Showing 12001 words to 15000 words out of 58121 words

Chapter 5 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

12 Jul 2025

2940

kawo,, domin
gudun sata ko afkuwar wani abu mara k'yawon gani..



**** **** **** ****





***Ab'angarensu Lado da Idi abokinsa kuwa bayan Lado ya jima sosai a wurinsa suna fira,,, to
zuwa wani lokaci mai tsawo yayi masa sallama zai wuce gidansa,,, Idi yaji dad'i sosai na ziyarar
da abokinsa ya kawo masa ya d'auko sabulun wanka da na wanki yace akaima Hassi,,,,Lado
yak'i amsa sai da Idi ya nuna matuk'ar b'acin ranshi sannan ya amsa da k'yar yana yi masa
godiya sosai,, Idi ya nuna masa babu komai ai yi ma kaine kuma maida k'yauta baya ne ka
tsinceshi acan gaba ne,, Lado yayi masa sallama sannan ya juya zuwa hanyar gidansa cikeda
matuk'ar sanyin jiki..

Hassi ce zaune saman kujera k'arama tana cin abinci,, bayan ta gama kukanta tun d'azu babu
abinda takeyi sai tunani da zullumin maganar Lado,,, ta ga Lado bai yarda da maganarta ba
balantana ayima abun tufkar hanci shiyasa ta bar abin cikin ranta,,,, da niyar gobe zata tambayi
Lado iznin zuwa gidansu ta sanar da iyayenta duk abinda ake ciki..




Haka dai ta cigaba da sak'a da warwara a cikin zuciyarta,,, tana cin abincinta sosai can naji
takun tafiyar Lado ya shigo da sallama a bakinsa,, hannunsa rik'e da ledar sabulun da Idi ya
bashi,,, Hassi ta amsa masa sallamar tareda juyar da kanta gefe saboda a d'azu taji matuk'ar
haushin akan yadda yak'i yarda da maganarta,,, tareda da nuna mata halin ko in kula da tana
kuka akan abinda ya faru..



Lado ya d'auko tabarma ya shimfid'a kusa gareta,, sannan ya zauna yana fuskantarta yace
"Innar Na'ima dan Allah kiyi hak'uri ki daina fushi dani,,, in dai akan abinda ya faru ne wlh na
yarda da maganarki na amince muje gidanku anemi mafita ".





Hassi ta juyo tana kallonsa tace "hmm naji komai ya wuce amma ni bance dole sai ka yarda da
maganata ba ".





"ki dai yi hak'uri Allah yana tare da masu hak'uri Hassi,, alal hak'ik'a nasan akwai mayyu a cikin
garin nan addu'a kawai ce mafita akan kowane lamari,, ina Na'ima take ne? Na ji banji muryarta
ba ".Inji Lado cikeda lalama.






Hassi tace "haka ne gaskiya,, Na'ima an aiko daga gidanmu an d'auketa ".

Lado ya bata ledar da ke hannunsa sannan yace "to ya yi k'yau kice yau zasu sha rashin ji da
b'arna,, wannan ledar da nazo da ita Idi yace a baki ".






Hassi ta bud'e ledar ta ga sabulun wanka da wanki,, murmushi kawai takeyi can ta nisa tace"ai
kuwa mun gode sosai Allah ubangiji yabar k'auna da zumunci,,, sannan da kake cewa Na'ima
rashin ji gareta ai acan gidanmu ustaziya ta ke zama,, idan ba haka idan tayi musu b'arna
Mariya kashi take bata saboda ita babu ruwanta da yaro "..




"Amin ya rabbi matata,, ai kuwa idan ta bugar min Na'imata zamu had'u gobe ni da ita".Cewar
Lado.




Hassi ta yi dariya tace "ina zaka ga Mariya kuma? Balantana ka had'u da ita ".





Lado yace "gidan zamuje gobe da ni da ke idan Allah ya yarda ".




Hassi tace "Allah ya kaimu gobe lafiya ".

"Amin amin ".Cewar Lado..




Hassi ta mik'e tsaye ta shiga cikin d'akinta,, ta kawo masa abincinsa da ruwa masu sanyi cikin
jug ta aje gabansa,,, Lado ya wanke hannunsa da ruwa sannan yayi bismillah ya fara cin
abincinsa cike da natsuwa da walwala,,, Hassi tana gefensa sai murmushi takeyi masa cike so
da k'auna..





*********************




Malam Mamman ne zaune yana wankin kayansa ga Inna Talatu xaune gefe tana kallonsa,,, sai
harararsa takeyi tana yatsina fuskarta cikin gadara da nuna isa,,, can Malam Mamman ya
dubeta duba na fahimta da natsuwa yace "Talatu wai mi ye dalilin abubuwan da kike yimin,,, mi
nayi miki ne? Na ga kina yimin wasu abubuwa wad'anda bana jin dad'insu ".




Inna Talatu tace "hmmmm kai dai Mamman kanada matsala,,, ka sha tambayata nace baka
yimin komai ba kawai rayuwa ce ta canza ,,amma kazo kana son matsa min da surutu ".





Malam Mamman yace "ba damuwarki nake sonyi ba,,, ina son zamanmu ne ya koma kamar da
babu tashin hankali ko hayaniya a cikinsa,, kuma bansan abinda nayi miki ba Talatu duk kin
tsane ni kamar auren dole akayi miki tun farko bada son ranki ba akayi auren ba kina sona ina
sonki ".

"hmmmmmmm Mamman ka gama tatsuniyar taka to bari kaji! Ni fa yanzu ba da ba ne babu
shegen da ya isa ya takura min,,, saboda ayanzu bana tsoron kowa ciki kuwa har da kai domin
na yi wuya na isa yanka! ".Inji Inna Talatu.




Malam Mamman ya cigaba da wankinsa yana shanyawa ga igiyar wanki,, bayan ya gama
shanya kayansa ya dubi Inna Talatu cikin tsananin b'acin rai da takaicin maganarta,,, yace
"Talatu ina son ki san wani abu guda d'aya naji ke baki tsoron kowa,, karki manta ni fa mijinki ne
aljannarki tana k'ark'ashin tafin k'afata idan na d'aga ki shiga ciki,,, idan na ta ke ba zaki shiga
aljanna ba,,, ya kamata ki san irin maganganun da za ki gaya min ba wai ki dinga yimin magana
tsauri tsauri ba kamar ke ce mijin ni ne matar,,, mace ta iya magana da tausasa kalamanta
zuwa ga mijinta ba wai ta dinga sako magana duk yadda ta gadama ba,, ni fa bari in gaya maki
kin isheni gaskiya! Ina raga miki ne saboda darajar 'ya'yan dake tsakaninmu ba wai domin ina
jin tsoronki ba ".







"ahayyeh ahayyeh nanayeh yau naji maganar banza da yofi! Ai ban san kana jin haushina ba
Mamman sai kayi min mugun bugu ka sakeni,,, sannan da kake cewa sai ka d'aga k'afarka
sannan in shiga aljanna to bana so ka take!!! Yanzu idan na mutu kazo ka kaini cikin wuta to wlh
rashin kwanciyar hankali da rashin zaman lafiya yanzu aka fara a cikin gidan nan ".Cewar Inna
Talatu cikeda matuk'ar masifa da son tashin hankali.






Malam Mamman yace "ba ni zan kaiki wuta ba mugun halinki ne zai kaiki cikin wuta,,,, saboda
haka to tunda abin naki bana arzik'i ba ne,,, ba zai yiyu in ta zama cikin rashin kwanciyar
hankali da tashin hankali ba saboda haka ki saurareni da k'yau Talatu aure zan k'ara yi! ".

Dummmm gaban Inna Talatu ya buga da k'arfi!,, zuciyarta ta girgiza hankalinta yayi k'ololuwar
tashi sosai,,,babu abinda zuciyarta keyi sai bugawa da k'arfi da k'arfi amma dolenta ta tattaro
natsuwarta da dauriya ta sanyama zuciyarta,, saboda kada Malam Mamman yayi saurin gano ta
firgita ko tsorata..



Cikin dauriya da nuna rashin tsoro Inna Talatu tace "Mamman kenan k'aryarka ta sha k'arya
tunda dad'ewa sosai baka tashi cewa zaka yimin kishiya ba sai yanzu! To wlh daga yau ka k'ulla
aure da masifa da tashin hankali,,, kuma wannan auren ba zai tab'a yiyuwa ba! Amma dan Allah
ka gwada ka gani idan ka na shakkar maganata ba zata iya yiyuwa ba,,, zan nuna maka ni
kishina yafi *KISHIN JAHILCI*".





Malam Mamman yace "mi zaki iya yi ne Talatu ai ko haukacewa zakiyi kibi duniya,,, sai na k'ara
aure Insha Allahu idan kika ga banyi ba to mutuwa na yi mahaukaciya wadda batasan ciwon
kanta ba ".





"mahaukata dai ga fili ga mai doki nan sauran sukuwa,,, kayi auren in gani ba sai kana raye
zakayi auren ba ko? Zan nuna maka ni na haifu ga iyayena ".Inji Inna Talatu cikeda matuk'ar
masifa..





"duk abinda zakiyi Allah ya fiki Talatu aure ne dai sai nayi,,, ina raye zaki gani da idanunki!
".Cewar Malam Mamman yaja takalminsa ya barma Inna Talatu gidan tana ta fad'a da tsinema
Malam Mamman..

Inna Talatu ta kama yin fad'a da zage zage kamar ta ari bakin kura,,, bakinta har kumfa yake
fitarwa akan bala'i idanunta suka rikid'a sukayi jajir saboda tsabar tashin hankali da bala'in da
suka bayyana k'arara akan fuskarta..





Ta sha alwashin babu ita babu zama da kishiya har abada,,, ta yanke shawarar irin matakin da
zata d'auka a cikin zuciyarta!!!.






**********************




***Washe gari da da rana misalin k'arfe hud'u 4:30pm na yamma,,, Lado da Hassi suka shirya
suka je can gidansu Hassi ziyara,,, bayan sun je gidansu Hassi lafiya k'alau suka iske Baba
Abubakar da Inna Lami sun gaishesu cikin girmamawa,,, suka amsa musu fuskarsu a sake cikin
fara'a da murna sosai. Mariya da take gefe tareda Na'ima ta gaisar da su Hassi,,, suka amsa
mata cikin sakin fuska da walwala,,, Mariya ce ta d'auko tabarma ta shimfid'a musu suka zauna
tare..





Hassi ce ta duk'ar da kanta k'asa tace "baba mun same ku Lafiya ".





"lafiya k'alau kuka same mu Hafsa ".Cewar Baba Abubakar.



Inna Lami tace "ina fatar kina zaune da mijinki lafiya Hafsa? ".

Lado yayi saurin yin magana yace "ai Hassi 'yar aljanna ce Inna tana yimin ladabi da biyayya
gwargwadon iyawarta,,, bata son b'acin raina ko fushina ko kad'an ban tab'a ganin mace mai
k'yawon hali ba irin Hassi ba,,, duk abinda nake so shi ta keyi min koda ace ita bata so Baba ai
ni banida abinda zan biya ku dashi na aura min Hafsa da kukayi,, sai dai inyi muku addu'a akan
Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairi ".




Mariya tace "Amin ya rabbi ".Cike da tsananin jin dad'i akan yadda aka yabi halayyar 'yar
uwarta.





Baba Abubakar da Inna Lami babu abinda sukeyi sai murmushi tsantsar farin ciki ne da jin dad'i
yake bayyana a fuskarsu,,, can dai Baba Abubakar yace "na ji dad'i matuk'a akan irin yabon da
mijinki yayi miki Hafsa,,, hak'ik'a na k'ara tabbatarwa yau ba ki yassuwa tarbiyar da nayi miki
ba,,, kai ma Lado nayi matuk'ar farin ciki akan yadda ka rik'eta amana,,, Allah ubangiji yayi
muku albarka ".




Hassi tace "Amin Baba amma akwai maganar da nake son in gaya maka ".




"wa ce irin magana ce Hafsa? fad'i ina saurarenki".Cewar Baban.




Hassi zata bud'i baki ta yi magana kenan! Kawai sai naga Lado ya fad'i k'asa kwance yana
birgima kamar mahaukaci,,, babu abinda ke fita cikin bakinsa sai jini mai kamar tsokar nama

gunduwa gunduwa,,, yana shure -shure da kakarin mutuwa!


Baba Abubakar da Inna Lami babu abinda suke fad'a illa ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Cikeda
matuk'ar tashin hankali da rikicewa,,, Hassi kuma kuwwa ta yi da k'arfi tana kuka tana cewa
"wayyo Allah wayyo kaina! Shikenan ta kashe min mijina,, rayuwata tazo k'arshe ni Hassi ".Wa
ce ce ta kashe miki mijinki ".Inji Inna Lami cikeda matuk'ar tashin hankali!.

Hassi ta sakewa cewa "ta kashe min mijina! ".Ta fasa wata gigitacciyar k'ara da kuwwa da k'arfi!
Ta fad'i k'asa ta sume,,,ai kuwa Inna Lami da Mariya suka sake rikicewa Na'ima banda
mahaukacin kuka babu abinda takeyi,, Baba Abubakar da ya ke kusa ga gawar Lado shi ma
duk ya rikice ya ya mutse kamar ba babban mutum ba.
Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Kawai yake ambato cike da tsananin rud'ewa da d'imaucewa.....










_Share&Comments_
[6/21, 9:56 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_

*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 9*



Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Kawai yake ambato cike da tsananin rud'ewa da d'imaucewa..



Hankalinshi ya yi k'ololuwar tashi duk ya gigice da rikicewa,,, Inna Lami ce yayi mata alama da
hannu ta d'ebo ruwa a cikin buta ko kofi ,,, ta nufi randar ruwa da saurinta cikin matuk'ar tashin
hankali tana ta kukan k'unci da bak'in cikin rayuwa,,,Mariya kuma sai jijigar jikin Hassi takeyi
tana zubar da hawayen tausayin kansu da bak'in ciki.



Na'ima tana gefenta tana kuka sai cewa take yi "Inna,, Inna ci ta ci dan anya (Inna ki tashi dan
Allah) ".






Inna Lami ta kawo ruwan da saurinta Malam Abubakar ya amshi ruwan ya yi addu'a mai
tsawo,,, sannan ya watsa ma Hassi rabin ruwan ya juyo wurin Lado ya watsa mishi ruwan
shima,, sannan yayi umurni da Mariya ta shige da Na'ima cikin d'aki ,,dole ne yasa Mariya taja
hannun Na'ima ta shige da ita cikin d'aki ba domin ranta yaso ba saboda ita taso ayi komai gaba

gare ta,,, ba sai ta tashi ba amma yata iya dole ta bi umurnin mahaifinta..






Bayan shigerwarsu Mariya cikin d'aki ba,,,, Malam Abubakar ya dubi Inna Lami yaga tana zubar
da hawaye yayi mata nuni da ta matso kusa gareshi,,, Inna Lami ta matso kusa gareshi jikinta
yanata rawar tsoro da fargabar abinda ke iya faruwa! Malam ya juyo da fuskar Lado ta yadda
zasu b'ullo ma lamarin cikin sauk'i,,, yana juyo da fuskarshi yaga duk idanun Lado sun k'ak'k'afe
ga kuma jinin da ya b'ata gaban rigarsa babu k'yawon gani ko kallo,,, yasa kunnenshi ya tara a
hancin Lado yaji ya ko zaiji yana numfashi..






Ya kai tsawon minti goma yana saurare ko zaiji fitar numfashin Lado amma shiru,,, kamar an
shukka dussa ganin haka ne Malam ya d'ago idanunsa wad'anda ruwa sun taru ciki sosai ya
dubi Inna Lami cikin matuk'ar sanyin jiki da damuwa,,, yace "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!!
Kulli nafsin za'ikatul mautt hak'ik'a Allah ubangiji yayi ma Lado rasuwa Lami! ".Gaban Inna Lami
ya buga da k'arfi rassssss! Fuskarta na bayyanar da tsoro da tsananin tashin hankali,,, dak'yar
ta bud'i baki tace "Subahanillah! Allah ubangiji ya jik'anshi da rahama yasa ya huta,,, mu kuma
idan tamu tazo yasa mu cika da imani Malam ".





"Amin Lami ".Cewar alokacin ne yasa hannunsa ya shafe idanun Lado..




Inna Lami tana shesshekar kuka tace "Malam fa ya kamata kaje ka sanar da iyayensa da
mutane,,, domin ayi masa wanka akaishi makwancinsa ".




"tabbas haka ne yanzu nan kuwa zan je in sanar da iyayensa da kuma mutane ".Inji Malam

Abubakar ya fad'a tare da mik'ewa tsaye,,, ya kama hanya ya wucewarsa zuwa waje..






Inna Lami na zaune ta zuba uban tagumi tana kuka mai ban tausayi da tarin damuwa,,, can
Hassi taja numfashi tari ne ya sark'eta ta falko daga suman da ta yi,,, Inna Lami tayi hamdala
cikin zuciyarta ta k'walama Mariya kira,,, Mariya ta shek'o da saurinta Inna Lami tace ta d'ebo
ruwa aba Hassi ta sha taje da saurinta ta d'ebo ruwa a randa masu sanyi aka bama Hassi
tasha,,, sai sannu kawai sukeyi mata cike da matuk'ar tausayawa. Bayan ta sha ruwan ne Hassi
ta kwanta babu jimawa barci ya kwasheta,,, Inna Lami ta dubi Mariya tace "tashi ki shiga cikin
d'aki kada Na'ima ta biyoki waje,,, saboda ta yi k'arama da ganin wannan tashin hankali ".





"ai Inna Na'ima tun d'azu ta yi barci fa,,, shiyasa ma kika daina jiyo kukanta ".Cewar Mariya..





Inna Lami tace "to Allah ya k'yauta ".






Mariya tace"amin".Tana rufe bakinta sai ga sallamar mutane su hud'u,,, sun shigo cikin gidan
Inna Lami ce ta amsa musu sallama, Malam Abubakar yayi musu jagora har cikin gidan suka
d'auki gawar Lado suka fita da ita waje,,, domin aje gidan mahaifinsa ayi masa wanka akaishi
gidan gaskiya..





Suna tafiya da gawar Inna Lami da Mariya suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi da

tsuma zuciyar mai sauraro,,, tausayin Hassi da Na'ima ya k'ara d'arsuwa a cikin zuk'atansu,,,
Hassi ta zama k'aramar bazawara yayinda Na'ima ta zama marainiya abar tausayi...






*** *** *** *** *** **






***Anje an yima Lado wanka da sanyashi cikin likkafani,,, anyi masa sallah sannan aka kaishi
makwancinsa.. *(Allahu Akbar duniya kenan rai bak'on duniya ,,,mutum ba'a bakin komai yake
ba a cikin wannan duniyar mai cike da k'unci da bak'in cikin rayuwa )*...





Kwatsam! Bayan mutuwar Lado sai da mutum kusan hud'u suka rasu a rana guda,,, mace uku
maza biyu gami da Lado hak'ik'a a wannan ranar mutanen sun shiga tashin hankali da rikicewa!
Akan mutuwarsu Lado ko'ina ka diba mutane ne zaune suna bak'in ciki da jimamin rasa 'yan
uwansu,,, mata da yara k'anana kuka kawai sukeyi cike da tsananin damuwa da bak'in cikin
rayuwa,,, to ya zasuyi wanda yafi sonsu ya k'arbi ran abinsa dama ita duniya haka ta gada
hak'uri shi ne kan gaba da komai,,,, shi ne kuma jigon rayuwa ko munk'i ko munso dole wata
rana za'a wayi gari babu mu cikin wannan duniya mai cike da k'alubalen rayuwa ".(Allah ubangiji
yasa mu cika da imani muna musulmai)...




_Kunga kenan babu abinda ya gagari mayyu,,, sai dai ikon Allah_..






*BAYAN KWANA HU'DU*

***Bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login