Showing 1 words to 3000 words out of 62597 words
Chapter 1 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
[03/05, 6:47 pm] Xayyeesherthul-humaerathí ¼í½‚: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
MABUÆŠI
Duniya da mutanen da ke kewaye cikinta sun jima yi mini kaura tun ina shakar matsakaiciyar
iska a cikin mahaifiyata,a lokacin da ko numfashi ban taɓa yi a cikin duniyar ba.
Abun mamakin sai ya zamto harda wanda ya zama silar kasancewar rayuwata acikin cikin ma
ana mahaifina!
Me muka aikata?
Me muka yi wanda ba daidai ba?
Shin Musuluntar da mahaifiyata tayi tare da sadaukarwa shi ne ya zame mana tikitin siyan rigar
da za a wofantar damu?
In danginta kirista sun gujeta domin bijerewa umarni da addininsu da ta yi.
Kuma suma musulman sai kyamacemu,saboda daga mara sallah ta dawo mai sallah?
Abar ƙyamace?
Abar guduce?
Abar kyamatace?
Ba ma wannan ba to ni kuma mene ne laifina?
Aa!
Addinin musulunci bai koyar da haka ba,hasalima ya nunar da a kyautattawa kowanni ÆŠan
Adam ko da kuwa ba musulmin bane,bare kuma wanda ya musuluntar.
Tabbas mahaifiyata jarumace da ke iya juriya,jajircewa hakuri tare da sadaukarwa wajen
tabbatuwar rayuwata a duniya ba tare da taimakon kowa ba kuma ba tare da jin cewa hukuncin
da ta yanke na kasancewarta a musulma laifi bane.
Ban da wata jarumar da ta zarce ta domin kuwa ta kara gasgata babu abun bautawa da gaskiya
sai Allah, a lokacin da take da tsananin bukatar taimako ta kauda kanta ga duk wata hanya da
zata iya sauya mata kudirinta,ta rayu ita kaÉ—ai,cikin kadaici,talauci da tsanani har zuwana
duniya kuma ta É—aurani akan Addinin musulunci ba tare da wani tantama ko jin cewa ba a
kyauta mata ba,illa kara nuna mini d take lallai duk rintsi ka da in bari zuciyata ta yi galabar
rabani da addinin gaskiya.
Yanzu na girma na mallaki hankalin kaina na yi karatu kuma na san daraja da kimata ina son
rama juya mun baya da duniya da mutanen cikinta da suka yi tun kafin zuwana cikinta ta wata
sigar da ni kadai na san mai nake aikata,to amman kuma sai ana yi mini kallon mara adalci?
mara gaskiya kuma macuci? Aa sam ba zan fasa ba na tabbata akwai tarin mutanen da ke
fuskantar irin kalubalen da ni da mahaifiyata muka fuskanta.....
PAGE-1
Malaysia
Kwance Farouq ya ke a cinyar mahaifiyarsa tana shafa gashin kansa,kamar an tsikaresa ya
tashi ya zauna yana kallonta.
"Lafiya?"Maah ta furta.
Murmushi ya yi kafin ya ce,"Maah."
Ta amsa da ,"Yes me ya faru?"
Farouq ya ce,"me yasa duk da cewa sanadin shiga musulunci duniya da mutanen cikin ta suka
juya miki baya amman kin gagara fita daga ciki?"
Numfasawa ta yi ita ma ta saki wani Murmushi kafin ta ce,"Dalilan suna da yawa amman kuma
kafin nan ina so in fara sheda maka cewa babu wani ingataccen addini fiye da muslunci domin
kuwa shi ne haƙiƙanin addini na gaskiya ba tare da sirki ba, duk zuciyar da ta shaƙu da
musulunci zai yi mata matukar wahala ta iya fita cikin sauki,kuma duk idanun da ya yi tozali da
hasken musulunci ba zai taɓa iya bari ya rufe idanunsa ba domin komawa duhu ba,duk da cewa
na wahaltu na azabtu kuma na tozartu sanadin canja addini na izuwa musulunci amman ban
taɓa jin ba dadi ba ko alamun dana-sani ba a rayuwata sam sam ko kadan hasali ma a kullum
ina jin cewa wannan shine hukunci mafi kyawu da na taɓa yankewa a cikin rayuwata tunda
kuwa gashi karshe naci riba ko ince ina ma cikin cinta dumu-dumu.
Ina son musulunci,zan rayu cikinsa kuma zan mutu cikinsa da ikon Allah. "Maah ta karasa
maganar tana ajiyar numfashi.
Farouq ya ce,"wannan gaskiya ne amman kuma Maah tunda ki ka dawo nan mahaifina ko
danginsa ba su taɓa nemanki ko jin cewa basu aikata miki daidai ba,ba su taɓa tunanin
waiwayarki ko don saboda ni da na kasance jini a garesu ba?"
Maah ta ce,"A kan me zasu neme ni? A tunaninsu abun da suka yi shine daidai tunaninsu ni
kazamiyar kafirace da baza su iya haÉ—a jini da ita ba duk da cewa na jima da daina amsa
wancen sunan na shiga addininsu,suna son kansu fiye da kowa suna jin cewa kyara ko
tsangwama ga wanda ya taɓa kasancewa ba musulmi ba inya musulunta daidai ne bana jin
cewa akwai ranar da zasu ji cewa basu aikata mun daidai ba aransu kai kuwa ai basa fatanma
ka zo duniya tunda hasashensu na basu cewa katon arne za a haifo masu cikin dangi ba ma
wannan ba basu amince da cewa kai din nasu bane,gani suke ai kasancewata ba musulma ba
yadda na yi mu'amula da mahaifinka haka nake yi da wasu sun manta da cewa kaddara ta
wuce komai kuma ba a iya taɓa tsere mata domin a rubuce take ga rayuwar kowanni Ɗan
Adam sun yi mini kazafi sun kore ni sun wulakantani da ya kai inji cewa addinin ya fita akaina.
Duk da cewa ba duk musulman bane suke da hali da É—abi'a irin tasu domin kuwa na ga zahiri
yadda wasu yan kasar nan suka jani a jiki mussamman da suka fahimci dalilin kasancewata ni
É—aya da cikinka a wancen lokacin ba wai anan dinma ban fuskanci kalubale bane aa amman dai
da sauki kuma na samu wa inda suka karbeni hannu bibbiyu duk da cewa ana nuna masu cewa
ni kafirarce kuma kazamiya sun toshe kunnuwansu sun rufe idannunsu sun fuskanci abubuwa
da dama silata amman hakan bai sa sun gujeni ba sai ma kara kusantata da nuna mini so da
kauna *amman abun na gagara ganewa shine tsakanin su na cen da musulman nan masu practicing
addini da dukiyarsu zasu iya ba da komai nasu domin ci gaban addini da da wa inda kuma
koda suna da dukiyar ba za su iya badawa sai dai furuci da nuna cewa su musulmai ne su waye
masu kishin addini na hakika tsakani?*." Farouq ya ce,"Allah ya kyauta ya rabamu da sonkai irin na zuciya amman dai kam a tunani
wanda zai iya sadaukar da dukiyarsa domin addininsa ai ya gama komai kuma ubangiji da
zuciyar mutum yake aiki ba furucinsa ba addini ya kwadaita mana sadaka indai inada hali kuwa
ya kyautu dukiyata ta zam bango ga al'umma." Maah ta ce,"kai ke nan da wannan tunanin".
Farouq ya kara fadin,"Ina neman wata alfarma a wajen ki ban sani ba ko hakan zai samu
amman na miki alkawari indai bakya so to na hakura."
Maah ta ce,"In sha Allah ina jin ka."
Farouq ya ce,"Ina so inje Nigeria niger state wajen mahaifina da danginsa amman hakan ba wai
yana nufin kin kasa mun bane akwai bukatar lallai inje ne domin tabbatar masu da
kasancewarmu tare da tunatar da su abun da suka manta da kara nuna masu hakikanin
rayuwar musuluncin da suke taÄ·ama da shi ba tare da amfani da ainihin haÄ·ikaninsa ba."
Shiru Maah ta yi take yanayinta ya canja idanunta hawaye suka cika.
Da sauri Farouq ya ce,"Na miki alkawari indai bakya so na bari kuma na bar maganar bana so
inga ɓacin rai ko damuwarki."
Shiru ta yi can kafin ta yi murmushin karfin hali,"aa innace ma na hanaka ban kyauta ba
Farouq,ban yi maka adalci ba kuma na tauye ma hakki,ka je ka ga mahaifinka amman ka sani
zaka fuskanci kalubale kila ma fiye da wanda ni na fuskanta kuma bana da adireshensu ban
san ta ya zaka samo bayanai akansu."
Farouq ya ce,"kar ki damu da wannan abu ne mai sauki aguna karki manta yaron naki computer
titan yanzu zan iya binciko komai nasu a media."
Murmushi ta yi ta ce,"tabbas to ina yi maka fatan alkairi,Ubangiji ya baka sa'a kuma yasa tafiyar
da za ka yi ya zame ma alkairi yanzu yaushe zaka tafi?"
"Ni da zan samu flight ma zan wuce amman zan bari zuwa gobe ko jibi haka."
Maah ta ce,"iye wannan saurin fa?"
Dariya kawai Farouq ya yi.
Ta ce,"Shikenan Allah ya kaimu."
Ya amsa da Ameen kafin ya tashi ya shige dakinsa da sauri yana daukan computer.
Kai tsaye Javed ya ma magana.
"Friend ina tunanin gobe zan tawo In sha Allah."
Javed ya ce,"Ok Ma sha Allah daman kasan mun kammala komai zuwanka kawai muke jira."
Bayan sun gama magana Farouq ya shiga 5stars group yana fadin,"Hi guys na kammala komai
fa kan batunmu na yiwa yara mata marasa karfi training akan computer a niger state I think
gobe zan wuce so a tayamu da addua."
Deejerh ta ce,"weldone our mummunan mutum Allah ya bada sa'a i wish u all the best ba don
abubuwa sunyi yawa ba da bika ai."
Dariya Farouq ya yi yana fadin,"wa? Yaushe wannan anacin mijin naki zai bari ki bi a yanzu ana
ganiyar cin amarci ai kiyi zamanki kawai."
Dariya kawai Deejerh ta yi.
Khalil ya katse su da fadin,"Ma sha Allah weldone mutumina abubuwa na kyau Allah ya bada
sa'a saura aje can a bige da neman mata kuma."
Dariya suka yi duka Farouq ya ce,"kai ma ai kasan wannan dole ne ko ni ban bisu ba suna
ganin handsome guy suke ruÉ—ewa,kun ga bara inje in fara shiri ba time."
HaÉ—a duk abun da yake bukata zai tafi dasu ya yi dake maganar flight ma ya riga ya yi booking
tun kafin ya sanarwa Maah.
Washegari
Ya kammala shirin tsaf kuma jirgin safe ya yi booking sai da Maah ta rakasa airport har jirginsu
ya tashi kafin ta koma gida.
Jirginsu ya sauka a abuja daga nan ya hau motar da za ta kai shi Niger.
NIGER STATE
Minna
Tsaye yake bakin titi dauke da lemarsa a hannu dake anyi sosai yana jiran Javed yazo ya
daukesa.
Kamar daga sama ya ji saukar ruwan laka daga fuskarshi har jikinsa.
Daga idanun da zaiyi ya ga wata budurwa ce ke kokarin tada motarta.
Cikin fushi da takaici ya yi saurin karasawa yana fisgar hannun motar ya bude ya..........
[03/05, 6:48 pm] Xayyeesherthul-humaerathí ¼í½‚: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAGE-2
Ganin yadda ta nuna bata ma san ta aikata wani abu ya fusata shi,janyota ya yi daga cikin
motar cike da zafin rai.
Budurwace da ba zata zarce shekara ashirin da biyu ba irin dogayen matan nan farare masu
diri irin na Nufawa sanya take da farar da abaya da glass a idannunsa kallo guda za ayi mata a
tabbatar da cewa cikakkiyar yar boko ce kuma wayayya.
Kafin Farouq ya samu damar magana cikin sauri ta fisge hannunta tana binsa da wani irin
mummunan kallo.
A harzuƙe ya ce,
"How could you be so careless with your dirty car and splash muddy water all over my clothes?"
Gyara zaman glass din dake fuskarta Janinah ta yi kafin ta saki wani guntun tsaki cike da tsiwa
ta fara magana,"As I see, there's no problem with your eyes, but it seems you are acting like a
blind person. Why can’t you stay off the road? sannan batun motata kuma da kake alakantawa
da kazanta ai gwanda ni ba a titi nake tsaye ba tamkar mabaraciya." Daga hannu Farouq ya yi zai mareta.
Ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar rike masa hannu.
"Kuskure mafi girma da ka tafka a rayuwarka shine tunanin kai min marin kafin ma ka aikata
din,So Don't ever try it in ko ka aikata za ka san ni wace ce za ka san wa ka taɓa sai ka yi dana
sanin kasancewar ka a duniya ma gabadaya. "
"Oh do you have this confidence?"
Farouq ya fada.
Girgiza kai ta yi.
Kafin ta ankare kuwa sai jin saukar wani azababben mari ta yi a fuskarta.
Ya ce,"So na yi kuskure mafi muni ko? Zan yi dana sanin zuwana duniya ko? Alright duk ina jira
ko wa zaki kira ki kira ina daidai da ke da rashin kunyarki and sai na gyara miki zama sai na
koya miki ladabi da biyayya da kuma ba da hakuri ya yin da kika aikata ba daidai ba ga wani na
lura da cewa yan kasar nan kuna dauke da É—abi'ar cewa duk abun da kuka aikata daidai ne ko
da kuwa ba daidai din bane."
Cikin É—imaucewa Janinah na kuka ta je cikin laka ta dibo tamkar wacce ta zauce tazo jikin
Farouq tana shafa masa.
"Na kara,na ce na kara duk abun da za ka yi kai ma ka yi inka isa kuma wallahi sai ka yi dana
sanin sanya hannunka da ka yi a fuskata kazamin banza da wofi kawai." Ta karasa maganar ita
ma tana kokarin marinsa.
Mutane ne suka cika wajen wata mata ta rike Janinah ta na fadin,"Stop this please Janinah ina
cen ina jiranki ace kina nan kina fada me zai kaki fada da namiji akan titi for god sake?"
Kokarin fisge kanta ta fara yi tana,"ki bari in nuna masa waya taɓa nina ce yazo ya tsaya akan
titi yanzu haka ma irin matsiyatan nan ne yaje ya kwaso talaucinsa zai sauke akaina,ni ki barni
inje in rama marin da ya yi mun ya san bai ci banza ba."
Dariya Farouq ya yi yana,"please ku saketa tazo ta rama,yau zata ga yadda ake maida mutum
laka,tunda ita lakar kasa ta shafa mun ni kuma lakar mutum zan maidata sannan ni bana
bukatar in zama wani ai indai arziki irin naku ne bana so ko da kuwa a mafarkine wawiyar
yarinya kawai." Hakuri mazan wajen suka fara bashi kan ya yi shiru ya kyaleta haka yarinyar take bata da
kunya sam ga tsiwa da raini.
Aranshi ya ce,"in ko hakane tabbas indai Allah zai hadani da ita sai na gyara mata zama ta san
daraja da kimar mutane."
Ihu da sambatun da Janinah take ne yasa ya dawo daga guntun tunaninsa ana janta ta shiga
mota tana kokarin dawowa wajensa.
Wani dutse ta dauka ta wurga masa tana kara fadin,"Wallahi Allah duk sanda na sake ganinka
na rantse ba makawa sai na rama marin da ka mun ka ci bashi kuma kasa aranka sai ka biya
indai zan ganka a duniyar nan you must pay for it."
Da haka ta shiga motar da kyar.
Shi ko Farouq wani irin murmushi ya sake wanda shi kadai ya san dalilinsa da kuma ma anarsa.
Wani namiji agun ne ya ce masa,"Sir ko za muje in baka kaya ka canja tunda wannan duk ya
jike? Ka yi hakuri fa yarinyar ce sai a hankali tana ji da cewa danginsu na da kudi a tunaninta
zata iya komai ba komai bane."
Farouq ya ce,"kar ka damu abokina nake jira kuma...kafin ya karasa maganar ma sai ga Javed
na kiransa ya iso yana ta ina ne.
Daga kan da Farouq zai yi suka hada ido.
Da sauri Javed ya karaso yana,"Subhanallah what's wrong with your clothes?"
Mika masa hannu Farouq ya yi suka gaisa kafin ya ce,"ina zuwa na fara cin karo da marasa
kunyan yaran kasarku ta ɓata ni da motarta."
Javed ya ce,"Sorry wasu yaran in suka gansu da mota jin kansu suke a wani matsayi daban na
shirmen tunaninsu yanzu dole kafin mu wuce sai mun nemo hotel ka yi wanka ka huta ka ci
abinci ka canja kayan nan kafin mu wuce Mokwa."
Farouq ya ce,"Okay tom shikenan ai har sai da na mari yarinyar Allah ta bala'in bata mun rai ni
ban saba ganin irin wannan rayuwar ba wato in danginku na da kudi shikenan kuma lallai
kasarku da gyara."
Javed ya ce,"wasu kam sai hamdala Allah dai ya kyauta."
Kai tsaye hotel suka wuce suka kama daki Farouq ya shiga ya yi wanka ya yi sallah ya canja
kaya kafin ya ci abinci.
Javed ya ce,"zaka dan huta kafin mu ci gaba da tafiya ko?"
"Hutun jaki da kaya? Ai inaga gwanda kawai mu karasa sai ayi hutawar mai gabadaya. "
Farouq ya fada.
Javed ya yi dariya.
"Alright mu je to."
Hanya suka dauka.
NIGER STATE/MOKWA
Da ke sunyi sauri tafiyar awa uku suka yi suka isa cikin mokwa.
Mokwa local government ne da ke cikin jahar niger state.
Gari ne mai kyau da kyawawa yanayi.
Garin ya kan kogin neja wanda ke taka muhimmiyar rawa a tattalin arziki na yankin.
Haka kuma tattalin arzikinsu ya dogara ne ta hanyar noma, filaye kusa da kogin neja suna basu
damar noma nau'ikan amfanin gona da dama kamar alkama,rake,riÉ—i,masara da shinkafa.
Sannan suna bawa kamun kifi mahimmanci saboda kogin da suke da shi hakan ya na samar da
sana'a ga mazauna yankin.
Suna da al'adu da dama tare da kabilu amman sai dai mafi akasarinsu nufawa ne.
Suna gudunar da bukukuwa na al'adunsu kamar su bukukuwan girki wanda ake shiryawa domin
girbe abun da aka noma,rites na wucewa shi kuma bikine da ake shiryawa matasa yayin da
suka kai wani mataki na rayuwa kamar shigar da su cikin manya.
Sai kuma bukukuwan aurensu wanda shi ma yake cike da kayatarwa da al'adu akwai kuma
bikin girmama kakani ana gudanarwa domin tuna gudunmawar da kakanni suka bada ga
al'umma da kuma bayyanar da hikimarsu ga matasa sai kuma bikin kirsimeti da sallah kamar
yadda sauran jahohi da garuruwa ke yi.
Suna da sarauta mai karfi mai karfi da tsari wacce ta hadda da sarkin gari,kakakin gari,sarkin
noma,sarkin kudi,sarkin Al'adu da sauransu.
Farouq sai kalle kalle yake yi karshe dai ya kalli Javed ya ce,"amman wannan garin na ku ya
matukar tafiya dani tsarinsa da komai tamkar wani babban birni a kasar waje kai kace ba a
Nigeria muke ba."
Javed ya ce,"gaskiya kam kowa na aikinsa bisa tsari ba wasa damuwar kowa yafi wancen yin
abun da ya dace