Showing 6001 words to 9000 words out of 58121 words

Chapter 3 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

12 Jul 2025

2928

a had'e cikeda
matuk'ar tausayin juna da girmamawa..


Familinsu family ne masu matuk'ar k'aunar juna,, da fahimtar juna haka suke tafiyar da rayuwar
aurensu cikeda zaman lafiya da soyayya..





***Iya Gwamma 'yar asalin Gumi ce gaba da baya,,, 'ya ce ga Malam Mamman da Ina Talatu
tanada k'ane guda mai suna Lawwali ita Iya Gwamma. Inna Talatu mayya ce da taci magani a
wurin wani babban boka mai suna LOK'ORO,, boka LOK'ORO shahararren boka ne da ya
shahara a cikin garin Gumi da kewayenta. Sunanshi ya bazama ko'ina a jahar zamfara da
k'auyukanta ,,,yana bada magani ne ga wad'anda suke son suyi kud'i sosai ko wani cimma
burinsu na duniya. Babban matsafi ne dake aiki da bak'ak'en aljannu da dodonni,, ya shahara
wurin mugunta da kashe rayuka na mutane harda aljannu. Bayan Inna Talatu ta amshi magani
domin ta zamo mai arzik'i to kwatsam! Bata zamo mai kud'i ba ta rikid'a ta zama k'usurgumar
MAYYA wadda nan da nan ta fara cin naman mutanen unguwa da na k'etaren gari,,, tun tanayi
a b'oye mutane basu sani ba har yazo ya bayyana afili kowa ya gano ita mayya ce. Nan da nan
mutanen gari da wad'anda take mu'amala dasu suka fara gudunta domin ceton ransu dana
iyalinsu,,,ko'ina ka gani anyi gungu a majalisu babu abinda suke fad'a idan ba Inna Talatu
*MAYYA CE* cin naman mutane takeyi da satar kurwa! Harda yaranta su Gwamma ake tarewa
a hanya ake ce musu d'iyan mayya kunyi hasara,, Gwamma kuwa kashi takeyima yaran mutane
idan ko warinta ne saisu kacame da dambe sosai. Ta samu yaro tayi masa mugun cizo sai jini
ya fito tasa halshenta ta lashe jinin ta had'iye mak'wat kamar mayya ,,,tabar yaron nan kwance
k'asa yana kukan ciwo wiwiwihhh.



Lawwali yana gefe guda yana kallon yadda take dukan yaron mutane kamar ta samu jaki,,, shi

dai babu ruwanshi saboda yanada matuk'ar natsuwa da sanyin hali. Bayason hayaniya ko
tashin hankali ko kad'an idan ka ganshi kana cewa ba Inna Talatu ce ta haifeshi ba,,, saboda
natsuwarsa da hankalinsa..



Gwamma ce take kakkab'e jikinta da k'asa bayan ta gama chasa d'an mutane,,, ta juyo ta dubi
Lawwali tana harararshi tace "shege raggon namiji kanajin ana zagin mahaifiyarmu amma kayi
shiru,, sai dai ka koma gefe kana kallona ina fad'a,,, Allah yayi wadaran naka ya lalace! Wawan
banza mai zuciyar kare ".




"yaya Gwamma kiyi hak'uri ni banyi shiru ba ne domin in b'ata miki rai ba,, nayi shiru ne saboda
aganina fad'a baya kawo maslaha a cikin wannan lamari,,, kuma ai duk abinda suka fad'a ai
gaskiya ne saboda Innarmu ta aikata maita! ".Inji Lawwali cikeda rashin son tashin hankali.





Gwamma ta zaburo mai da k'arfi cikeda jin haushin maganarsa,,, tace "Innarmu ce mayya
saboda bakada hankali,, lallai Lawwali anyi tsinannen yaro d'an banza! Yanzu nan zanci ubanka
".



"Eh mana na fad'a ai gaskiya d'aci gareta k'arya kuma tanada matuk'ar dad'in d'and'ano mai
zak'i yaya Gwamma ".Cewar Lawwali cikin jin haushin maganar Gwamma.




Nan da nan cikeda matuk'ar zafin nama da jin bak'in cikin maganar Lawwali,,, aiko Gwamma
bata tsaya b'ata lokaci ba ta kwashe Lawwali da wani mugun mari mai matuk'ar zafi da rad'ad'i
tareda gigita rayuwar d'an Adam! Ai saboda k'arfin marin saida Lawwali ya wintsilo k'asa da
k'arfi,,, saida bakinshi ya fashe da jini jinshi da ganinshi suka d'auke na wucin gadi..

Yana kwance k'asa Gwamma ta nuna shi da yatsa cikeda zafin rai da tafasar zuciya tace "ina yi
maka gargad'i da kada ka kuskura ka k'ara aibata mahaifiyarmu,,, idan ana zaginta kana kallo
kana k'yalewa toni bazan k'yale ba,,, duk wanda ya nemi da ya zagi uwata to sai inda k'arfina ya
k'are ciki kuwa harda kai da muke ciki d'aya,, wallahi wallahi! Akan mahaifiyata zan iya kashe rai
har lahira!!! Kuma duk wanda ya shiga cikin gonata saina afka mishi koda kuwa kaine Lawwali,,
yaron banza mara kishin uwarsa ".





Nan taja jikinta tabar Lawwali kwance a k'asa yana kukan rad'ad'in marin da tayi masa mai zafi
sosai,,, ta kama hanyar zuwa gidansu babu abinda Lawwali keyi sai zubar da hawayen bak'in
ciki da takaicin abinda Gwamma tayi masa,, kuma yasan ya fita gaskiya a cikin wannan lamari
yasa hannu ya share jinin dake fita daga cikin bakinsa yana shassheka da ajiyar zuciya.....




_Share&Comments_




*I luv you my fans more more*
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_

*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 5*



Yasa hannu ya share jinin dake fita daga bakinsa yana shassheka da ajiyar zuciya,, idan banda
rad'ad'i da ciwo babu abinda zuciyarsa keyi saboda marin ya shigeshi sosai matuk'a. Dak'yar
Lawwali ya mik'e tsaye yana shafa kuncinsa da yake yi masa zafi da rad'ad'i,,, ya kakkab'e
jikinsa daya b'aci da k'asa ga shatin hannun Gwamma nan ya fito b'aro b'aro a fuskarsa,,, haka
dai yaja k'afafunsa yana tafiya dak'yar domin ya nufi gidansu...





Gwamma ce naga harta iso gidansu ta afka cikin gidan ba tare da sallama ba,, Inna Talatu ce
da Malam Mamman ta iske ya dawo gida domin yayi wani mantuwa a gidan,,, ya dubi Inna
Talatu yace "Talatu baki ga wata bak'ar leda ba dana yi mantuwa da ita ba,, ta mutane ce idan
kin gani ki mik'omin sauri nakeyi zan wuce ".Inna Talatu ta harari Malam Mamman sannan ta
buga tsoki mtsssss tace "maganar banza kenan Mamman mi zanyi da bak'ar ledarka idan na
gani,, ko kuwa ni na sakaka yin mantuwa ne? Da har zaka zo kana damuna da surutunka na
banza da yofi! "."Kinga Talatu ba haka ba ne ai tambaya baya zama laifi,, daga tambaya sai
masifa wai miyasa rayuwarki yanzu ta chanza ne? Idan wani abu nayi miki ya kamata ki sanar
dani in gyara kuskurena mu fahimci juna,, batare da wasu sun jimu ba ".Inji Malam Mamman
cikeda lalama,,, yana dibe dibe ko zai gano inda ya ajiye ledarsa da ya manta,,, Inna Talatu ta
k'ara hasala sosai tace "babu abinda ka yimin Mamman tambaya ce kawai bana so,, domin ni
tambaya b'atamin rai takeyi da ka shigo cikin gidan nan ya kamata ka bani ajiyar ledar,, amma
baka bani ba ka ajiye da kanka sai yanzu da baka gani ba kake neman takuramin da tambayar
munafurci,, to ka diba inda ka ajiye kada ka dameni da tambayarka "."Allah ubangiji ya huci

zuciyarki Talatu nasan nayi ba dai -dai ba amma kiyi hak'uri kinji ".Cewar Malam Mamman
bayan ya shige cikin d'akin yana cigaba da bincikensa..




"da hak'uri ta mutu sadakar nawa ka bani tsohon banza bak'in munafiki! ".Cewar Inna Talatu
cikeda bala'i da masifa.




Tun d'azu Gwamma tana tsaye babu abinda tace,, illa kallonsu da takeyi uwarta tana zagin
ubanta. Sai alokacin ne Gwamma ta bud'i baki tace "Inna na dawo fa naga tun d'azu baki lura
dani ba,, kinata surutunki ".



"To d'iyar k'warai sannu da zuwa ya gajiyar hanya,, ina kika baro k'anenki ne? ".Inna Talatu ta
fad'a yayinda take dube dube ko zata hango Lawwali a bayan Gwamma..




Gwamma taja numfashi tace "lafiya k'alau na dawo Inna Lawwali kuwa na baroshi a bayana kan
hanya ".Saiga Malam Mamman ya fito daga cikin d'aki rik'e da ledarshi a hannunsa,, alamar
kenan yaga ledar ya dubi Gwamma da Inna Talatu yace "aaa Gwamma kin dawo ko ".




"Eh na dawo baba ".Cewar Gwamma.





Malam Mamman yace "to yayi k'yau Allah ubangiji yayi muku albarka ".




Tace "Amin baba ".

Malam Mamman yace "to ni Talatu zan wuce can kasuwa naga ledar da na tambaye ki,, kika
yimin bak'ar magana wadda babu dad'in ji balantana saurare kamar ni ba mijinki ba ne ".




"to tunda ka gani ka isa barka kada ka gayamin maganar da batada dad'i,, inko rama wallahi
domin ba tsoronka nakeji ba! ".Inji Inna Talatu MAYYA.




Malam Mamman yace "ai nasan bakijin tsoro na Allah ubangiji ya shiryeki Talatu! Rayuwarki
tanada matsala sosai wlh,, ni inada aikin yi na barki lafiya masifaffar banza ".Yana fad'in
wannan maganar yasa kai yayi tafiyarsa zuwa kasuwa,, batare da ya tsaya ya saurarin irin
martanin da zata mayar mishi ba..




"kaine masifaffe ba ni ba ai wannan rainin wayo ne,,, daga kawai kaga ina maka shiru-shiru sai
raini da walak'anci ya shigo,, wallahi bazan tab'a barin ka gayamin magana ba dad'i ba amma
ba komai zanyi maganinka! ".Cewar Inna Talatu tana d'aga murya k'warai ta yadda wanda yake
bakin garka,,, zai iya jiyo muryarta.




Sai asannan ne Gwamma ta iya bud'a baki tace "kiyi hak'uri Inna wannan abin bai kawo kallo
ba,,, kuma bai dace ba kina d'aga murya sosai har na waje suna jinki ".






Inna Talatu tace "haka ne d'iyar albarka rayuwata ce ta b'aci sosai wlh,, shiyasa ki kaga inata
fad'a amma yanzu tunda kinsa baki na daina fa,, mi ya faru ne naga kamar bakinki yanada

magana ?".




"ke dai bari Inna ayau Lawwali yayi masifar b'ata min rai da bani takaici ".Cewar Gwamma.




Inna Talatu tace "mi yayi miki ne har ya b'ata miki rai ne? ".




Gwamma ta kwashe labarin duk irin fad'an da takeyi da yaran mutane da suke kiran Inna Talatu
mayya,,, da kuma marin da tayima Lawwali da kuma maganganun da sukayi,, babu abinda ta
b'oyewa Inna Talatu komai ta gaya mata..




Inna Talatu taja dogon numfashi tareda huci mai zafi,, sannan tace "yanzu Lawwali ni yake zagi
harda kirana da mayya,, yau ko wa yayi masa tsaye saina halakashi! Nayi masa mugun bugu
sosai wlh,,, yadda idan yaji ana zagina ko baiyi fad'a ba bazai saka bakinsa ba waishi mara
kuny....




Inna Talatu bata k'arasa maganar da take sonyi ba,, saiga sallamar Lawwali yayi sannan ya
shigo cikin gidan da fasasshen bakinsa. Inna Talatu ta jawo hannunsa kamar abin arzik'i tana
k'ara shafe masa jikinsa da jinin dake fita daga cikin bakinsa..



Sannan ta tambayeshi kamar batasan komai ba tace "Lawwali uban waye ya fasa maka baki
harda jini,, wa ye ya mareka harda shatin yatsu? Ka gayamin yau ko ni ko maishi mutuwa kad'ai
ke rabamu wlh ".

Lawwali yace yana zubar da hawayen takaici "Inna Yaya Gwamma ce ta mareni saida na fad'i
k'asa,, sannan ta dinga zagina babu iyaka ".




"ita Gwamman to naji mi kayi mata ne data mareka? ".Inji Inna Talatu.



"haka kawai ne banyi mata komai ba ".Cewar Lawwali.




Inna Talatu ta harzuk'a da hasala sosai,,, batayi wata wata ba ta kwashe Lawwali da matsiyacin
mari biyu masu k'yau,,, ta ka mashi tana ta kashi kamar ta samu jaki. Babu abinda Lawwali keyi
sai kuwwa yana kuka domin ya samu agaji cikin gaggawa,,, saboda ba k'aramin duka Inna
Talatu takeyi masa cikeda matuk'ar takaicinsa da zafin rai tana cewa "da kai za'a had'a baki ana
zagina ko ana cemin mayya baka damu ba,, saboda bakasan zafina ba amma 'yar uwarka da
tasan zafina shi ne za kace mata ai gaskiya yaran suke fad'a domin na aikata maita! Yanzu
saboda munafurci na tambayeka kace bakayi mata komai ba ,,,yau saina kasheka in kashe
banza! ".Haka dai Inna Talatu ta kama dukan Lawwali sosai tana zaginsa..






Babu abinda Lawwali keyi sai kukan bak'in ciki da zafin duka,, yana cewa "na tuba na tuba
Inna,, Inna bazan sake ba wallahi sharrin shed'an ne ki ya femin zan mutu zan mutu! ".Nan ya
fad'i k'asa ya some duk da haka bata daina dukansa ba,,, sai da tayi masa lilis da duka sannan
daga baya ta gano cewa ya suma,, taje ta d'ebo ruwa a randa masu sanyi ta watsa mishi a
jikinsa. Gwamma dai tana zaune tana kallon duk abinda ke faruwa hankalinta kwance,, can yaja
dogon numfashi ya tashi zaune yana kuka duk gaba d'aya jikinsa yayi rud'u rud'u akan duka,,,
Inna Talatu tace "gobe ma ka k'ara da sai naci namanka d'anye wlh! Kuma yau duk ubanda ya
d'aure maka gindi ba za kaci abincin dare ba,, mu zuba mu gani ni da kai shege ya fasa! ".Tana
gama fad'in maganganunta taja hannun Gwamma sukayi shigewarsu d'aki.

Lawwali yaja jikinsa sannu ya shige cikin d'akin da babu komai sai tarkacen kayayyakin aikin
gida,, ya samu wata tsohuwar tabarma data yakuce akan tsufa ya kwanta. To haka abin ya
kasance kuwa domin Inna Talatu hanama Lawwali tayi abincin dare da yunwa ya kwana,,
mahaifinsa kuma baisan abinda yake faruwa ba a cikin gidan ba..




*********************




Da misalin k'arfe 12:00am na dare ne Inna Talatu ta tashi sannu a hankali,, tana dubawa ko
Malam Mamman da Gwamma sunyi nisa cikin barcinsu. Ai kuwa taci sa'a babu abinda sukeyi
sai minshari da gurnani na barci,, ta lab'ab'a sannu a hankali ta fito waje tareda zare sakatar
gidan..




Tana fitowa waje ne duk unguwar tsit ta ke kowa yayi barci babu abinda kakeji sai kukan
tsuntsaye dana wasu halittu,, ga wata irin sansanyar iska da ta ke busowa mai dad'in gaske. Sai
da Inna Talatu ta dubi yamma gabas,,, kudu da arewa sannan ta duba kowace hanya babu
kowa,,, sannan naga ta kama wata hanya siririya wadda ta nufi cikin daji,, tana ta tafiya har ta
kawo wurin wata bishiya nan da nan naga ta cire tufafinta ta koma zindir haihuwar uwarta. Tana
cire tufafinta ta isa wani wuri inda babu abinda ke tashi sai wuta wal wal wal,, wai ashe wurin
'yan uwanta mayyu ta zo domin suyi bugun wuta..




Wasar bugun wuta shi ne abinda mayyu keyi da daddare musamman alokacin zafi,, zindir
haihuwar uwarsu sukeyi tareda canza kamanninsu ,, suna taruwa a cikin daji suna wasar bugun
wuta shi ne su kama zagayar dajin gari bakinsu da hammatarsu sai fitar da wuta sukeyi wal wal
wal zad tsoro!,, zasu jima sosai sunayi sannan daga baya kowa ya kama gabansa.

Suna gamawa ne Inna Talatu taje wurin bushiyar da ta aje kayanta ta d'auka ta sanya ta nufi
gidan mijinta,, tana cikin tafiya kawai gani nayi ta girgiza da k'arfi! Ta rikid'a ta koma karya mai
k'wala k'walan ido da halshenta ya kai tsawon igiyar shanya,, bakinta sai feso wuta yakeyi jawur
tana kukan karnuka ohww ohww ohww babu dad'in saurare da ji hayak'i bak'i kawai ke fita daga
cikin jikin karyar.



Ta kusa kawowa gida ta had'u da Lado zaiyi fitsari,,, komai na kayan cikinsa tana gani kamar
irinsu hanji,, hanta ,, zuciya da duk wani abu da ku ka san d'an Adam ya keda haka suke ganin
komai na mu kamar yadda ku ka ga skeleton,,, ai kuwa babu b'ata lokaci tasa halshenta mai
kamar igiya ta jawoshi sai da tayi sama da shi ta koma tayi k'asa dashi,, sannan ta bugashi a
k'asa cikeda maita. Lado babu abinda yakeyi sai kuwwar neman agaji amma ina dare ne
kuwwarka banza.


Babu wanda zai jishi balantana ya kawo masa agajin gaggawa,, haka kawai yaji kamar an
tsinke mishi jijiyoyin jikinsa saida Inna Talatu tayi masa azaba da mugunta iri iri daban daban
sannan tayi wani mugun sihiri,,, wata irin mahaukaciyar guguwa ta ga me wurin tana zagayesu
na wani lokaci,, saiga wani farin abu mai surkin ja ya bayyana a tafin hannun Inna Talatu,,,
yana bayyana ta karanta wasu d'alamisai na tsafi da sihiri abin ya zama fa ra ta tura cikin
jakarta ashe kurwar Lado ce ta mayar fa ra ta nufi gida da saurinta.


Tana shiga cikin gidan ta girgiza ta sake rikid'a ta koma mutum,,, sannan ta lallab'a sannu a
hankali ta kwanta domin kada wani daga cikin d'iyanta ko mijinta su ganta.....







_Share&Comments_
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*









*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 6*



Tana shiga cikin gidan ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma mutum wato ainahin siffarta,,sannan
ta lallab'a sannu a hankali ta kwanta domin kada wani daga cikin d'iyanta ko mijinta ya ganta..



Washe gari tunda safe Inna Talatu ta tashi ta share gidan tsab,,, sannan ta aza tukunya saman
murhu ta zuba ruwa ta barta nan wuta na ci bal bal bal harta dad'e saman wuta,, bayan ruwan
sun tafasa ta d'auko gunba ta dama kunu,,, sannan ta d'auko kaskon suyar k'osai ta aza saman
wuta tareda sanya mangyad'a a cikin kaskon. Nan da nan ta shiga cikin d'akin ta d'auko k'ullun
k'osai ta fara suyar k'osai cikin natsuwa da kwanciyar hankali,, k'amshi sai tashi yakeyi yana
game gidan baki d'aya,, haka dai Inna Talatu ta cigaba da aikinta tana wak'e wak'enta irin na
mutanen da,, daga ganin yadda takeyin aikin tana cikin nishad'i da farin ciki sosai,, ta jima sosai
tana suyar sannan ta kammala ta fissuwa kaskon saman wuta ta aje gefe,, tareda kashe wutar
murhu..

Tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login