Showing 12001 words to 15000 words out of 62597 words

Chapter 5 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

2361

DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials

- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-8

Yana gudu ba, kai tsaye ya faɗa bayi.
Cikinsa ya riga ya burga kafin ya ƙarasa toilet ɗin har wandonsa ya fara ɓaci.

Janinah da ta kalli kowa anyi tsuru-tsuru ta haɗa ido da kilishi tuntsirewa da dariya suka yi har
da riƙe ciki.
Cike da ɓacin rai da fushi mai martaba ya yi gyaran murya.
Ba shiri suka guntse dariyar suka yi nutsuwar dole.

Cike da izza ya fara magana.
"Javed garin ya ya ka kawo mana mashirmaci irin haka? Me hakan da ya yi yake nufi? Ni fa ba
wani son alaƙa da turawan nan nake ba."
Ya yi shiru ya na jan numfashi kafin ya ce. "Ni ban gama yarda ma yana sallah ba, domin
yawanci duk 'yan ƙasashen wajen nan ko sun ce su musulmai ne, a baki ne kawai ba su cika
yin addinin ba."

Kan Javed na ƙasa ya ce. "Ranka ya daɗe a yi mana afuwa, amman ga dukkan alamu cikinsa
ne ya ɓaci, tunda ba saba cin irin cimarmu ya yi ba, sannan kuma batun ibada gaskiya ba ya
wasa da ita sam."

Mai martaba ya ce. "Maddalla! Amman ba hakan ne zai bashi damar zuwa yana karya mana
dokoki da ka'idoji ba, daga yau ba na buƙatar sake ganin sa a duk wani taro ko zama da za a yi
har ya tafi, hasali ma ban so ya shiga duk wasu lamura da suka shafi sarautar gidan nan."

Ta ido Janinah da Kilishi suka kalli juna cikin jin daɗi.
Ba wanda ya yi magana sai can Abba Malik ya ce. "Kar ka manta wannan bako ne kuma ya
nuna yana sha'awar kasancewa cikinmu aka ce bakonka annabinka, ko ba komai in muka masa
halacci zai ji daɗin bayyanawa yayin da ya bar ƙasar nan, kuma ga dukkan alamu ba da son
ransa ko da gangan ya yi ba."

Mai Martaba ya ce. "Na riga na gama magana kuma ka san ba na magana biyu."
Hajiya Kaka ta ce, "Da dai an yi masa lamuni yaron na da hankali. "

"Ko da a ce jinin gidan nan ne zan iya dakatar da shi balle kuma wani bare, kun wani dage
kuna son kare shi kun manta cewa maganata ba mai canjuwa ba ce."
Mai martaba ya faɗa cikin fushi yana miƙewa.
Cikin sauri dakaransa suka rufesa har zai fita sai kuma ya tsaya ya ce. "Ba ma shi kaɗai ba,
daga yau ba na buƙatar wani bare cikin zaman da ya shafi al'ada." yana gama faɗa ya fice.

Ba abin da Abba Malik ya iya furtawa sai. "Allah ya kyauta."
Shi ko Farouq yana nan zufa ta jiƙe shi shakaf kamar wanda aka kwara wa ruwa.
Da ƙyar ya rarrafo ya kwanta a kan gado domin ƙarfin jikinsa kaf ya tafi.

Mai martaba na fita da Sauri Javed ma ya bisa ya je gun Farouq.
Yashe a kan gado ya gan shi yana ta murƙususu.
Ƙarasawa ya yi ya riƙe shi yana. "Ya dai cikinka ke ciwo?"
Farouq ya girgiza masa kai alamar eh.
Javed ya rasa ta ina zai fara daga kan da zaiyi sai ga Abba Malik ya shigo.
"Subhanallah ya kamata asamu abashi magani gashi ba ma kusa da asibiti kuma kar abashi
maganin gargajiya ya zame masa matsala tunda ba saba sha ya yi ba."
Javed ya ce,"Abba ko dai za a gwada domin jinkirin zai iya zama wata matsalar kuma."
Abba Malik ya ce. "Eh to haka ne kuma, yi sauri ka kira Baban ganye mu ga ko da taimakon da
zai iya yi masa."
A hanzarce Javed ya fita ya kira Baban ganye, yana zuwa kuwa wani ruwa ya fara ba wa
Farouq ya sha cikin mintuna kaɗan ya fara dawowa hayyacinsa.
Tambayoyi ya fara yi masa me ya faru.
Farouq ya ce,"Ehto na fara cin abinci sai na ji yaji ya yi yawa ba irin wanda na sababa daga nan
kawai sai na ji cikina ya fara murɗawa kuma cikin ya yi zafi sosai kamar wuta na ci."

Numfasawa Baban ganye ya yi ya ce. "Ba matsala In sha Allah, wannan ruwan ma da na baka
kawai ya wadatar, zan ajiye maka sauran zuwa anjima sai ka ƙara sha, da izinin Allah cikin zai
wanku ko ma miye a ciki zai fita, yanzu ka samu ka huta ka ɗan yi bacci ko da zaka farka zuwa
anjima."
Abba Malik ya kallesa ya ce. "Sannu ko Malam Umar, Allah ya ƙara sauƙi, ka kwanta ka huta
ɗin."
Cikin muryar rashin lafiya Farouq ya amsa "Amin Abba, na gode Allah ya saka da alkairi. "
Ya kalli Baban ganye ma ya ce,"Na gode Baba Allah ya saka da alkairi. "
"Ba komai sannu ko."
BabanGanyen ya fada yana haɗa kayansa kafin ya fita.

Abba Malik ya kalli Javed ya ce,"Sai ka zauna da shi Incase ko zai buƙaci wani abu."

Javed Ya ce,"Okay tom In sha Allah Abba."
Sallama ya yi masu ya fice.
Farouq kuwa wani barcin wahala ne ya yi awun gaba da shi.
Javed ya hau kujerar da ke gefen gadon shi ma ya fara barci.
Karfe biyun dare na yi tsilif kamar an tsikari Farouq ya tashi.
Da sauri ya dauki System dinsa cikin Foldern Gidan Sarkin Al'adu ya fara shiga.
Wasu abubuwa ya yi tickin sannan ya yi kansil ɗin wasu ya yi saving kafin ya shiga Yanar gizo
bincike.

Jin motsin da Javed ya yi ya saka shi farkawa.
Yana farkawa ya ga Farouq ya duƙufa kan System sai shiga da fita yake.
Cike da mamaki ya ce,"Ah mara lafiyan ke nan?"
Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Na dameka da mutsu-mutsu ka farka ko? Sorry ko zaka koma
dakinka to na ji sauki fa."
Javed ya ce,"Ba wani damu wallahi,amman dai wannan ƙarfin hali ne sai ka ce aikin barin
duniya ba za ka kwanta ka huta ka samu ishasshen barci ba?"
"Umm Allah na ji ni kamar wani abu bai same ni ba,gaskiya ban ga laifin mai martaba ba da
yake riƙo da al'adu sosai ka ga maganin gargajiyan nan ko kaɗan ban yi tunanin zai yi mun aiki
ba, amman gashi cikin mamakina ina ji na tamkar wani abu bai sameni ba, kai ba ma wannan
ba ashe kuma kuna da kasurgumin barawo a gari." Farouq ya faɗa.
Da sauri Javed ya ƙarasa inda yake yana,"Kamar ya ? A ta ina kuma?"
Farouq ya ce,"Anan Niger State mana mai kwamushe kudaden mutane amman ba halin ganin
address Location ɗin ma da ya bari aka ga Nigern ina ga akwi dalili kuma ban san wani tsari
yake bi ba amman dai zan san yadda za ayi mu kulla alaƙa da shi ta yadda zamuji bayanai duk
da hakan zai yi wuya."
Javed ya ce,"Ikon Allah yoo ni wannan abun naku ai na kusa in sare ace mutum ba hutu ba
lafiya ma bazai huta ba."

Farouq ya yi dariya,"Kai dai ai ragon namijine ne je ka yi barcinka."
Aiko tashi Javed ya yi yana,"Sai da safe ma karasa magana."
Farouq ya daga masa hannu yana ci gaba da danna System dinsa.

Washegari
Karfe Bakwai na safe ya gama shiryawa zasu bangaren Hajiya Kaka shi da Javed ya ji alamar
sako ya shigo wayarsa.
Yana dubawa ya ga.
,"Ya dai? Ya Kashin? Ya tsaya ko dai sai an kawo taimako, yau kam na san da kyar ai a iya
motswa,KAƊAN KA GANI asha jinya lafiya."
Da number aka turo sakon amman dake yana amfani da tracker yana dubawa ya bayyana
masa da details din Jinanah.

Murmushi ya yi yana karanta saƙon.
Javed ya ce,"Lafiya ? Mu tafi ka tsaya kanata kallon waya kana murmushi."
Farouq ya ce,"Oh Sorry mu je ko."
Suna zuwa bangaren Hajiya Kaka kuwa da Janinah suka fara cin karo.
Da mamaki ta kallesa tamkar wanda ba wani abu da ya sameshi.
Karshe ma kallonta ya yi yana sake mata matsakaicin murmushi ya wuce ya shige ciki ya barta
da suman Tsaye.
Hajiya Kaka na ganinsa tai rau da fuska,"Ayyah mijin yanzu nake cewa Janinah ta zo ta rakani
mu duboka ashe kana tafe,jikin yi sauki ke nan."
Zama ya yi daidai da lokacin da Janinah ta karaso cikin falon ya na kallonta ya ce,"Kin san ba a
taba jinin sarauta cikin ruwan sanyi ko da ace wanda ya taɓa shin kuwa shi ma yana dauke da
jinin ne."
Hajiya Kaka ta ce,"Kar dai kace mun kuma acen kasar wajen akwai sarauta."
Farouq ya yi dariya kafin ya ce,"Sosai ma ai ako ina akwai jinin sarauta bare ma ni tunda nake
da mata sarauniya kuma gimbiya ai dole jinin sarauta ya zagaye jikina."
Dariya Kaka ta yi ta ce,"Lallai kam mijin ba ka da dama yanzu dai na ji dadin ganinka haka don
ni ban shirya takaba ba ga lokacin shagali na karatowa ina so in dau wanka in kashe kala ai
nace muje ka sakeni kawai kafin ka mutu."

Suka yi dariya Farouq ya ce,"Wato ma ta ado da kwalliya kike ba lafiyata ba."
Hajiya Kaka ta ce,"Aa fa tunda dai ka ji sauki ka fasa mutuwar to aurenmu na nan gam gam ba
motsin komai yawwa."


Dariya suka yi duka.
Farouq ya tashi yana fadin,"Tom mun tafi ayi mana addua."

"Allah ya bada sa'a,aje lafiya adawo lafiya kuma ubangiji yasa muku albarka a dukkanin
lamuranku."
Hajiya Kaka ta fada.

Da Amin duka suka amsa Farouq ya ce,"Amman yau ba ke ba iskirim."

Hajiya Kaka ta ce,"Haba Masoyi na har a bada,bari in maku irin na yarenku ma na yan gayu
Elubuyu haka ake cewa ko Janinah."
Ta karasa maganar tana kallon Janinah.
Tintsirewa da dariya duka suka yi ba tare da sun bata amsa ba.
Ɓata rai kaka ta yi ta ce,"Dadin abun ma nima ina da yarena ai sai in fada da shi Na mi ve eko
(Ina sonka)."

"Na mi ve eko kwo (nima ina sonki) dole a siyo miki iskirim yau kam harda shawarma ma."
Farouq ya fada yana dariya suna fita.
[13/05, 9:57 am] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear

- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-9

DigitalCraft suka nufa,suna zuwa Farouq ya yi Lectures Room.
Karatu suka kutsa kai tsaye.
Bayan kowacce ta kunna system dinta.
"Yau za mu magana ne akan HACKERS
Hackers mutane ne da ke da kwarewa a fannin kwamfuta da tsare-tsarenta suna bincika salo
da tsarin kwamfuta,hanyoyon sadarwa da kuma software don fahimtar yadda suke aiki,suna
gano rauninsu da kuma yiwuwar canzasu,sarrafasu ko ma tarwatsasu.
(Hackers: Individuals who use technical skills to gain access, manipulate, or exploit computer
systems, networks, or data, often with varying motivations (malicious, ethical, or neutral).)

Sannan sun rabu kashi kashi kamar su:
White Hat Hackers
Sune masu amfani da kwarewarsu dom kare tsarin kwamfuta suna taimakawa kungiyoyi da
ma'aikata wajen sanya tsaro mai karfi a kwamfuta da kuma gano rauninta kuma suna bada
shawarwarin hanyoyin da za abi domin inganta tsaro da izinin masu na'ura.

Black hat hackers
Waddannan sune masu gudanar da aiyukan cutarwa ta hanyar bin raunin tsaron kwamfuta
domin sato bayanai don wata manufa na cutarwa ko kuma tarwatsa tsari da shirin na'ura ba tare
da izinin masu shi ba.


Gray hat Hackers
Su kuma wa innan suna tsakanin white hackers da black Hackers sukan iya yin kutse ga na'ura
ba tare da izini ba amman kuma ba da niyar cutarwa ba sai dai don duba raunin tsaro kuma su
kan yi kokarin sanar da kungiyoyin ko ma'aikatan domin suyi gaggawar Gyara a wasu lokutan
kuma sukan iya neman kudi bayan sun gano wasu bayanai.
Wa innan ukun sune jiga-jigai da kan iya aikata komai amman bayan su kuma akwai.

Script Kiddie

Wa innan masu harin basu da kwarewa sosai suna amfani da rubutun da wasu suka kirkira ne
don gudanar da hare-harensu.

Hacktivist
Su kuma wa innan suna amfani da hari ne matsayin nuna ra ayi na siyasa yawanci suna kai hari
ne kan shafukan yanar gizo na gwamnati ko kamfanoni don nuna adawa da manufofin ayyukan
da basu yarda da su ba.

State Sponsored Hackers
Su kuma wa innan gwamnati ne suke daukan nauyinsu suna cikin harkokin leken asiri na yanar
gizo,kuma su kan iya sato bayanai masu mahimmanci daga wasu kasashen ko kuma katse
muhimman hanyoyin sadarwa.

Phreakers
Su kuma suna maida hankali wajen harin tsarin sadarwa a tarihi suna yin amfani da tsarin waya
don yin kira kyauta ko kuma amfani da hanyoyin sadarwa na waya.

Amman karku manta The three main types of hackers to consider are:

White Hat Hackers: Ethical hackers who help organizations improve security.
Black Hat Hackers: Malicious hackers who exploit vulnerabilities for personal gain or harm.
Gray Hat Hackers: Hackers who operate in between, often without malicious intent but without
permission.
Dukkanin wa innan guda ukun zamu gudanar da practical kan yadda kowannensu ke gudunar
da aiki In sha Allah.
Ina fatan kun gane?"

"Yes Sir." Suka amsa cike da kwarin gwiwa.

Farouq ya ce,"Ko da kwai mai tambaya?"
Kamar kullum Meemah ce dai ta fara daga hannu ta ce,"Sir Ke nan mu mata zamu iya zama
white hackers ko black Hackers dinnan nan?"

Farouq ya ce,"Eheen me zai hana? Ka da kiyi tunanin akwai wani abu da ba za ki iya ba don
kasancewarki mace muddin ba addini bane ya haramta miki,mata sun fi maza naci da dagiya
ma indai suna son abu har sukan zarce namiji kwarewa ka da al'ada tana ruɗarku kuna tauyewa
kanku hakki indai abu ba ubangiji bane ya haneku ga aikatawa mussamman bangaren neman
ilimi ko dogoro da kai ka da kuyi wasa da shi sam sam kuma In sha Allah kafin in bar kasar nan
sai kun zama kwararrun mata na farko da a bangaren na ura kaf nigeria ba iya Niger state ba
babban burina shi ne kusa aranku za ku iya."

Tafa masa suka fara yi cike da jin dadi.

Farouq yana komawa office ya tarar da Javed zaune suka shiga hira yake bashi labarin yadda
yake jin dadin tambayoyi da nutsuwar da Meemah ta ke yi "Ga dukkan alamu yarinyar na da
basira sosai ba laifi."
Javed ya ce,"Gaskiya nima na lura da hakan,ni fa ba don kar ace na cika azarɓabi bama sai
ince ni tamun kamar in shiga daga ciki amman kuma inna tuna yanayin gidanmu sai inji ban da
kwarin gwiwa hakan yasa ma ni ko tunanin aure ban sa a gaba ba domin ina gudun kada inje in
faɗa kogin da zan azabtu kuma in azabtar da 'Yar da mutane."
Farouq ya ce,"Ban gane ba, Ke nan hatta matar aure ma ba ku da hurumin zaɓa sai dai a zaɓa
maku?"
Javed ya ce,"Kwarai kuma Mai martaba ne da kanshi yake shedawa mutum ya je ya ga 'Yar
wane kaza su sasanta kuma dole sai jinin sarauta,kuma ni sam lamarin sarautar nan bai taɓa
birgeni ba shiyasa na ke jin dadin kasancewa da Abba Malik rayuwarsa ba tsanani sam."

Farouq ya numfasa kafin ya ce,"Lallai abun babba ne shawarar da zan baka kawai shi ne ka
dage da addu'a domin babu abun da yafi karfin ubangiji in yaso sai ka ga ka auri yarinyar da
kakeso take sonka cikin aminci ba tare da takura ba."
Javed ya ce,"Hakane kam In sha Allah mussamman yarinyar tun farkon ganina da ita nake
kwana nake tashi ina daurewa ne kawai."
Farouq ya yi dariya,"Ka bayyana a gareta kawai sannan ka mikawa ubangiji yakinin cewa indai
ita alkairi ce a gareka zaka sameta."
Javed ya gyara zama,"Ko?"
Girgiza masa kai Farouq ya yi yana murmushi.

Javed ya ce,"Yess ban taba samun kwarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login