Showing 42001 words to 45000 words out of 62597 words
Chapter 15 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! í ½íºš*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAÆŠINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAÆAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-25
Mai Martaba ya yi gyaran murya yana,"Fatan kowa na cikin lafiya,cikin aminci da kwanciyar
hankali." Ya É—an tsawaita kafin ya ci gaba da magana.
"Na san cewa ba lallai Al'adu,tarbiya da riƙon addininmu ya zama iri ɗaya dana yan ƙasar waje
ba,domin yawancinsu da suke musulman suna amsa sunan kasancewa a addinin musulunci ne
kawai wanda in an bibiya ko ibadar ba iyata suka yi ba bare aje ga sauran lamura don haka zan
yi tunatarwa." Nan ma ya ɗan yi shiru ka fin daga bisa ni ya ci gaba da magana wanda daman a ƙa'idarsa ba
wanda ya isa ya tanka in yana magana har sai ya ƙare ko ya bada izinin yin hakan.
"Addininmu ya haramta kasancewar mace da namiji tare wa inda suke ba muharraman juna
ba,wanda na ji labarin cewa wannan ƙwamacalar ta fara afkuwa a wannan masarautar tsakanin
baƙon da ya zo daga kasar waje da Janinah,kila shi a gunsa hakan ba komai bane domin sun
saba mafiyin hakan wanda sam mu kuma ba zamu dauka ba domin muna da riko da addini da
kuma al'ada dakatar da hakan ya sanya ni yin wannan kiran da gaggawa,duk da cewa Janinah
ta san haramcin hakan ta danne saninta don haka hukunci ba zai taɓa barinta ba har sai
ladabtar da ita tunda tasan cewa akwai baiko akanta wanda ana daf da daura mata aure nan da
wata guda sannan daga yau har ranar É—aurin auren zata kasance a dakin ajiya na tsawon
kwana wata guda ba tare da ta fito ko da farfajiya bane sai dai duk wani bukatunta ta yo su a
ciki shi kuwa baƙo indai yana son ci gaba da kasancewa cikinmu ya zame masa wajabi da ya bi
dokokinmu na addini da al'ada domin mu ba ma rayuwar yahudawa anan."
Kuka Janinah ta fara tana rungumar Mahaifiyarta.
Abba Malik ya ce,"Ayi hakuri Ranka Ya dade amman zan yi magana,Janinah ce 'Ya Mace ta
farko a jikokin masarautar nan,ba laifi don an haneta ga kula wanda ba muharraminta
ba,amman kuma batun auren nan yinsa ake kawai ba tare jin amincewarta ba sannan kuma
kulleta a dakin ajiya ma sam ba mafita bane hakan tamkar danne hakki cikin hakkin ne,ina
rokon alfarmar da abarta ta ci gaba da rayuwa yadda ta saba sannan batun aurenma abari ta
gama samun fahimta da shi Arham din kafin ya kammala karatunsa ka da ya kasance cewa
masarauta na kokarin danne hakkin 'Yara matan da ke cikinta kuma.....
Mai Martaba ne ya katse shi da fadin,"Wannan umarni ne ba shawara ba kuma dole ne abi ba
tare kaucewa ko musawa ba daga yau Janinah zata fara rayuwa a dakin ajiya aure ma kuma
babu fashi, a ko ina mace take cikin wannan masarautar bata da ikon kanta sannan baiwa ce
ga mijin da zata aura domin karshen rayuwata zata kare ne cikin yiwa miji da yaran da zata
haifa hidima."
Kuka Janinah take har tana shashsheƙa.
"In ni na zam Baiwa gareka da yaranka 'Yata ba za ta taɓa irin wannan rayuwa mara galihun
ba,Janinah zata auri Arham ne kawai in har zuciyarta ta amince da ta aure shi,auren so da
ƙauna da kuma daraja juna,sannan batun ɗakin ajiya ma babu inda 'Yata zata domin ba laifin
sata ko na zina aka kamata da yi ba."Mammah ta faÉ—a tana share hawayen da ke kwaranya a
fuskar Janinah.
Gabadaya Falon shirun sa'o'i ya yi na mamaki tare da kasa gasgata cewa shin Mammah ce
take magana ? Kuma cikin kakkauran lafuza haka?,shi kansa Mai Martaban kamewa ya yi
domin a rayuwarshi da ita ko cikin idanunsa bata taɓa iya kallo ta yi masa magana bare kuma
bijirewa umarninsa.
Kilishi ce ta katse shirun nasu da fadin,"Ah lallai Yiniyetsu kin samu sake,yaushe har kika samu
yancin yin magana irin haka gaban Mai Martaba har ma da bijirewa umarninsa?"
Ta tsaya gaban Mammah tana nuna mata hannu.
Bige hannun nata Mammah ta yi tana,"A daidai lokacin da na ga ana kokarin dakilewa yata
rayuwar 'Yanci daraja kima da mutuncinta na 'Ya mace."
Tana gama fadan hakan ta ja hannun Janinah suka fice a falon.
Murmushi Farouq ya yi ya tashi zai fita daidai setin mai martaba ya ce,"masu karya da addini
sune asali da tushen yahudawa."
Yana fadin hakan ya fice.
GabaÉ—aya kowa ya bar falon aka bar daga mai martaba sai kilishi da yake daman ba Hajiya
Kaka a zaman.
Kilishi ta karasa gaban Mai Martaba tana fadin,"Lallai lamura sunyi sanyi na kara gasgata cewa
akwai babban al'amarin da ke kokarin dumfaro mu,wai har Yiniyetsu ce ke iya jayayya da
furuncinka kuma take musayan yawo dani? Matar da ko ni karan kaina bata taɓa tankamun ba
bare kai. "
Shiru mai Martaba ya yi na tsawon lokaci kafin ya ce,"Ada ana yaƙin ne a ɓoye yanzu kuma na
zahiri da zahiri za ayi sannan zan fara ne daga cikin gida,sai ta yi dana sanin fara yin fito na fito
da hukuncina sannan shi ma wancen karamin mara kunyar yana daf da cin kashinsa."
Yana karasa fadin hakan ya shige dakinsa.
Ita ma Kilishi a fusace ta yi bangarenta,kai tsaye dakin Arham ta yi,ya cire kaya yana sa na
barci ke nan.
"Kai kam wani lokacin sai in dauka cewa tamkar bani na haifeka ba,ba don a cikin masarautar
nan aka yi nakuda da haihuwar taka ba tabbas zan iya musawa,shin ke ko kishin mazan nan
baka da shi? ban taba gani ka nuna damuwarka kan lallai sai ka auri Janinah ba, Anya ma kana
son abun da nake so maka kuwa?"
Murmushi Ya yi kafin ya ce,"Mama Ina son Janinah amman soyayyar da nake yi mata ba ita
zata sa inyi kokarin dakileta ko tauye mata hakki ba,a yau in Janinah ta ce bata sona wallahi
Allah zan hakura da ita domin ni ba zan iya rayuwar jahilcin da ake yi a wannan masarautar
ba,ana rayuwa da sunan bin addini da al'adar gargajiya amman kuma tsantsar jahilci ake
nunawa kuma.....
Kafin ya karasa ya ji saukar mari a fuskarsa.
Cikin fushi Kilishi ta ce,"Ka yi mini shiru, na ce ka yi mini shiru kuma daga kai har Janinah ko
kuna so ko kuna ƙi ya zama dole ku mallaki juna. " tana faɗa ta fice daga dakin tana ja mishi
kofa da karfi cikin fushi.
[24/06, 4:40 pm] Xayyeesherthul-humaerathí ¼í½‚: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! í ½í¸Š
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! í ½íºš*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAÆŠINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAÆAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-26
Janinah suna shiga É—aki da Mammah ta zaunar da ita gefen gado tana fadin,"Kar ki sa wata
damuwa aranki,ba zan taɓa bari ki yi rayuwa irin tawa ba muddin ina raye ko da kuwa ace
numfashi zai bar jinin jikina sai na tabbatar da cewa kin samu ingatacciyar rayuwa sannan ana
girmama ra ayi da darajarki na mace a gidan aurenki,don haka ka da tursasa zuciyarki kan lallai
sai ta so Arham in dai bakya son shi to na miki alkawarin cewa ba za ki taɓa aurenshi ba
sannan Dakin ajiya ma ina kara jadadda miki cewa in dai zaki kasance a ciki to sai dai in har
dani nima domin na yarda da cewa ba za ki taɓa aikata mummunan abun da suke son fara binki
da shi ba hatta a cikin littafi mai tsarki an bayyanar da daraja da kimar mace
Suratul Baqarah, Aya ta 187
Ubangiji yana fadin
"...Su mata sutura ce a gare ku, ku ma sutura ne a garesu.
Wanda hakan na nufi
Sutura a nan na nufin tufafi ko riga, wanda ke nuni da cewa:
Miji da mata suna kusa da juna kamar yadda tufafi ke kusa da jiki.
Suna kare juna daga sharri da cuta, kamar yadda tufafi ke kare mutum.
Suna lullube juna, suna ɓoye aibu da raunin juna.
Suna zama ƙawata da cika juna, kamar yadda tufafi ke ƙawata mutum.
Wannan ayar na nuna irin girmamawa, soyayya, kariya da haÉ—in kai da ya kamata ya kasance
tsakanin ma’aurata. Musulunci ya ɗaga darajar aure da zaman gida, yana mai jaddada hakkoki
da nauyin juna a tsakanin miji da mata.
Musulunci ba ya nufin mace ta zam Baiwa ga mijinta haka kuma musulunci baya nufin a dunga
tauye hakkin mace.
Da na yi aure ido a kulle amman yanzu tunda na fahimci darajar mace a musulunci ba zan taɓa
bari kiyi rayuwa irin tawa ba lokaci ya kure gareni amman ke ba zai kure miki ba domin ko da
ace kowa zai juya miki baya ni ina tare da ke,ki san kanki kuma ki so kanki kafin kowa hatta
kasuwanci bai haramta ga 'Ya mace ba muddin za ta kiyaye dokokin da mutuncinta,ki sa aranki
cewa zaki rayu irin rayuwar da kike so ne kawai Janinah ba wacce ake so kiyi ba."
Mammah ta karasa maganar tana rungumar Janinah.
Farouq da Javed kuwa tunda suka koma bangarensu harkar shirye-shiryen taronsu suka fara
ba tare da sun ko daga maganar abun da ya faru a falon Mai Martaba ba domin kuwa
washegari ne zai kasance ranar.
Hakan yasa gari na waye ma da sassafe suka bar gidan domin ganin komai ya gudana cikin
tsari.
An fara taro,sun gayyaci manya sosai har sun cire tsammanin zuwa Ceo din SiftaCore
Technologies kamar daga sama kuwa sai ga shi,shi da manager.
Javed ne ya je ya taresa da sauri ya ba shi wajen zama kasancewar Farouq na tare da mutane.
Ya yin da za abawa Dalibar da tafi kowa hazaƙa award Wacce ta kasance Ameemah ce Ceo
aka kira domin ya damka mata.
Bayan ya bata aka bashi damar yin jawabin shawarwari da kwarin gwiwa ga daliban da aka
yaye.
Da fara'arsa ya tsaya gabansu yana fadin,"Assalamu Alaikum warahmatullah,
Ina taya ku murna da kammala wannan muhimmin mataki na rayuwa akan na kammala samun
horo a bangaren na'ura. Wannan ba ƙaramin nasara ba ce, kuma hakan yana nuna irin
jajircewa da ƙwazonku wajen neman ilimi da ci gaban duniya ne gabadaya.
Na ji matukar dadi da farincikin kasancewar wannan makaranta domin 'Ya'Ya mata hakan ba
karamin tallafawa zai yi wajen samun yin amfani da baiwar da kowacce a cikinku take da shi.
Ga wasu yan shawarwari gareku:
Kada kuce za ku tsaya anan – Ilimin kwamfuta yana iya canzawa kowace rana. Ku ci gaba da
koyo, ku nemi takardun ƙwarewa (certifications) kamar CompTIA, Cisco (CCNA), Microsoft,
Google, ko Adobe bisa ga fannin da kuka fi sha’awa,atakaice dai ina kara baku shawarar cewa
ku kasance a kullum kuna bibiye da yanar gizo domin daukan darusa wannan tushe ne aka
muku wanda kuma ina da yakin cewa tushe ne mai kyau da zaku iya amfani da shi wajen
inganta rayuwarku da ma sauran al'ummar dake kewaye da ku.
Ku Yi amfani da abinda kuka koya Kada ku bar ilimin ku ya tsaya a takarda. Ku fara yin
practice sosai: Ku taimaka mutane ko kungiyoyi da basu da masaniya sosai akan kwamfuta.
Haka zai ƙara ƙwarewar ku kuma ya buda muku ƙofofi.
Ku kasance masu kyawawan dabi'u domin kuwa Fasaha ba zata taimaka ba sai da ɗabi’a mai
kyau: gaskiya, amana, da himma Jajircewa. Wadannan suna kara darajar ku fiye da takardar
shaida.
Sannan Ku nemi abokan hulÉ—a masu amfani (networking) Ku hada kai da sauran masu ilimi a
fannin, ku shiga ƙungiyoyi ko online communities domin samun sabbin dabaru da damar aiki.
Ku yi aiki da niyyar taimakawa Duk inda kuka samu dama, ku nuna ƙwarewarku ta hanyar
taimakon jama’a, makarantu, ko ƙananan kasuwanni. Wannan na iya zama matakin farko zuwa
ga kasuwanci ko guraben aiki.
A ƙarshe, ku kasance masu tawali’u da godiya. Ilimin da kuka samu wata kyauta ce daga Allah,
don haka ku yi amfani da shi ta hanyar da zata kawo cigaba a rayuwar ku da al’umma baki
É—aya.
Ina rokon Allah Ya kara muku ilimi da basira, Ya buda muku ƙofofin nasara a fannoni
daban-daban na rayuwa.
Allah ya albarkace ku da mu gabadaya.
Na gode."
Tafa masa suka shiga yi daga nan aka ci abinci an rabawa system dinta taro ya tashi cikin
aminci.
Ceo zai tafi Farouq da Javed suka je masa sallama.
Yana miƙawa Farouq hannu su gaisa kai hannun da Farouq zai yi idanunsa suka sauka akan
zoɓen da ke hannunsa,da sauri ya riƙe hannun yana taɓa zoben ya ce,"Zoben nan? Zoben
Maah."
Cike da yanayin mamaki daga Ceo har javed suke kallon Farouq ya fara wani abu tamkar
zautacce.
Dubawan da zaiyi kuwa suna ya ga an rubuta Mariam&A.
Dafe kai Farouq ya yi ganin cewa yana kokarin fita a hayyacinsa.
Ya ce,"Father....sai kuma ya yi shiru."
Ceo ya ce,"Father?" Cike da mamaki.
Durkusawa kasa Farouq ya yi ya daga hannunsa sama yana
fadin,"Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah. "
Ya dago ya kallishi kafin ya ce,"Mu koma daga ciki please."
Ceo ya ce,"Ciki? Me ya faru?"
Farouq ya ce," Please abu na ke so in nuna ma."
Shiga ciki suka yi duka suna mamakin sambatun da Farouq yake da kuma yanayinsa da ya
canja daga ganin zobe kawai.
Hoton daidai zoben hannun Mammah ya ciro yana nuna masa wanda aka rubuta
Abdul-Rasheed&M,Sake baki ceo ya yi ya kasa magana can ya ce,"Mariam?."
Ya fada yana kallon Farouq.
Farouq ya girgiza kai ,"Yeah ni din yaronta ne."
Ceo ya ce,"So you are my son? Where's Mariam? Ina fatan tana raye."
Ya fada suna rugume juna.
Javed da Manager sai kallon kallo.
Farouq ya ce," Maah na lafiya kullum tana nan dauke da wannan zoben irin naka wanda shi ne
ya tabbatar mun da cewa kaine mahaifina domin kuwa ta ce mun da kanku kuka je kukasa aka
yi muku ku biyu sannan naka an rubuta Mariam&A nata Abdul-Rasheed&M tana matukar
kaunar zoben duk da cewa ka gujeta a lokacin da tafi bukatarka."
Numfashi Ceo ya ja kafin ya ce,"Ta ya zan guje bayan ni kaina ban san a wacce duniyar nake
ba lokacin da muka rabu? Sannan daga baya na je har cen Netherlands din nemanku Iyayenta
sun tabbatar mun da cewa su kansu basu san inda take wanda a lokacin na je daukanta ne mu
tafi china tare,ba yadda na iya haka na tafi domin a lokacin zuciyata bata son ko da zance ne na
nigeria bare tunanin dawowa a karshe bayan na samu abubuwan da nake bukata na fara jin
sha'awar dawowa gida nigeria wanda hakan bai samu ba sai da na dage da adduoi kafin na
samu ikon zuwa cikin garin nan kuwa kawai alkawarin da na yi ma ne ya sa ni dauriyar zuwa
dole amman jina nake kamar akan ƙaya ban da burin da zarce ace in ga na fita ,Yanzu ina
mariam? A ina kake da zama? Kar dai ta dawo da ku nan? Kenan gidanmu sun karbeku?"
Ya jero masa wa innan tambayoyin.
Farouq ya ce,"Maah na Malaysia bayan ta koma Netherlands Iyayenta sunki karbanta karshe
shine ta dawo malaysia har ta haifeni,bata san duk abun da ke faruwa da kai ba hasalima na
dawo kasar nan ne domin nemanka wanda a yanzu ina zama ne a gidanku amman babu
wanda ya san ni wane ne."
Javed ya ce,"Oga ni fa ban gane wannan jawaban naku ba please ku fahimtar dani kaina ya
fara daurewa na shiga ruÉ—ani."
Farouq ya kalleshi ya ce,"Wannan mahaifina ne kuma shi din Yayane ga mahaifinka Mai
Martaba ya bar gida tun yana da karancin shekaru,ba za ka gane komai a yanzu ba sai mun
koma cen gida."
Javed na kallon Ceo sai a lokacin ya ga tsantsar kama tsakaninsa da Mai Martaba