Showing 45001 words to 48000 words out of 62597 words

Chapter 16 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

2364

wanda abun
da zai sa in ba an fada ba mutum ba zai gane bane shine banbancin yanayin shiga da kuma
gyara domin kowa yaga ceo yasan cewa dan gyaye na karshe wanda hakan kan iya ɓoye
shekarunsa tamkar saurayi. Numfasawa ya yi domin ya ma rasa abun faɗa.

Ceo ya kalli Javed yana,"Ke nan wannan yaron Abdul-Raheem ne?"
Farouq ya girgiza masa kai.

"Ikon Allah, alamu ya nuna kasan abubuwa da dama har ma wa inda ni ban sani ba garin ya
ya?" Ceo ya fada.

Farouq ya yi murmushi,"Baba Malam Shi ya sanar da ni komai."

Bude Ido Ceo ya yi yana fadin,"Yana raye?"

Farouq ya ce,"Kwarai kuwa,kuma yanzu ma wajenshi zamuje domin Ka dawo gida kowa sai ya
san da zamanka kuma sai na kwanta ma yanci da hakikinka."

Ceo ya ce,"Aa ba za ayi haka ba,Ni bana son tashin hankali kai ma barin gidan zaka yi,ba dai ni
kazo nema ba? Ai gani nan ka sameni ko? To tafiya zamuyi. "


Farouq ya ce,"Ka yi mini alfarma matsayin Ɗanka kuma ka yi mini alkawari ba za ka ƙi aminta
da duk abun da zance ba ina so ka yarda dani,duk abun da zanyi bana zalinci bane ko na cutar
wani illa tsantsan gaskiya da adalci,sannan na tabbatar da cewa mahaifiyarka zata fi kowa
farinciki da ganinka."
Har cikin ransa yana jin tsoron duk wani abu da zai haɗa shi da Abdul-Raheem to amman kuma
yana matukar kaunar Hajiyansa sannan baya so ya yi abun da zai bakanta ran Ɗansa wanda ya
fidda tsammani da kasancewa da shi,ba yadda ya iya haka ya amsa.

Kai tsaye wajen Baba Malam suka wuce,shi ko Mai Martaba tunda ya ga tarwatsewar tulunsa
yasan cewa tabbas wani babban lamarin ya kara dumfaro shi.
A firgice ya tashi yana sambatu.
"Tabbas in dai Abdul-Rasheed ya shigo gidan nan an tabbatar mun da cewa dukkanin sihirin da
na yi zai tarwatse,na shiga uku,shi ne? Yana rayen dai kenan? Aa." Ya tashi yana kai kawo.
Wata irin busa da ya jiyo anyi ne ya kara tarwatsa masa tunani a hanzarce ya fito tare da
dukkanin mutanen gidan ana cincirindo.

Wata irin iska da guguwa ce suka fara tashi....
[26/06, 6:34 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON

ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAGE-27

Suna zuwa daidai gidan Baba Malam suka tsai da motar,dake yana zaune akan tamburma ya
shingiɗe da bango,idanunshi na kansu ganin suwaye haka.
fitowar da Abdul-Rasheed zaiyi kuwa mamaki ne ya kasa ɓoyuwa a fuskar Baba Malam,tashi ya
yi yana fadin,"Abdul....Abdul..Rasheed ko...ko..dai...ida..nuna..ne." ya karasa faɗa yana
ƙarasawa gareshi tare da shafa shi domin tabbatar.

"Babu shakka Mutum ne dai gabana ba Aljan ba." Ya furta.

Murmushi Ceo Abdul-Rasheed ya yi yana fadin,"Baba Malam ni ne,mu je mu zauna."
Ya faɗa yana rike masa hannu suka ƙarasa taburmar suka zauna duka.

"Lallai Ubangiji ba azzalimin bawanSa bane,ko da ban fidda yaƙinin cewa za a ganka
ba,amman ban taɓa tunanin cewa zan ganka cikin aminci kamar haka ba, a zato da tunanina
amman da ke Allah na tare da bayinsa ga ka a halin da ban taɓa hasashe ba."

"Ai kuwa wannan duk kudirace ta Ubangiji da karfin ikonsa tare da kariyar da yake bawa
BayinSa." Ceo ya faɗa.

"Lallai kam ba bu shakka. "Ya tsagaita maganar yana kallon Farouq kafin ya ce,"Lallai ka cika
Ɗa na haƙiƙa,ka cika Ɗan da duk wani uba zai yi alfahari da kai Maddalla da samun irinka."

Ceo ya ce,"Ya sheda mun cewa agunka ya samu dukkanin bayanan komai da komai nima banyi
tunanin cewa zan riske ka araye ba ko dayake ma kwata-kwata araina kimanin shekarun da
suka shuɗe ban taɓa jin sha'awar ko tunanin dawowa cikin garin Niger ba,amman da yake Allah
ya riga ya tsara komai sai gashi na zo ta dalilin bikin yaye dalibai wanda kuma hakan shi ne
silar bayyanar Umar a gareni."

Baba Malam ya ce,"Alhamdulillah Alhamdulillah ba abun da za mu ce da Allah sai godiya
garesa,na tabbatar da cewa a yanzu bayyanarka ya amsa cikin garin niger da jahar mokwa da

kewayenta,kai tsaye yanzu abun da ya rage maka shine sanya kafafunka a cikin gidan
mahaifinka."

Yana faɗan hakan Ceo ya ji gabansa ya yi wani irin mummunan faduwa.
Kallonsa Baba Malam ya yi ya ce,"Ka tsorata ko? Ka da ka damu kafarka na shiga cikin gidan
dukkanin wani tsoro da firgici ya kare."
Tashi suka yi suka nufi gidan kaitsaye.

♡♡Dokunan da ke gidan Sarkin al'adu ne suka fara tada wannan ƙurar,suna yin wata irin ƙara
da kuka mai tada hankali, wanda ke kara tabbatar da faruwar wani babban al'amari,
ba su daina wannan kukan har sai da Yarima Abdul-Rasheed ya sanya kafafunsa a cikin
gidan,tare suka yi shiru suka daina tsalle tsalle,sulalewa sukai suka zauna a ƙasa.

Shi kuwa Abdul-Rasheed a lokacin ya ji tamkar an zare masa ilahirin wani nauyi da ya dauka na
tsawon shekaru a tsakiyan kansa,kwakwalwarsa da gangar jikinsa,wani irin karfi da jarumta ya ji
yana riskarsa tare da duk wata izza da kamala ta jinin sarauta.


Gabadaya mutanen cikin gidan sun yi cincirindo a katafaren filin gidan cike da zaƙuwa tare da
damuwar ganin lamarin da ke daf da afkuwa.

Bayyanar Yarima Abdul-Rasheed ne ya ƙara gigita Hajiya Kaka,Mai Martaba
Abdul-Raheem,Abba Malik,da Kilishi.
Mussamman Hajiya Kaka ji ta yi kamar ana dawo mata da wasu lamura da suka faru a
rayuwarta ta baya.
Muryarta na rawa jikinta na ruwa ta daga hannu tana nuna shi da fadin,"Ya....ri..ma."
Tana karasa faɗan hakan ta faɗi warwas a ƙasa sumammiya.
Da sauri Abdul-Rasheed ya ƙarasa gareta yana fadin,"Subhanallah Hajiya."
Dakatar da shi Mai Martaba ya yi yana fadin,"baka da izinin taɓata akan me ba mu san kai waye
ba."
Kautar da Kai Yarima Rasheed ya yi yana faɗin,"In kai ba ka san ni wane ne ba,ita tasan ni
wane ne."
Ya bangajesa yana daukanta sannan ya kalli Farouq yana,"Ku dauko mota akaita asibiti."
Abba Malik ma ya karasa hawaye na zuba a idanunsa ya kasa furta komai.
Kilishi kuwa sai kame-kame.

Mai Martaba ya ce,"Ba a zuwa asibiti a cikin gidan nan muna da masu lura da komai don haka
ba mai fidda ta."
Ya karasa maganar yana umartar dokarai da kar su bar kowa ya fice daga Masarautar.

Yarima Rasheed zaiyi magana kenan Baba Malam girgiza masa kai yana fadin,"Aa kar ka damu
a shiga da ita ciki nan dinma zata samu waraka In sha Allah. "

Hakan kuwa ya kasance,ana shiga da Hajiya Kaka ciki Mai Martaba ya kara umartar dakarai
kan cewa a kara tsaurara tsaro kuma kar abar kowa ya fita sannan kar kowa ya fita kafin ya
shige ciki shima.

BabanGanye da tawagarsa ne kan Hajiya Kaka.
Ya bata jikon magani cikin ikon Allah kuwa ta farka.
Tana farkawa ta fara kuka tana rungumar Yarima Rasheed "A kullum ina jinka araina amman na
rasa dalilin kasa furta komai dangane da kai kuma ban da dukkanin amsoshin tarin tambayoyin
da suke danƙare akaina ,na kan ji cewa tamkar wata rayuwace wacce na yi a cen wata duniyar
ba wannan ba kuma innace zan zurfafa kan tunaninka na kan fita a hayyacina."
Rungumeta shi ma ya yi ya ce,"Na dawo gareki Hajiyata,In sha Allah daga yanzu ba za ki kara
gagara samun sukuni akaina ba, haka kuma dukkanin wani shamaki da ke tsakaninmu ya kau
har abada zamu ci gaba da rayuwa a tare kamar farko."

Jammal babban yayansu Javed ne ya ce,"Mu kam dai an bar mu cikin duhu,a fahimtar da mu
meke faruwa Don Allah."
Dukka sauran ma suka girgiza kai alamar suma suna da bukata.

Kallon Baba Malam Yarima Rasheed ya yi ya ce,"Baba Malam wannan bayanin naka ne."

Idon Mai Martaba na kan Baba Malam ya kuresa.
Murmushi Baba Malam ya yi yana kawar da kansa kafin ya ce,"Wannan Wan Mahaifinku ne
Abdul-Rasheed domin kuqa su yan biyune sun taso tare sannan wannan da kuke gani shi ne
wanda akayiwa laƙabi da Yarima Rasheed tun yana yaro kasancewar an hasaso cewa shi ne
mafi cancantar zamowa magajin sarkin al'adu ga kakanku Marigayi Mai Martaba sai dai kuma a
lokacin da ya kamata ya hau karagar mulki adaidai lokacin lamura suka dunga tasowa marasa
dadi wanda a karshe ma an nemesa an rasa kuma bakin kowa ya rufe babu wanda ke tunanin
nemansa ko jin duniyar da yake sai yanzu da Ubangiji ya dawo da shi mu ka gan shi cikin
wannan hali da yanayi mai ky....

Kafin ya karasa Mai Martaba ya katse shi da fadin,"Baka faɗa masu cewa Arniya baturiya ya bi
ba domin babu wani batun ya ɓace,saboda soyayyar kafira arniya ya bar gidan iyayensa
tubabbiya."
Yana wa innan maganganun wani zafi Farouq yake ji a cikin ransa zuciyarsa na bugawa da
gudu gudu.

Yarima Rasheed da Baba Malam ne suka dakatar da shi da ido da hannunsu.
Sannan Yarima Rasheed ya ce,"Ai wa inda basu da addini ake kira da arna kafirai kuma suna
nan a ko ina har ma anan sannan a wajen Ubangiji ba ruwanShi da wannan tubabbiyace ko an
haifeta a musulunci zuciya da aiki kawai yake duba."

Cikin Daga murya ya ce,"Dakata,me ka sani a musuluncin? Har kai kanka yanzu kana kallon

kanka a musulmi ne a yadda kake? Ni ina tantama ma da kyar in ba tajaka kun kafirci duka
ba.......
[28/06, 1:55 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAID ADVERT

INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAGE-28
domin ko a yanayin shigar ma kadai ya isa ya bayyanar da cewa ka jime da ficewa daga cikin
addininka tunda daman cen ba so kake ba ."

Tsilif cikin bacin rai Farouq ya zo ya tsaya gaban Mai Martaba yana nuna ma shi yatsa,"Shin an
ce maka addinin musuluncin ta shiga ake gane haƙiƙaninsa? na ba zan yi mamakin jin hakan
ba domin yau na ƙara tabbatar da cewa kai ɗin kasurgumin jahi....
Kafin Farouq ya ƙarasa Yan fada suka dakatar da shi suna riƙeshi da fadin,"Ahir dinka,Mai
Martaba ba tsaran ubanka ba ne bare kai,hattara dai."
Bige su Farouq ya yi ya zame jikinsa,za su yi kokarin ƙara rike shi Mai Martaba ya dakatar da
su,"Ka da ku damu da wannan rainon kasar waje irin ta tsagera ne."
Ya kalli Farouq din shi ma yana nuna masa hannu,"Ina umartarka da ka fita a cikin lamuran
dangina,na yi maka duk wani kashedi da ya kamata amman tamkar ana ƙara maka karfi? To a
yau za ayi na karshe,ka fice ka bar gidan nan da kafafunka ko kuwa in sanya a fiddaka."

Murmushi Yarima Rasheed ya yi ya tsaya gaban Farouq yana faɗin,"Shi ba bare bane,sannan
ba zai taɓa barin gidan nan ba muddin ina cikinsa domin shi ɗin mallakina ne,Ɗana ne."

Kallon kallo aka fara yi.
Da sauri Abba Malik ya je ya rike hannun Farouq yana faɗin,"Ɗanka ? Ɗanka ne? Babu shakka
ranar da na fara ganin yaron nan jikina ya bani cewa shi din jinina ne,wani gurbi ne a garemu."
Yana ƙarasa fadan hakan ya rungume Farouq.

Hajiya Kaka ta ce,"Yarima, Umar Ɗanka ne?"
Girgiza mata kai ya yi yana faɗin,"Kwarai Hajiya jikanki ne."

Miƙawa Farouq hannu Hajiya Kaka ta yi ya ƙarasa ita ma ta rungumeshi,Maganar Mai Martaba
ce ta Dakatar da su da fadin,"Duk wannan shirine,Karya ne,ya je ya samo Ɗa ne kawai a kasar
waje ya turo mana shi domin leƙen asiri daga karshe ya zo ya ce Ɗansa ne da tunanin cewa
zasu ƙwaci sarauta da dukiya kuma mijin kafira ba zai taɓa jan ragamar sarautar Gidan Al'adun

Mokwa ba."

Murmushin takaici Farouq ya yi ya ce,"Kai Sarauta da dukiya ta dama,kuma batun da kake ta yi
na danganta Mahaifiyata da Kafirci ya isheka,domin babu kafiri sai mai mai dangata musulmai
da kafirci,Na lura da cewa shekara da shekaru kana nan kafe kan bakar dabi'arka na
tsangwama,kyara da tozarci ga tubabbu babu haufi kuma bana tantama a yanzu Ilimin addini da
kare hakkokinsa da mahaifinka take da shi sam baka da makamancinsa,Ubangiji da kanSa ya
furta cewa"َنيِذَّلٱَو ْاوُنَماَء ْاوُرَجاَهَو ْاوُدَهٰ
َجَو ىِف ِليِبَس ِ
هَّلل ٱ َنيِذَّلٱَو ْاوَواَء ْآوُرَصَنَّو َكِئ
ٰٓ
َلْو
ُأ
ُمُه َنوُنِمْؤُمْلٱ ا
ًّقَح ۚ مُهَّل ٌةَرِفْغَّم ٌقْز
ِ
رَو ٌمي
ِ
رَك
Waɗanda suka yi imani kuma suka yi Hijira suka yi jihadi a kan hanyar Allah, da kuma waɗanda
suka karɓi baƙuncinsu suka yi taimako waɗannan su ne haƙiƙanin muminai, suna da alƙawarin
gafara da kuma arziƙi mai girma."
Shin kai kana ɗaya daga sahunsu?
Kwatanta wa inda suka kasance akasin masu karɓar baƙuncinsu mene ne makomarsu?
Haka Ubangiji ya ƙara fadin"
َنيِذَّلٱَو ْاوُنَماَء ۢنِم ُدْعَب ْاوُرَجاَهَو ْاوُدَهٰ
َجَو ْمُكَعَم َكِئ
ٰٓ
َلْو
ُأَف ْمُكنِم ۚ ْاوُلْو
ُأ
َو
ِ
ماَحْر
َأْل
ٱ ْمُهُضْعَب ٰىَلْو
َأ
ٍۢضْعَبِب ىِف ِب
ٰ
َتِك ِ
هَّلل ٱ ۗ َّنِإ َ
هَّلل ٱ ِّلُكِب ٍءْىَش ۢ
ٌميِلَع
Kuma waɗanda suka yi imani bayan haka (Hijira) kuma suka yi Hijira kuma suka jihadi tare da
ku waɗannan suna cikin ku. Kuma ma'abota zumunta ('yan'uwa na jini) su ne suka fi cancantar
gadon junansu a cikin littafin Allah. Allah Masani ne ga dukkan komai."

Bara in tambayeka ma akwai wasu ayoyin muminai da Ubangiji ya kawo cikin Littafi mai tsarki
ka san me suke faɗa?
Faɗa mana tunda dai kana jin kanka a matsayin wanda ya fi kowa sanin addinin musulunci."

Gajeran tsaki Mai Martaba ya yi yana faɗin,"Mamaki nake,kai din har waye a musulunci za kana
tunanin akwai abun da ka fini sani,babu shakka muminai uku su ne, masu zalintar kansu,masu
matsakaita,masu yin kyawawan ayyuka."

Murmushi Farouq ya yi kafin ya ce,"Ko wannan jawaban naka kadai sun isa su ƙara tabbatar da
cewa babu abun da ka sani dangane da musulunci domin kuwa a cikin ayoyin Allah Ya kasa
muminai kashi uku:

Kashi na farko: Su ne waɗanda suka yi imani a karon farko tun Manzon Allah yana Makkah,
kuma suka yi Hijira tare da shi zuwa Madina, suka halarci yaƙe-yaƙe kamar Badr da Uhud da
sauransu.

Kashi Na biyu: Su ne Ansaru waɗanda suka yi imani bayan kuma suka karɓi baƙuncin Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam tare da Muhajirai kuma suka taimake su, dukkanin waɗannan
Allah Ya tabbatar musu da haƙiƙanin imani, sannan ya yi musu alƙawarin gafara na duk abin da
suka kasance a kan shi kafin imani, da kuma arziƙi mai girma da yake jiransu.
Kashi na uku:
Su ne waɗanda suka yi imani daga baya, daga cikin mutanen Makkah, waɗanda suka
musulunta bayan Manzon Allah Ya yi hijira kuma suka yi hijira suka bi shi suka yi jihadi tare da

shi, to su ma Allah Ya tabbatar da cewa suna cikin muminai, kuma za su samu abin da suka
samu na gafara.

Shin ko anan ka ƙara tabbatar da kima da darajar gami da alfarmar da Ubangiji ya bawa
Tubabbu wanda wa inda aka haifa cikin musuluncinma basa da shi?
Ba ma nan ba hatta hadisai Manzon Allah ya faɗi,"

1. نع ورمع نب صاعلا يضر الله هنع :لاق
لاق لوسر الله :ﷺW
مالسإلا" مدهي ام ناك ،هلبق ةرجهلاو مدهت ام ناك ،اهلبق جحلاو مدهي ام ناك ".هلبق

هاور ملسم E121F

Ma'ana: Musulunci yana shafe dukkan abin da ya gabata (na zunubi), Hijira tana gogewa, Hajj
ma haka.

Ma'ana duk abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login