Showing 54001 words to 57000 words out of 62597 words

Chapter 19 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

1636

sannan ya ja dogon tsaki ya tafi.
Yana zuwa wayarsa ya dauka yana ,"Kana ji ko sun fita daga gidan nan zasu kai Janinah Asibiti
ko da ace yanzu baka samesu ba a hanyarsu ta dawowa ka tabbatar na ji labarin cewa
dukanninsu numfashi ya bar gangar jikinsu,kar ka ragawa kowa hatta Yiniyetsu da Janinar kai
koma da waye ka gansu ba ka da matsala kawai ka sanya aga bayansu."
Daga cikin wayar aka amsa shi da fadin,"Kar ka damu Ranka Yadade an gama wannan karan
dai kam In sha Allah ba za asamu wata matsala ba,za ka jiyo sakamako mai kyau kawai ka
zauna cike da jin cewa komai ya kammala."

Katse wayar ya yi kawai ba tare da ya ce komai ba,ya jefata kan kujera,sannan ya zauna.


☆☆General Hospital Mokwa suka kaita,suna zuwa kuwa aka karbeta aka fara yi mata
taimakon gaggawa.
Likitoci na kanta na tsawon awa biyu wannan ya shiga wancen ya fita,har suka samu nasarar
ceto rayuwarta.
Likita ya sanar da Yarima Rasheed cewa Janinah na bukatar hutu sosai sannan ta sanya
damuwa aranta wacce take barazana da ranta haka kuma akwai yanayin takura a tattare da ita
don haka tana bukatar hutu da kulawa sosai.
Bayan ya gama yi masa bayani an rubuta masu magunguna sannan aka sallamesu duk da
cewa shi likitan ma bai so sallamarsu aranar ba acewarsa ya so ace ta kwana ko da uku ne ta
dan huta tukunna,Yarima Rasheed ya sheda masa cewa ba matsala a gidanma zata samu fiye
da yadda suke zato.
Ana fito da Janinah ta kalli Mammah tana fadin,"Mammah ina Yah Farouq? Shi ma an fito da
shi? Yana ina? Ku kaini in ganshi wallahi bai yi ma Mai Martaba komai ba,bai aikata laifin komai
ba."

Yarima Rasheed ne ya katseta da fadin,"Yayanki na lafiya Janinah yana gida,ki kwantar da
hankalinki kuma ki nutsu mu tafi gida."
Hakan yasa ta yi shiru ba don ta gamsu ba kawai ta dunga binsu da kallo tana sake-sake a
zuciyarta.

Suna cikin tafiya suka ji mota ta fara masu misbehave tana kokarin jefa su cikin rafi,duk kokarin
Abba Malik ya yi don ganin sun kauce abu yacitura,ga wasu motoci daya a gabansu ɗaya a
baya duk sun ƙi basu space sannan kuma inda suke waje ne da ba cika wucewa sosai ba ya yi
bayan gari.
Sun fara galabaita dukkaninsu,tun suna iya addua har sunyi shiru sun fidda tsammani domin
motar har ta haye gadar tana kokarin fadawa cikin rafin.

Kamar daga sama suka ga motar ta kame ƙam jikin wani dutse bayan duk sun gama sadakarwa
sun mutu.
A hankali suka fara bude idanunsu.
Juyawan da Abba Malik zaiyi ya ga tarin jami'an tsaro tare da Xavier kamar an zubosu.
Wa innan masu motoci biyun kuwa fara neman hanyar tserewa suka yi,suna yi suna taresu da
kyar suka samu suka gudu.

Bayan sun tafi aka kira babbar mota ta janyo tasu Yarima Rasheed suka fito duk sun gama
galabaita mussamman Janinah da daman ba lafiya gareta.

Xavier ya ce,"Fatan dai dukkaninku babu wanda ya ji rauni?"

Abba Malik ya ce,"E kam Alhamdulillahi. "

Ya ci gaba da fadin,"Sun gudu amman In sha Allah za a kamasu domin turosu akai."

Yarima Rasheed ya ce,"Lallai kam sannunku da kokari muna godiya Allah saka da alkairi ."

Murmushi Xavier ya yi ya ce,"Ai Ɗa baya bukatar godiya daga wajen Mahaifi. "
Shi ma murmushin ya yi kafin ya ce,"Wannan haka yake,To Ubangiji ya yi muku albarka duka. "
Da Amin ya amsa aka basu wata motar da jami'ai biyu suka nufi gida domin tasu ba zata yi aiki
ba.

Mai Martaba nata zirga-zirgan jiran sakamako,sautin gate da aka bude ne ya bashi damar bude
labule yana leƙe ta window.
"Su ne suka dawo." Abun da ya furta kenan cikin yanayi na rashin kwarin gwiwa.
Haka kuwa ya ga duk sun fito,Mammah rike ta tallafe Janinah wata irin kwafar takaici ya yi yana
dafe kansa.
Waya ya dauko cikin sauri ya kara a kunne yana fadin,"Wannan wani irin iskanci ne? Sau biyu
ina saka aiki kwanan nan amman shiru baka iya yin komai? Wannan ai shashanci ne."

Da ga wayar aka amsa da fadin,"Haba Yallaɓai kai dai kasan shekara da shekaru muna tare ba
a samun matsala sai wannan karan kuma ba wai gagara mukai ba kawai dai na lura kamar
yadda muke shiri akansu haka suke shiri akanmu domin yau da kyar muka samu tsiratar da
rayuwarmu da saidai kaji asirinmu duk ya tonu amman dai ka yi hakuri da ikon Allah idannunmu
na kansu duk har sai mun aiwatar da muradinka."

"Duk yadda za ayi nidai kawai ka aiwatar kuma wanda zaku fi sa idanu akai Rasheed ne kawar
da numfashi a jikinsa shi ne samun zaman lafiya na da ku dinma gabadaya. " Maimartaba ya
fada yana katse wayar.
[12/07, 9:40 am] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAGE-33

A bangaren Hajiya Kaka aka aje Janinah tukun su Rasheed suka fita,Mammah na fita kawo
mata abinci Janinah ta kalli Hajiya Kaka ta ce,"Hajiya Kaka an fito da Yah Farouq? Yana
lafiya?"
Taɓe baki Hajiya Kaka ta yi cikin yanayin damuwa ta ce,"Aa kuma ma bamu san halin da yake
ciki ba."
Shiru Janinah ta yi,take hawaye suka fara ambaliya a fuskarta,zuciyarta ban da zafi babu abun
da take yi mata,duk da cewa Mai Martaba mahaifinta ne ba yadda za ta yi da shi amman har
cikin ranta ji take babu wanda ta tsana a duniya yanzu sama da shi.

Cikin dare kamar daga sama suka fara jiyo dirowar mutane cikin gidan,fuskokinsu a
rufe,bangaren ka aka fara sanyawa makulli aka rufe sannan bangaren su Junaid ta yadda ba za
su taɓa iya fitowa ba.
Wasu irin manyan maza ne masu kirar samudawa,wajen Yarima Rasheed suka fara nufa suka
daukoshi tamkar daukan amarya suka direshi gaban Mai Martaba sannan suka kulleshi tamkar
dabba,Murmushin mugunta Mai Martaba yake yana binsa da kallo sannan suka je suka dauko
Mammah da Abba Malik ma duk suka dauresu.
Kallon Mammah mai martaba ya fara yi yana faɗin,"Karshen alewa ƙasa,ina yanzu ke kina
ganin cewa kinfi karfin bin umarni na? Kin fi karfin inyi magana kiyi shiru? Ina faɗa kina faɗa?
Idanunki cikin idanuna? To ki sani ni bana tuna alkairan mutum ko ya yamun kuskure rufe idanu
nake take in dau mataki."
Mammah ta ce,"Sai dai hakan ya zam silar katsewar numfashina amman ina kara fada kuma
zan fada a ko ina ba zan taɓa bari 'Yata tai rayuwa irin wacce na yi ba,ba zata zam baiwa ba
kuma ba zata zama tamkar tsummar goge takalmi ga mijinta ba,sannan ba za ayi mata auren
dole ba har sai da amince.... Kafin ta karasa maganar ya buga mata wani katon karfe aka har sai dai ganinta ya dauke ta
fara ganin dishi-dishi da wani duhu-duhu azaba na ratsata, har cikin kwakwalwarta sai da ya
amsa.
Mai Martaba ya ce,"Ni Sarkine ba iya na al'adu ba,sannan duk wanda zai rayu a cikin wannan
gidan zai rayu ne cikin karkashin ikona don haka duk wanda ya ce zai bijire mun zan iya hallaka
rayuwarshi zuwa lahira da ga ke har 'Yarta ki da wa inda kuke goyawa baya duk sai kunyi dana
sanin bijire mun."

Cikin Muryar Kuka Mammah ta ce,"Baka isa ka yi muna abun da Ubangiji bai mana ba,kuma ina
ji a jikina cewa ƙarshen zalincinka ya zo."
Cikin fushi ya buga mata kafarshi a bakinta sai da ya fashe jini ya fara zuba ya ce,"Ki yi mun
shiru nan domin rayuwarki bata da amfani a yanzu."
Komawa ya yi gaban Yarima Rasheed yana dariyar mugunta,"Rasheed ke nan,ka manta ni
wane ne ko? Ka manta cewa tun lokacin yarinta bana raga maka bare yanzu? Ko kana tunanin
dukiyarka ce zata iya sawa kafi karfina a yanzu? Ka yi makahon tunani,ka dawo ka karfi sarauta
ko? To haramiyarka domin ba zaka taɓa samu ba shi kuwa wancen Ɗan naka Shege tunda na
fahimci ba zai iya gadon sarauta ba,tunda a garin yawon tambaɗa da tazubar aka sameshi na
fita a sabgarsa ba don yana son shiga mini hanci ba da tuni na barshi domin ko a hakan ma
kadai rayuwarshi watsatsiyace shiyasa kawai na turashi wancen dakin har ya gaji ya mutu in ya
yi mushe sai ma jefar cikin rafi."

Cikin Karfin hali Yarima Rasheed ya ce,"Duk da kasancewar mun sameshi ta hanyar da bata
dace ba amman yafi yara dubu da aka haifa ta hanyar da ta ce inganci ɗaya daga ciki kuwa
harda kai." Ya karasa maganar yana nuna Mai Martaba.

Cikin Fushi Mai Martaba ya tashi tsaye yana zagaye Yarima Rasheed can kawai yana daga
wani katon karfe ya sake mishi a baya sai da jini ya fara fitowa ta cikin bakinshi idanunsa suka
rufe.

Dariya Mai Martaba ya ci gaba da yi kafin ya ce,"Ni kuwa da kake gani ai nafi yara miliyan ma
ba ɗari ba,domin ni kadai gayya."

Cike da azaba Yarima Rasheed ya ke fadin,"Ina Mai Tabbatar maka da cewa Ɗana ba zai barka
ba ko da ace ni ka kasheni to ka san da cewa tamkar ka ƙarawa kanka nauyi ne ba wai sauki
ba,Farouq ne maganinka kuma zaiyi maganinka ba makawa."

Mai Martaba ya tallafo fuskar Yarima Rasheed ya ce,"Wai kai ko kunya ma baka ji? da ɗan
shegen kake alfahari da taƙamar zai iya yi mun wani abu? To bari ka ga yanzu zansa a ciro mun
shi duk in gama daku anan kafin zuwa safiya labarinku ya kau a duniyar nan."

Abba Malik ne ya yi magana,"Haba Don Allah, wai kai wani irin azzalumin mutum ne mara imani
mara tausayi da jin kai."
Wani zazzafan mari ya kai masa wanda sai da hannayensa sukai shata a fuskar kafin ya ce,"Ni
Mutum ne mai son sarauta wanda zai iya komai akan mulki domin har ubana na kashe domin
inyi sarauta don haka inna kasheku ba komai bane."
Ya karasa maganar yana umartar daya daga cikin yaran nasa da su dauko mishi Farouq.
Hakan kuwa ya kasance zuwa suka yi suka fito da Farouq daga dakin duhu suna shiga da shi
hasken dakin ya kanne masa ido tuni ya rufe ba tare da ya fahimci suwaye ba kuma meke
faruwa ba.
Durkusar da shi suka yi shima suka ɗaure.

Mai Martaba ya riƙo gashin kan Farouq yana faɗin,"Kai Ɗan shege ga shegen mahaifin naka
nan kuma shi ne ya janyo maka mutuwa cikin azaba domin ada na so ace ka yi mutuwar sauƙi
ne cikin wancen dakin."

Janye kansa ya yi ya fisge idanunsa a rufe ya ce,"Kar ka kara kuskuren kira Mahaifina da
Shege domin shi ba shege bane kuma bai haifi shege ba, in ma akwai shege to babu wanda ya
fika."

Mai Martaba ya janyo kan Farouq yana sheƙe masa wuya,"Ayyah ashe dukan ku haka kuke da
taurin kan ko? Ah lallai Maddalla,ba za kuyi mutuwa cikin sauki ba har sai nasa dukkanin ku an
gama jigata mun ku."

Ya faɗa yana komawa kan kujera ya zauna,umarni ya bawa masu kirar samudawan da su fara
jibgarsu har sai jikin kowa ya yi la'asar.
Hakan kuwa aka yi,ita kam Mammah da ta ji bugu tuni ta sume a wajen suka bar ta kanta.
Jibgar Farouq,Yarima Rasheed da Abba Malik suka dunga yi har sai da suka jijji masu raunuka
duka,sun gama fita a hayyacinsu domin ko magana basa iyawa sai jini da keta ambaliya daga
gaɓobinsu.
Bindiga yasa aka miƙa masa yana faɗin,"Da hannuna zanyi wannan aikin domin samun
nutsuwar zuciya da ruhina."
Daga bindigar ya yi ya seta daidai setin Yarima Rasheed yana ja........
[12/07, 3:26 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace

- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA

INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH

AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.

DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP

PAGE-34

Suka jiyo wata karar harbin bindigar daga waje.
Yarima Rasheed da su Farouq sun gama sadakarwa Mai Martaba ya harba ashe ba shi bane.
A zabure ya tashi yana,"Su waye? Ba na hana shigowa gidan nan ba tare da amincewata?
Cikin wannan daren ma?" Ganin Xavier suka yi da tawagar shi ta jami'an tsaro da su Khalil har
da Maah.

Tuni masu kirar samudawa suka fara neman hanyar guduwa,cikin kankanin lokaci aka nemesu
aka rasa,dibi-dibi Mai Martaba ya fara yana,"Ku kuu kuu su waye wa innan? Yana nuna su da
yatsa yana baya da bindigar da ke hannunsa.

Fara kunce daurin goron da aka yiwa su Farouq suka.

Ƙara Mai Martaba ya yi ya kira dakaranshi suka tsaya a bayansa sai a lokacin tsafin barcin da
ya dasawa sauran yan gidan ya fita,a tare duka suka farka cikin razana kowa yana kokarin bude
kofa amman sun kasa.
Hakan yasa Xavier yasa jami'an suka bibbige kofofin kowa ya fito,gabadaya a falon Mai
Martaba suka haɗu kowa na kallon kallo,ga mutane da basu taɓa gani ba kuma gasu Mammah
cikin wali hali.
Da sauri Janinah ta rungumi Mammah tana fadin,"Me ya sameki? Mai Martaba ne ko? Na san
shi ne shi ne." Ta karasa maganar tana rungumeta tana kuka.

Hajiya Kaka na zuwa ita ma wajen Yarima Rasheed ta yi ta rugumesa ta kasa fadin komai sai
kuka.

Zoe kuwa gun Farouq ta wuce tana cire dankwalinta ta daure masa gwiwar hannunsa da jini ke
kwarara,har a lokacin baya gani sosai.

Cikin karfin Hali Mai Martaba ya ce,"Ko ma ku su waye,zuwanku ba zai haifar da komai ba ko
ince ba zai taɓa hanani cika muradina ba,babu shakka sai na kashesu dukanninsu kuma babu
abun da aka isa ayi mini."

Maah ce ta kallesa cikin karfin hali bayan ta shafa kan Farouq ta ce,"Ina mamakin da kake iya
tutiyar cewa kai musulmi ne amman kuma kake rayuwar da wasu Christian din ma basa
yi,dukkanin wani musulmi an san shi da tausayi,adalci da kuma gaskiya amman kai ko guda
ɗaya ban ga hakan a tattare da kai ba."
Dariya ya yi yana karewa Mammah kallo.
"Oh har da su jaɓa a cin ɗanko? Ai sai ki ce mun ga ki nan kinzo Arniya,kafira kodayake shiyasa
daga shigowarki na ji kamshin gidan ya sauya ya kamata ace ko da hakan in fahimci cewa
akwai kafira a tare da mu."

Murmushi Maah ta yi kafin ta ce,"Ko ada da nake ba cikin addinin musulunci ba ni ba kafira ba
ce kuma ba arniya ba ce domin wa inda ake dangatawa da wa innan sunayen sune marasa
addini ni ko ina da shi,bare ma yanzu da nake cikakkiyar musulma, kai fa akanka ne ma nake
tantamar cewa kafi kama da kafiran domin rayuwarka sak tasu ce,kana shiga cikin rigar addini
kana yin baɗala da sunan kai musulmi kuma jagora,musulmi na kwarai baya shirka kuma baya
danne hakkin kowa,ka tozartani a lokacin da na fi bukatar tarairaya cikin addinin Allah ka
wulaƙantani duk da cewa ni tubabbiyace baka duba hakan ba illa danganta tuba da tuban
muzuru,ka nuna mini cewa duk wa inda ba a haifesu a musulunci ba ko da sun tuba ba za su
taɓa zamtowa ɗaya da wa inda aka haifa ciki ba,bayan kuma Ubangiji bai ce hakan ba hasalima
ya yiwa wa inda suka tuba rangwamen da wa inda aka haifa ciki basu samu ba,irinka ne masu
hana al'umma rayuwa cikin addinin Allah."
Ɗaya daga cikin dakaran ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login