Showing 6001 words to 9000 words out of 62597 words

Chapter 3 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

1624

jin hakan a jikina kuma ina fatan hakan dai."

"Ka sa aranka akwai nasarar ka bawa Ubangiji yaƙini sai ka ga ya tabbatar da abun da ba ka
taɓa zato ba,ka rokesa cike da yaƙin samun abun da kake nema kuma kasa aranka tamkar ka
samu babu shakka Ubangiji shi ne mai badawa kuma shi ne mai hanawa ina ji araina komai zai
zo da sauki,ni dai babban buri da fatana duk yadda za ayi kar ka karaya kuma kar ka fidda
tsammani daga rahamar Ubangiji ." Zeeyter ta fada.

Farouq ya ce,"Ta ya ma zan karaya bayan ina da ke jarumar jarumai Yel? Dadina da ke wani
lokacin akwai guntun hankali ko da yake ina ga mijinki ne yake sammiki."

Dariya Zeeyter ta yi ta ce,"Za ka sani zan yi maganinka Oyaa Sai da Safe Mijina na bukatata."

Farouq ya ce,"Umm Cingom ba to Allah tashe mu lafiya."
Kashe wayar suka yi duka suna dariya.

Wajen karfe biyu na dare ne sai da Farouq ya yi alwala ya yi nafila kafin ya kwanta.

Washegari da safe
Bayan ya yi wanka za akai masa breakfast Janinah ta ce ita zata kai masa har da rawar jiki ta
karbe a hannun masu aiki.
Ya fito daga wanka ke nan yana zaune daga shi sai towel.
Ko sallama ba tai ba ta kutsa dakin kawai da ke bai rufe kofar ba turawa ya yi.
Motsin da ya ji ne yasa shi daga kai.
Ta saki wani munafikin murmushi ta ce,"ga abinci nan an kawo sai a zauna aci ko don na
tabbata wannan ko a malaysian ma kila dan aiki ne ko mai gadin gida."
Murmushi kawai Farouq ya yi bai kulata ba ya ci gaba da goge ruwan da ke jikinsa da towel din.
Da ya ji shiru a tunaninsa ta fita.
Sai kawai saukar mari ya ji a kumatunsa.
A razane yago da jajayen idanunsa har ta isa bakin kofa tana fadin,"ÆŠaya kenan ko ince kadan
ka fara gani don wallahi Allah sai na yi ma abun da zai saka zubda hawaye kamar yadda nima
kasani zubarwa."
Tafasa zuciyar Farouq ta fara,ya ji aransa ya bita ya yi maganinsa wani bangaren kuma
zuciyarsa na basa hakuri da dannesa.

Tana daga bakin kofa
Ta yi masa wani dogon tsaki tana fadin,"mai gadi kawai."
Kawar da kai Farouq ya yi zuciyarsa cike fal da sake-sake.

Tana fita ta ci karo da Javed da mamaki ya kalleta,"Janinah ke kuma me ya kawo ki nan?"
Inda inda ta kama can kuma sai ta ce,"ansa su talatun aikine shi ne nace bara in kawo wa
bakon breakfast dinsa kar ya gaji da jira."

Javed ya ce,"okay shikenan kin kyauta."
Ya wuce dakin da Farouq yake.
Yana shiga yaga yanayin Farouq ba yadda ya bari.
"Ya dai? Ba dai yarinyar can bane ta maka shirme."
Javed ya fada cike da zakuwa.

Murmushin dole Farouq ya yi ya ce,"aa fa sam kaina ne na ji ya fara ciwo na sha magani kuma
naji kamar karuwa yake."

Javed ya ce,"Ayyah Sorry kila gajiyan hanya to ka karya in mun fita sai mu fara bi ta asibiti."

Farouq ya amsa da ,"Okay tom."
Abincin ya ci bayan ya gama ya ce,"To mu je in gaida amaryata kafin mu fitan ko."
Bangaren hajiya kaka suka nufa.
Bayan sunyi sallama ta amsa Farouq ya ce," Tsarugu anu." (wai yana nufin ina kwana da
nupanci)

Dariya Hajiya Kaka ta yi ta ce,"Ai kaine Tsarugu anu din wato kai a dole ka fara iya nupanci."
Farouq ya yi dariya,"Yo ina gudun yellow card ba dole ba."
Hajiya kaka ta ce,"To Tsaragi Anu ake cewa ka rike da kyau."
Farouq ya ce,"Anyi an gama Yan Maya tsaragi anu."
Hajiya kaka tayi dariya."lafiya lau,kofo eze anu (ya ka ke)."

Farouq ya ce,"Lafiya lau kawai amsar ce dai sai naje na kara koyowa amman fa ina fahimta."
Dariya suka yi duka.
Janinah ce ta shigo da sauri hannunta dauke da bowl ga dukkan alamu farfesun nama ne mai
romo.
Gefen Farouq tabi da niyar tunkude kafadarsa.
Ya yi kaman bai ga tana zuwa ba ya sa mata kafa ta kasa daga ita har bowl din sai gasu
kwance shaɓe-shaɓe kan tais farfesun kuwa ya yi mata fenti domin bowl din kifewa ya yi a
daidai setin fuskarta.
[06/05, 6:26 pm] Xayyeesherthul-humaerath🍂: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! 😊
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace

- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! 🚚*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-5

Ya ji ya shigan mata ido gashi farfesun da zafi.
Wata irin karya ta sake.
"Wayyo Allahna wayyo na shiga uku,idona,fuskata."
Kau da kai Farouq ya yi kamar bai san me ke faruwa ba.
Da sauri Javed da Kaka tare da mai aiki suka yi kanta.
"Subhanallah Janinah sannu Javed taimaka adagata aje ban daki a wanke fuskar in kuma da
matsala a kira BabanGanye ko da taimakon da zai iya bata."
Sai a lokacin Farouq ya tashi ya karasa wajen shi ma yana fadin,"Ya ilahil alamina garin ya ya
haka kuma sannu ko."
Toilet suka shiga da ita aka wanke mata fuskar amman duk da haka idanunta zafi yake yi mata
haka ma fatar fuskar domin farfesun yaji kayan yaji matuka.
Hannunta na kan fuskar tana fadin,"wallahi radadi yake mun Yaya Javed zafi sosai kamar an
zuba mun barkwano." Ta karasa fadan suna zaunar da ita kan kujera.
Hajiya Kaka ta ce,"To a kira BabanGanye ba zai rasa abun da zai shafa mata ya dauke zugin
ba."
Caraf Janinah ta ce,"cab wallahi gwanda ma abarni inta jin zugin yazo ya wani zubamun
abubuwa masu wari a fuska,wai ku gidan nan ba dama akai mutum asibiti sai ace sai dai wani
BabanGanye saboda mu muka yankewa Gargajiya cibiya."

Hajiya Kaka ta ce,"ungo nan kinci gidanku yo ba dan su BabanGanyen ba ai da baki girma cikin
walwala da karfi haka ba,tun kafin kizo duniya kika shan kayan ganye da itacuwa,Javed maza
zai ka kira wo mun shi."

Kallon Javed ta yi ta ce,"Yah Javed Please ni abari kawai. "

Wani kallo ya bita da shi ba tare da yace komai ba kawai ya fice.
Shi ko Farouq na zaune yana danna wayarsa kamar ma bai san me ake yi ba.

Kai tsaye Javed ya je ya kira BabanGanye dake a cikin masarautar duk masu magungunan
gargajiyan suke.
Da buhunsa yazo kuwa cike fal da kaya dake Javed ya fada masa abun da ya faru.
Yana zuwa ya baje yana fadin,"ai Hajiya Kaka wannan babban al'amarine in ba ayi saurin sanya
tsari ba sai ya jawo mata matsala cikin kwayoyin hallitar fuskarta da cikin idon."

Hajiya Kaka ta ce,"Babu shakka ai shiyasa na ce a kira mun kai cikin gaggawa."

Ita dai Janinah sai cuna baki take tana kananun maganganu.
Shiko BabanGanye tuni ya hada kwamacalarsa kayen da itace da wani irin ruwa ya fara shafa
mata a fuska sannan sauran ya mika mata yana tasha."
Wani irin kallo Janinah ta bisa da shi tana fadin,"ni ba abun da zansha abarni ma inji da
daddawar da ka raƙafa mun a fuska wallahi har amai nake ji."

Hajiya kaka ta ce,"Ko ba amai ba? Aa hanjinki kike ji zai fito ki waje wannan bajajjen bakin naki
ki kurbe tun muna mu biyu kafin in mai martaba ya ji labari."
Tana jin batun mai martaba tuni ta amshe ta rufe ido ta kwankwaÉ—e domin ta san sarai mai
martaba na jin labari ba za ta ji da dadi ba.

Haka ta sha ba don taso ba tana gyatsine fuska.
Farouq na kallonta dariya na son suɓuce masa ya make yana fadin,"aiko dai gwanda aka shafa
magani kar fuskar yar budurwa ta dagargaje abata mai gadi."
Wata irin harara ta bisa da shi.
Hajiya Kaka ta yi dariya.
"Ai wannan ba dai mai gadi ba sai dai aba almajiri."
Duka suka kyalkyale da dariya.
Wani irin takaici Janinah ta ji aranta ta gama kula cikin fushi ta tashi fuuu ta fice daga falon cike
da ɓacin rai.

BabanGanye ya mikawa Hajiya Kaka sauran hadin da ya shafa mata a fuska ya ce,"Hajiya
Kaka a ajiye wannan zuwa safe ta dan kara shafawa don naga yanayin fatar ta sauya kuma ga
dukkanin alamu ruwan dabgen ya shiga cikin ruwan idanunta."
Hajiya kaka ta bude baki.
"To fa ka ga kuma a haka ja'ira ke son wasa da lafiyarta ita zata nuna mana boko wai aje
asibiti."
BabanGanye ya tashi yana fadin,"Yoo ai yaran zamanin yanzu ba ra su gane bane abun da su
kansu asibitotin da itattacuwa da ganyayyenki mu suke hada nasu maganin tare da karin
bulaguronsu."
Hajiya kaka ta taɓe baki,"ai kuwa dai."
Daura buhunsa ya yi aka ya fita.

Javed ya kalli Farouq ya ce,"Oga mu tafi ko."
Karaf Hajiya Kaka ta ce,"Ah ku tafi kamar ya zan yi hira da sabon mijina dan kwalisa."
Farouq ya ce,"Wajen aiki zamu je Yan Mata amman na miki alkawari ina dawowa anan zan
dira."

Hajiya Kaka ta ce,"to ai shikenan a dawo lafiya,Ubangiji ya ba da sa'ar abun da aka je nema."
Farouq ya amsa da ,"Amin tsaraba me zan kawo miki?"

Hajiya kaka ta ce,"Da Goro da wannan abun sanyin yaran iskirim yake ko me?"
Javed ya katseta da fadin,"Hajiya Kaka ba an hanaki shan Ice cream dinnan ba?"
Harara Hajiya Kaka ta bisa da shi kafin ta ce,"wato ku kusha dadi ni kuma in mutu ina cin goro
da garin goruba to ahir dinka sai na sha Mijin a siyo mun iskirim ka ji ko."

Dariya Farouq ya fara yana,"Au wai daman Ice Cream ne iskirim din Hajiya Kaka? Kice inzo in
zauna darasi biyu zanna koya ga turanci ga nupanci."

Hajiya Kaka ta kyalkyale da dariya har sai da wawulun bakinta ya bayyana tas.
Ta ce,"Babu shakka je ka dawo yau zan koya ma is me is you is turanci."
Dariya suka yi duka.
Ganin lamarin kaka ba mai karewa bane Javed ya ce,"Hajiya Kaka kinga sai mun dawo."
Farouq ya ce,"sai mun dawo yan matana. "
Duka suka fita suna dariya.
Kai tsaye makarantar Javed suka nufa.

Dake babu nisa sosai cikin mintuna goma suka isa Makarantar da tamabarin makarantar suka
fara cikin karo mai taken DIGITALCRAFT.
(Transforming Ideas Into Digital Reality)
Makarantace ta kwamfuta da ke horar da matasa ilimin kimiya mussamman bangaren
computer,yadda zasu gina shafukan yanar gizo (web development)
Zane-zane na hoto da kirkiran tambura (graphics design)
Bayar da horo mai karfi
Kan tsarin kare kwamfuta da hanyoyin sadarwa daga hare-hare da kan iya lalata ma'adanan
sirri (Cyber security) da kuma hanyoyin yin kasuwanci ta intanet.
Sai yanzu sabon horon da Farouq zai ja ragamar badawa wato aiki na haÉ—a kwamfutoci da
sauran na'urori,raba bayanai da kuma samar da ingatacciyar hanyar sadawarwa (Networking).

Tsari da yanayin makarantar ya birge Farouq sosai mussamman yadda dakunan karantun suka
kasance dukkanin dalibai suna da kwamfuta da suke amfani da ita kuma ga dukkanin yanayinsu
ana tabbatar da cewa sai sun samu kwarayewar aiki da kwamfutar.

Kallon Javed ya yi bayan sun gama zaga makarantar sun dawo office dinsa ya ce,"yanayin
tsarinku gaskiya sun birgeni sosai har na ji sha'awar bude irinta a malaysia."
Javed ya yi murmushi,"na tabbatar da cewa zaka iya bude mafiyin hakan ma na yarda da kai."

Shi ma murmushin Farouq ya yi ya.
Javed ya kara da fadin,"yanzu ka dan huta akawo mana shayi mu sha don nasan rayuwar ture
sai da shayi zuwa 11:00am zamu gana da dalibanmu kuma yanzu 10:30."

Dariya Farouq ya yi ya ce,"wato rayuwar turai sai da shayi to ai shikenan."
Bayan an kawo masu shayin sun sha 10:55 suka fita zuwa babban hall din makarantar.
Zaune matan suke dukanninsu sanyi da riga wacce aka rubuta DIGITALCRAFT a gaba da
tambarin makaranta a gefen dama gefen hagu kuma tambarin NACOSS wato National
Association Of Computer Science Student sannan a bayan rigar kuma aka sanya sunan
kowacce a jiki. Karamin hijabi fari da kuma bakin wando rigar kuwa daman blue black ce ga dukkan alamu
makarantar ce ke tadar da komai domin komai nasu sak iri É—aya kuma ba karamin kyau da
haskawa suka yi.

Farouq ne ya fara yi masu jawabi.
,"Welcome, Students!

My name is A. Umar Farouq, and I’m from Malaysia. I am here to collaborate with
DIGITALCRAFT under my team’s five-star company to provide you with training and knowledge
in my field of Computer Science.

Da farko dai bara in baku shawarwari da nake tunanin zasu taimaka mana a wannan tafiyar har
ma da rayuwarmu duka.

Always Ask Questions
Kar kuji tsoron yin tambaya aduk lokacin da baku fahimci wani abu ba,haka kuma
Practice coding
Adadin yadda kukata maimaita yadda zakuyi saurin iyawa da kwarewa
Work with others
Ku kasance kuna da hadin kai wajen yin aikin gayya yana taimakawa sosai domin cimma
nasara
Stay organized
Kar kuyi wasa da lukutanku ku kasance masu tsara komai akan lokacin da zai tafi cikin tsari.
Don't give up
Karantar ilimin na'ura na da wuya amman kuma yana da matukar dadi tare da sakamako mai
kyau indai an samu sadaukarwa.
A karshe ina jaddadda muku cewa kar ku manta kasancewarku Yara Mata Iyayen wasu a nan
gaba karatun ku na da matukar muhimmici ga rayuwarku,iyalanku har ma da al'umma
gabadaya.
Allah ya bamu sa'a kuma yasa an fara asa'a ina yi muku fatan alkairi sannan zan fara da bada
aiki inaso kowacce a cikinku ta je ta yi bincike akan Networking gobe In sha Allah zamu fara
tattaunawa."
Cikin fara'a da jin dadin jawabansa suka fara tafa masa tare da yi masa godiya.

Komawa office ya yi shi kuma Javed ya ci gaba da gabatar masu da abubuwa da tsare tsare.

Wayar Javed ce ta fara kara dake ya bari a office din Farouq ya share ya ci gaba da danna
wayarsa ya ga kiran yaki karewa yana katsewa wani na kara shigowa.
Daukan wayar ya yi yana dubawa Yaga Sister Janinah.
Tsaki ya yi ya ajiye wayar yana "ashe wannan mara kunyar yarinyar ce ma."
Ci gaba da kiran ta yi da ya ga bata da alamun dainawa sai ya amsa wayar ya kara a kunne
yana fadin,"....
[07/05, 6:25 pm] Xayyeesherthul-humaerath🍂: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! 😊
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240

*Nationwide Delivery Available! 🚚*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-6

"Hello, he's not around. He's a bit busy. You can call him later, okay?"
Ya karasa maganar yana kokarin datse kiran.
Wani irin dogon tsaki Janinah ta ja tana,"Mtswwww Rubbish Who says you must pick up the
call? bana son shisshigi da neman gidin zama wallahi."
Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Ayyah Ashe mai fuskar ambaliyar romoce,ya fuskar? Ina fatan
dai da sauki? Sannu ko."
Ya fada cike da mugunta.
Katse wayar ta yi ba tare da ta ce komai ba tsabar takaici.
Ta kalli Kilishi ta ce,"Kin ga Aunty Kilishi barin wayarsa ma ya yi fa gun wancen bakon kuma ina
so in lallaɓashi ya karbo mun wani cream ne a asibiti in zai dawo don wannan abun
BabanGanye tunda ya maka mun har na wanke fuskata bata daina mun warin nan ba duk a
tsarge nake ko fita ba zan iya yi ba." Kilishi ta ce,"Miye na tada hankali ga Arham nan ki kirashi ya tawo miki da shi cikin sauki."
Janinah ta taɓe baki,"Umm Aunty Kilishi Yaah Arham dinne fa kin san shi ya cika tsari shi ma
yanzu sai ya fara mun wasu jawaban da ban sani ba."
Kilishi ta kalleta ta ce,"Haba Janinah karki manta fa shi ne wanda zaki aura in tun yanzu baki
koyi yadda zakina mu'amulantarsa ba in anyi auren ya za kiyi? Namiji fa a tafin hannu Mace
yake in kinso kuma kin isa cikakkiyar Mace zaki iya juyar da Arham yadda kikeso yanzu zan
kirashi ya tawo miki da shi amman daga yau kar in kara ji kuma kar in kara gani inaso duk wani
abu da kike da bukata ki fada ma shi kai tsaye."

Janinah ta ce,"To In sha Allah Aunty."

Kilishi ta gyara zama,"Yawwa Yarinyar kirki,kin fara bani labarin wancen mara kirkin bakon ina
fatan dai kin masa marin da ya ji a jikinsa."

Janinah ta ce,"Sosai fa sai da na sace shi naga alamun bai sani irin abun da mutum zai ji ba
zato ba tsammanin nan kawai sai jin saukar mari ya yi a fuska,amman ni fa duk da haka hankali
na bai kwanta ba tunda bai fara jin shakkata ba ina so in masa wata mugunta ta mussamman
yadda ko mai irin sunana ya ji sai ya gudu ya bar wajen karshen ya kwashe kayansa ya gudu a
masarautar nan ba shiri."

Dariya Kilishi ta yi ta ce,"Wannan shine gado kuma da kika tashi gadonma gani nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login