Showing 42001 words to 45000 words out of 58121 words
Chapter 15 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf
tsaye yace musu "shi
zai tashi ya kira Ummu Salma domin su gaisa da juna ".
Kabiru yace "to baba muna jiranta ".
Maigari ya tashi tsaye ya shige cikin d'aki domin ya kira Ummu Salma,,,, yana shiga ba dad'ewa
ba saiga Ummu ta fito daga cikin d'akin ta duk'a har k'asa ta gaidasu,,, sannan suka amsa mata
cikin fara'a da walwalar fuska.
Kabiru ya dubi sama da k'asan Ummu Salma da k'yau ba laifi tanada k'yau matuk'a ba k'arya ,,,
sannan daga baya yace "Ummu Salma ina fatar kinsan dalilin da yasa mukazo wurinki,,,,
saboda ku fahimci juna keda Ummaru ".
"baba ya sanardani komai dangane daku,,, saboda haka na amince da duk abinda babana ya
gindayamin".Cewar Ummu Salma cikeda matuk'ar kunya ..
Ummaru yayi murmushi yace "masha Allah komai yayi k'yau matuk'a naji dad'i sosai da kika
amince da kina sona,,, nima ina sonki fiye da tunaninki kuma ba za'a samu wani matsala ta
wajena ba,,, zan rik'e ki amana da hannu bibbiyu Salma saboda haka kada kiji wani shakku ko
kwankwanto akaina ".
Salma tace "babu matsala nima awajena zan kasance mai biyayya da ladabi agareka matuk'ar
ina raye a cikin duniya,,, zan sanyaka cikin farin ciki da nishad'i mai d'orewa".........
_Share&Comments_
~Kuci gaba da bina ni Mugirat~
[7/4, 11:20 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 24*
"Zan sanyaka cikin farin ciki da nishad'i mai d'orewa,,, zan zamo fitila mai haskaka rayuwarka
zan sadaukar da farin cikina domin samun farin cikinka,,, biyayya ga iyaye ya zamo wajibi
agareni domin samun aljannata agobe k'iyama ".Cewar Salma cikeda matuk'ar natsuwa da
hankali. Alal hak'ik'a Ummaru yaji dad'in kalamanta sosai wani sanyi ne da jin dad'i ke kwaranya
acikin zuciyarsa,,, ayanzu ya tsinci kansa cikin tsananin farin ciki da murna mara misaltuwa,,, ya
kuma k'ara tabbatarwa da yayi dace da masoyiya ta gari abar alfahari ga kowane d'a namiji,,, ya
riga ya sadak'ar idan Allah ya yarda ba zaiyi nadamar auren Salma ba a rayuwarsa,,, saboda
daga ganinta kasan yarinya ce mai tarbiya da natsuwa gata da hankali da girmama na sama
gareta,,, gata da sanyin hali da k'yakk'yawar d'abi'a ta ko'ina tayi batada matsala a rayuwa,,,
tanada tausayi da jink'ai musamman akan yara ko nakasassu,,, batada girman kai ko kad'an..
Cikin tsananin farin ciki da shauk'in so,,, Ummaru ya d'ago idanunsa ya kalleta cikeda matuk'ar
farin ciki da samun mace tagari yace "hak'ik'a Allah ubangiji abin godiya ne daya had'a ni da
mace tagari d'iyar mutanen kirki,,, wadda takeda tarbiya da girmama manya,,, nima zan rik'eki
amana bisa gaskiya da tsoron Allah zan zama jigon rayuwarki abar alfaharinki akodayaushe,,,
zan kasance inwa agareki domin kada rana ya illatamin ke ".Cewar Ummaru cikeda matuk'ar
nishad'i sosai.
Salma tayi murmushi wanda ya k'ara bayyanar da tsantsar k'yawon fuskar da Allah ya bata,,,
sannan tayi masa kallon soyayya tace "naji dad'i matuk'a Allah ubangiji ya gwada mana lokacin
auren lafiya,,, sannan idan muka zamo miji da mata Allah ya bamu zaman lafiya da kuma juriya
da hak'urin xama da juna ".
Sai asannan ne Kabiru ya sake magana yana murmushin jin dad'i,,, saboda yadda suka amince
da juna farat d'aya ya matuk'ar bashi sha'awa.
Yace "hak'ik'a nayi farin ciki matuk'a ta yadda kuka fahimci juna batare da wata matsala ba,,,
sannan kukayi biyayya ga maigirma baba maigari,,,, ku masu biyayya ne da bin maganar
manya Allah ubangiji ya gwada mana lokacin aure lafiya,,, sannan kuma ya baku yara masu
albarka da biyayya agareku ".
"Amin amin abokina amma fa ka iya addu'a mai k'yau,,, Allah ya sauki matarka Hanne lafiya".Inji
Ummaru cikeda zolayar Kabiru.
Salma tace "amin ya rabbi ".Kanta duk'e tana mai wasa da yatsun hannunta.
Alokacin ne Kabir ya harari Ummaru da wasa,,, sannan ya d'auko dubu hud'u daga cikin
aljihunsa ya mik'awa Salma yace "gashi ta sayi kayan kwalliya ba yawa tayi hak'uri ".
Salma ta nok'e tak'i amsa,,, tana jijjiga kai alamar a'a ba zata amsa ba,,, "bangane mi kike nufi
da haka ba Salma ".Cewar Ummaru.
"ai shine na gani ina bata tana wani jijjigar kai kamar mage ".Inji Kabiru cikeda fara'a.
"ina nufin ni bazan amshi kud'inka ba saboda babana ya gargad'eni akan na daina amsar kud'in
samari ".Inji Salma cikeda ladabi.
Kabir yace "dama kin saba amsar kud'in wasu ne? Kuma naga Ummaru ba wani bane mijinki ne
idan Allah ya yarda ".
"a'a nidai kawai ku barshi baba zaiyimin fad'a agida wlh nagode sosai da soyayyarka agareni,,,
ina sonka ba domin abin hannunka ba Ummaru idan kukaje gida ina gaida Hanne da sauran
mutanen gida,,, na barku lafiya cikin aminci da k'auna ".Inji Salma cikeda natsuwa tana gama
fad'ar wannan magana tayi shigewarta cikin gidansu,,, batare da tsaya ta saurari kalaman da
zasu fito daga cikin bakinsu ba..
Sukayi tsaye suna mamakin irin tarbiyar da Salma takedashi,, sannan ga iya tsara magana mai
ma'ana da muhimmanci.
Can dai Kabiru ya dubi Ummaru yace "abokina mu wuce zuwa gida Allah ne ya tausaya maka,,,
ya baka mace mai tarbiya da sanin ya kamata ".Yace tareda mayarda kud'in cikin aljihunsa ya
ajiye.
"haka ne Kabiru mu wuce zuwa gida yanzu,,, aini nayi matuk'ar farin ciki domin kakata ta yanke
sak'a ".Cewar Ummaru tareda da jan hannun Kabiru suka d'unguma zuwa gida,,, suna tafiya
suna fira cikeda matuk'ar farin ciki da walwala sosai..
*********************
***Bayan sati d'aya ya zagayo mutane da dama aranar assabar,,, suka shaida d'aurin auren
Ummaru Sala mafarauci da Ummu Salma Garba maigari akan sadaki dubu talatin
lak'adan,,,,d'aurin auren ya samu halartar mutane da dama daga wasu garuruwan daga nesa
abokanin maigari,,, anyi taro lafiya an watse lafiya cikeda mutunci da karamci,, anyi abinci kala
kala aka rabawa mutane k'yauta ,,,,an raba lemun k'walba irinsu fanta,, coke da dai sauransu..
Komai na bikin anyisa a wadace cikin rufin asiri da wadatar zuci,,, amarya tasha kwalliya da
chanza kaya kala kala masu k'yawo sosai..
'Yan uwa da abokan arzik'i sunzo na nesa da na kusa,,, dare nayi da misalin k'arfe 9:00pm na
dare dai dai aka d'unguma akaje aka kai amarya d'akin mijinta,,, sai dai muce Allah ubangiji ya
basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba mai tarin albarka.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SHEKARU UKU*
Bayan shekaru uku abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda k'aruwar haihuwar da Ummaru
mafarauci ya samu,,,,,matarsa Salma ta haifi d'a namiji na farko mai suna Habibu,,, ta biyu
kuwa ba'a dad'e da haihuwarta ba mai suna Husna. Shima Kabiru d'iyansa biyu da Hanne
matarsa ta farko Yusrah na biyu Yusuf shima dai k'arami ne,,, haka dai suke kula da iyalansu
tareda basu kulawa da nuna soyayya na gaskiya,,, zumuncinsu ya k'ara k'arfi sosai a
tsakaninsu komai tare suke yinsa cikeda yarda da aminta da junansu,,, idan kaga yadda
sukeyin zumunci saikayi mamaki sosai saboda kana rantsewa da Allah kace 'yan uwan juna ne
amma abin ba haka yake ba sone gamon jini da kuma k'auna matuk'a..
Ba laifi Kabiru da Ummaru yanzu sun zama shahararrun masu kud'i,, musamman Ummaru da
ya zamo shahararren mafarauci wanda ya gaji ubansa Sala mafarauci,,,,,yafisa zamowa
babban mafarauci a cikin garin Gumi da sauran k'auyukkan dake kewayenta,,, babu inda labarin
jarumtarsa da shahararsa baije ba,,, kowane irin daji komai hatsarin daji da aljannunsa yana iya
shiga ciki yayi farauta ya dawo gida lafiya k'alau,,, babu dabbar da take gagararsa kamawa ba
sai dai idan baiyi idanu biyu da dabbar ba,, alk'awarin daya d'auka na fansar jinin iyayensa dana
baba Labaran bai manta ba yana nan dai yana shirye shiryen d'aukar fansa!.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
***Ab'angarensu Sagiru,, Ila da Lawwali sun zama shahararrun 'yan kasuwa masu kud'i dai dai
gwargwado,,, ganin sunyi kud'i yasa suka gina gidajensu kusaga juna,,, sannan kowane daga
cikinsu ya nemo mata budurwa baba Labbo yayi musu auren soyayya.
Lawwali sunan matarsa Aliya,, Sagiru Adama,, shi kuma Ila Ladidi haka dai aka d'aura aurensu
cikin wadatar zuci da rufin asiri sosai,,, d'aurin aurensu ya tara mutane da dama 'yan uwa da
abokan arzik'i duk sunzo wurin bikinsu Lawwali,,, haka aka kai kowace amarya gidan mijinta
cikin mutunci da lumana..
_Allah ubangiji ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba mai tarin albarka,,, wad'anda basuda
aure ya kawo musu mazajen aure nagari masu halayyar k'warai._
Gwamma kuwa haka dai ta cigaba da cin naman mutane da mu'amalar iskanci da Sule,,, duk
da irin matakan tsaro da aka sanya mata bai hana mata aikata maita ba! Babu abinda ta bari na
naman mutane dana aljannu kowa bata bari ba,, gashi mutane sai tsoronta sukeji saboda
amintattun maigari sun tabbatar masa da Gwamma *MAYYA CE* babba kuwa,,, komai na
Gwamma cikin wayo da dabara takeyinsa na kamun kurwar mutane da aljannu!.
Maigari yanajin wannan maganar hankalinsa ya d'unguma sosai gabansa ya bada rasssss!
Jikinsa sai makarkatar tsoro yakeyi saboda yaga alamar Gwamma ta zarce Inna Talatu MAYYA
rashin imani acikin maita,,, ya aika dogarinsa guda ya kira masa surukinsa wato Ummaru d'an
Sala mafarauci,,, batare da b'ata lokaci ba sukazo tare maigari ya kwashe labarin komai ya
gaya masa cewa Gwamma ce shahararriyar mayyar da ta addabi rayuwar mutane sosai,,,
Ummaru ya nuna masa ya kwantar da hankalinsa shine zai kamata da hannunsa sannan daga
baya ya kasheta har lahira,, Ummaru yaba maigari shawarar asanarda mutane domin susan irin
abubuwan da suke faruwa agari,,, maigari ya sanardasu komi gameda Gwamma mayya da
kuma irin tsafe tsafen da take aikatawa ya gaya musu tafi mahaifiyarta shahara da gunguma
akan maita,, domin ita har naman aljannu ci takeyi bawai ga mutane kawai ta tsaya ba.
Mutane suka k'ara rikicewa da d'imaucewa akan tashin hankali,,, gashi yanxu sun k'ara
tabbatarwa Gwamma tafi mahaifiyarta shahara da gunguma akan maita da mugunta iri iri daban
daban,,, sannan batada tausayi da imani ko kad'an,, bayan maigari ya gama nasa jawabi.
Ummaru yayi nasa jawabi inda ya nuna musu dasu kwantar da hankalinsu zai d'auki babban
mataki akanta sannan zai kamata ya gana mata azaba sannan ya kasheta! Ya k'ara nuna musu
dasu k'ara dagewa da yawan yin addu'a domin Allah ubangiji ya kawo musu k'arshen zaluncin
Gwamma,,, kuma su kulada iyalansu tareda yin taka tsan tsan domin gujewa afkawa cikin
tarkon Gwamma mayya,, yana kawo k'arshen maganarsa suka umurci mutane kowa ya watse
ya kama gabansa,,, kallo d'aya zakayiwa mutane ka hango tashin hankali da rikicewa k'arara
akan fuskarsu,,, masu raunin zuciya banda hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa babu abinda
sukeyi,,, suna tafiya suna jimamin abinda yake faruwa marasa dad'in saurare da kuma ji,, ga
kuma zullumi da fargabar akan kodayaushe mutum ana iya kame masa kurwa ya mutu har
abada.........
_Share&Comments_
[7/4, 11:36 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 25*
**Mutum ana iya kame masa kurwa a cinye ya mutu abanza,,,, batare da anyi saurin ganowa ba
sai daga baya ai kuwa mutane suna komawa gidajensu,,, maganar Gwamma k'usurgumar
mayya ce ya bazu ko'ina a cikin garin Gumi,,, mata da k'ananan yara suka tsorace da rikicewa!
Wasu ma babu abinda sukeyi sai kuka da zubar da hawayen bak'in ciki da tsoron mutuwa,,,,
gashi babu halin mutum yace zai gudu yabar gari yayi gudun hijira,,, to ganin haka ne yasa
mutane suka rage yawan fitar dare ko irin gungu nan da samari da dattijawa keyi acikin dare
suna fira yanzu babu shi,,, saboda kowa yana tsoron masifar Gwamma da kuma ta cinye
mutum a banza babu me cetonsa,,,, Ummaru mafarauci shi kad'ai kawai ke fitowa acikin tsakar
dare yana yawon farautar kamun Gwamma mayya,,, kullum kullum yake fitowa nemanta amma
har yanzu shiru Allah bai bashi ikon kamata ba,,, domin duk yawon nemanta da yakeyi tana
ganinsa acikin madubin tsafinta,,,,, idan taga yadda Ummaru d'an Sala mafarauci yake yawon
nemanta kamar yadda mafarauci ke neman namun daji saita bushe da muguwar dariya sosai
tace "hhhhhhhhhhh Ummaru kenan ba zaka iya kamani cikin sauk'i sosai ba sai kasha bak'ar
wahala,,,, kafin ka kamani sannan kashe mutane yanzu na fara! Babu ubanda ya isa ya
hanamin cin naman mutane dana aljannu duk duniya,,, kafin na mutu sainayi abubuwan da har
abada ba zaku tab'a mantawa dani ba,,,,,,saina shayar daku ruwan guba da bak'in cikin da zai
kasheku d'aya bayan d'aya,,,, babu gudu babu ja da baya wannan alk'awari ne na d'auka araina
kuma saina cikasa,,, saina cikasa! ".
Haka dai takeyin maganganu iri iri daban daban na d'aukar fansar jinin mahaifiyarta,,,,,saboda
ita Gwamma duk da mutane sun gano ita mayya ce bata damu ba,,, sannan hankalinta kwance
yake alokacin ne ma ta k'ara k'aimi wurin cin naman mutane da aljannu,,,,, mutum sai yana
zaune cikin kasuwa ko majalisarsu akirasa ace 'yarsa ko d'ansa ko wani d'an uwa nasa ya
mutu! Kullum safiyar Allah idan gari ya waye saita kashe kusan mutum goma ko fiyeda hakan,,,
ganin mutuwar da akeyi ne yasa maigari da sauran mutanen gari suka fita cikin hayyacinsu,,
tsoro,, tashin hankali,, fargaba duk suna taredasu akodayaushe akowane lokaci,,, Ummaru ma
abin yana matuk'ar damunsa na yadda Gwamma take shammatarsa ya kasa kamata,,,, amma
sai ya nasa acikin zuciyarsa duk daren dad'ewa sai ya kamata sannan komai b'oye b'oyenta da
sihirinta tabbas wata rana sai dubunta ya cika..
**Washe gari da safe misalin k'arfe 11:00am na safe,,, bayan Gwamma ta share gidan gaba
d'ayansa tsab,,, dayake nan Sule yake kwana acikin gidan akodayaushe sukayi wanka tare,,,
sannan tayi musu breakfast tea da bread suka karya.
Bayan sun gama karyawa ne kowanensu ya shirya cikin sabbin kayansu mai k'yau,,, sannan
Sule da Gwamma sukazo har bakin k'ofar gidan zatayi masa rakiya,,, suna zuwa bakin k'ofar
Sule ne ya dubeta cikeda so da yaudara yace "farin cikin rayuwata mi kike buk'ata ne,,,, Idan
zan dawo in sayo miki ?".
Gwamma tayi murmushi tace "zumana ka siyomin kifi mara k'arni da lemu da ayaba,,, sannan
ka biya wurin Iya Abu mai saida langab'u ka sayomin shi ".
"hmmm duk a ina zaki saka wad'annan abubuwan da kika lissafo?,,,mata dai akwai ku dason
cin dad'i da kwad'ayi".Cewar Sule cikin zolaya da wasa.
Gwamma ta hararesa da wasa sannan tace "duk acikin cikina kaidai ka sayomin babu
ruwanka,,, muradinka dai kada nak'i ci ya lalace a banza aiku maza bakuda son dad'i ko kad'an
sai d'aci ".
"ke ni ban iyawa da masifarki wasa nake nakeyi miki,,, zan siyo miki duk abinda kike buk'ata
Gwammata,,, ai bakisan yadda nake sonki ba saboda haka ki daina shakku akan zan sayo ko
bazan sayo ba ".Cewar Sule cikeda matuk'ar lallashi da dad'in baki.
Gwamma tace "to naji yanzu dai kayi magana mai ma'ana sosai ".
Sule yace "to ni dai yanzu zan wuce saina dawo ko ".
"to saika daw...... ".Bata k'arasa maganar ba saiga Lawwali yayi musu sallama,,, Sule ya amsa
masa cikeda fara'a da murna sosai yayinda Lawwali ya dubesa ya tamk'e fuskarsa alamar
bayason wata magana da Sule,,, Sule ya hango k'iyayyarsa acikin idanun Lawwali saboda haka
batare da b'ata lokaci ba yaja k'afafunsa yayi wucewarsa zuwa inda zaije,,, Gwamma kuwa tana
ganin irin kallon da Lawwali keyiwa Sule dole itama tasha masa toka tareda da yi masa jagora
zuwa cikin gidanta.
Suna shiga cikin gidan ta d'auko tabarma ta shimfid'a masa,, tareda da kawo masa ruwa masu
sanyi cikin jug,,, Lawwali ya zauna saman tabarma tareda yin bismillah sannan ya dubeta duba
na fahimta da natsuwa yace "yaya Gwamma mun yini lafiya,,, ya bayan rabuwa? ".
"lafiya k'alau bayan rabuwa kuma ai kasan inda nike baka nemeni ba,,,, sai yau ka tuna dani
ashe dai naka naka ne duk yadda ya lalace ".Cewar Gwamma cikeda jin haushin maganarsa .
Lawwali yaja dogon numfashi yace "Allah ubangiji ya huci zuciyarki yaya Gwamma,,, niba tashin
hankali ya kawoni wurinki ba magana ce mai matuk'ar muhimmanci da amfani ta sanya nazo
gareki,,, sannan kuma ai nasan hannunka bai tab'a rub'ewa ka yanke kayarsuwa ".
"to ina saurarenka mi yake tafe dakai? ".Inji Gwamma.
Lawwali ya nisa yace"da farko dai inason komai zakiyi a duniya ki sanya tsoron Allah
azuciyarki,,, sannan duk abinda mutum zaiyi arayuwarsa yasan Allah ubangiji yana ganinsa
koda lullub'e yake acikin rami,,,, shaidun duniya shine shedun lahira