Showing 36001 words to 39000 words out of 58121 words
Chapter 13 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf
sake buga gigitacciyar k'ara namansa ya rabu ga
kansa agefen d'aki sai hawaye suke fitowa daga cikin idanunsa! Inna Yashe itama ta buga wata
irin kuwwa tana fisge -fisge da soshe soshe can ta fad'i k'asa d'immmmm naman jikinta ya rabu
filla -filla kamar yadda na Sala mafarauci yayi,, abin babu k'yawon gani d'akin gaba d'aya ya
garwaye da jininsu Inna Yashe!.
Baba Labaran da Ummaru suka rungume juna akan tsananin tashin hankali da firgicewa! Babu
abinda sukeyi sai zubar hawayen bak'in ciki,,, sun rud'e sun d'imauce basu tab'a ganin tashin
hankali ba kwatankwacin wannan ba,,, zuciyarsu sai rad'ad'i takeyi da tafasa sun kasa cewa
komai balantana suje neman agajin mutane ko taimako akan rikicewa da gigicewa! Bayan
sassan naman jikinsu Inna Yashe ya gama yin filla -filla kwatsam sai suka ga tsutsotsi k'anana
suna yawo a cikin jinin da sassan jikinsu Sala mafarauci,, can taga tsutsotsin suna shiga cikin
wata k'wara d'aya tsutsar ita kuma tana rikid'a tana k'ara girma,, suna gama shigewa gaba
d'aya tsutsar ta koma guda wargajejiyar k'atanya,, tayi amfani da bakinta ta kama shan jinin da
cin namansu Inna Yashe tana k'ara zama k'atuwa!Taci naman taci taci saida ta cinye naman da
kuma shanye jinin kaf baki d'aya! Sannan ta dubisu baba Labaran ta dinga feso musu wuta tana
bugunsu gefen hagu da dama tayi musu lik'is da matsiyacin duka,, babu abinda ke tashi sai
kuwwarsu da kukansu idan zasu gudu tayi amfani da tsafinta ta mayardasu cikin d'akin, haka
dai ta cigaba da gana musu azaba da uk'uba iri iri daban daban na tsananin zalunci da rashin
tausayi! Idanunta sunyi jawur kamar barkono jijiyoyin tsutsar ya tashi rud'u rud'u acikin fuskar
tsutsar ana hango fuskar Gwamma mayya yana yawo,, amma su basu lura ba saboda tashin
hankali da bala'i! Kunsan jikin wanda ya kwana biyu basa d'aya dana tsoho sai naga baba
Labaran ya kama shure shuren mutuwa! Yana kururuwar zafin ciwo gashi ji yakeyi kamar ana
soka masa allura ko wuk'a a cikin jikinsa,, nan da nan naman jikinsa ya daskare yana yin
gunduwa gunduwa ya mutu dis batare da b'ata lokaci ba!.
Ummaru yana ganin abinda ya faru da baba Labaran ya buga kuwwa da gigitacciyar k'ara da
k'arfi! Ya tunkaro tsutsar domin yayi mata kisan gillah,, tsutsar tana ganin ya nufota ta hura
masa wani abu acikin fuska ya shiga cikin idanunsa yana fara lalube tayi amfani da sihiranta ta
jujiyashi a sama! Sannan ta nunasa da yatsa yaje ya bugi bangon d'akin gauuuuuu! Ya fad'i
k'asa d'immmmm kansa ya fashe da jini sannan ya suma.
Tsutsar tana ganin irin rashin imani da zaluncin data aikata,, ta bushe da mahaukaciyar dariya
tareda rikid'a zuwa ainahin siffarta Gwamma! Ta dubi Ummaru tareda da nunasa da yatsa
tace"yanzu muka fara wasar ni da kai na rantse da jinin mahaifiyata baxan tab'a barin kaji dad'i
a cikin rayuwarka ba! Kafin ka zamo ajalina saina cusa maka bak'in cikin da har abada ba zaka
tab'a mantawa dani a rayuwarka ba! Zuri'arku saina kassarasu baki d'aya munafiki azzalumin
ubanka Sala ya ja maka ,,,saboda haka ni babu ruwana da kowa laifin Sala mafarauci ya
shafesa! ".
Tana gama fad'in wannan maganar ta girgiza sannan ta rikid'a,,, ta b'ace b'at daga cikin gidan
Sala mafarauci,,, suui suuu suuuu kawai kakeji alokacin da ta b'ace.
Tana barin gidan saida taje gidajen mutane tana kashe musu mata da d'iya,,,,,,amma fa
wad'anda sukayi walimar murna na mutuwar Inna Talatu MAYYA da kuma wad'anda sukayi farin
ciki sosai akan mutuwarta! Duk saida ta bisu gida gida tana kashe d'iya da mata,, wannan ta
kashe matarsa wannan ta kashe masa wancan ta kashe masa d'iya haka dai ta kamayi saida ta
kashe kusan mutum ishirin gamidasu Sala mafarauci ishirin da uku! Ina lillahi wa inna
ilaihirraji'un! Wannan masifa tayi yawa sosai,,, bayan ta kamalla kashe duk wanda ya dace ya
d'and'ani zafin mutuwa! Ta b'ace b'at ta koma gidanta ko nace na iyayena,,, tana komawa gidan
tayi wanka sannan ta dawo ta shirya domin ta kwanta kawai sai ganin mutum zaune tayi a
saman gadonta yayi kwance rashe rashe,,, kallonta kawai yakeyi yana lasar baki dak'yar ta
bud'a baki tace "wai Sule miyasa bakajin magana ne? Kace kana sona nace maka bana sonka
to mi ye na bibiyata aduk inda naje ,,,,miyasa bakada lura ne kai aganinka iyayenka zasu bari
ka aureni bayan sun san ni d'iyar mayya ce ".
"nidai nace ina sonki ba iyayena ba sannan nine zan zauna dake ba wasu ba,,, mi ye nayi miki
kika tsaneni ko ganina bak'ya sonyi inzo wurinki? Ina sonki sosai babu wanda ya isa ya rabani
dake Gwamma ni koda kece mayyar ba mahaifiyarki ba ina sonki a hakan ".Cewar Sule cikeda
matuk'ar lallashi da dad'in baki.
Kalaman Sule sunyi matuk'ar tasiri a zuciyar Gwamma jikinta duk yayi mugun sanyi sosai,,, can
ta nisa tace "bazaka tab'a gane matsalar tarayyarka dani sai nan gaba kad'an Sule,, ni nan da
kake ganina rayuwata tana cikin matuk'ar hatsari akodayaushe akowane lokaci za'a iya kasheni!
Amma ba komai na yarda da soyayyarka Sule na aminta ".
Sule yayi murmushi yace "nagode sosai da kika amshi soyayyata hannu bibbiyu ina sonki aduk
yadda kike,,, sannan ai mutuwa dole ce kowa lokacinsa yake jira ".Ya fad'a shi bai gane inda
maganar Gwamma ta dosa ba,, na cewa akwai lokacin da zaizo akasheta ba.
Gwamma tace "babu damuwa Sule duk yadda kace haka za'a yi saboda bazaka tab'a gane
manufar maganata ba ".
Yace mata "aiko ni nake gane inda maganarki ya dosa saboda k'auna da soyayyar da nake miki
daban yake a cikin zuciyata ".
"da gaske na kuwa gode da soyayyarka agareni Sule ".Tace tareda d'auko man shafi ta fara
shafawa a jikinta tana shafawa Sule ya matso kusa gareta gab da gab sunajin numfashin juna
yace "babu godiya a tsakaninmu masoyiyata,, ya amshi manshafin daga hannunta ya cigaba da
shafa mata jikinta tareda tab'a duk wasu gab'ob'i da sassan jikinta 'har wani lumshe idanu takeyi
akan dad'i sosai sannan b'ata tsintsar kanta cikin irin wannan yanayi ba ya bita da shafe shafe
duk ya kashe mata jiki,,, ai dayake tsakanin baligi namiji da baliga mace idan suka keb'e a
tsakaninsu na uku d'insu shed'an ne nan da nan yasa hannunsa ya jaye mata zane suka
afkawa juna suna lashe lashe da kisses,, ina ganin sun sun fita cikin hayyacinsu naja k'afafuna
nayi waje naja musu k'ofa.
Bayan wasu mintuna kad'an na jiyo ihu da kururuwar Gwamma tana kuka mai cike da zafi da
rad'ad'in zama cikakkar mace,, hmmmm aikin gama ya gama Sule ya kwashi gararsa da jin
d'adi.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Baba Labbo ne ya shigo aguje cikin gidansa da gudun bala'i duk jikinsa yayi faca faca da zawo
da fitsari,,, yana shigowa ya d'unguje Inna Tani da sauri ya afka cikin d'akinsa garaffff garaffff
garaffff ya rufe,, Inna Tani ta wintsilo k'asa bakinta ya fashe d'immmmm ta tashi tsaye tana
share d'an jinin da ya fito daga cikin bakinta,, Inna Tani ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai harda rik'e ciki akan dariya tace "maigida
lafiyarka k'alau kuwa,, ka fito waje ka gayamin abinda ya faru dakai bayan kaje d'auko
Gwamma,, ko acan ne aka baka tsoro ne? ".Tace tanata k'yalk'yalar dariya sosai........
[7/2, 7:56 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 21*
Inna Tani ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai tace "maigida lafiyarka k'alau kuwa,,, ka fito
waje ka gayamin abinda ya faru dakai bayan kaje d'auko Gwamma,,, ko acan ne aka baka tsoro
ne? ".Ta k'yalk'yale da dariyar mugunta.
Baba Labbo ya lek'o ta tagar d'akin yana wuru wuru da idanu,,, da nishin wahala alamar yasha
wuya sosai da yake fitarwa yace "wallahi Tani danaje can d'auko Gwamma domin ta dawo gidan
nan,,, bayan munyi magana da Gwamma ta shiga cikin d'akin saboda ta d'auko kayanta mu
wuce ,,,tana shiga kafin ta fito daga cikin d'akin macijiya ta fito daga cikin d'akin Gwamma tana
ta tsoratani!........ ".Ya kawo labarin komai ya sanar da ita duk irin abubuwan da ya faru a cikin
gidan Gwamma,,,, ya sanar da ita babu abinda ya b'oye mata dangane da irin tashin hankali da
bala'in daya gani...
Yana gama fad'ar wannan magana,,, bayan ya kawo k'arshen magana Inna Tani ta kama salati
tana wuru wuru da idanunta cikeda matuk'ar tsorata da kid'emewa! "Ina lillahi wa inna
ilaihirraji'un!!! Lallai kaga tashin hankali da bala'i maigida,, Allah kawai ne yasa da rabon zaka
kawo labari da ka mutu tunda dad'ewa,,,, dama saida nace karkaje kaje da yanzu ni aka bari
cikin bak'in cikin rayuwa da kuka ".Inji Inna Tani cikeda matuk'ar sanyin jiki da tsananin tsoro!.
Baba Labbo yace "nima Tani banyi zaton Talatu xatabar macijiya domin tayi gadin Gwamma
ba,,, saboda naga wanda ya mutu ya riga ya mutu har abada ".
Inna Tani ta fyace majina tace "haka ne amma dan Allah kada ka sake zuwa gidan nan,,,
saboda ina tsoron kada macijiyar ta kasheka a banza da yofi! ".
"wa! Ni in kikaga naje gidan to saidai gawata ce aka kai,,, to ko gawata ban yarda akaita gidan
ba idan har na mutu ".Cewar baba Labbo cikeda matuk'ar tsoro da fargaba!.
Inna Tani tace "Allah dai ya tsare gaba maigida,, to fito waje in wanke maka jikinka naga duk ya
b'aci da zawo sosai ".
"inajin tsoro Tani ayau d'in nan naga tashin hankali da bala'i wanda ban tab'a gani ba,,,,bazan
iya fitowa ba tsoro nakeji sosai ".Inji baba Labbo cikeda matuk'ar tashin hankali!.
Inna Tani tace "babu abinda zai sake faruwa sai alkhairin Allah,, kuma idan Allah ya yarda ba
zaka sake mugun gani ba,, saboda wannan tashin hankali da rikicewa yaja ma harsu maigari
gudu da sauran mutanen gari fargaba da zullumi! ".
Baba Labbo yace "nikam bazan fito ba inajin tsoro sosai wallahi Tani "..Dak'yar da lallashi,,
rok'o,,, gamida da magana mai dad'i sosai Inna Tani ta samu baba Labbo ya fito daga cikin
d'akin,,, yana fitowa ta tara masa ruwa a bokiti takai mishi cikin toilet,, ta d'auko towel irin na
zane ta bashi ya shiga wanka kayan da duk suka b'aci sosai da zawo tasa klin da sabulun
wanki ta wanke tass zad sha'awa,,,, tana gama wankewa ta shanya kayan a saman igiyar
wanki,,,, ta shimfid'a tabarma ta zauna tana jiran fitowar baba Labbo daga cikin makewayi..
Ba'a jima sosai ba saigashi ya fito daga cikin toilet,, ya shiga cikin d'akin ya shafa manshafi
sannan ya d'auko wasu kaya ya sanya,,, bayan ya sanya kayan ya fito waje ya zauna kusa ga
Inna Tani,,,, ta tashi taje ta kawo masa abincinsa da ruwa masu sanyi cikin jug,,, yayi bismillah
ya fara cin abincinsa cike da natsuwa da walwala,, ita Inna Tani sai firfita takeyi masa da fai -fai
tana kallonsa cikeda matuk'ar tausayi da k'auna matuk'a..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Ab'angaren Sule da Gwamma bayan ya gama biyan buk'atarsa,,, babu abinda Gwamma keyi
sai hawayen ciwo da rad'ad'i,,, yaje ya d'ebo ruwa a randa ya aza mata ruwan zafi a saman
murhu,,, bayan ruwan sunyi zafi sosai yazo ya surka da ruwa masu sanyi ya kai mata ruwan
acikin toilet,,,, yazo ya taimaka mata ta tashi tsaye ta dafa kafad'arsa,, ya kaita har cikin toilet ya
gwada mata yadda zata gasa jikinta sosai da ruwa masu d'umin ya fito daga cikin toilet d'in.
Yana fitowa ta kama gasa jikinta sosai tareda zama acikin ruwan zafin,,, tana kuka a hankali
cikeda matuk'ar rad'ad'in ciwo da zafi,,, haka dai ta daure ta cigaba da gasa jikinta sosai lungu
da sak'o ko'ina a cikin jikinta,,, bayan ta gama ne taji zafi da rad'ad'in da takeji ya ragu sosai
acikin jikinta,,,, sannan daga baya ta fito daga cikin toilet d'in ta shiga cikin d'akin ta shirya.
Bayan ta kammala shiryawa ne Sule ya bata maganin rage rad'ad'in zafi,,, ta amsa tasha da
ruwa masu sanyi ya dubeta yace "sannu Gwamma nagode sosai da kika sanyani cikin farin
cikin da ban tab'a jin irinsaba,, kika bani abu mafi daraja da tsada a rayuwarki,, kika sanyani
cikin nishad'i da jin dad'i sosai matuk'a,,,, Allah ubangiji ya baki lafiya kuma yabarmu tare har
abada ".
Saida Gwamma ta dubi Sule cikeda takaicin rabata da budurcinta da yayi,, acikin zuciyarta sai
sak'e sak'e takeyi na irin mugun hukuncin da zatayi wa Sule can ta nisa tace "hmmmmm babu
komai ai wannan yana daga cikin irin soyayyar danake yi maka har acikin zuciyata,,,, kuma kafi
k'arfin komai a wajena Sule ".
Yayi murmushi yace "haka ne gaskiya masoyiyata dama haka so yake,,, gamon jini ne shi kuma
farat d'aya yake shiga acikin zuciya babu sallama ko neman izni ".Cewar Sule cikeda matuk'ar
yaudara da dad'in baki..
Gwamma tace "babu k'arya acikin maganarka masoyina,,, abin sona akodayaushe ".
Sule yace "Allah ubangiji ya baki lafiya da k'arfin jiki masoyiyata,, ni zan wuce zuwa gida ".Yace
tareda mik'ewa tsaye alamar zai wuce. Tace "amin amin Sule ".Ta tashi tsaye domin ta rakashi a
waje,,, suka nufi k'ofar gida ta kaishe har waje tana yi masa sai wata rana
Sule yayi tafiyarsa ita kuma tayi dawowarta cikin gida,,, ta zauna saman tabarma tayi tagumi
tace "hmmmm Sule kajawa kanka masifa da bala'i wlh!,Budurcina daka amsa baka amshesa ga
banza da yofi ba,,,, saina kasheka in kasheka banza! Saika d'and'ani zafin fitar rai amma ba
yanzu zan kasheka ba saina k'ara shan zumarka ".
Hhhhhhhh haka dai ta bushe da mahaukaciyar dariya sosai,,, sannan ta murtuk'e fuska ta
cigaba da surutunta na son rai da haukahhhh...
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN KWANA BIYU*
***Bayan faruwar mutuwarsu baba Labaran da Sala mafarauci da matarsa,,, garin duk ya rikice
da kacamewa da mutuwar mutane ishirin acikin garin Gumi! Ko'ina ka duba acikin garin kukan
mutane da ifface iffacensu,,, yara da mata sai kuwwace-kuwwace kawai sukeyi da kuka harna
tashin hankali da bak'in cikin mutuwar mutane kusan ishirin. Ganin haka ne yasa suka k'ara tsoracewa akan al'amarin mayyu,,, tsoro da fargaba ya bayyana
k'arara akan fuskar mutanen gari,,, kowa ka kalla kuka sukeyi kamar ransu zai fita daga cikin
gangar jikinsu saboda bak'in ciki da matuk'ar fargaba akan lamarin mayyu.
To da yake mutum biyu sun rasu daga cikin danginsu Sala mafarauci da baba Labaran,, shiyasa
mutane suka fara zuwa gidan baba Labaran domin su sanardashi abinda yake faruwa,,, Innar
Lado kawai suke iske zaune tayi tagumi zuciyarta sai fad'uwa takeyi da k'arfi da k'arfi rassssss!
Sukayi mata sallama ta amsa mutum guda kawai ya shigo cikin gidan ya sanar da ita abinda
yake faruwa acikin gari,, hankalinta ya k'ara tashi zuciyarta ta cigaba da bugawa da k'arfi
d'immmmm! Dak'yar ta sanarda mai aike baba Labaran bai dawo gida ba,, tana ganin yana
gidan Sala mafarauci suje can zasu samesa itama anan shi take jiran ya dawo,, dan aiken ya
juya waje yaje ya sanardasu maigari abinda yake faruwa..
Batare da b'ata lokaci ba suka d'unguma gaba d'ayansu kusansu goma sha biyar zuwan gidan
Sala mafarauci,, domin su sanardasu shida baba Labaran abinda yake faruwa acikin garin,,
bada jimawa ba suka kawo bakin k'ofar gidan Sala mafarauci sukayi sallama a waje,, shiru babu
amsa sukayita sallama babu adadi sunyi tsaye shiru harna tsawon minti talatin sannan daga
baya suka yanke shawarar shiga cikin gidan gaba d'ayansu,, suna shiga filin gidan babu motsin
komai saina awaki da kaji babu kowa nan ma saida sukayi shiru sannan daga baya suka yanke
shawarar shiga cikin d'akin gabansu sai fad'uwa yakeyi yana bugawa da k'arfi da k'arfi! Tsoro ne
da tashin hankali ya bayyana a fuskokinsu k'arara! Maigari shine shugaba amma yafi kowa
tsoro da rawar jiki,, dak'yar suka daure suka afka acikin d'akin.
Suna shiga cikin gidan saida numfashinsu ya kusa d'aukewa,, tashin hankali da rikicewa ne
akan fuskokinsu k'arara saboda ganin Ummaru sukayi kwance ya some sannan ga k'asusuwan
mutane nan su baba Labaran yasshe acikin d'aki,,, sukaje wurin Ummaru domin su bashi
taimakon gaggawa babu abinda ke fita daga cikin bakinsu ila "Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!
Allahumma ajirni fi musibati wa'akhalufni khari minha!.......
_Share&Comments_
[7/2, 8:15 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_