Showing 33001 words to 36000 words out of 62597 words

Chapter 12 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

1633

fara sabon shiri da na shi
aikin,kowa ya san Abdul-Rasheed ne ya cancanci zama sarkin al'adu kuma shine wasiyar mai
martaba. Hakan yasa Abdul-Raheem ya shiga ya fita ya fara kokarin duk yadda zaiyi ya yiwa mahaifinka
Kurciya mai dauke da mutuwa da yazo mun da lamarin naki aminta da hakan karshe sai ya fita
sabgata ya bi hanyoyinsa tare da shiga kungiyoyi domin tabbatar da burinsa.
A karshe ya yi sa'a domin kuwa an wayi gari an tashi babu Abdul-Rasheed babu labarinsa
kuma bakin kowa a rufe babu wanda yake batunsa tamkar anyi ruwa an dauke,ya rufe bakin
kowa ta yadda kowa zai manta da batunsa inko mutum ma yyi kokarin tunasa ko tada zancen
karshe ya kan iya rasa ransa,Don dole aka naɗa shi sarkin al'adu na mokwa ya yin da ni kuma
ya yi fatali dani daga cikin gidan tunda dai ni ba zai iya mun komai ba kar tasan kar ne,to

wannan shi ne dalilin da yasa ba ka jin ana batu ko labarin mahaifinka hatta kakarku da ta fara
tuna shi take ficewa a hayyacinta domin ya riga ya yi aiki mai karfi akan hakan sannan yanzu
abun da zaifi daure masa hankali shine bai san da cikinka ba kuma a tunaninsa yanzu
mahaifinka baya raye tunda kurciyar mutuwa ya yi masa, mun yi artabu sosai nayi kokarin hana
shi aikata hakan amman na gagara yana amfani da shedanun aljanun da suka fi karfina ni kuwa
ina ganinka jikina ya bani cewa kai Ɗan Abdul-Rasheed ne."

Idanun Farouq ya yi jajur
Ba don namiji bane kuma jarumi hawaye ba zai taba saurin tsayuwa daga idanunsa ba bare ƙin
zuba.

Wata irin ajiyar zuciya ya yi
"Kenan dai yanzu ba asan inda mahaifina yake ba? Yana raye ko baya raye ?"

Baba ya ce,"Kwarai kuwa amman ina ji araina cewa yana raye,kuma yana rayuwa mai inganci
da jin dadi,kai zaka nemo shi amman ka sani sai ka yi taka tsantsan da Abdul-Raheem mutum
ne mai hatsari matuka yana kuma girmama al'ada da kiyayeta ba kadan domin ta hanyar yake
samun aiwatar da munanan lamuransa nima zan taimaka maka iya yina har mu kai ga cin
nasara domin akwai wani babban sirrin da na gano nake son sanar da mahaifinka in Allah yasa
ka nemo shi."

Farouq ya dafe kai yana,"Na fahimta,tabbas na fahimta kuma ba makawa indai mahaifina na
raye cikin duniyar komai nisa da fadin inda yake zan nemoshi da karfin ikon Allah."

Baba ya ce,"Allah ya baka iko amman ina kara jaddadda maka cewa ka yi a hankali domin
kuwa cikin daren jiya ma na jiyoshi yana zama da manyan muƙarabbansa iblis,ifrit,da su
zalambur,kuma duk akanka suke aiki."

Wani irin yanayu Farouq ya fara ji duk da cewa a zaune yake amman jiri yake ji idanunsa na
kokarin rufewa.
Murya na rawa ya ce,"Baba bara in tafi zan dawo."

Baba ya ce,"zaka iya tafiya ko in rakaka dai?"

"Aa na gode zanje ka zauna."

Ya fada yana tafiya.
Har gari ya yi haske rana ta fito.
Tafiya Farouq ya dunga yi kamar ɗan maye,a hankali har ya shiga part din Javed.
Yana shiga kuwa ya faɗi a kasa tum tamkar wanda aka hankaɗa.
Da sauri Javed ya tashi ya karasa....
[02/06, 6:28 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!

*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-20

Dakyar Javed ya yi kokarin daga shi ya shigar da shi ɗaki yana,"Subhanallah Oga me ya faru?
Lafiya?"
Daga masa kai ya yi alamar eh yana ajiyar numfashi.
Raɗaɗi da azabar da kansa ke yi masa tamkar zai tsage hakan yasa shi saurin rike wajen,daga
kan har gangar jikin ko ina ya dauki wani irin zafi tamkar wuta.
Javed da yaga lamarin kara girmama yake ya rasa yadda zaiyi da gudu ya fita ya kira
BabanGanye.

Aiko yana zuwa ya tafa kan Farouq da jikinsa sannan ya ce,"Harda ciwon kai ne ko?"
Nan ma daga masa kan kawai Farouq ya yi ba tare da iya furta komai ba.
BabanGanye ya kalli Javed yana fadin,"Daman ko dazu na kammala dafa ganyen dogon yaro
(Neem) da na ganyen ɗanyen allayahu wa inda daman su haɗi ne mussamman domin maganin
ciwon kai da zazzabi mai tsanani ka ga ke nan anyi sara akan gaɓa In sha Allah yana sha nan
da yan mintuna zai samu sauƙi amman in ce dai ya ci abinci?"
Javed ya ce,"Aa Baba bai ci ba gaskiya."

BabanGanye ya ce,"Dole sai ya ci abinci domin kuwa babu dama ya sha ruwan maganin nan ba
tare da ya ci abinci ba akwai matsala ko yane ana bukatar ya ci wani abu tukunna."

Tashi Javed ya yi yaje ya haɗawa Farouq kakkauran ruwan shayi,ya tallafa masa ya zauna
sannan ya samu ya sha ɗan kadan.

"Yawwa to da babu dai gwara babu dadi yanzu bara muga ko nan da mintuna biyar ne ruwan
shayin ya dan sauka da kyau sai asha maganin,ka san fa ba sai maganin bature bane ake so
aci abinci kafin asha,hatta namu ma na gida yana da ƙa'idoji,dokoki da kuma tsari."
BabanGanye ya faɗa.
Sai da ya dan hutu na mintuna kafin aka bashi ruwan maganin ya sha rabin kofi.
BabanGanye ya zuba masu wani a gora sannan ya ce,"Ga shi nan zuwa yamma zai iya kara
shan rabin kofi,sannan kuma a tabbatar ka da asha ya zarce kwana uku duk da dai ma na san
iya shan na yau ya isa zai samu sauki."

Javed ya ce,"Ok To Baba Allah saka da alkairi mun gode sosai."

"Ameen Allah kara sauki ko."
Ya fada yana kallon Farouq wanda idanunsa a rufe ma suke kam,haka kuma dayan hannunsa
na kan kanshi ya kankame ban da ruwan hawaye babu abun da ke kwarara daga idanunsa.

Zama Javed ya yi kusa da shi yana,"Oga ko dai wani abu ya faru ne? BabaMalam dinne?"

Girgiza masa kai Farouq ya yi.
Ban da tuna maganganun Baba babu abun da yake yi mussamman "Aka samu cikinka ba ta
hanyar aure ba...Ya yi wa Mahaifinka kurciya mai ɗauke da mutuwa."
Wa innan maganganu biyun ne suka dunga yawo a kwakwalwar Farouq.
"Me yasa Maah bata faɗa mun cewa bata aure aka same ni ba? Me yasa? shin yanzu mene ne
matsayin rayuwata? ke nan ba musuluntar da mahaifiyata ta yi ba ne kadai zai zame mun za
me mun kalubale ba harda kasancewata a matsayin wanda aka haifa ta haramtacciyar hanya?
duk da cewa ban ta so da son duniya da abubuwan da ke cikinta ba amman babu shakka a yau
na kara jin cewa dama ace ban kasance a cikinta ba, Astagfirrullah! Ubangijina na tufa ka yafeni
amman a yau kai kadai ka san zafi da ƙunar da nake ji a cikin zuciyata,na so in maida komai ba
komai ba in nemo mahaifina amman kuma yanzu ji nake na gaza ba zan iya ba! ba a haifeni ta
aure ba, na gama zama a kasar nan ban ga amfanin kasancewata anan ba na hakura da komai
domin sani ko nemo mahaifina baya da amfani gareni tafiya zan yi,tafiya zan yi."
Ya karasa laburta hakan a zuciyarsa yana ƙara sakin wasu zafafan hawaye wasu na bin wasu.

Cikin ikon Allah kuwa ciwon kan ya ragu masa cikin kashi ɗari bai fi saura kashi talatin
ba,sannan zazzaɓinma ya tafi.
Javed na komawa daƙin ya ganshi zaune ya yi tagumi,komawa ya yi ba tare da ya ce masa
komai ba ya dauko masa abinci.

"Oga ga abinci nan ka samu ka ci ka ga tun safe ruwan shayine kadai a cikinka." Javed ya fada
yana kokarin zuba masa.

Cikin muryar damuwa Farouq ya ce,"Aa kar ka zuba please ba zan iya cin komai ba a halin da
nake ciki yanzu kam bakina baya mun dadi komai ba dadi sannan ina ga gobe zan tafi indai na
samu flight. "

Ajiye Abincin ya yi cikin sauri ya karasa kusa da Farouq,"Subhanallah Oga me aka yi ma? ko
dai anyi ma wani abune a gidan nan? ka yi hakuri ka fadamun ko me ne ne Don Allah za a
gyara."

Murmushin karfin hali ya yi ya ce,"Aa Maahnah ce bata ji dadi ba bata da lafiya shi ne duk
hankalina ya tashi amman babu abun da aka yi mini a kasar nan ma duka."

Javed ya ce,"Ayyah dole ka shiga damuwa,Allah ya bata lafiya,amman dai in kaje ka ganta ta ji
sauki zaka dawo ko?"

Farouq ya ce,"In sha Allah. " a zuciyarsa kuwa cewa yake ,"Ni bama kasar nan ba duniyar
gabaɗaya ji nake tamkar in barta,in mutu in huta. "

Ranar wuni Farouq ya yi zuciyarsa cike fal da damuwa da ya fara neman flight kuwa cikin sa'a
ya samu wanda zai tashi gobe da yamma hakan yasa ya kudurta aranshi cewa gobe da sassafe
zai bar mokwa ya je Abuja domin anan zai hau jirgin.

Suna da meeting da 5stars wanda aka saba conference call tunda aka fara duk suka fahimci
cewa Farouq na da damuwa domin ko yar tsokanar da ya saba yi ma bai yi ba kawai komai
akace sai da ya bisu da Yes ko Okay.

Cikin zolaya Haidar ya ce,"Wannan fa ina jin sarautar ta motsa ne kodai a kira maka gimbiyar
taka ne?" Ya fada ya kwallawa Zeeyter kira.

Zeeyter na zuwa ta kalli Farouq duk da cewar a waya ne amman tabbas jikinta ya bata cewa
akwai babban lamari.
Ta ce,"Aa yanzu ku dai yau a yafe mana meeting dinnan,ku ci gaba da yi ni bara inje muyi na
mu da friend."

Khalil ya ce,"To ai muma duk jikinmu ya yi sanyi anya zamu iya wannan meeting din ? Kawai dai
a sauke na yau din ku je ku tattauna."

Farouq ya ce,"No ba komai fa a ci gaba kawai ban jin dadi ne."

"Aa kam an dakata ai kuma kar ka manta dukkaninmu ɗayane kuma ba zamu taba jin dadin
kasancewa a halin da muka ganka ciki ba." Zahra ta fada.

Zeeyter ta ce,"Yawwa Taurari biyar dina da aka hanani zama ta shida yanzu bara mu je byee
all,Oga muje."
Ta karasa maganar tana dagawa Farouq hannu.

Katse wayar suka yi duka.
Zeeyter ta kirashi privately
Ta ce,"Faɗa mun mene ne matsalar?"

Farouq ya ce,"Ko na faɗa wannan ba wacce za a iya mun maganinta bane."

"Ka manta cewa babu abun da yafi karfin Ubangiji ko da ace ya fi karfin mutum? Ai addua ma
takobi ce mai karfi ko and ban yi tunanin cewa akwai abun da zaka gagara faɗa mun ba kamar
yadda muka san damuwoyin juna. "

Numfasawa Farouq ya yi kafin ya ce,"So nake gobe in bar nigeria in koma malaysia ba zan iya
zama ba kuma ko na zauna ma babu amfani."

Zeeyter ta ce,"What?? Ban gane ba fa ai ba ka gama abun da ka je yi ba ko kuwq an samu
Baban ne?"

Farouq ya ce,"Aa."

"To me ne ya faru? Ko sai mun zo dinne dai,wani abu ake ma? Ka fadamun meke faruwa
please na shiga damuwa."

Zayyana mata duk abun da ke faruwa Farouq ya yi sannan ya ci gaba da fadin,"kin ga ke nan
zamana anan ba abun da zai janyo mun illa kaskanci da tozarci na tabbatar da cewa suka san
cewa An samen ne bata hanyar aure ba sai anmun tozartar da ta zarce wacce aka yiwa
mahaifiyata,da a zuciyata ina jin cewa zan iya daurewa in nemo mahaifin nawa amman yanzu
na karaya ba zan iya ba,gida zan tafi na gwammace in ci gaba da rayuwa a haka har karshen
numfashina in zan rayunma kenan."

Zeeyter ta ce,"Kar ka manta cewa komai yana da dalilin faruwarsa kuma ma kai ai gwanda kai
ni fa da banma san ta ya aka haifenin ba kuma ban san ko da ɓarin tsinke ba na iyayena bare
danginsu,shin na kasa komai? Na ce ba zan rayu ba? Zan gwama da kyarar mutane sam bata
gabana,ansha yi mun gorin asali amman ko da wasa ban taba sa hakan araina ba bare ya
dameni ko ya kawo mun damuwa tun suna yi har suka gaji suka dawo yabamun,saboda na
yarda da Allah kuma na san cewa shiri da tsarinsa shine daidai ga rayuwata."

Farouq ya ce,"Nima na yarda da kaddarata amman dai tafiya gida shi ne mafita gareni a yanzu."

Zeeyter ta ce,"Okay amman ka yi hakuri zan kira Zahra ta zo muyi magana tare duka kafin
sauran su shigo."

Kafin ya bata amsa ta inviting Zahra,tana yin joining kuwa ta fada mata duk abun da ke faruwa.

Zahra ta numfasa kafin ta ce,"Ba a fushi da tsarin Ubangiji kuma ba a fidda rai da rahmarsa
ka sani cewa ka zo duniya ne da izinin Allah, ba tare da kuskure daga gare Ka ba. Ka kasance
abin ƙauna a wajen Ubangijinka, kuma ba ka da laifi ko ɗan komai na abin da ya faru kafin
zuwanka.

Allah Mai Rahama ne, kuma baya hukunta bawa sai da aikinsa. Idan iyayenka sun yi kuskure,
ka bar shi a tsakaninsu da Allah – kai kuma ka gyara naka tafarkin.”

Ka sani, Annabi Ibrahim (A.S.) ya ce: “Wanda ya halitta ni, kuma shi ne ke shiryar da ni.”
(Qur'ani 26:78)

Shi Allah ne ya ƙaddara zuwanka, kuma akwai wata hikima mai girma a cikin hakan. Kada ka ji
ƙasƙanci, kada ka ji kuncin rai. Mutum mafi daraja a wajen Allah shi ne mai tsoronSa da aiki
nagari — ba wanda aka haifa da aure ko ba tare da aure ba.

Ka dage ka ci gaba da zama na gari. ka tsayu cikin addu'a, ka yi ci gaba halin kirki. Ka zama
misali ga duniya cewa Allah yana ɗaukaka bawa bisa kyakkyawan hali, ba bisa asalin
haihuwarsa ba.

Idan duniya ta kallaka da ƙyama, ka sani Allah yana kallonka da rahama. Idan mutane sun
rainaka, ka ɗaukaka kanka da ibada. Idan ka dage a kan gaskiya, ka fi dubban masu asali da
nasaba – saboda nasaba mafi girma ita ce nasaba da Allah ka da wani raunan tunani ya sa ka
fasa neman mahaifinka ka ci gaba da nemansa na tabbatar da cewa hakan zai kasance
alkairine ba wa kai kadai bama harda shi da sauran al'umma."

Tana cikin maganar Zeeyter ta yi inviting su Khalil Da Deejerh.

Farouq ya ce,"Na yarda zan ci gaba da nemanshi amman dai yanzu ku amince mun in koma
malaysia please,ba zan iya zama anan ba."

Khalil ne ya katse shi da fadin,".....


[17/06, 9:35 am] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs

- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAGE-21

"Na riga na sa an yi rejecting ticket dinka yanzu So abun da ya fi shi ne kawai ka fito a asalin
centuar dinka,ka fuskanci dukkkanin wani kalubale,ka ajiye rauninka na dan adam a gefe ka
bayyanar da kwazo da jarumtarka,kar ka manta cewa ba asamun da ragwanci ko fidda
tsamanin nasara ba,a ko ina muke kuma a kowani hali sannan a kowanni yanayi duk rintsi dadi
da wuya muna nan daram ko da kuwa za ata jan mu ƙasa ne muna jin rauni hakan ba zai taɓa
sanyawa mu nuna gazawarmu ba domin kuwa kowacce jarabawa da ubangiji zai mana muna
daukanta matsayin haske ne ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login