Showing 60001 words to 62597 words out of 62597 words

Chapter 21 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

1639

farin ciki.’

Kuma Allah Ko da Alqur’ani ya na cewa: “Ku tuna Ni, zan tunaku. Ku gode mini kada ku
kafurta.” Wannan yana nuna Allah yana son bauta mai cike da kauna, ba tsoro kawai ba.

A Musulunci babu banbanci tsakanin fari da baƙi, talaka da mai kudi, mace ko namiji kowa dai

Allah yake duba zuciyarsa da ayyukansa.

Haka kuma Tawakkali da Aminci
Musulmai suna dogara ga Allah (SWT) a dukkan al’amura kuma hakan yana basu kwanciyar
hankali da karfin zuciya, musamman a lokacin damuwa. Wannan yana birge mutane masu
neman natsuwa a zuciya.

Akwai wasu ayoyi biyu ma da suka kara bayyanar mun da cewa a cikin duhu muke rayuwa.
Suratul Ma’idah (5:75) ta ce:

"Almasihu ɗan Maryam ba komai ba ne face Manzo. Lalle an riga an yi wasu Manzanni kafin sa.
Kuma mahaifiyarsa mace ce mai gaskiya. "

Sannan shi da kan shi Almasihu a Suratul Maryam (19:30) ya ce,"

[ َلاَق يِّنِإ ُدْبَع ِ
هَّللا َيِناَتآ َباَتِكْلا يِنَلَعَجَو اًّيِبَن
Lalle ni bawan Allah ne, Ya ba ni Littafi kuma Ya sanya ni Annabi,ka ga kenan hakikanin
gaskiyar cewa shi ba Allah bane kamar yadda muke ɗauka,shi annabin Allah ne.

Da kuma
maganar da Yesu (Almasihu) ya faɗa a Bible lokacin da aka daura shi akan cross.

In Matthew 27:46 and Mark 15:34, Jesus said,"
My God, My God, why have you forsaken me?
Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?"

Dana bincika a Musulunci kuwa,
Babu irin wannan magana saboda Qur’ani ya ce Isa bai sha wannan azaba ba kuma Allah bai
taɓa yashe shi ba.

Sannan kuma yadda kuke rayuwa tsakaninku aminai biyar na matukar birgeni anan na kara
gasgata cewa tabbas hakan koyarwar addininkune kuma Zeeyter ta bani labarin cewa dukkanin
ku ba yan uwa bane hasalima a yanar gizo kuka hadu amman kuke rayuwa da son juna da
kuma goyon bayan juna fiye da wasu yan uwanma tun farkon haduwata da ku kuka fara bani
sha'awa nake jin cewa dama nima a cikinku nake,kuma ina da wani friend da yake Christian
ada amman yanzu ya zama Muslim tunda ya shiga Prison a London ya ga yadda musulmai ke
da hadin kai da kaunar juna ga rikon ibada tuni ya shige cikinsu shi ma ya musulunta, harda shi
a masu kwadaita mun cewa in shiga musulunci yana yawan bani labarai masu dadin
sauraro,kuma ga ku da son kyauta domin an kwadaita maku cewa wanda kuka bada shi ne
naku ku bada kadan Ubangiji ya ninka maku masu yawa ni dai ina son wannan addinin sosai
kuma ma kasan miye?"

Farouq ya ce,"Aa sai kin fada." Cikin zaƙuwa.

Zoe ta ce,"Duk lokacin da nake cikin damuwa na yi wannan sallar na yi addu'a sai inji dadi
araina mussamman in na karanta suratul fatiha dinnan ita kadai kuma na iya ina son surar sosai
tana mun dadi tun ina sauraro kawai har na ji na haddaceta sannan kuma
Qur'an Application da Omar Sulaiman suna yi yana bada komai dalla-dalla mussamman ga
wanda ke son musulunta.
Ko kai da kake musulmin ma zan so ace ka sauke wa innan Applications din Deen Body,True
Ilm,Qur'an Application na su Umar Sulaiman na tabbatar da cewa zaka ji dadin kuma zaka kara
kaunar addininka."

Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Tabbas dukkanin abubuwan da kika fada gaskiya Musulunci
addini mai dadi kuma mai daraja,na ji dadi sosai ba kadan ba."

Ya karasa maganar yana tashi ya ce,"Kin ga wannan daddan labarin ba zan iya barinsa haka ba
yanzu zanje in sanar."



"Alright byee,Love you." Zoe ta fada tana murmushi.
Amsata mata ya yi da,"Love you too." Shi ma yana murmushi ya fice da sauri.

☆☆☆Bayan anje Masallaci Zoe ta musulunta suka koma daki.

Suna zaune duka suna cin abinci da dare.
Zeeyter ta ce,"Muna da biki fa afara shiri."
Kallonta duka suka yi cikin yanayin tuhuma.
Haiydar ya ce,"Bikin wa kuma?"

"Friend da Zoe saura kiris ni kawai ma a daura mana anan kafin mu tafi." Zeeyter ta fada.

Khalil ya ce,"Ma sha Allah ga dawowa cikin musulunci ga aure,ni daman na so hakan araina
ashe abun na tafe."

Deejerh ta ce,"Maddalla yanzu dai yan mata zasu huta da yaudara."

Dariya duka suka yi.
Farouq ya ce,"Tunda aka ce miki innayi auren kasuwata mutuwa za...
Yana cikin fada suka hada ido da Zoe ya yi shiru dariya suka kara kyalkyalewa.

Ana saura kwana ɗaya Farouq ya cika sati akan kujerar sarauta aka daura aurensa da
Zoe,Janinah da Arham,Javed da Meemah.
Simple wedding aka yi ba taron jama'a zallan yan gida ne aka ci aka sha aka yi murna kawai.
A daren ranar Farouq ya sheda cewa Jammal ne zai karfi sarautar al'adu domin Abba Malik ma

ya nuna baya so kuma da ya duba sai ga Jammal ne mafi cancanta.
Hakan yasa aka naɗa shi.
Hakan yasa a ka sanar da sarkin Bida domin acen zasu je ayiwa Jammal naɗin.

Wani abun mamakin da farincikin kuma a daren ranar aka sanar da cewa Aunty Heedaya matar
Abba Malik na dauke da cikin yan biyu bayan tsawon shekaru.
Farinciki ta ko ina ya kewaye gidan.

Washegari kuwa da sassafe suka nufi bida domin yiwa Jammal naɗi anyi raye-raye anyi
waƙe-waƙe basu kwana ba aranar suka koma mokwa cikin dare saj ga Xavier ya zo da labari
mai dadi an kama Naƙif wanda ya kasance shi ne shugaban yan ta'adadan da Abdul-Raheem
ke amfani da shi suna kashe mutane sannan an samo sauran yan uwansa wanda suka kasance
suna kasashen waje Adams tsohon Mijin Zahra da kuma Zaid Uncle din Deejerh kowannensu
Xavier yasa an kamasu a inda suke har ma akaisu gidan yari,dukkaninsu team guda ne da suka
addabi rayuwar al'umma kuma suke safarar miyagun kwayoyi da mata.

Kowa ya yi farincikin jin labarin sosai mussamman Zahra da Deejerh domin yanzu sun tabbatar
da sun samu yanci rayuwarsu babu barazana.

(MASU KARATU KILA BAKU FAHIMCI DALILIN SAKO SU BA KO? TO KU KARANTA
YEL,FREEYA,VIXEEN zaku fi fahimta domin wannan Chronicle novel ne CENTUAR shi ne na
karshen.)

Ko da aka je duba Mai Martaba Abdul-Raheem ya gama yayyaga kayan jikinsa har fatar jikinsa
ya dunga ci karshe sai gawarsa aka gani hakan yasa aka yi masa wanka aka binnesa.

Zaune dukansu a falon Hajiya kaka ana hira,Hajiya Kaka ta katse su da fadin,"Yarima yanzu kai
ba za ku yi aure ba haka duk zaku zauna?"
Ta karasa maganar tana kallonsa shi da Maah.

Murmushi Yarima Rasheed ya yi ya ce,"Ban jin cewa Mariam zata amince da aurena kuma ban
ga laifinta ba sannan dukanmu muna farinciki a rayuwar da muke yanzu Alhamdulillahi ga
Farouq muna gani ina ganin ko a haka ai mun dace."

Hajiya Kaka ta ce,"To ai shikenan na ji tana batun komawa malaysia,Allah ya tabbatar da
alkairi, Ina fatan zumuncinmu ba zai kare haka nan ba. "

Maah ta ce,"In sha Allah ai an zama ɗaya Hajiya."

Yarima Rasheed ya ce,"Yawwa daman ina son sanar da ku cewa na maida hakkin mallaka na
kamfanina ga Farouq domin na san inna bar duniya ba ya da gadona."

"Ma sha Allah hakan ya yi sosai kuma na ji dadi Ubangiji ya kara tabbatar da alkairi. "
Godiya suka yi masa da fatan alkairi


Daga nan sun sha hira sosai har dare.

Zoe da Farouq kuwa ranar ɗaki ɗaya aka kwana ana shan soyayya.

Washegari da safe suka haɗa General Meeting na 5stars wanda Khalil ya kira.
Shi ne ya fara jawabi da fadin,"Bana so mu bar kasar nan ba tare da mun ƙara aikata wani abun
kwarai din ba domin garin nan ya birgeni matuka mai zai hana mu fidda wata hanya da za a
samarwa da wasu aiki kuma."

Farouq ya ce,"Gaskiya wannan Idea ce mai kyau nima na fara tunanin hakan domin ka ga garin
suna da kyan noma sannan akwai kayan ma adanai."

Zeeyter ta ce,"Oganni zan iya yin magana?"

Farouq ya ce,"Bismillah mana Madam ai ba sai kin tambaya ba. "

"Yoo wai ai ina tsoron sa bakine a maganar dangi kar amun gori tunda dai anki amaida lamarin
6stars ko ni ba tauraruwa ba ce oho." Ta fada.

Dariya suka yi duka Haiydar ya kalleta ya ce,"Haba dai a dukkaninmu kawai muna amsa sunan
ne amman kece asalin hasken boyen da ke haskaka mu Uwargida."

Farouq ya ce,"Tabbas Gimbiyata."

Taɓe baki ta yi ta ce,"Yawwa ga shawara mai zai hana ayi PPP public-private partnership ina
nufin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu kamar dai mu kenan
sai ayi akan harkar noma da kiwo,kun sanni da shige shige garin bincikena na ga garin nan
suna da wannan tsarin kuma gaskiya abun ya birgeni."
"Nice Idea Our Yel gaskiya na ji dadin wannan batu,to ku ya kuke gani?" Khalil ya fada.


Dukansu amsawa suka yi da suna goyon baya.

Farouq ya ce,"Amman ko za ki iya mana karin bayani kan tsarin su?"

Zeeyter ta gyara zama ta ce,"Public-Private Partnership (PPP) wata hanya ce da ake amfani da
ita domin haɗa ƙarfi tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wajen gudanar da
manyan ayyuka da kuma samar da kayayyakin more rayuwa. Wannan tsarin yana taimakawa

wajen rage nauyin kashe kuɗi ga gwamnati da kuma samar da ingantattun ayyuka ga al’umma.

Gwamnati tana bada dama ko ƙasa,
Kamfani yana saka jari da gudanarwa,
Ana amfani da aikin don amfanin al’umma.

Misalan PPP

Gina hanyoyi,Wutar lantarki,Asbitoci,Noma da kiwo kamar yadda kuka ce akwai kyan noma
anan da sauransu.

Ga kadan daga Fa’idodin PPP

Rage nauyin gwamnati wajen kashe kuɗi.
Samar da ayyukan yi ga jama’a.
Inganta inganci da ƙwarewa a ayyukan more rayuwa.
Rage talauci a ƙasa.
Yin ayyuka bisa tsari da sauransu.

Zahra ta ce,"Maddalla da ke."

"Me zai hana mu dau bangare biyu to na noma da kiwo? Ai ina ganin za a iya yinsu a tare."
Haiydar ya fada.

Deejerh ta ce,"Gaskiya ya yi sosai hakan ma in akayi."

Khalil ya ce,"Zai fi tafiya da yanayin garinma fiye da tunaninmu."

Farouq ya ce,"Yes kuma mu namu ma ina tunanin abu uku zamu haɗa tunda muna da
wadatattun filaye akwai wani wanda yake Na gidan nan akwai ma'adainai zamu haɗa har dashi
a fara haƙowa."

Zahra ta ce ,"Ma Sha Allah to yanzu suwaye kuke ganin zamu fi maida hankali a dauka aikin?"

Haiydar ya ce,"Mata,Mata irin wa inda suke da matukar bukata,ma ana wanda mazajensu basa
sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ko wa inda mazansu suka rasu da dai sauransu domin
hakan ma tamkar wata hanyace da za a budewa mata a nuna masu hanyar da zasu tashi su
nemi na kansu da kuma nuna darajar sana'a ga 'Ya mace na tabbatar da cewa zamu samu lada
ko awajen ubangiji."

Dukaninsu sun amince da shawarar da suka yanke,Farouq da Haiydar zasu yi kokarin wajen
shigar da batun gwamnati shi kuma Khalil ya fara tsara yanayin ginin da zasu fitar.

Ko da Farouq ya sanarwa da Abba Malik da Yarima Rasheed sun yi farinciki sosai kuma sun
basu goyon baya ɗari bisa ɗari,hakan yasa ma suka shige masu gaba wajen tabbatar da komai
ya tafi daidai,cikin wata guda kuwa suka kammala komai da gwamnati.

Ginin da zasu yi ne kadai ya rage shi ma suka fara don Khalil ya riga ya gama tsarawa,Javed
ma ya yi masu kokari sosai da shi aka dunga shiga da fice hakan ma yasa Suka yanke
shawarar cewa in sun tafi shi zai dunga lura da wajen duk da cewa suma zasuna zuwa lokaci
bayan lokaci.
Cikin ikon Allah aka kammala komai aka dauki mata aiki kamar yadda suka tsara, anyi nasarar
fara haƙo zinare sannan an fara kiwo da noma.

Nomar shinka da alkama har sun fara fitowa saboda kular da suka samu domin da kansu suke
yin taki, a cikin matan da aka dauka aiki aka ware wasu aka koya masu yadda zasu na yin
ingataccen taki na gargajiya.
Sai da suka tabbatar komai ya tafi daidai kafin suka fara shirin tafiya.

Janinah da Ameemah an maida su School duka suna university sannan Farouq ya kara karfafa
mata kan Foundation dinta yanzu an santa an san ita ke gudanar da komai.



Gabadaya 5-Stars Malaysia suka nufa domin wai acen zasu ce su yi shagalin auren Farouq da
Zoe tunda aure kawai aka daura a Nigeria.
Hakan ne kuwa ya kasance duk da Farouq ya so hana Zoe daukansu a Jet dinta ganin ita
Amaryace ta ce aa ita kam da kanta zata kaisu.

Sunyi sallama da Mokwa Janinah da Hajiya harda kukan rabuwa da Farouq ya masu alkawari
ba zai jima ba zai dawo ya gansu.


Kafin su isa Malaysia Maah ta haɗa masu tarba sosai domin tana matukar kaunar Zoe
mussamman da kasance kamar ita da ta musulunta.

Suna zuwa washegari gari aka fara shagalin biki.
Zeeyter da Haiydar ba wasa sun tiƙi rawa son ransu anyi wasa anyi dariya sannan anyi farinciki.
Bayan an kammala biki kafin kowa ya koma sai da suka yi saukar Qur'ani suka yi Adduoi sosai
sannan suka yi sadaka ta mussamman kafin kowa ya kama gabansa.

Zoe na kwance a cinyar Farouq ta ce,"Ka san mene ne?"
Farouq ya girgiza kai.
Tashi ta yi ta zauna kafin ta ce,"Da ace a duniya za asamu irin 5stars da rabi da kwatan

matsalolinta sun ƙare ko ma duka matsalolin a nemesu arasa,dukaninku kowa na da labari mai
ban al'ajabi da tausayi amman saboda jajircewa da rashin cire tsammani da rahmar ubangiji ji
yadda kuka zama abun alfahari ga duniya,ni dai ina fatan nima na zama jajirtacciya kamar
yadda Marubuciya Aisha Sani Abdullahi ta ce "Namiji kokari garesa mace kuwa jajircewa gareta
zan so haɗa dukkanin biyun,domin yin aiki tuƙuru,har in kai ga cin nasara a rayuwa." To nima
hakan biyun zan haɗa duk waje guda domin inyi koyi daku."

Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Da farko ki fara yarda da kanki,kuma kiji aranki cewa za ki iya
duk wani abu da kika sa a gaba,duk rintsi duk wuya,domin nasara binta ake tana gudu sai an
dage kuma an tsammaci cimmata duk tsanani sai adace."

Rugumesa ta yi kafin ta ce,"In sha Allah ai ma nasan ko da na yi kokarin sarewa ba za ka taɓa
barin hakan ya faru ba."



ALHAMDULILLAHI
Alhamdulillah! I have finally completed my book series “5-Stars Chronicle” after three years
(2022 to 2025) of dedication and hard work. The series includes Yel, Freeya, Vixeen, and
Centuar.

My heartfelt gratitude goes to all my amazing readers who have stood by me from the very
beginning until now, and to my mentor who tirelessly supported and guided me throughout this
journey. Thank you for your love, encouragement, and loyalty.

I hope you all enjoyed the books and learned valuable lessons from them. For those who
haven’t read Yel, Freeya, and Vixeen yet, I invite you to do so because I’m confident you won’t
regret it.

I wish you all the very best and send you my love. There’s also a possibility of a small giveaway
to celebrate the completion of this journey. Stay tuned! ❤️



Urs Aisha Sani Abdullahi Xayyeesherthul-humaerath
08103080717

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login