Showing 18001 words to 21000 words out of 58121 words

Chapter 7 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

12 Jul 2025

2931

masa addu'ar fatan
alkhairi a cikin auren da zaiyi,,, haka ya nufo gidansa cikin farin ciki da walwalarsa,, bayan ya
shigo cikin gidan tareda sallama a bakinsa ya samu wuri ya zauna yace "Talatu albishirinki ".





Inna Talatu ta hararesa sannan tace "dallah rufamin bakinka tsohon munafiki! Azzalumi maciyi
amana,, wato kazo ne kayimin albishir da ka kusa zama ango ko to ai kana bari har a d'aura
auren bawai kazo kana yimin cika bakin banza!! Zaka gani idan zakayi auren ayi dai mu gani
idan tusa zata hura wuta ".






Yace mata "haukarki ko kishinki na jahilci baya tayar mini da hankali aure ne kamar an d'aura

kina gani da idonki,,, saboda haka ki iya tsabtace kalamanki zuwa gareni Talatu ".







Inna Talatu ta juyo ta dubeshi da jajayen idanunta b'acin rai k'arara akan fuskarta ta
bayyana,,,tace masa cike da jin haushin maganarsa "bakasan wa ce ce ainahin Talatu ba
ganina kawai kakeyi Mamman,,amma zan nuna maka banbanci a tsakanin suga da gishiri
zakasan ni ba sakaryar mace ba ce da zata zauna da kishiya,,, wannan auren ba komai ba ne a
wurina da ya wuce rusasshe ".





"ba zaki iya ba Talatu aurena kumada Lawiza kamar an d'aura ne ".Cewar Mal. Mamman.






Inna Talatu ta bushe da mahaukaciyar dariya sannan tace "zaka ko gani lokaci ne kawai zai
tabbatar da zan iya ko bazan iya ba amma zaka gani da idanunka idan wannan munafikin auren
naku zai yiyu! "......










_Share &Comments_
[6/21, 9:56 PM] Mugiratmusa66:






*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 11*





Inna Talatu ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai sannan tace "zaka ko gani lokaci ne kawai
zai iya tabbatar da zan iya ko bazan iya ba,, amma zaka gani da idanunka idan wannan
munafikin auren naku zai yiyu! Kuma yanzu ka cigaba da fuskantar barazana da tashin hankali
kenan har abada a cikin rayuwarka Mamman,,, saina nuna maka ainahin mummunan
halayyarta sai ka gwammace ma kid'i da karatu saina wargaza duk wani farin ciki naka! ".

Mal.Mamman yace "ni surutunki ko haukarki baya tayarmin da hankali,,, sannan farin ciki yanzu
na fara kasancewa a cikinsa gida dai nawa ne inada ikon in auri mace d'ai d'ai har guda uku
bayan ke Talatu,, domin ba gidanki ba ne nawa ne ko kare na jawoshi na kawoshi cikin gidan
nan baki isa ki koreshi ba bale mace matata uwar yarana masu zuwa ".





"hmm tun yanzu kaje ka d'aukota ku kwana idan har ka cika namiji bak'in jarababbe,,, nifa bana
magana biyu magana d'aya nakeyi tak saboda haka kasha kuruminka angon Lawiza aure dai ko
to kaje kayi! ".Inji Inna Talatu cikin bak'ar magana..








Malam Mamman yace "aiko baki ce ba sainayi aure saboda haka ki daina b'ata miyan bakinki a
banza ".







"naji mijin mace hud'u ".Fad'ar Inna Talatu ta tashi sannu a hankali ta shige cikin kitchen,, tana
cigaba da aikace aikacenta batare da ta k'ara sauraren maganar Mal. Mamman ba..






Shi kuma Malam ganin Inna Talatu ta fita batunsa,, tana aikace aikacenta dole yasa ya mik'e
tsaye yayi shigewarsa cikin d'aki,,, domin yayi barci dama ya gaji sosai...

**********************




Lawwali ne zaune bakin k'ofar gidansu da leda cikeda nama yana ci,,, ga pure water masu
sanyi guda biyu yana sha..




Yana tsakar cin naman saiga Gwamma ta fito daga cikin gidan,,, tana fitowa idanunta ya kai ga
ledar naman da Lawwali keci akan kwad'ayi irin na Gwamma ta fitar da halshe tana lasar baki,,,
sai naga ta matso kusa ga Lawwali tana kallonsa shi kuma ya k'ara juyar da kansa kamar bai
ganta ba tare da tamk'e fuska. Gwamma ta dafa kafad'arsa tace "Lawwali juyo da fuskarka mana nice fa kawai domin ka samu
nama,, zaka juyamin baya ko mi nayi maka ne?".






"aini banma lura da ke ba yaya Gwamma,, to yanzu mi kikeson inyi miki ne? ".Inji Lawwali yana
cigaba da cin naman..







Gwamma tace "ban gane mi nake so kayimin ba ai kasan abinda nake so,, to naman da kakeci
zaka sammini nima in had'iye kwad'ayina ".

"hmm yaya Gwamma kenan har kin manta ko to bari in tuna miki,, ranar nan ba kece kikasa
Innarmu ta dokeni ba harda gaya mata nace mata ita mayya ce,, ta bani mugun kashi har na
suma ke kuma sai dad'i kawai kikeji abinki saboda haka bazan sammiki namana ba ".Cewar
Lawwali..








Gwamma tace "dama inada niyar baka hak'uri k'anena dan Allah kayi hak'uri ka yafemin,,,
abinda ya faru ya riga ya faru wlh bazan sake yi maka munafurci a wurin Inna ba,, muddin ka
bani nama naci kuma ai nasan abinda ake fad'a gaskiya ne Innarmu k'usurgumar *MAYYA CE*,,
kuma babanmu kishiya zaiyi mata saboda mugun halinta da bayada k'yawo kullum kullum ci
masa mutunci takeyi akodayaushe akowane lokaci ".





Lawwali yace "ya isa abar maganar domin ke bakinki bayada linzami,, saura kuma gobe ki
k'ullamin munafurci ko gulma da ko idan kikaga abu a wajena mutuwa zakiyi bazan baki ba,,
saboda haka kiyaye ".







"bazan ma k'ara ba wallahi aini banda kamarka a cikin wannan duniya,,, daga yanzu ko wani
naga zai tab'a min kai sai inda k'arfina ya k'are ".Cewar Gwamma.

Lawwali yace "Allah yasa da gaske kikeyi har cikin zuciyarki ".Sannan ya bata sauran naman da
ya rage da pure water guda,, da sauri Gwamma ta fisge ledar saboda kwad'ayi har miyau ya
fara dalala daga cikin bakinta,,, ta fara d'aukar tsoka biyu tasa cikin bakinta tana ci tana gyad'a
kanta cikeda matuk'ar jin dad'i ..






Sannan tace "da gaske k'anena nagode sosai,, amma fa kada ka fad'ama kowa ka bani nama
naci ".Tana cin naman tana lasar yatsun hannunta..








Lawwali yace"to aini ba irinki ba ne mai tonon asiri,, ni kinga tafiyata nayi wurin wasa kuma
naman da kikaga inaci babane ya sayamin domin kada kiyimin wata fassarar ta daban ".Bai
saurari abinda zata ceba ya k'ara gaba yayi tafiyarsa.






Gwamma tace "ni dai ko satowa kayi ina ruwana muradina shine ni dai inci nama mai dad'i,,,
saboda haka ko naman mutane ne ka samo saina cishi babu abinda ya dameni ".Ta cigaba da
cin naman bayan ta cinye tas tareda lashe takarda da hannunta,, sannan ta sha ruwan pure
water ta kuma wanke hannayenta,,, sannan ta juya tayi cikin gida..

********************






***Inna Talatu ta cigaba da kamun kurwar mutane tana mayarda su fa ra ko kaza,, daga baya ta
gasa naman mutane ko ta cishi hakanan d'anye kullum kullum saita fita kamun kurwa a kowane
lokaci,,, idan ta hango mutum daga nesa ta kama tsura mishi idanu kenan domin tana hango
kayan cikin mutane,,, idan kai ma'aboci yawan addu'a ne da iznin Allah ba zata iya kamaka ba,,
idan mutum ya zama lusari mara son addu'a kallo d'aya ne ta chafke kurwar mutum tayi gaba
da ita.
Haka zataje ta aje kurwar wurin murhu ko wurin randar ruwa masu sanyi,,, idan abin yayi kwana
biyu mutum ya kama tsananin rashin lafiya sosai wani za'a samu jikinsa da sanyi wani ko yayi
mugun zafi kamar garwashi,, to wanda jikinsa yakeda sanyi kurwarsa tana aje ne a wurin randar
ruwa wanda jikinsa yakeda zafi kuma ta aje kurwarsa kusa ga garwashi,, haka mutum zaiji
kamar ana sukar jikinsa allura saboda zafi da rad'ad'in ciwo..








Wani ma idan ya gagari mayyu aljannu suke ba kurwar mutum,, domin a halaka mutum kowa ya
huta.








_Allah ubangiji ya karemu daga muyagun k'addarori da kuma fad'awa tarkon wahala_.

**Kwanakin auren Malam Mamman da Lawiza sai k'ara gabatowa yakeyi,, Inna Talatu kuwa sai
k'ara cin mutunci da tozarci takeyi masa kala kala daban daban,,, ta k'untaceshi ta hana mishi
zama cikin gidan sosai saboda tsabar masifa da fitina irin tata,,, bayada halin ya dad'e k'warai
cikin gidansa batare da sun kachame da rikitaccen fad'a ba. Komai ta d'auko jefarsa takeyi
dashi ba adda ba na wuk'a ba,, harda duwatsu jifarsa takeyi dasu sai ya kauce domin kada tayi
masa illa ko ta halakashi..








Ganin haka ne yasa dole ya rage yawan zama cikin gidansa,, sai dai idan ya dawo daga
kasuwa yayi wanka ya fita can wurin majalisarsu ya zauna,,, idan yaga abokansa sunyi gidansu
su dawo shi sai dai kuma ya k'ara gaba wata majalisar ya zauna,, acan waje zaici abinci yayi
komai sai tsakar ya daidaici tayi barci ya dawo gida,, amma duk da hakan bai tsira ba ashe tana
nan tana jiranshi yana dawowa ta aza mishi ruwan bala'i da masifa tana zage zage,, da yake
yaga dare ne yayi kunnen uwar shaggu da ita yayi kwanciyarshi cikin d'akinsa..







Tayi fad'anta na rashin dalili ta gaji,,, sannan daga baya ta kwanta tana jin haushin rashin kulata
da baiyi ba..

Ana saura kwana uku auren Malam Mamman da Lawiza Kwatsam!! Inna Talatu ta tashi da
tsakar dare,,, misalin k'arfe 12:15am na dare ta girgiza sannan ta karanta wasu d'alamisai na
tsafi da sihiri,, nan da nan wurin ya gameda da bak'ar guguwa da tururin hayak'i,,, guguwar ta
daina yawo ta tsaya cak hayak'in ya shige cikin jikin Inna Talatu ta rikid'a ta koma mage......






Managed it please munada matsalar wutar nefa shiyasa.











_Share&Comments_
[6/21, 9:56 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_

*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 12*





Inna Talatu ta rikid'a ta zama mage mai fari da bak'i,,,,,sai naga ta fice da sauri daga cikin dak'in
kamar k'iftawa da bismillah,,tana kawowa wurin sakatar ta kalli k'ofar da idanunta wani farin
haske ne ya fito daga cikin idanunta ya shafi sakata,,, sai kawai naga k'ofar ta bud'e kanta,,,
magen ta wuce da saurinta tana wani masifaffen gudu mai cike da al'ajabi da matuk'ar ban
tsoro!..






Abin ya matuk'ar bani mamaki kuma ya d'auremin kai ni Mugirat ,,,nabi magen da sauri saboda
kada ta b'acewa ganina tana sauri ina biye da ita har muka kawo k'ofar gidansu Lawiza,,, sai
naga magen ta tsaya tana duban k'ofar gidansu Lawiza na d'an lokaci ,,,,ta bud'e bakinta kenan
saiga jar iska ta bayyana suu suu suu ta nufi k'ofar gidan ya bud'e da sauri,,, magen bata tsaya
b'ata lokaci ba ta afka cikin gidan da gudu..
Tana shiga sai na ga ta nufi d'akin dake gefen dama ta afka cikin da sauri,,, tana shiga ta iske
Lawiza kwance kamar matatta tana barci,,, magen ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma mutum
wato ainahin siffarta Inna Talatu,, saboda k'arfin hali da kuma rashin imani saida tayi wani sihirin
da ya tayar da Lawiza daga barcinta mai dad'i sosai,, Lawiza ta falka a firgice! Cikeda matuk'ar
tsoro da gigicewa ta daure dak'yar tace "wa ye yake tayar dani a cikin wannan tsakar dare? ".

Inna Talatu ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sosai,,, wanda akan haka saida d'akin ya
kama girgiza tanbal tanbal,, abubuwan dake cikin d'akin suka kama fad'uwa k'asa suna
halakewa,,,idanun Inna Talatu suka k'ara ja hannunta ya k'ara tsawo zago zago farcenta yayi
tsini kamar allura,,,ta dubi Lawiza cikin takaici da haushi tace "nice Talatu matar Mamman
wanda kike shirin aura saboda bakida hankali! ".Lawiza taji gabanta ya buga da k'arfi rasssss
tsoro da tashin hankali ya bayyana akan fuskarta ,,,tace "baiwar Allah mike tafe da ke,, shin mi
ne ne dalilinki na zuwa wurina a cikin tsakar dare ,,,a ina kika shigo saboda nasan rufe gidanmu
akeyi idan dare yayi sosai? ".







Inna Talatu ta banka mata harara da idanunta jawur kamar kan maciji,,, sannan tace "yanzu
kuwa zan baki amsar tambayoyinki yarinya! Ni da kike ganina ayanzu gaba gareki *MAYYA CE
NI TALATU*,,, ta sihiri na shigo cikin gidanku dalili kuma shine nazo ne in kasheki har lahira!
Saboda mijina da kikeson ki aura ni talatu nafi k'arfin inyi kishi da kowace irin jakar mace a
duniya,,, saboda kishi dani masifa ne son mijina bala'i ne kallona ma jafa'i ne,,, saboda haka ba
gargad'i nazo yi miki ba d'aukar ranki nazo yi in kasheki in kashe banza shegiyar bazawara! ".







Hankalin Lawiza yayi matuk'ar k'ololuwar tashi zuciyarta duk ta karaya,,, ko'ina a jikinta zufa ne
ke tsattsafo mata saboda tsananin tashin hankalin da take cikinsa..






Ta fara zubar da hawayen bak'in ciki da afkawa cikin tarkon wahala,,, tace "dama ashe maganar
da mutanen gari ke fad'a akanki gaskiya ne ke mayya ce! Na rok'eki dan girman Allah kiyimin rai
kada ki kasheni,, idan har domin mijinki ne wlh na hak'ura dashi har abada dama saida nace

masa bazan auresa ba amma ya nacemin,, ashe da rabon zan fuskanci abinda yafi k'arfin
tunani nabar miki mijinki wlh nabar miki mijinki! ".Ta sake fashewa da wani irin gigitaccen kuka
mai tsuma zuciyar mai sauraro!.







"k'arya kike munafuka azurakar mace! Bazan tab'a yarda da maganarki ba domin ku 'yan Adam
kunada sab'a alk'awari,,, kuma na riga nasha alwashin duk wadda ta kusanci mijina ko ta nuna
tana son uban 'ya'yana hukuncin mace shine mutuwa! Mutuwa! Saboda haka wallahi bazan
tab'a barinki a raye ba,,, kwanciyar kabari shi yafi dacewa dake daga yau zuwa kwana biyu ".Inji
Talatu cikeda matuk'ar hasala sosai..







Lawiza tayi kuwwa da k'arfi ta sake fashewa da kukan bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,,, jikinta
babu abinda yakeyi sai makarkatar tsoro! Tashin hankali da rikicewa ne ya bayyana a fuskarta
dak'yar cikin rud'ewa tace "na shiga uku ni Lawiza! Na kawo kaina gidan mutuwa ka cuceni
Malam Mamman ka cuceni Malam Mamman,,,saboda saida nace bazan aureka domin matarka
mayya ce amma kace sharrin mutane ne ba haka ba,,, gashi yanxu na jawowa kaina masifar da
zata kashe batare da na cika burina ba,, iyayena ku yafemin 'yan uwana ku yafemin! ".Tana ta
kukan bak'in ciki da takaicin rayuwa..









Inna Talatu tace "maganar banza da yofi lokaci yana tafiya,, saboda haka yanzu zanyi miki
abinda ya kawoni in wuce gidan mijina wanda ni kad'ai ce matarsa a duniya! ".Hhhhhhhh ta
fashe da dariya sosai sannan tayi amfani da hannunta,, tana ta surutai na sihiri wani bak'in abu
ne ya bayyana a cikin hannun Inna Talatu MAYYA,, Lawiza babu abinda takeyi sai kukan bak'in
ciki tana ja da baya da baya cikin firgici da tsananin tsoro! Ganin haka ne yasa ta fasa wani irin

uban kuwwa da k'arfi domin neman wanda zai iya kawo mata agajin gaggawa! Tace "kiyi hak'uri
Talatu na tuba na biki ki yafemin wlh bazan sake ko kallon mijinki ba ".







Inna Talatu tace "kije kiyita kuwwa Lawiza babu wanda zai jiyo kuwwarki bale yazo ya ceceki,,,
kafin nazo saida nayi wani mugun sihirin da ko kinyi kuwwa babu wanda zai jiki balantana yazo
ya ceceki,, hmmmm gashi kuwa harna kwad'aitu da namanki!Saboda ina hango komai na kayan
cikinki da k'asusuwanki kin tara mai sosai fa ".Kiyi hak'uri ko nawa kikeso zan baki koda zan
rasa duk abinda mahaifina ya mallaka zan baki,, nidai burina da fatana kada ki kasheni da duk
abinda kike buk'ata zan b.... ".
Inna Talatu bata bari ta isuwa maganar da take sonyi ba,,, tayi amfani da hannunta ta kame
mata kurwa ta sanya kurwar Lawiza cikin jakarta da sauri..








Tana kama kurwar Lawiza ta some tare da ruwan hawaye saman fuskarta,,, Inna Talatu ta ganin
haka ta girgiza ta sake rikida ta koma mage,, tana komawa ta fice da sauri daga cikin gidan
zuwa gidan mijinta..









**********************

***Washe gari da safe koda Lawiza ta tashi daga barci lafiya k'alau ta tashi kamar babu abinda
ya faru da ita jiya,,, ci kin gidan kuwa har mutane sun fara taruwa 'yan uwa da abokan arzik'i sai
ayyuka kawai sukeyi na 'yar garar da za'a kai gidan miji,,, babu abinda ke tashi sai surutu da ya
yar mutane cikin gidan kowace ka kalli fuskarta farin ciki da murna kawai zaka hangowa,,,Inna
Lawiza kamar ta zuba ruwa ak'asa tasha akan murna da matuk'ar farin ciki saboda mijin da
Lawiza ta fara aure rasuwa yayi ya barta yaro guda mai suna Audu,,, haka dai suka cigaba da
gudanar da komai cikin natsuwa da nishad'i sosai..







**Abangaren Malam Mamman shima sai shirye shiryen aurenshi kawai yakeyi cikeda matuk'ar
farin ciki da nishad'i sosai,,,, ya gyara d'akin da zai saka Lawiza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login