Showing 36001 words to 39000 words out of 62597 words
Chapter 13 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
rayuwarmu duka. "
Numfasawa Farouq ya yi yana ajiyar zuciya kafin ya ce,"Hakane kun tunatar dani abubuwa da
yawa dana manta kasancewarmu tare babbar nasarace haɗakar ruhi mabambamta da suka
sha gwagwarmayar rayuwa,zamu ci gaba,ba zamu taɓa fasawa ba har sai mun kai ga cin
nasara." Ya karasa maganar yana sakin murmushi.
Zeeyter ta ce,"Ko kai fa, da har na fara tantamar cewa ko an canja muna kai ne in bazama
nemo na asalin. "
Dariya suka yi duka kafin suka yi sallama.
Duk da cewa Farouq ba zai taɓa jin sanyi aransa kamar baya ba,amman tattaunawa da
aminansa ya rage masa raɗaɗin da yake cikin zuciyarsa kashi saba'in cikin ɗari hakan yasa
suna katse wayar ya tashi ya yi sallah raka'ah biyu ya nemi gafara wajen Ubangiji sannan ya
roƙi nasara da kuma budewar hanya cikin gaggawa domin nemo mahaifinsa.
Javed dai ranar barci rabi da rabi ya yi gabadaya hankalinsa a tashe yake kan tafiyar Farouq
hakan yasa asuba na yi kai tsaye ya kutsa dakin yana,"Oga zuwa karfe nawa zaka tafi kenan?"
Jikinsa a sanyaye yake fadin hakan.
Farouq ya fito daga toilet kenan ga dukkan alamu alwala ya yi.
Farouq ya yi murmushi ya ce,"Na fasa In sha Allah sai an kammala komai kafin in tafi."
Tsabar farinciki Javed bai san lokacin da ya rungume Farouq ba yana,"Maah din ta ji sauki ko?
Alhamdulillahi nikam ma in son ganinta kake asa tazo mana kawai."
"Umm kar ka damu yanzu dai muje sallah na ji ana shirin shiga." Farouq ya faɗa.
Mai Martaba ma daren ranar baiyi barci ba sunata faman bincike da tsubbuce-tsubbucensu.
Cike da gajiyawa ya ce,"Cai ni fa na gaji,na fara karaya da lamarin nan,da gaske yaron nan
yana so ya fi karfina, ban san me ya taka wanda ni ya gagareni ba."
Moli ya sheƙe da dariya kafin ya ce,"Oh ka dauka wasa ne da duk nake fada maka cewa za a
sha wuya? Yanzu ai ka ga zahiri ko ni kaina na galabaita bare kai da kake bil adama haka ma
yarana kaf sun fita a hayyacinsu har wa inda kasa sarki ya turo mana domin tallafawa sun gaji
lamarin babu sauki sam kuma ga dukkan alamu in har muka ce zamu tsaurara za a samu
matsala da har zata iya shafar rayuwarki."
Mai Martaba ya ce,"Wai wannan wane ne yake so ya ga bayana ne? Wane ne yake kokarin
tona sirrinkan dana binne?"
Dago wani farin kyalle moli ya yi anyi rubutun ajami da jini a jiki yana,"Anyi nasarar samu wasu
bayanan bayan shafi awanni ashirin da hudu muna fama." Ya karasa yana kyalkyalewa da
dariya.
Da sauri Mai Martaba ya maida dubanshi ga Moli cikin zakuwa ya ce,"Me aka samo? zamu iya
koranshi dai ko?."
Moli ya daga kyallen ya sa shi cikin bakinsa hadiye yana wani irin tauna ya ce,"Wannan yaron
jinin masarautar nan ne,kamar yadda jinin sarauta ke guduna a cikin jikinka haka shi ma ko ince
ma nasa ya fi naka karfi domin bangarori biyune da shi,ba wanda ya isa ya koreshi a cikin gidan
nan ko kasar nan ba zai taɓa yiwuwa ba domin jinin kasar ne kuma jinin gidan ne."
Cikin ruɗu Mai Martaba ya ce,"Ke nan Abdul-Rasheed na raye? Wannan yaronshi ne ko shi ne?
Ke nan shi ya turo Ɗansa domin ya tona mun asiri? Yaushe ya yi aurenma? To ai baici ace ya
haifi yaro kamar wannan ba bayan ɓatar da shi din da na yi, ko da ace yana Ɗa to ba dai
wannan ba,to in ba haka ba ke nan shi ne ya dawo yaro? Ah ah." Ya karasa maganar yana rike kansa da ya fara sara mishi yana juyawa.
Moli ya yi ihu kafin ya ce,"Duk bamu da amsar wa innan tambayoyin naka kuma ban ga kofar da
zamu iya samo su ba,abu ɗaya ne bincike ya nuna cewa babu wanda ya isa ya fidda wannan
yaron daga masarautar nan kuma hakan ma kasan sai da duk muka ki jiki mun kwana cur akan
wannan yaron abun ma mamaki yake bani ta yadda yake da wannan power haka,ban taba
samun bil adama haka ba,lallai na gasgata cewa akwai jinin sarauta mai karfi da ke guduna a
jinin jikinsa yanzu sai dai muyi iya bakin kokarin mu wajen danne taurarinsa da kuzaharinsa
yadda ba zai iya bamu kowacce matsala ba da zai daga ma hankali."
Mai Martaba ya ce,"Yawwa yawwa ni dai damuwata a rufe bakinsa akaina kuma inma
Abdul-Rasheed na raye a kara kaɗa hankalinsa ko da ma shi ya turo shi domin in ba hakan ba
akwai matsala gaskiya akwai matsala."
Moli ya ce,"Kai dai kawai ka dage ka daure kuma ka ci gaba da zama kan tsarin da
kake,mussamman batun sallar nan kar ka kuskura ka yi domin kana yi za a iya samun matsala
sai dai ka ci gaba da yi kamar yadda kake ka je ka tsaya kamar kana yi amman baka komai."
"Yanzu ma na ji sun shiga,bara inyi sauri inje domin in ban fita ba za a iya zuwa nemana." Mai
martaba ya fada yana saurin sanya rigarsa.
Take Moli da muƙarabbansa suka ɓace shi kuma ya fita masallaci.
An riga an tada ma kafin ya karasa haka yaje ya tsaya ba abun da yake illa ruku'u da sujjada in
anyi ba tare da fadin komai ba.
Ana idar da sallar ya fito zai wuce ke nan suka haɗa ido da Farouq.
Ƙura masa idanu Farouq ya yi ido cikin ido yana yi masa kallon tuhuma.
Sai da jikin Mai Martaba ya amsa alamun rashin gaskiya ya bayyana a gareshi jiki na rawa ya yi
saurin barin wajen.
A zuciyarsa yana saƙawa ,"Lallai ba makawa wannan yaron yasan wane ne ni,babu wanda ya
taɓa yi mini kallon tuhuma irin haka sai shi amman ba komai koma miye saidai ya faru amman
sai na rufe sirri na da kuma ganin bayan duk mai son tonawa,in aikin sihiri ya ƙi yiwuwa ai akwai
na zahiri." Ya faɗi hakan yana kai kawo.
Ya kasa zaune ya kasa tsaye yana ta saƙa da warwara.
♡♡♡
Farouq na zaune suna karyawa da Javed ya ce,"Oh Sorry ban faɗa maka ba gabadaya na sha
afa SiftaCore fa sun ba mu date din ranar da zamu hadu dasu tun shekaran jiya suka kara yi
mini Gmail kan cewa on 16th this month ka ga yau 15 gobe 16 kenan ya kamata yau ka tsaya
tafiya Abujan gobe in Allah ya kaimu sai ka je ko."
Javed ya ce,"Ni kuma Oga? Aa kai dai ni ai kasan ban saba lamura da mutane haka ba kuma
ma zai yiwuwa akwai tambayoyin da zasu ma ni ban sani ba."
Farouq ya ce,"Sai dai muje tare ai da hakan zaka koya gwanda ka saba."
Dariya Javed ya yi yana,"E na yarda muje taren dai in ba haka ba ai ni ba abun da zan iya
tsinanawa."
Dariya duka suka yi.
Javed ya ce,"Ka ga ma bara inje in sanar da Mai Martaba tun yanzu kar azo asamu matsala."
Ya karasa maganar yana ajiye spoon kafin ya fice.
Yana zuwa ya sanar da Mai Martaba da mamakinsa Mai Martaba na jin cewa da Farouq za ayi
tafiyan kuma da motar gida tuni ya amsa da furucin sai sun dawo abun yaso ya daurewa Javed
kai saidai kuma farincikin hakan ya mantar da shi ya je ya sanar da Farouq kawai sannan suka
wuce School. Bayan sun dawo da dare suka kammala duk wani shirye-shiryensu na tafiya da duk wani
document na su kafin suka kwanta da wuri kasancewar tafiyar safiya zasuyi.
Da wuri suka tashi suka shirya suka yiwa Hajiya Kaka da su Maah sallama kafin suka dauki
hanya.
Suna cikin tafiya tsakiyan daji ya yi shiru motoci sun dauke sai su kaɗai lokaci guda suka wasu
mutane sun zagayesu ta ko ina dauke da wuƙaƙe da bindiga.
Gabaɗayansu sun razana ban da salati babu abun da suke yi.
Fito da su daga cikin motar suka yi duka,a lokacin Farouq ya yi kokarin fara kai masu hari da
duka.
Ganin da gaske Farouq na son fin karfinsu ya suɓuce masu hakan yasa wani cikinsu ya biga
masa gefen bindiga akai.
Nan take ya fadi a wajen jini na zuba daga gefen kansa.
Shi kuwa Javed daman tun farkon faɗan aka turgudeshi ya sume.
Karasawa suka yi suna daga Farouq babu alamar numfashi a tattare da shi ɗaya a cikin su ya
ce,"wannan fa ya mutu kawai jan shi zamuyi muje mu sa shi cikin rafin cen."
Sun fara jan Farouq din kenan suka jiyo sautin karar motar jami'an tsaro da sauri suka.....
[18/06, 4:40 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-22
Suka fara kokarin tarwatsewa basu san ma lokacin da suka jefar da Farouq din gefe ba suna
gudun ceton rai.
Sanya Farouq da Javed din suka yi a motarsu wani cikinsu kuma ya shiga motar su Farouq din
zai tuka ya kaita Abuja, taimakon gaggawa suka fara basu kafin suka ci gaba da tafiya har suka
isa cikin abujan kai tsaye asibiti suka nufa kafin su isa ma shi kam Javed har ya farfado dake
masu yi masa wani duka lahani mai karfi ba,Farouq aka shiga da shi wajen likita shi ma din
kuma cikin sa a duk da jinin da ke zuba daga kansa ana yi masa treating wajen ba jimawa ya
farka yana salati.
Ganinshi da ya yi a asibiti ya dawo masa da tunanin abun da ya faru.
Zai tashi da sauri Javed ya karasa yana,"Sannu Oga ka farka? Ya kan dai?"
Farouq ya ce,"Alhamdulillah, yanzu karfe nawa?"
Ya fada yana duba agogon hannunsa.
"Subhanallah ai yanzu ya kamata ace muna can wajen sune 3pm ya kamata mu hanzarta mu
tafi."
Javed ya ce,"Haba dai Oga ai lafiya tafi komai da dai ka dakata tukunna sai mu basu report din
matsalar da aka samu in munci sa'a ko zuwa gobe ne sai kara bamu lokaci. "
Farouq ya ce,"Aa ni bana jin komai daidai nake jin kaina muje kawai."
Ya tashi kenan sai ga Ɗaya cikin jami'an tsaron da suka kawosu ya shigo dakin yana.
"Ma Sha Allah Sannu da kokari."
Mika masa hannu Farouq ya yi yana,"Kune da kokari Godiya nake Sir don banyi tunanin kiran
dana muku ma ya tafi ba,mun gode sosai Allah saka da alkairi,yanzu nake so mu wuce gun
kamfanin da muka zo daman."
Jami'in tsaron ya ce,"Alright Allah ya kara kiyayewa a dunga lura sosai." Ya karasa maganar
yana bashi keyn motarsu.
Javed ne ya je ya biya kudin treatment din da akawa Farouq kafin suka bar asibitin.
Karfin hali Farouq yake yi kawai amman gabadaya jikinsa babu karfi.
Suna fita suka duba location din SiftaCore Technologies suka ga kuwa ashe babu wani tazara
sosai tsakani da asibitin za a iya karasawa da kafa ma amman da yake suna da mota sai suka
karasa cikin minti biyar.
Suna isa aka bude masu gate kasancewar an riga an san da zuwansu.
Daidai lokacin da suka yi parking motar adaidai lokacin C.E.O ya fita da kamfanin kuma.
Ciki suka shiga secretary ya hada su da manager sun tattauna sosai sannan an nuna masu
dukkanin computers din da aka tanadar masu dauka kawai zasu yi.
Farouq da Javed sunji matukar dadi da farinciki.
Ganin cewa sunyi yamma kuma basa son tafiyar dare zuwa mokwa saboda hanya hakan yasa
suka bar computers din da nufin washegari zasu koma su karɓa sai su tafi da safe.
Hakan ne ya kasance suka yi sallama tukun suka je suka kama hotel sun kwana da safe misalin
karfe goma suka koma.
Bayan sun gama da manager har Farouq ya shiga mota ya fito yana,"Sir in ba matsala ina so
mu gaisa da C.E.O Please. "
Murmushi ya yi ya ce,"Alright ba matsala bara in masa magana ka zo muje. "
Tare suka je Farouq ya tsaya a kofar office din manager ya shiga ya yi ma ceo magana ya bashi
izinin shigar Farouq kafin ya fito ya ce masa su shiga.
Da fara'a ceo ya karbi Farouq suka gaisa ya masa godiya sosai sannan ya nemi alfarmar da
inda hali yazo masu cikin mokwa taron yaye ɗalibansu.
Shiru ya yi sai can kuma ya amsa da ,"Ba matsala In sha Allah zan duba indai akwai damar
zuwan zamu zo ko ma bani ba manager zai zo."
Farouq ya ce,"Please Sir inda hali dai ku zo duk muna da bukatarku kasancewarku a wajen
yana da matukar muhimmanci a garemu."
Murmushi ya yi ya ce,"Okay Za a duba In sha Allah. "
Suka yi sallama suka rungume juna kafin ya fita.
har cikin ransa ya ji mutumin ya birgesa mussamman da ya kasance babban mutum kuma
masanin kwamfuta sannan uwa uba mai son mutane ga taimako.
Yana shiga mota yake shedawa Javed cewa ya nemi alfarma a wajen ceo domin zuwa wajen
yaye dalibansu,ba karamin dadi da jin hakak Javed ya yi ba ya ji farinciki sosai.
Addua suka yi kafin suka hau hanya.
Dake Farouq sunyi magana da securities an sanya tsaro a hanya ba abun da ya faru har suka
isa cikin mokwa lafiya.
Suna isa kai tsaye School suka wuce,suka ajiye computers din sannan suka wuce
gida,gabadaya sun gaji suna shiga suka yi wanka sukai sallah sannan suka wuce part din
Hajiya Kaka domin Farouq ya ce ya yi kewarta kuma agunta yake so ya ci abinci.
Hajiya Kaka na ganinsu ta taɓe baki,"Ummm ai ni da so nake ma in turoma da takaddar saki
hamsin da bakwai domin na lura baka auren."
Farouq ya karasa inda take yana kwantar da kansa a cinyar ta.
"Haba dai Amaryata ni na isa? Ai ban isa ba,ni da ke kinsan mutu ka raba takalmin kaza."
"Bawani nan mutu ka raba shine har zaka kwana kusan uku ne ma ko fi baka nemi ne ba yoo
wannan ma ai a ƙa'ida ya ci araba auren ko kutu aka je."
Farouq ya ce,"Laifin Javed ne bai sanar da ke cewa bana da lafiya ba,har sai da BabanGanye
ya dubani ya bani magani da sai dai kiji ance miki ki fara takaba kawai."
Hajiya Kaka na jin batun takaba da mutuwa ta marairaice.
"Ayyah ashe baka da lafiya shiyasa na dunga jini ba daidai ba,zuciyata na ta fadi mun Faruqu
faruqu ashe ashe tana nufin baka da lafiya ne,ka san fa ni ko da Mai Martaba yake raye in bai
da lafiya nima ciwon nake farawa,sannu ka ji ko batun takaba kam ai ba yanzu ba,fadamun me
zaka ci? Me kakeso a kawo maka."
Farouq ya shagwaɓe,"wannan tuwon da ake miki mai dadin nan ni nake son ci."
Tuni Kaka ta kira mai aikinta tasa aka kawo masu tuwo shi kam Javed binsu da kallo kawai
yake yana dariya.
Sai da suka gama ci suka sha hira akayi wasa da dariya da suka tafi sallar isha kafin suka wuce
part dinsu.
Farouq na shiga dakinsa ya ga system dinsa na danger alamar an kara attacking dinsa.
Dauka ya yi yana fadin,"Yau kam koma waye ke wannan aikin sai na lalubo ba makawa."
Aiki ya shiga yi gadan gadan ya shiga nan ya fita nan.
Ya kira Zeeyter yana fada mata duk abun da ke faruwa ita ma ta dauko System dinta suna yi
tare.
Dukufa details din mai yin hacking din kudin mutanen da suka fara magana da shi ya bata ta
duba sai ta ga ai yana da alaka da mai bin diddigin sa dake gidan.
Har wajen karfe ɗaya na dare kafin suka fara samo asalin location din.
Fita ya yi da system dinsa yana tafiya yana indicating har ya kai daidai wani daki a gidan wajen
da ma bai taɓa shiga ba.
Daidai window din dakin ya tsaya dake wanda ake iya ja ne ya ja ya ɗaga a hankali,mace ya
hango gaban system ta duƙufa tana dannawa......
[19/06, 5:46 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in