Showing 21001 words to 24000 words out of 62597 words

Chapter 8 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

1643

bangaren Hajiya Kaka suka nufa
tana zaune an wage kafafu da hannaye duk an rufesu da leda.
Farouq ya bude baki,"Ah Me zan gani?"
Hajiya Kaka ta ce,"Lalle mana ado ai na yi maka angon."
Zama ya yi daf da ita yana,"Ai kuwa dole in biya kudin wannan ado."

Hajiya kaka ta cuna karamin bakinta tana,"Yoo ba ma dole ba ai wajibi ne a gareki."
Farouq ya ce,"To ni yanzu ba ma wannan ba so nake abani tarihin kasar bidan nan tunda ni dai
ba zan samu zuwa ba aiki zai mun yawa."

Hajiya Kaka ta gyara zama,"Tabbas kuwa ka zo gidan tarihi ka karkade kunnuwanka da kyau ka
saurareni."

Hannu Farouq yasa a kunnuwansa yana karkadewa suna dariya.
Hajiya Kaka ta ce,"Yawwa Bida na ɗaya daga cikin birnin da suke sahun farko a jahar niger a
Nigeria.
Domin ta kasance matsayin cibiyar kasuwanci tun daga zamanin da kakanni da kakannin
kakanni domin ta kasance hanya mai mahimmanci ga masu safarar kayayyaki daga arewa
zuwa kudu.
Haka kuma birin yana da tarihi mai zurfi a fannin addini, tare da kasancewar shi a matsayin
wurin taron al'ummar musulmi.

Bida an kafa ta a farkon ƙarni na 19 kuma ya zama sananne a lokacin Jihadin Fulani da Usman
dan Fodio ya jagoranta. Birnin ya zama muhimmin cibiyar kasuwanci da ilimin Musulunci,
wanda ya taimaka wajen yada addinin Musulunci a wannan yanki. Masarautar Nupe, wanda
Bida ta kasance cikin ta, ta taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin siyasa na tsakiyar Najeriya.
A cikin shekarun baya bida ta kasance gida ga masarautar Bida wacce ta kasance daya daga
cikin manyan masarautu a Nigeria kuma masarautar ta yi fice wajen bunkasa al'adun gargajiya
da kuma gudunar da harkokin zamantakewa a yankin.
Sannan tana da kyawawan wurare da suka shahara kamar su gidan sarauta da kuma wuraren
tarihi da ke jawo hankalin masu yawon bude ido haka kuma birnin na da alaka da harkokin
noma inda manoma ke samar da kayan amfanin gona da dama to wannan ita ce bida kuma
kuma garin su Matar Abbanku Malik kenan domin yar sarki ce wato babban sarki kenan da su
mokwa karkashinsa na ma manta Jahar bida na bawa Al'adu muhimmici matuka

Bida tana da shahara wajen sana'o'in gargajiya, musamman a fannin tukwane da zane-zane.
Hakanan birnin yana da shaharar bukukuwan al'adu na shekara-shekara, wanda ke nuna
arzikin al'adun mutanen Nupe, ciki har da kiɗa, rawa, da tufafi na gargajiya kamar dai yadda
yanzu muke shirin tafiya bikin Gani.
Hakazalika
A zamanin yau, Bida ta ci gaba da girma, tana zama muhimmin cibiyar gudanarwa da
kasuwanci a Jihar Neja. Hakanan birnin yana da manyan makarantu, wanda ke taimakawa
wajen bunkasa ilimi a wannan yanki kasan duk da mun tsufa amman ba ma gajiya da sauraren
redio domin jin ya duniyar da lamuran cikinta suke tafiya."
Farouq ya numfasa ,"Ma sha Allah ai kuwa tarihi ya fita fes to amman yanzu ke nan ban da
mokwa akwai wasu garuruwa da ke karkashin bida?"

Hajiya Kaka ta ce,"Kwarai kuwa akwai Mokwa nan ke nan inda muke sai
Katcha
Yawwa akwai agaie ma dukkaninmu muna karkashin masarautar Bida ne."

"Kenan yanzu duk yan garuruwan cen ma zasu tafi bida shagalin bikin Gani?"
Farouq ya fada.
Hajiya Kaka ta ce,"Kwarai ma kuwa ai nan ne tushenmu duk."

Farouq ya ce,"To shi kuma wannan Bikin Ganin fa mene ne ma anar yinsa? Kuma kwana nawa
za ayi ana yi?"

Tashi Javed ya yi yana,"Oga in ka shigo ma hadu na lura wannan zantukan naku ba mai karewa
ba ne."

Kafin Farouq ya amsa caraf Hajiya Kaka ta ce,"Yo dole ka tashi mana kana nan da takunannen
hanci kamar sabuwar kalwa yara basa son jin tarihi da al'adunsu sam sam bare ma ku koyi riko
da su sai shegen.... kafin ta karasa tusa ta suɓuce mata ga shegen wari ga kara kamar an fasa
bomb.
Javed ya kalleta ya ce,"Oku (sannu) ganin yadda ta karkace kafin ta sambado tusar yasa bayan
ya ce mata sannu ya fashe da dariya,Farouq ma dai ya gagara rike dariyar toshe hanci ya yi
yana yi.
Tsaki Hajiya Kaka ta yi ta ce,"Cuta ce dai na fitar ba wani abu ba kuma kwai na ci dafaffe guda
takwas dazu abuna ahto inma zaku bude hanci ku bude wannan iskar da na fitar ma ta
albarkace zasu samu."

Da gudu Javed ya fice yana,"ni dai na yafe wa wannan albarka Oga akwasa da kyau."
Ya karasa yana dariya.

Hajiya Kaka ta ce,"Rabu da shi bara in ci gaba da fada ma yawwa Bikin Gani.....l
[20/05, 7:19 am] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor

- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-13

Bikin Gani na daya daga cikin manyan bukukuwan al'adu da ake gudanarwa a Bida. Wannan
biki yana da matuqar muhimmanci ga mutanen Nupe da kuma al'ummar da ke zaune a Bida.
Ma'anar Bikin Gani kuwa
Bikin Gani yana nufin bikin da aka shirya don nuna al'adun gargajiya, kiɗa, rawa, da sauran
abubuwan al'adu na musamman. Ana gudanar da wannan biki a kowanne shekara, kuma yana
jan hankalin mutane daga sassa daban-daban na Najeriya da ma waje.

A lokacin bikin, ana gudanar da wasannin kwaikwayo, gasa tsakanin matasa, da kuma
nune-nunen kayan tarihi. Hakanan ana jin dadin kiɗan gargajiya da rawar al'adu da suka
shahara a cikin al'ummar Nupawa.

Sannan Bikin Gani yana ba da dama ga matasa da su yi koyi game da al'adun su da kuma
yadda za su ci gaba da su a cikin zamani. Hakanan yana karfafa haɗin kai da zaman tare
tsakanin al'umma.

Domin kuwa Bikin Gani a Bida yana zama wata hanya mai kyau ta bayyana kyawawan al'adun
gargajiya da kuma taron al'umma, yana kara dankon zumunci da haɗin kai a tsakanin masu
halartar biki."

Farouq ya numfasa,"Ma sha Allah abun birgewa kuma kwana nawa ake yi ana shagalin?"

Hajiya Kaka ta ce,"Kwana Uku ne amman mu wani lokacin har mako guda muna yi bida mu
huta da ke muna da bangare guda namu da ake ware mana a cen gidan Mai Martaba Babba."

"Gwanin Sha'awa,Yanzu bara in barki ki kwanta in tafi dare ya yi."
Hamma Hajiya Kaka ta yi ta ce,"Aiko kamar ka san na fara jin barci,Bara in kira yarinyar nan ta
zo a kunce lallen nan."

Sallama suka yi Farouq ya tafi Javed har ya dade da barci kai tsaye dakinsa Farouq ya wuce.

Gari na wayewa gida ya cika fal anata shige da ficen shirin tafiya Bida.
An jero motoci bisa tsari masu tsaro a gaba kafin motar mai martaba sannan ta sauran mutanen
gida.
Farouq na cikin bangarensu ko fitowa bai yi ba tunda
Misalin karfe Ɗaya na rana suka dau hanya bayan sunyi sallah sunci abinci.
Da ke ba tazara sosai awa biyu da mintuna suka yi a hanya kafin suka shiga cikin garin Bida.
Kai tsayen Bangaren da aka tanadar masu suka wuce,suka wuta suka ci abinci sannan suka yi
sallah.
Daga nan Mai Martaba Sarkin Al'adu ya tafi ganawa da Sarki Mai Martaba na garin Bida.

Cikin dare Farouq ya isa garin da ke da yamma ya bi motar haya,yana isa TASTE PALACE
HOTEL ya sauka domin da ya tambayi Javed hotel mai kyau nan ya yi masa recommending
kuma da ya duba google ma ya ga alamun ingancin hotel din hakan yasa ya wuce nan kai
tsaye.
Sai da Javed ya tabbatar da cewa Farouq ya iso cikin koshin lafiya kafin hankalinsa ya kwanta
ya yi da Farouq dinma akan zai je hotel din su gana ya ki fir gudun kar a samu matsala cewar
Farouq haka Javed ya hakura dole ba don ya so ba.
Daren ranar kuwa Farouq bai yi barci ba gabadaya kwana ya yi yana bincike tare da wasu
ayyukansa.
Misalin karfe goma na safe ya shirya cikin kananun kayansa ya sanya pacing cap sannan ya
dauki wani bakin glass mai dan girma yasa.
Yanayin yadda ya yi shigar zai yi wahala mutum ya ganesa ba in ba wanda ya yi masa sani
sosai ba.
Masarautu Bida ya nufa cikin sa'a kuwa yana taran wata taxi cike take da matasa suma can
zasu hakan yasa shi jin dadin bin ayarin nasu.
Ya shiga shima tamkar sahun yan gari ya zauna cikin wa inda suka je tare,Javed ne ya masa
test kan har yanzu bai gan shi ba.
Farouq ya maida masa da cewa ,"Ni ko na ganka cikin tawagar mai martaba ya karasa
rubutawa ya na daga masa hannu.
Murmushi Javed ya yi yana girgiza kai,"Tabbas nima na ganka to Maddalla. "
Anyi wasan kwaikwayo na al'adu sannan kowanni gari sunzo sun kafa dandalin abun da suke
saidawa cike da alfahari haka kuma an yi nune-nunen kayan tarihi na gargajiya sannan anci
ansha da abincin gargajiya kala kala sai wanda mutum ya zaɓa kamar su cingini (sakwara),Ezo
(wake) Kunu ,Akara (Alale),tuwo,Ɗankuwa,Kuli_kuli da dai sauransu. Da ke ranar farko ne an gama shagalin da wuri kowa ya watse wanda gobe zasu gabatar da
rawa da abubuwan sarauta na gargajiya.

Ba wanda ya lura da Farouq har aka watse.
Ya karbi number ɗaya cikin wa inda suka zauna tare.

Rana ta biyu

Ranace ta mussamman domin ba iya mutane ke kasancewa wajen ba harda aljanu da sukan
iya yin shiga a siffar mutane,cika ake na mussamman abubuwa da yawa na wakana ciki harda
tsafe-tsafe da bori.

Wajen taro ya dau harama sarakai kowanne na rufa tare da tawagarsa yan bori ne suka fara
anata fama.
Sarkin Raki wanda Aljani Sarki Fahad ne akansa kamar an tsikaresa ya juya inda su Farouq
suke, suna haɗa ido ,Farouq ya ji zuciyarsa ta fara bugun tara-tara da sauri ya kawar da kai
yana sunkuyar da kai,bai san dalili ba amman babu shakka ya ji nauyin ci gaba da Kallon Sarkin
Raki. Kafin ya ankare ji ya yi an riko hannunasa yana daga kai ya ga sakice ta rike hannunsa,jan sa
zuwa filin borin ta yi ta tsayar da shi rawani ta dauko ta fara naɗamasa tana yi sauran suka
zagaye shi suna rawa,nan fa fada ta rikice kowa na son ganin wane ne wannan domin dole zai
kasance na musamman ne,abune da bai taɓa faruwa ba a tarihin Bikin da ma masarautar.
Tana gama naɗa mashi ta fara yi masa Kirari ita da Sarkin Raki da sauran kujerar sarauta
wacce take cikin na Sarkin Bida ta zaunar da shi daf da Babban Sarkin suna ci gaba da yi masa
Kirari.


Ana zaunar da shi Mai Martaba Sarkin Al'adun mokwa idonshi idon Farouq bai san lokacin da
ya tashi tsaye ba gabansa na wani irin mummunan faduwa.

Sai ji yake zufa na keto masa ta ko ina,Shi ko Farouq kara zagayeshi aka yi ana yi masa wasu
lamura,wani irin zobe Saki ta dauko ta dauko a jakarta mai kyalkyali zata sanya masa zoben
kenan tana fara zurawa a hannunsa gari ya hade nan take akayi wata tsawa cikin sa'i guda
wani irin ruwa ya barke.
Sarkin Bida ya ce,"Tabbas akwai babban lamari tare da wancen bawan Allahn domin ba lokacin
damuna muke ba,kuma ba kowa yake iya samun wannan zoben ba bare har a sanya masa kai
tsaye daga masarautar Sarki Fahad zoben ke fitowa."

Wani irin zazzaɓi ne ya rufe Farouq take idanunsa suka kada suka yi jajur cikin karfin hali ya
rufesu ruf.

Mai Martaba Sarkin Al'adu ne ya tashi zai karasa gareshi cikin sauri Saki ta......
[25/05, 3:29 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *

You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-14

Ta dakatar da shi tana fadin,"Hattara dai."
Ba yadda ya iya ya koma ya zauna yana wani irin muzurai,babban abun da ya fi damunshi shi
ne ya rasa gane wane ne Farouq kuma da wacce manufa yazo,duk kokarinsa ya gaza fahimta
shi dai tun ganinsa na farko jikinsa ya bashi cewa akwai wani abu,to mene ne wannan abun?
"Sirrin da na binne?" Ya furta a zuciyarsa. Da sauri ya kawar da kai yana girgiza hannunsa da ke kan cinyarsa azahiri ya furta,"Aa bai isa
ba,ba zai yiwu ba,na rufe kowacce kofa,ba mai iya budewa."
Bai san cewa duk furucin da yake azahiri bane sai da ɗaya cikin fadawanshi ya yi
magana,"Ranka Ya dade lafiya?"
Tukunna ya dawo hayyacinsa yana wani irin numfashi da haki,"Lafiya,lafiya ba komai,ba komai.
"
Ya karasa maganar yana ajiyar zuciya.
Yanayinsa duk ya firgice.
A cikin ransa ya ci gaba da saƙawa,"Sai dai wani lamarin ba dai sirrin da na binne ba jinin mu
ma basu isa ba bare wani bare,ka kwantar da hankalinka ka da a fahimci wani abu. "
Da hakan ya yi kokarin maida hankalinsa waje guda a zahiri wanda kuwa a badini sai saƙe-saƙe
yake duk da cewa zuciyarsa na ƙara jaddada masa cewa abun da yake tunani ba zai taɓa
faruwa ba domin ya riga da ya rufe dukkanin wata ko ƙofa ko alama.


Farouq kuwa idanunsa kankamewa suka yi a rufe,cikin sauri Sagi ta je tasa wani ƙoƙo daidai
inda ruwan saman ke zuba ta taran masa.
Tana zuwa ta buɗe bakinsa ta fara zuba masa ruwan yana sha sannan ta shafa masa a fuska.
Take ya nemi zazzaɓin da yake ji ya rasa idannunsa kuwa fari kal suka dawo da da yadda suke
ma a baya saɓanin canja kalar da suka yi cikin ƙaramin lokaci.
Murmushi Sagi ta yi ta kallesa ta ce,"Sannu da kokari ko,Babu shakka kai hasken fitila ne da
kan iya haskaka al'umma ko da kuwa kana cikin duhu,bare ma duhu bai isa ya kara bin hanyar
da kake ba ko tunanin kai maka farmaki,ka fi karfinsu ba za su taɓa iya ja da kai ba in ko suka yi
gigin hakan daidai yake da kokarin salwantar da rayuwarsu da tushensu." Gabadaya jawaban da take ya sanya Farouq shi ga cikin ruɗani da rashin fahimta hasali ma
kansa fara juya masa ya yi yana yi masa wani irin ciwo wanda bai taɓa riskarsa ba.

Karuwa ruwan ya yi cike da iska da wasu manyan kankara dake sauka iska na kaɗa bishiyoyi.
Babu alamun tsayuwa ga ruwan hakan ya sanya aka tashi ga taron hakan nan.


Javed ne ya je ya rike hannun Farouq suka wuce bangaren da suka sauka.

Suna shiga Farouq da ya samu gado sai barci.
Cike da tambayoyi Fal Javed ya zauna kusa da Farouq zuciyarsa na saƙa masa.


Zaune su Kaka suke duk an taru ana cin abinci,
Arham ya shigo yana,"Ikon Allah yau dai an kafa babban tarihi a bikin Gani kowa na ta mamaki
ga ruwa sai karuwa yake,lallai Bakoncen na da abun mamaki."

Kilishi ta ce,"Wato yaron cen tsabar na ci sai da ya biyo mu wajen taron bikin nan,kuma ma fa ni
har yanzu ban yarda da shi ba wallahi ko kadan kara jin tsanarsa nake araina,ga shi wai Saki
sanya masa rawanin sarauta? Irin rawanin da ta sanya masa fa ko mai martaba ba a taɓa sawa
shi ba."
Hajiya kaka ce ta ce,"Ke Khalisa ki raba kanki ba tun yau ba ina ji a jikina cewa wannan yaron
wani ne,ba gama garin irin mutanen da kike zato bane akwai wani abu na mussamman a tattare
da shi."

Janinah ta ce,"Ko ma shi wane ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login