Showing 18001 words to 21000 words out of 62597 words

Chapter 7 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

1644

taba gigin karya mun doka sai kai? Kana jin ka
isa kenan ko kuma zama da wancen ne ya janyo?"
Ya karasa maganar yana nuna Farouq dake tsaye yana bin kowa da kallo yana ganin ikon
Allah.
Caraf Kilishi ta ce,"Yoo shi ne ma mana shi ne zai ja shi yawon ma kuma ni ina zarginma gidan
rawa ya kai shi domin yanayin yaron nan sam ba na kirki bane kila ma ba wani dan kasar waje
bane yafi kama da sadakayalla,kana ganinsa ka ga munafu....

Tsawar da Abba Malik ya yi mata ne yasa ta shirun dole.
Cikin ɓacin rai ya ce,"Wato ke dai babu alkairi a bakinki ko? Sam ke ba kya nufin kowa da alkairi
ne sai sharri? Ki rabani da wannan mummunan dabi'ar taki Kilishi."

Kau da kai ta yi tana faɗin,"Ai daman kai baka son gaskiya ni kuma wallahi ko za a mutu sai na
faɗi gaskiya ehee."
Shi dai Farouq yana ta binsu da ido.
Gyaran muryan da Mai Martaba ya yi ne yasa dukkaninsu yin shiru.
Jan numfashi ya yi, cikin isa da izza ya ce,"Bakonka na da zaɓi biyu, ko ya bi dokokin wannan
masarautar ya zauna ko akasin hakan ya barta,sannan daga yau ba za ku kara fita daga kai sai
shi ba za a hadaku da ɗaya cikin dogarai yana lura da motsinku in aka kamaku da aikata wani
abun da ba daidai ba babu shakka kowannenku ya karbi hukuncin bulala ashirin sannan kuma
in an kammala hukuncin bakonka tafiya zai yi ba zai kara zama ba ya tabbata dai kenan muddin

yana son zama sai ya bi tsari da dokokinmu."
Yana gama faɗa ya fice.
Tsaki Kilishi ta yi azahiri wanda ya bayyanar da ɓacin ranta ta fice,ita ma Janinah ta bi bayanta.

Sauran matan da mazan ma duk suka fice sai Hajiya Kaka,Abba Malik,Farouq da Javed.
Abba Malik ya kalli Farouq ya ce,"Malam Umar sai dai ana hakuri fa nan ba kamar can ba
mussamman wannan masarautar ana riko da al'ada sosai tamkar addini. "
Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Hakan ma yana da kyau ai."
Hajiya Kaka ta ce,"Gashi duk kun jike,ku je kuyi wanka ku canja kaya ku samu ku kwanta in
kuma ba za ku iya ba ko mu je in muku?"

Dukkaninsu basu san lokacin da dariya ta subuce musu ba da jin maganar Hajiya Kaka duk da
cewa basa cikin yanayi mai daɗi.

Abba Malik ya ce,"Hajiya ke ina ke ina yiwa garadan nan wanka,mu je dai ki kwanta."
Ya karasa maganar yana riko hannunta.
Taɓe baki ta yi ta ce,"Yo miye a ciki dukkannsu mazajena ne ai in sun gagara sai in saɓesu tas
ba don jikin tsufa ba ma har goyasu zan da majanyi."
Abba Malik ya ce,"Ah lallai wa innan Mazaje ana ji dasu."
Farouq ya ce,"Yanzu dai mun yafe ki je ki huta sai da safe ko yan matana."
Ya karasa maganar yana bata hannu suka tafa kafin suka fita suma suka koma bangarensu.
Bayan dukka sunyi wanka sunyi sallah gabadaya ko abincinma sun kasa ci mussamman Javed
ya zauna ya yi shiru a falon.
Farouq ya zauna kusa da shi yana,"Ban san ta yadda zan fara baka hakuri ba domin dukkanin
abun nan da ya faru nine sila,Don Allah ka yi hakuri gobe zan koma hotel in sha Allah ba zan so
ace sanadina kana samun saɓani da family dinka ba."

Javed ya ce,"Ya Subhanallah ka daina fadan cewa za ka tafi hotel,ba wani hotel din da zaka
tafi kuma ni ba abun da ka zama sanadi a gareni sai alkairi ni kawai na gaji da wannan tsarin ne
na gidan nan ba zan jure ci gaba da rayuwa cikinsa ba ace wai mu bamu da yancin kanmu
kwata-kwata? Ba mu isa muyi rayuwar da muke so ba sai wacce aka tsara mana? Ba zai yiwu
ba ina ji araina akwai abun da ake aikatawa da ba daidai ba cikin wannan masarautar."

Farouq ya ce,"Ni dai ka yi hakuri kuma ka maida komai ba komai ba indai da gaske baka so in
koma hotel to ka ci gaba da bin umarnin Mai Martaba za ka ci ribar rayuwa."

Javed ya yi ajiyar zuciya ba tare da ya ce komai.
Tashi Farouq ya yi ya dauko masu Drink da snacks ya mikawa Javed kafin ya zauna
yana,"Yawwa ni kam ya batun wancen Bikin Ganin ne? yaushe ne? Ina son zuwa fa."

Javed ya yi guntun tsaki "wallahi ni na manta ma amman dai a cikin satin nan ne za a tafi ni fa
lamuran gargajiyan nan ba sonsu nake ba a dole nake bi,kuma ni yanzu ban san ya za muyi ba
mai martaba ya ce ka da ya kara ganinka akan abubuwan da suka shafi gidannan da ma

Al'ada."

Farouq ya numfasa,"Alright ba matsala karka damu dani."

Javed ya ce,"Amman kuma kana son zuwa ai."
Farouq ya yi murmushi,"Eheen ina so amman kuma son da nake zai iya ja maka matsala ni
kuma bana so in kara saka cikin wata matsalar."

Javed ya ce,'Kasan yadda za ayi?"
Farouq ya girgiza kai,"Aa sai ka faɗa."

"Zan bi ayarin yan gida mu tafi kai kuma sai in hadaka da wani ko cikin abokaina ne ka ga ba
wanda zaiyi tunanin zaka je sannan kuma sai ka yi kokarin yadda baza ka gamu da Mai
Martaba ba, ko kilishi dama sauran yan gidan."

Farouq ya ce,"Ba matsala zan so ma inje ni kadai domin in kara ganin gari karka damu komai
zai tafi daidai In sha Allah."
Da haka suka dan yi hira kafin Javed ya fara tafiya daki ya kwanta ya bar Farouq shi kadai.
Waya suka dunga yi da Zoe yana tsokanarta tana tsokanarsa sunata dariya sai da ya kalli
agogo ya ce,"Madam yanzu a Nigeria karfe uku ne,ina son inyi Tahajjud Prayer."

Zoe ta ce,"Ah Har cikin dare kuna Sallah kenan ban da guda biyar din da kuke yi?"

Farouq ya ce,"Nop Wannan Ita ba farillah ba ce sunnah ce ma ana ba wajibi ba bace amman
kuma tana cikin sallar da ake matukar so a cikin musulunci kuma tana da matukar muhimmanci
domin yana ƙara kawo kusanci tsakanin bawa da ubangiji sannan ana yinta ne karshen rabi na
dare lokacin aka dauka a matsayin mafi alheri don sallah da addua tare da tabbatuwar biyan
bukatu domin a lokacin Ubangiji yana amsa bukatun bayinsa babu shamaki."

Zoe ta numfasa ta ce,"Da kyau kuma har guda nawa ake yi?"

"Ba adadi zaki iya yin raka'a biyi ma kiyi sallama ki roki ubangiji shikenan wannan raka'a biyun
ta fi duniya da ma abun da ke cikinta inko kina so zaki iya yin takwas har fi ma." Farouq ya faɗa.


"Kenan dai ita wannan sallar in anyita ana samun biyan bukata ko?"

Farouq ya ce,"Yes In sha Allah mussamman kasa aranka zaka samu abun da kake nema din
wajen ubangiji. "

Zoe ta ce,"Sai na ji ina son yi da ace ba matsala zan iya da yau na tayaka nima in roki Allah ya
biya mun bukatuna kuma ma time dinmu ba daya ba zan iya?."
Farouq ya yi murmushi,"Mai zai hana? Ai kuma yanzun dare ne ba sai lokaci daya ba,yanzu zan

je da wayar toilet muyi alwala kiyi duk yadda na yi sai muzo mu yi sallar ma tare."
Hakan kuwa aka yi suka yi alwala yana mata bayani ta dauko gyaranta ta yi rolling ta dauki wani
dankwali ta shimfida matsayin sallaya suka fara sallah tana kallon yadda Farouq yake ita ma
tana yi har suka idar.
Rufe ido ta yi ta daga hannu sama tana addua ,"Allah ka bani komai da komai ka kara mun
kyau,kudi,jin dadi,lafiya,hutu da komai da komai Allah jikina ya yi kyau sosaiii."
Da karfi take adduar idonta a rufe.
Dariya ce ta suɓucewa Farouq ya ce,"To Amin wato harda kyau bayan wanda kike da shi."
Alama ta masa da hannu a baki ,"Shiiiii." Ka yi shiru.

Ta ci gaba da cewa ,"Allah kasa in samu masu zuwa Nigeria in dauko Farouq in gudo da shi."
Shi dai kallonta yake kawai yanata dariya.
Sai da ta gama jero adduointa kafin ta ce,"Eheem kai ba kasan ba kyau mutum na addua ana
magana ba zaka sani."
Ya yi dariya,"To ai na ga kin dage ne harda batun kyau."

Sigina ta masa ta ce,"Eheen naka wasa ne sai ka kasa ganeni ai innazo daukanka." ta karasa
maganar tana hamma.

Farouq ya kara dariya kafin ya ce,"To Shikenan yanzu dai kije ki kwanta ni zan fara aiki."

"Alright Goodnight. "Ta fada.

Farouq ya ce,"Nighty Night byee."
Da haka suka katse kiran ya dukufa kan System kamar yadda ya saba.

Yana kunnawa ya ga alamun yana kokarin kawo masa hari system din ta nuna akwai matsala.
Cike da mamaki ya fara bi ya rasa gane wane ne ke son bincikar bayanansa duk da cewa
yasan ba za a taɓa samu ba muddin in ba shi ya bada kofar hakan ba.
Abun da ya matukar bashi mamaki shine da ya duba location ya ga abun da ake son yi din a
gidan ne.
A tunaninsa error ne ko kuma location dinsa system din ke basa amman duk dubawan da zai yi
babu shakka mai kokarin bincikarsa na cikin gidan.

Dakin Javed ya je ya gansa yana barci cikin kwanciyar hankali har system dinsa ya kunna
amman bai ga wani abu makamancin hakan ba.
Ji ya yi kansa ya fara ciwo domin abun ya daure masa kai matuka.
Ya dafa kansa yana zama gefen gadon tare da tafiya dogon nazari.


Misalin karfe Goma na safe Kilishi ce zaune da Janinah a falonta.
"Aunty Kilishi ni wallahi jiya na ji haushi sosai da Mai Martaba bai kori wancen gayen ba."

Tsaki Kilishi ta yi kafin ta ce,"Ke ko ni Janinah? Wallahi da abun na kwana araina ban san dalili
ba amman kullum inna gansa kara tsanar yaron nake wallahi amman kar ki damu faɗan yanzu
nawa ne ba naki ba,ni na san matakin da zan dauka sai ya yi danasanin zuwansa kasar nan
inma da gasken zuwa ya yi bare kuma shigowarsa gidan nan." Ta karasa maganar tana cije baki.

Janinah ta ce,"Aunty ki fadamun in tayaki mana."
Murmushi Kilishi ta yi kafin ta ce,"Kar ki damu zan fada miki bari in kammala shirina."

Farouq na office a digital craft kokarin bincikar mai bin diddigin sa yake tun jiya yanata fama
karaf ya ji wayarsa na kara alamar shigowar sako.
Yana dauka......
[18/05, 2:54 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!

*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-12

Ya ga text message ne aka turo "Ko da ka shahara tarwatsa tsari da shirin wasu,ina jadadda
maka cewa ba za ka taɓa kaucewa nawa ba,kila kana jin kanka cewa yanzu kana rayuwa ne a
fili saɓanin cewa ni kallonka nake a cikin rami mai zurfi takurararre cike da duhu mara
misaltuwa."
Murmushi Farouq ya yi ya gyaɗa kai kawai ya ajiye wayar yana ci gaba da duban system dinsa.

Shigowar Javed ne ya katse shi da fadin,"Oga Mun gama,lokacin ka ne yanzu."
Tashi ya yi yana ,"Okay to."

Tashi ya yi ya tafi lecture room din.

"Good morning class."

"Morning Sir."
Suka amsa

"OYaa On your systems Yau za mu yi bayani ne akan White Hat Hacker,na san da cewa

dukkanin ku kun san wane ne White Hacker to amman ta ya yake gudanar da aikinsa na shiga
na'ura? Me da me yake bukata?"
Ya karasa maganar yana zama gaban system dinsa kafin ya ci gaba
"Karku manta sai har an bashi izini kafin yake fara gudanar da aikinsa kuma abu na farko da
yake yi shine Binciken tsaro wato
(security assessment) sai kuma gwajin shigarwa (penetration testing) a karkashinsa shi ne ake
kirkirar kwayoyin yanar gizo da kirkirar hanyoyin kariya masu inganci da karko

Kayayyakin amfani da aikinsu wato Utilizing tools

Na farko akwai Nmap: Don nazarin hanyoyin sadarwa da gano na'urorin da ke haɗe (for
network scanning and identifying connected devices)
Na biyu Metasploit: Don gunadar da hare-hare da kuma gwajin rauni (for executing attacks and
testing)
Na uku WireShark: Don nazarin zirga-zirgar bayanai a cikin hanyar sadarwa (for analyzing data
traffic within the network)

Sai kuma Access Control tsarin kariya ke nan
Suna amfani da tsarin kariya domin tabbatar da cewa suna kan tsarin da aka ba su izinin aiki
akai.

Sannan Tantancewa da rahoto ma ana Evaluation and Reporting
Bayan an kammala gwaji ana tantance bayanai kafin a rubuta rahoto wanda ya kunshi raunin
da aka gano da shawarwarin yadda za abi domin yin gyara.

Wannan kenan kafin kuma su shiga kan aikin inganta tsaron,yana da matukar mahimmanci abi
wannan matakan domin in babu su ba za a taba samun abun da ake nema ba kenan kuma
akwai bukatar ku fahimta da kyau."

"Yes Sir."
Suka furta.
Tun kafin ya bada izinin tambaya Meemah take ta daga hannu.
"Go on Memah." Farouq ya fada.
Tashi ta yi ta ce,"Sir yanzu kenan ko waya tace nasa security wanda ba mai karfi ba akwai
wanda yana iya zuwa zai cire?"

Farouq ya ce,"Sosai ma,musamman ku da ke sa password ko pin mara karfi fada mun
password dinki inji yanzu zan iya fada miki cikin minti nawa zan iya kwamushesa ba tare da
kinsani ba ma ."

Ta ce,"Mima12 ne Sir."
Farouq ya ce,"A cikin 11 minutes zan iya cire password din wayarki ko kasa da hakan
ma,shiyasa da an samu kuskure an sace wayoyinku cikin sauki ake kwasar bayananku, yanzu

tunda kin fadamun wannan canja wani ki bani in gwada cirewa."
Canjawa ta yi ta bashi wayar.
Cikin 8minute kuwa ya cire password din sunata mamaki.
Meemah ta ce,"To Sir a koya mana yadda ake cirewa kuma a koya mana yadda zamu sa
security mai kyan da ba za a iya canjawa cikin sauki ba."

Farouq ya ce,"For now dai yanzu koya muku yadda zakuna duba karfin password kafin kusa
ako ma miye naku amman yadda ake cirewa ba mu zo nan ba."
Suka amsa da ,"Okay Sir."

Farouq ya ce,"Yawwa dukkanin ku ku shiga Google a systems din ku ku yi searching Password
Strength Meter. "
Cike da zakuwa dukka suka yi.
Farouq ya ce,"Kowa ya yi?"
Suka amsa
"Okay za ku ga an rubuta TYPE A PASSWORD ko kamar haka."
Ya nuna masu a system dinsa.
Ya ci gaba da fadin,"Yawwa nan zai na fada mana karfin password din da zamu rubuta da
lokacin da za a iya dauka kafin a iya cirewa yanzu ni bara in gwada rubuta nawa so simple
amman kuma very strong bari mu ga na rubuta [U@M@R_F@R@Q],kun ga dai yadda na
rubuta ko me kuka sunsa?" Karantawa suka yi duka
"Very Strong Password,Time to track your password 1million years. "
Suka karasa fada cike da mamaki suna bude baki.
Farouq ya ce,"To yanzu kowacce ta rubuta a system dinta muga."
Dukkaninsu suka rubuta hakan ya fito sunata jin dadi.

"To yanzu kunga anan zaku iya rubuta kowanni kalan password ku duba ingancinsa kafin kusa
a wayarku ko a system dinku zai na indicating maku in mai kyau ne ko akasin hakan."

Da murnar su suka ce,"Thank you Sir."
Fita ya yi ya barsu sunata faman gwada password kala kala.

Farouq na komawa office ya samu Javed na waya Yayansa ya kira yana sheda masa cewa
gobe zasu wuce bida domin jibi za a fara bikin gani.
Javed na gama wayar ya ce,"Yawwa ka ga daman yau za a tafi hutu ba mu da matsala
dangane da makarantar nan domin jibi ne ma wai ashe za a fara bikin zamu koma gida da wuri
domin inje in fara shiri."

Farouq ya ce,"Okay to shikenan Allah ya kai mu amman ni nidai ina so inji tarihin garin bida
dinnan da aketa batun acen asalin sarki yake."
Javed ya ce,"Wannan in ka samu Hajiya Kaka ai labarin tarihi sai ka ture ta sha bamu amman
yanzu innace zan fada ma na tabbatar da cewa ba zan baka in details kamar ita ba."

Farouq ya ce,"Ai ba na ma son naka ni da nake da Mata guda,yau muna komawa a part dinta
zan tare gaskiya. "
Dariya Javed ya yi ya ce,"To mai mata."

Da haka suka kammala wuninsu na ranar har suka koma gida kamar yadda mai matarba ya
umarta kuwa akwai mai binsu duk inda zasu je.

Bayan sun koma masarauta sun idar da sallar isha Kai tsaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login