Showing 27001 words to 30000 words out of 62597 words
Chapter 10 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
hakan ya shiga cikin tsarina kuma dole in binciko."
Ya karasa maganar yana daukan System din.
Sabon file ya bude ya shigar da yanayin yadda ake kokarin kawo masa harin kafin ya ci gaba
da aikinsa.
Bayan sun idar da sallar asuba Farouq ya ke cewa Javed,"Ka ga ruwan kuwa ya dauke
gabadaya kamar ba ayi ba."
Murmushi Javed ya yi,"Ai kuwa kamar yadda yazo lokaci guda haka ya dauke yanzu ma."
Farouq ya ce,"ai kuwa har karfe hudu ma fa anayi amman ana kiran sallar asuba ya dauke nan
take ikon Allah ke nan ba ya karewa."
Yana karasa maganar ya ji alamar shigowar saƙo wayarsa.
Yana dubawa kuwa ya ga Gmail ne sako daga SiftaCore Technologies.
Ta shi ya yi cikin murna yana fadin ,"Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah. "
Cike da zaƙuwa Javed ya ce,"Oga ya dai wannan murna har ina?"
Nuna masa sakon Approval din ya yi,cikin rashin fahimta Javed ya ce,"Ban gane komai ba fa
Oga na ga dai kamar za a bada kyautar Kwamfutoci. "
Farouq ya girgiza kai cikin jin dadi ya ce,"Eheen zauna yanzu zan fahimtar da kai,daman ban
sanar da kai bane saboda ban tabbatar da samuwar hakan ba shiyasa na yi shiru amman
yanzu komai ya tafi daidai."
Zama suka yi duka a kujerar da ke gefen gado.
Farouq ya ce,"SiftaCore Technologies wani kamfani ne mallakin wani Dan Nigeria mai suna
Rasheed kwararren mai ƙyera na'ura ne wanda ya yi rayuwa a kasar South Korea kafin daga
bisani ya dawo nigeria nan Abuja ya kafa kamfanin SiftaCore Technologies suna kirkirar
Kwamfutocin AI-ready
Na'urorin super-computing don manyan cibiyoyi tare da
SiftaBox – kwamfutar tafi-da-gidanka mai amfani da sabuwar hanyar sarrafa bayanai.
da kuma kananun kwamfutoci domin ɗaliban fasaha.
Burin kamfanin shi ne Inganta rayuwa ta hanyar fasaha mai fahimta.
Sannan kuma a duk shekara suna kokarin bada tallafin kwamfutoci ga kananun kungiyoyi ko
makarantu domin ingata karatu mussamman na yaran da iyayensu basu karfi,marayu ko
marasa galihu.
Ina cikn gabar bincikena na ci karo da su sai na tuna cewa fa mun yi maganar inda hali muna
son saiwa kowacce daliba kwamfuta kafin kammala samun wannan horon shiyasa kawai na
shirya na tsara letter na tura masu karkashin DigitalCraft da dukkanin kudirorinmu to cikin ikon
Allah sai gashi muna cikin sahun wa inda za abawa wannan tallafi." Tsabar farinciki Javed bai san lokacin da ya rungume Farouq ba yana fadin,
"Ban san ma me zan ce maka ba,ban san taya zan nuna ma jin dadi da farincikina ka gamsu
ba,tun da na sanka babu abun da ke fitowa daga gareka sai alkairi da son ci gabana,Na gode
Oga,Na gode Allah ya saka da alheri ubangiji ya biya maka dukkanin bukatunka,ina ma ace
akwai wani abu da zaka nema a gareni da na ji dadi na yi maka shi cikin jin dadi duk da cewa
na san ban da abun da zan iya ma fiye da wanda kake mun."
Murmushi Farouq ya yi,"Yiwa kaine ai duk wanda ya zam silar ingata rayuwar wa inda basu da
bangon jingina gini yake yiwa kansa a lahira,ladan dani da kai duka zamu samu,babban abun
da kuwa zaka mun ka biyani ai ka jima da yimun tunda ka yarda dani kuma ka aminta dani."
Kara rungumeshi Javed ya yi yana,"Na gode,na gode sosai."
Shi ma Farouq ya rungumesa.
Sunata murna da farinciki kallon agogo Javed yyi ya ga 7:am
Da sauri ya mike yana "Oga nasan ba za mu wuce 8 a garin nan ba,ka shiga ka yi wanka bara
inje in karbo mana abincin karyawa."
Tashi Farouq ya yi yana,"Okay to shikenan. "
Ya wuce toilet shi kuma Javed ya tafi dauko masu abinci.
Dukkaninsu sunyi wanka,sun ci abinci daidai lokacin aka sanar da su cewa Mai Martaba ya ce a
fito za a tafi.
Kai tsaye dukkaninsu suka fita.
Kowacce tawaga ta kowanni gari sun shirya suma an fito ana bankwana.
Sarkin Bida ne yasa a kira masa Farouq,Farouq na zuwa ya dunga sanya mishi albarka sannan
ya mika masa wata jaka.
"Wannan kyauta ce ta mussamman, ka cancanci riketa,kila a yanzu ba ka san dalili ba amman
ka rike wata raba zai yi ma amfani kuma za ka fahimta."
Karba ya yi cike da fara'a yana godiya.
Sauran sarakunan sai zuwa suke suna gaisawa da Farouq kafin su tafi.
A cikin ransa shi kansa ya gagara fahimtar dalilin hakan da kuma abun da yasa suke nuna
masa kauna.
Zasu je su shiga mota tare da javed kenan mai martaba ya ce aa sai dai Farouq ya zo motarsa
su tafi.
"Tare a motata zamu tafi."
Mai Mai martaba ya fada yana shigewa cikin motar.
Da mamaki duk suka bi mai martaba da kallo.
To mai zai sa ya ce Farouq ya shiga motarsa?
Shi kuwa Farouq ba tare da tsoro ko shakka ba ya shiga cikin motar a zuciyarsa yana karanto
adduar shiga abun hawa.
"Bismillahi, Allahumma inni as'aluka khayraha wa khayra ma fiha, wa a'udhu bika min sharriha
wa sharri ma fiha."
Ya shiga ya zauna.
Tunda ya shiga motar nan kan Mai Martaba ya shiga sara masa tamkar za a fisge, kokarin dafe
kan ya yi da karfi ya zauna.
Ina lamarin ya citura,da karfi ya ce,"A Dakata...."
[28/05, 11:08 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-17
Cikin firgici driver ya ja birki,yana jan birki duka sauran motocin ma suka tsaya cak.
"Yallaɓai,Lafiya?"
Nuna Farouq ya yi da hannu da alamar ya fita.
"Ya fita?"
Ya girgiza kai alamar eh.
Da mamaki Farouq ya bi shi da kallo,aka bude masa kofa ya fita.
Farouq yana fita Mai Martaba ya ji tamkar an zare masa azabar da yake ji.
Ya kalli security ya ce,"ka sa shi a motarsu Javed."
"An gama Ranka ya dade. "
Ya fada suna tafiya da Farouq,bude masa motar su Javed ya yi ya shiga kafin ya koma.
Farouq na shiga motar cikin yanayin rashin fahimta Javed ya kalleshi ya ce,"Ya lafiya dai."
"E, lafiya kamar Mai Martaba zai yi wayar sirri."
Farouq ya fada a gajarce.
Javed ya ce,"Okay shikenan. "
Nan aka ci gaba da tafiya suna yi suna hira, har suka isa cikin Mokwa.
Ana shiga Fada cikin hanzari Mai Martaba ya wuce bangarensa ko cikin fadarsa bai yi ba.
Yana shiga ya kulle kofa,ya fisge rawanin da ke kansa,babbar rigar ma ya jefar da ita tsakar
dakin,hannu yasa a cikin aljihunsa ya dauko wani ɗan karamin tulu.
Yana budewa ya fara juya hannunsa wannan karamin mutumin ne ya kara fitowa.
Dariya mutum yake har yana tuntsirawa.
Shi ko Mai Martaba ya ɓata rai cikin yanayin fushi.
"Moli ka daina dariyar nan wannan lamarin yana da girma ba abun wasa bane."
Dariya ya ci gaba da yi sai da ya yi mai isarsa kafin ya ce,"Yo daman kai Abdul-Raheem kana
ganin cikin sauki ake iya taɓa mai kusanci ga ubangiji? ai sai dai irinka masu Musa a baki
fir'auna a zuci."
Ɓata rai Mai Martaba ya yi ya ce,"Ina ruwanka dani? Ni muyi abun da ya dameni,ke nan yanzu
shi ba za mu iya taɓa shi ba ko yaya kake nufi?"
Dariya Moli ya yi kafin ya ce,"Za a iya samun nasara amman fa sai anci kwakwa na fada maka
yaron sam baya wasa da lamuran ubangiji farilla da sunna kai har ma da mustahabi kuma taɓa
irin wa innan akwai ƙalubale sosai bare shi har yanzu na rasa gane kan gabanshi bare bayanshi
dole akwai manyan da ke tare da shi."
Mai martaba ya yi tsaki,"Yaron fa dan ƙasar malaysia ne ban jin cewa yana da riko da addini
don yawanci yan kasashan wajen nan sukan fifita duniya ba wani practising addini suke ba."
Moli ya buga wata iska kafin ya kalli Mai Martaba,"Ku fa musuluncin da yawanku a bakine kawai
yan nigeria su kuma yan kasashen waje musuluncinsu yawanci ga zuciya yake ba ga zahirin
rayuwarsu ba,sannan wai kai yau ka yi tunanin za ka iya cutar da shi ne? kana son wasa da
lafiyarka ko? Ka da ma kara wannan gigin cikin sauki."
Mai Martaba ya ce,"Eheen na yi tunanin zan iya kokarin dunkufar da shi ko samun wani abu
dangane da shi amman maimakon hakan sai na fuskanci barazana yafi karfina ba zan iya zama
inuwa guda da shi ba,ji nake tamkar mala'ika na kokarin zare raina."
Moli ya ce,"Ka sani komin makirci da karfin tsafinka kariyar ubangiji ta fi su tasiri,ka bani lokacin
in gama bincikar shi din wane ne tukunna ta hakan ne kadai zamu iya samun damar sanya
rauni ga karfin Adduoinsa sannan kuma ka dage wajen yin aikinka in zai samu bakinsa ya rufu
kamar yadda akaiwa sauran duk da cewa ba mu san manufarsa ba."
Numfasawa Mai Martaba ya yi,"Wannan ba matsala zan yi kokarin rufe bakinsa tare da kawar
da idanunsa akai na,amman nidai babbar damuwata ka samo mana mafita Don wallahi ni kadai
na san azabar da na sha yau cikin mintuna kalilan ba don nasa ya fita ba inaga zan iya samun
matsala babba kuma zaman wannan zoben tamkar barazana ce ga rayuwata." Dariyar mugunta Moli ya ci gaba da yi,"Dole a karbo wannan zoben dolene,dole ne domin shi
ma din wata kariyace a gareshi sannan kai ka cancanci sanya wannan zoben ba kowa ba."ya
karasa maganar yana wasu irin yare da sambatu kafin ya ɓace ɓat lokaci guda.
Yana tafiya mai martaba ya dauko wani ruwa shi ba ja ba kuma ba yellow ba a cikin kwarya ya
kafa kai yasha yana sambatu sannan ya diba ya shafa a fuska da kuma tsakiyan kansa.
Wasu fararen kaya ya dauka yasa kafin ya hau kan gadonsa ya kwanta ,"Tun ranar farko
zuciyata bata aminta da wannan yaron ba,Zoben nan mallakina na ne ba na shi ba,dawo ya
dawo hannunaaaaa."
Ya fada a zahiri yana shiga cikin bargo.
☆☆
Farouq suna shiga cikin Bangarensu bayan ya yi sallah sunci abinci Javed ya shiga cikin gida
ya dauko jakar da Sarkin Bida ya bashi.
Hannu yasa a ciki ya zaro wani irin rawani mai kyau da sheƙi da daukan ido.
A zahiri Farouq ya ce,"Ko amfanin me wannan rawanin zai mun oho."
Ya na kokarin maidawa ciki sai ga zoben da ke hannunsa na sheƙi yana fitar da haske irin na
jikin rawanin.
Tsayawa kallon ikon Allah ya yi.
Yana maida rawanin kuma sai wutar ta dauke,alamu dai sun nuna cewa wannan rawanin da
zoben suna da alaƙa mai karfi.
Karfe ɗayan dare daidai,Farouq ya hango wani yazo masa a siffar mutane baƙinƙirin ƙato,kokari
yake ta karfi zai kwace zoben da ke hannunsa.
Cikin karfin hali Farouq ya dunkule hannunsa yana ihu.
Sheƙe masa wuya mutumin ya yi,da kyar yake numfashi yana ta kokarin cire hannunsa a
wuyansa,ɗayan barin kuma ya ƙara dunkule hannun.
Da kafarsa ya fara kokarin dukan mutumin.
Yana sa hannu kan zoɓen sai ya fara wani irin jan wuta yana hayaki.
Ja yake amman sam zoben yaki fita ya maƙale hannun Farouq tamkare da shi yazo duniya.
Tun suna yi a kwance har suka tashi suna dambe da juna,sosai suka sha dambe har Farouq ya
jiwa wancen mutumin a fuska shi kuma ya cijesa a hannu.
Ganin bai da alamun samun galaba akan Farouq yasa shi ya gudu.
A tsorace Farouq ya farka daga mafarkin da yake.
Kamar yadda Manzom Allah SAW ya umarta ga duk wanda ya yi mummunan mafarki ya yi
addua ,"Allahumma inni a'udhu bika min sharri maa ra’aytu."
Hakan Farouq ya karanta yana goge zufar da ta gama jiƙa masa jiki.
Jin yanayin jikinsa ya yi ya masa nauyi sosai,hasken da zoben yake yasa shi kunna wuta domin
ya gagara daga hannun da zoben yake.
Yana kunnawa kuwa yaga jini na zuba ga alamar cizo nan asaman hannunsa daf da yatsan da
zoben yake.
Cikin jin mamaki ya furta,"Ke nan ba mafarki na yi ba? A gaske hakan ya faru? To ina mutumin?
Me yasa ban ganshi a dakin nan ba."
Ya karasa yiwa kansa tambayoyin yana tashi.
Duba lungu da sako na dakin ya yi,ba alamar mutum sannan kuma kofarsa ma tana nan a kulle
kamar yadda ya bari.
Gajiya ya yi ya koma ya daure wajen cizon.
Ya koma ya kwanta kenan yana kashe
Motsi yafara ji a karkashin Gadonsa hakan yasa shi saurin sunkuyawa
[31/05, 9:21 am] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-18
Yana sunkuyawa yaga babu komai bare alamun wani abu,duk da hakan bai yarda ba ya kunna
hasken wayarsa ya haska sai da ya tabbatar bai ga komai ba kafin ya koma yana ajiyar zuciya
a kan gadon.
Ji ya yi barcin da ke idanunsa sun kafe kaf ya gagara komawa,hakan yasa ya tashi ya je ya yi
alwala ya yi nafila.
Har gari ya waye bai koma ba karshe ma hira suka fara yi da Zoe sai da lokacin sallar asuba ya
yi kafin ya yi mata sallama ya je ya yi sallar,yana idarwa kuwa wani irin barci ya cafkeshi take ya
koma kan gado ya kwanta.
Kamar wasa Javed ya ga har karfe takwas ta yi Farouq bai fito ba kuma yasan yawanci bai cika
barcin asuba ba,har an kawo masu abin karyawa ya ci nasa amman ba alamun Farouq,hakan
yasa ya gagara jurewa ya tashi ya nufi dakin.
Buga kofar ya fara yi cikin magagin barci Farouq ya tashi ya bude.
Da mamaki Javed ya kallesa ,"Oga wai yau kaine da barci haka?"
Miƙa Farouq ya yi, "Wallahi kuwa wani irin sahihin barci ne ya kwasheni ina idar da sallah dake
jiya ban wani samu dama ba."
Idon Javed jaraf akan hannun Farouq,"Subhanallah me ya sameka haka a hannu?"
Javed ya fada cikin yanayin nuna damuwa.
Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Ciwone na ji jiya da daddare a toilet,ka ga bara inyi wanka inzo."
Ya fada maganar yana saurin wucewa domin katsewa tambayoyin Javed.
Wanka ya yi ya shirya sannan ya fita falon ya samu Javed,Zama ya yi ya fara
karyawa,hayaniyar mutanen da ya fara jiyowa yasa shi dakatawa yana kallon Javed.
"Wannan hayaniyar fa lafiya kuwa?"
Javed ya ce,"Lafiya lau,ni na manta ma ashe yau ne ake murnar bikin Gani na nan
mokwa,maraba da dawowa daga Bida da kuma murnar bikin Ganin na shekara sai da na fita
dazu na gani."
"Oh Ma sha Allah,Shiyasa na ga ka dauko rawani kenan."
Farouq ya faɗa yana kallon rawanin dake gefen Javed.
"Yes kasan dole a naɗa asa kayan gargajiya ko mai martaba ya yi hukunci." Javed ya faɗa.
Farouq ya ce,"Nima ko ina sha'awar yin shiga irin takun nan kuma daman an bani kyautar
rawani,da zan samu kayan sai insa."
"Me zai hana? Ai sai in baka akwai sabin kaya da ban saba kasan lokaci zuwa lokaci duk ake
sabunta mana kayyayyaki irin na al'ada ko da baka da rawani ma ai dole a nemo indai kana son
sawa." Javed ya fada cike da zumudi ya tashi ya je ya daukowa Farouq manyan kaya da
alkyabba dukkanin su sabi fil ruwan ƙasa.
Da farinciki Farouq ya karɓa yana "aiko gasu kalan rawanin nawa har ma takalmin. "
Ya karasa maganar yana daukan takalmin.
Javed ya ce ,"To yanzu dai ka gama