar Iya Gwamma cikin shammata,, ai kuwa ta fasa gigitacciyar k'ara da kuwwa da k'arfi!
Bakinta ya fashe da jini tasa hannunta ta lakato jinin dake zuba daga cikin bakinta,, tana ganin
abinda ya faru da ita rayuwarta ta k'ara b'aci idanunta suka k'ara ja ta girgiza sannan ta rikid'a ta
koma gwaggon biri,,, ta sake afkawa Ummaru suka sake rungutsumewa da wani rikitaccen fad'a
cike da bak'in rai da mugun nufi! Dajin gaba d'aya ya kama girgiza da rawa tanbal tanbal kamar
zai kife acikin k'asa,, masifa tayi masifa bala'i yayi bala'i dajin gaba d'ayansa ya kama da wuta
yana k'onewa,,,tsuntsaye da dabbobi sai hijira sukeyi suna barin dajin baki d'ayansa.






Haka dai suka cigaba da azababben fad'a cikeda tashin hankali! Ummaru ganin wankin hulla
zai kaishi dare yasa ya k'ara k'aimi,, tareda tattaro dauriya da zafin namansa ya chanza salon
fad'ansa nan da nan ya rikita hankalin Iya Gwamma,, ya samu ya yanketa a cinyar k'afar dama
ihu da kururuwar Gwamma kawai kakeji ta fad'i k'asa cikeda matuk'ar zafi da rad'ad'in ciwo!
Ummaru yayi hanzari da sauri yasa igiya ya d'aure Gwamma,,,, ya d'auketa ya azata saman
kafad'unsa ya nufi hanyar zuwa cikin gari fadar maigari Garba.





********************

Alhaji Suleiman da Mama Sa'ima sunje gaisuwar rasuwar Fadila cikeda jimamin mutuwa da
sanyin jiki,, anan ne suke k'ara jajantawa juna hak'ik'a Mama Nafisa tayi matuk'ar basu tausayi
sosai,,, saboda duk ta fita acikin hayyacinta kallo d'aya zaka yi mata kasan tana cikin rad'ad'in
zafin mutuwar Fadila,, anan ne Alhaji Suleiman yake sanarda baba Nura akwai Malam Usama
da zaizo gidansa yayiwa su Fatima magani,,, baba Nura ya nuna babu matsala ya umurci Fadil
daya d'auki Fatima ya sanyata cikin motar Alhaji Suleiman,, Fadil ya d'auki fatima ya sanyata
cikin motar baban Maryam,, shima ya zauna bayan motar rungume da Fatima Alhaji Suleiman
yaja motarsa suka wuce direct zuwa gida.
Ya parker motarsa a waje sannan suka fito daga cikin motar gaba d'ayansu,, Fadil ya d'auko
Fatima daga cikin motar suka nufi cikin gidan suna shiga suka iske Malam Usama zaune,, Alhaji
Suleiman yayi murmushi tareda bayyanar da farin cikinsa da fara'arsa,, yaje wurin Malam
Usama sukayi musabaha da sallama da juna,, Mama Sa'ima ta shige cikin d'akinta.





Malam Usama ya aje casbaharsa da qur'ani agefe,,, ya kalli Alhaji Suleiman yace "akawomin
ruwa masu tsabta yanzun nan ".





Alhaji Suleiman yace" to Malam Fadil jeka ka kira Maman Maryam sannan kace tazo da ruwa
masu k'yau".







Fadil yace "to baba ".Tareda mik'ewa tsaye ya nufi hanyar zuwa d'akin Mama Sa'ima,, babu
jimawa sosai saiga Mama Sa'ima ta fito tareda Fadil d'auke da jug d'in ruwa a hannunta,, suna
isowa ta aje ruwan agaban Malam Usama ta koma gefe ta zauna.

Malam Usama ya d'auki ruwan ya fara karatun qur'ani da addu'o'i na tsari da sihiri,, ya jima
sosai yana yin addu'ar sannan daga baya ya tsaya ya d'auko gagarin maganin ya zuba acikin
ruwan yana jijjigewa da sauri,,, yana gama jijjigar ruwan maganin ya watsasu ajikin Maryam da
Fatima ,,,ai kuwa batare da b'ata lokaci ba sukayi wani irin gigitacciyar k'ara da kuwwa da k'arfi!
Suka kama zabure zabure da shure shuren zafin magani,,, Malam Usama ya cigaba da yi musu
karatun qur'ani da addu'o'i kala kala,,, kuwwa da kururuwarsu Maryam kawai ke tashi acikin
parlourn su Mama Sa'ima jikinsu sai rawar tsoro yakeyi itada Fadil cikeda matuk'ar firgita da
fargaba! Ya dad'e sosai yana yi musu karatu sannan daga baya kowacessu tayi atishawa da
k'arfi sau uku nan da nan barci ya d'aukesu batare da b'ata lokaci ba.







Malam Usama yayi murmushi sannan yace "Alhmdlilah yaran sun samu lafiya Alhaji Suleiman
dama mayya ce ta kamasu,,, sannan ta had'asu da miyagun aljanu domin kada suyi saurin
samun waraka,, yanzu dai godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikkai wanda ya bani ikon k'ona
aljannu da yardar Allah,,,, shikenan da sun tashi daga barci sun warke har abada,,, zan basu
wani turare da garin maganin da zasu cigaba da shafawa garin kuma wanka akeyi dashi ".Yasa
hannun cikin leda ya d'auko turare kwalba biyu garin magani leda biyu,,, kowacce su d'ai d'aya.









Tsananin farin ciki da murna ne suka bayyana a fuskokinsu k'arara mara misaltuwa,, Mama
Sa'ima hawayen dad'i ne suka cigaba da kwaranya daga cikin idanunta,, Fadil ma sai kwallar
murna yake fitarwa,, Mubarak daya shigo ayanzu cikin parlour amma yaji abinda Malam ya
fad'a bakinsa yak'i rufawa akan murna da farin ciki sosai,, ya samu wuri kusa ga Fadil ya zauna
fuskarsa d'auke da farin ciki da nishad'i sosai.

Alhaji Suleiman akan farin cikin dake d'auke afuskarsa har rungume Malam Usama yayi yanata
zuba masa godiya,,, tareda da kwararo masa addu'o'i na gamawa lafiya. Can ya bud'i baki yace
"hak'ik'a godiya ta tabbata ga Allah ubangijin sammai da k'assai wanda yake sanya ciwo
alokacin da yaso,, sannan ya warkar da bawa aduk lokacin da yaga dama,, Malam Usama mun
gode sosai Allah ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairi yasa ka gama da duniya lafiya ".








Gaba d'ayansu yan parlourn sukace "amin amin ".Fuskokinsu d'auke da farin ciki da nishad'i
sosai k'arara,, daga gani babu tambaya kasan suna cikin jin dad'i da farin ciki sosai.








"wannan ba wani abu bane Alhaji ai an zama d'aya,, Allah ubangiji dai ya tsare gaba ni yanzu
zan wuce zuwa gida ".Ya aje ledar maganin ya tashi tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin
parlorn,, Alhaji Suleiman ne ya bisa a baya domin yayi masa rakiya,, bayan sunje waje ne Alhaji
Suleiman ya bashi kud'i masu yawa wanda shi kansa baisan ko nawa bane,, dak'yar Malam
Usama ya amsa sannan sukayi sallama da juna ya shige cikin motarsa,, Alhaji Suleiman shi ko
ya juya zuwa cikin gidansa fuskarsa d'auke da farin ciki da annashuwa mara misaltuwa.

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤






Ummaru d'an Sala mafarauci d'auke da Iya Gwamma akafad'arsa,, ya kawota ya ajeta saman
k'asa agarkar maigari Garba cikin halin somewa,, jini sai zuba yakeyi daga cinyarta yana ajeta
saman k'asa,, ya shiga cikin gidan maigari ya jima sosai sannan suka fito tareda da maigari da
dogarawansa,, nan da nan maigari yasa akayi sanarwa acikin gari kowa da kowa ya taru mata
da maza,,, yara da manya da tsofaffi,, bayan mutane gaba d'aya sun gama taruwa wani dogari
ya ciko bokiti da ruwa aka juyesu ajikin Iya Gwamma mayya,,, batare da b'ata lokaci ba ta
farfad'o daga suman da tayi jikinta d'aure da igiya,, kallon mutane kawai takeyi d'aya bayan
d'aya,,,Maigari ne yayi gyaran murya sannan yace "muna godiya ga Allah daya bama Ummaru
nasarar kama wannan k'usurgumar mayya wadda ta addabi rayuwar mutanen gari shekara da
shekaru,, ta dad'e tana cin amana da zaluntar mutane da dama ta kashe mana
iyaye,,mata,,,,'yan uwa,,, yara da abokan arzik'i,,,, dama duk abinda kakeyi wata rana sai
dubunka ya cika komai yayi farko k'arshensa yana nan zuwa,,, mai hak'uri mawadaci ne saboda
haka gashi yanxu Allah ya tona asirin Gwamma an kamata !Dama na gaya muku duk wadda
/wanda aka kama yana yin maita hukuncin kisa shine ya kamacesa,,, saboda haka yanzu nan
za'a yankewa Gwamma hukunci dai dai da abinda ta aikata,, ina dogari Tukur ne yake? ".






Tukur ya matso da sauri kusa ga maigari ya durk'usa yace "gani rankashi dad'e ".





"kaje cikin gida ka d'auko fetur da tayar mota yanzun nan ka kawomin ".Inji maigari. Tukur yace
"angama ranka ya dad'e ".Ya mike zubur da saurinsa ya shige cikin gidan maigari Garba.






.

Maigari ne ya bada umurnin a d'auki Iya Gwamma amatsa da ita kusaga icce a d'aureta,, nan
da nan aka cika umurnin maigari tareda daureta tamau ga icce,, Iya Gwamma sai kuwwa da
kururuwa takeyi tana cewa "ku sakeni ku sakeni wallahi idan na kwance kaina duk saina
kasheku,, saina kasheku ! Nayi alk'awarin bazan bar ko d'aya daga cikinku ya rayu yaji dad'i
ba,, Garba tsohon munafiki dakai zan fara kaida shegen yaron nan Ummaru! ".Haka dai suka
d'auketa d'aureta ga iccen,, bada jimawa ba saiga Tukur ya fito da tayar mota da fetur yana
kawowa Ummaru ya amshi tayar da fetur,,, ya sanyawa Gwamma taya a wuya sannan ya
dubeta yana murmushin mugunta yace"dama na gaya maki duk daren dad'ewa saina kamaki da
hannuna,, shiyasa akeson mutum ya kasance mai aikata alkhairi akodayaushe akowane lokaci
baki tab'a jin ance gaskiyarka ta k'are ba,, sai dai ace k'aryarka ta k'are saboda haka yanzu nan
zan aikaki can inda kika saba aika mutane da dama ".Gwamma ta kama kuwwa da k'arfi tana
kuka tana cewa "wallahi baka isa ba nice zan kasheka da hannuna,, saina kashe duka mutanen
garin nan saboda su suka duka munafukan......... ".Bata k'arasa maganar ba ya kyasta ashana
tareda zuba mata fetur ajiki,,, Iya Gwamma ta saki wani irin gigitaccen kuka tana cewa "kada ku
kasheni wallahi duk sainaga bayanku,,, saina zare muku rai daga cikin gangar jikinku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login