Showing 39001 words to 42000 words out of 62597 words
Chapter 14 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! í ½íºš*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAÆŠINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAÆAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-23
Dagowar da zata yi suka suka haÉ—o da shi.
Suman tsaye ya yi yana mamaki.
Janinah ce,hannu yasa yana ƙara murza idanunsa.
Da gaske dai Janinah ce ba wata ba.
Jikinta ya bata ce ya gano ta hakan yasa ta zura masa ido kawai ba tare da ta ce komai ba.
Ya ce,"Zan iya shigowa please?"
Girgiza masa kai ta yi alamar aa kafin ta ce,"Aa ka shigo ka dakeni."
"Ba zan miki komai ba,na yi alkawari, please magana kawai za muyi." Farouq ya fada.
Kara girgiza kai ta yi ita dai bata yarda da shi ba.
Farouq ya ce,"Na rantse da Allah ba zan yi miki komai ba Janinah,da ace wani naniji na gani na
yi mini wannan aikin tabbas sai inda karfina ya kare amman ke kam mamaki abun ma ya
bani,ba zan miki komai ba magana za mu yi."
Ganin yadda yake magana yasata bude masa kofa ya zaga ya shiga.
Jikinta a sanyaye duk wannan tsiwar ta ta tayi sanyi kanta a ƙasa ta tsaya.
Karasawa gun system dinta ya yi kai tsaye.
Ita din ce kuwa ga dukka detail's din har ma É—ayan wanda yake chat da shi matsayin namijin
nan.
Zama ya yi yana kallonta kafin ya ce,"Me yasa kike bibiyata?"
Kanta na kasa ta ce, " saboda kawai in bata ma dukkanin ayyukan da kake yi."
Farouq ya ce,"Me yasa kikeson bata mun ayyukan nawa?"
"Saboda ina jin haushinka,ka maraini ba wanda ya taɓa marina sai kai." Ta faɗa.
Farouq ya yi ajiyar zuciya.
"Yanzu daman duk kutsen da kikeso kimun ba ma damuwarki kwashe bayanaina bane,kawai
damuwarki ki tarwatsa mun abubuwana kiji dadi kawai saboda na mareki?"
Ta girgiza kai.
Farouq ya ce,"Javed ya ce mun kinyi training din computer na yan watanni ban yi tunanin kina
da kwarewa haka ba."
Shiru ta yi masa.
Farouq ya kara fadin,"ki sake jiki ki mun magana ba zan miki komai ba."
Janinah ta ce,"Bayan na gama na ci gaba da karatu online ne ba tare da sanin kowa ba ina yi
ina bincike mussamman a bangaren Cybersecurity."
Farouq ya dauko System din nata ya zauna kusa da ita yana,"Shin a gidannan an san cewa
kina charity? Kina diban kudin gwamnati kina yiwa al'umma hidima?"
Ta ce,"Aa babu wanda ya sani."
"To me yasa?"
Ta ce,"Saboda in an sani Mai Martaba zai iya hanani kuma bana bukatar asan ni wace ce,domin
a zahiri kallon yarinya mara tarbiya ake yi mun hakan kuma baya damuna domin daga ni sai
ubangiji ne suka san abun da ke raina da abun da nake aikatawa sai kuma kai da kasani
yanzu,hatta wa inda nake aiki da su basu taba ganina ko conference meeting za ayi da
rufaffiyar fuska nake zuwa masu kuma a matsayin namiji hakan kuma na yi ne domun rufe duk
wata hanyar da zata nuna ni wace ce."
Da mamaki Farouq yake kallonta ,"Me yasa kika zabi wannan hanyar to domin taimakon
al'umma?"
Janinah ta ce,"Saboda Al'ada ta rufe dukkanin wata kofar nasarar ga duk wata ya mace da ke
rayuwa cikin wannan masarautar,na san cewa ba zan iya aikata komai da zahiri na ba hakan
yasa na yi amfani da badini na domin aiwatar da muradaina cikin sauki,duk da cewa ba za su
iya rayuwa a fili kamar yadda sauran mata ke samun wannan yancin ba ina jin dadin rayuwarsu
a ɓoyen domin sun zam bango abin jinginar al'umma da dama wanda har ya kai ga a halin
yanzu ina da gidan marayun da ni na gina kuma nake kula da dukkanin rayuwarsu kai ne na
farko da ka sani kuma kai ma din don ban da yadda zanyi ne ka riga ka gano komai in da zaka
bar mun dukkanin buruka su ci gaba da rayuwa a ɓoye da na ji dadi kuma na gode maka domin
ana sani a masarautar nan kashina ya bushe kuma kofofin nasarata sun kulle kenan a kowacce
hanya."
Farouq ya ce,"Ni in ban baki goyon baya ai bana nuƙusar da ke ba,kuma In sha Allah na miki
alkawarin cewa zaki ci gaba da karatu ko a kasar nan ko ba a kasar nan sannan zaki fito a
jarumar macenki ba tare da tsoro ko shakka ba,zaki zam yar al'ada da gargajiya mai capacity. "
Dariya Janinah ta fara tana,"Wayaga yar gargajiya mai capacity."
Farouq ya ce,"Eheen to yanzu me zan yi ki daina jin haushin nawa adaina bi mini diddigin
system?"
Dariya ta kara yi tana,"An daina ai yanzu tunda asiri ya tonu."
Ya kalli agogon hannunsa yana,"Dare yyi past 3 bara in tafi kije ki kwanta zamu karasa magana
gobe."
Janinah ta ce,"Ok Gudnight amman sai na yi sallah zan kwanta."
Farouq ya ce,"Hakan ya yi kyau nighty night. "
Ya fada yana fita a dakin ya kulle mata kofa.
Komawa dakinsa ya yi ya bawa Zeeyter labarin Janinah da komai ta yi mamaki matuka,suka
tattauna kafin suka yi sallama,shi ma sallah ya yi tukun ya kwanta.
♡♡♡Yana tashi zaiyi sallar asuba ya yi gamo da laya a tsakiyan gadonsa.
Ganin bai san mene ne ba ya ajiye suna dawowa daga Sallah yake nunawa Javed.
Karba ya yi ,"Ikon Allah wannan ai Layar sihiri ce,a ina ka gani?"
Farouq ya ce,"Kan Gadona ina tashi na gani,Layar Sihiri kamar ya?"
Javed ya numfasa,"E abun ne da ake amfani da shi domin sihiri ko tsafi atakaice dai domin
cutar da mutum."
Farouq ya karɓa yana dubawa gabadaya zagaye take da wasu irin rubutu da baza su iya
karantuwa ba,murmushi ya yi ya tafi duniyar tunani.
Maganar Javed ce ta katse shi yana fadin,"Ni yanzu babbar damuwata kar ya kasance wannan
layyar domin ka aka turota kuma ma in ya kasance ai ba wanda ka sani ko ya sanka da har zai
nemi hanyar cutar da kai,abun nan akwai sarƙakiya inaga ya kamata mu kaiwa Mai Martaba a
sanar da shi tun wuri adakatar da koma waye." Ya karasa maganar yana kokarin karba agun Farouq.
Kautar da hannu Farouq ya yi yana,"Aa kar ka fadawa kowa please,babu wata matsala kuma
zata komawa duk wanda ya turota da kanta."
Javed ya ce,"Anya? Kar a samu matsala fa."
"Aa na ce ma karka damu ni dai kamun alfarma karka bari kowa ya ji." Yana faÉ—an hakan ya
shige É—aki.
Zuwa ya yi ya adana tukun ya ci gaba da sabgoginsa.
Sun je DigitalCraft sun gama lamuransu sannan suka koma gida,suna komawa Farouq zama ya
yi ya suka fara chatting da Janinah tana bashi hakuri kan abubuwan da ya faru tsakanin ita da
shi.
Sun sha hira sosai kafin ya mata sallama kan zaiyi aiki.
Karfe Takwas da rabi ranar ya yi sallama da Javed ya shige daki acewarsa yana so ya kwanta
da wuri domin zai tashi ya yi aiki.
Hakan ya kuwa kasance yana zuwa ya yi addu'a ya kwanta.
Sai karfe Biyu daidai ya farka yana tashi ya yi fara salatul tasbihi bayan ya idar ya roƙi Ubangiji
da ya maidawa dukkanin mai binsa da sharri kansa,ya yi adduoi sosai ya yi karatu har sai da
aka kira sallar asuba yana zaune kan sallaya.
♡♡♡Barci Mai Martaba ya ke yi cikin nishaɗi da kwanciyar hankali,tamkar a mafarki yaji saukar
abu a goshinsa,zabura ya yi ya farka a firgice......
*SAI ANA MUN AFWA DA RASHIN TSAYIN PAGES AN KOMA SCHOOL YANZU LAMURAN
SAI A HANKALI,ZAMU RARRAFA HAR A KAMMALA IN SHA ALLAH*
[21/06, 1:38 pm] Xayyeesherthul-humaerathí ¼í½‚: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! í ½í¸Š
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! í ½íºš*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAÆŠINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAÆAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-24
Yana kallon gabansa ya ci arba da wannan layar sahirin da ya turawa da Farouq,hakan yasa shi
ƙara firgita yana ja da baya.
"Me wannan yaron yake nufi dani ne? Ya dawo mun da abuna? Ya dawo mun da shi? Wato
ƙaiƙayi koma kan masheƙiya? Aa ba zai yiwu ba,sai ya koma dole ne,Moliiiiii."Ya faɗa da karfi
yana dauko tulun ya bude.
Tuni Moli ya bayyana yana,"Wannan kiran fa tamkar ana kokarin zare mini rai?"
A fusace Mai Martaba ya ce,"Wannan fa? Kana gani ya dawo mun da abun da ka tura masa ka
na gani? Me hakan yake nufi?"
Wani irin kallo ya bi Mai Martaba da shi sannan ya daga hannunsa wani haske ya janyo masa
Layar sihirin zuwa hannunsa.
"Lallai wannan Yaron ya zarce tunanin duk mai tunani,har ya yi karfin da zan yi ajiya ya dawo da
ita? Ba shakka yana ji da kanshi amman in yasan wata ai bai san wata ba."
Mai Martaba ya ce,"Ina layyar an andanata wajen da ba ma zai ganta bane to?"
"Kwarai kuwa,amman taurin kai da karfin da ke tattare da shi yasa layar ta gaza samun mafaka
dole ta fito ya ganta kuma ya dawo mana da ita,kar ka damu wannan fadan yanzu ba naka kai
kadai bane harda ni kuma zan dau mataki."
Farouq na tashi ya je ya duba inda ya ajiye layar bai gani ba.
"Alhamdulillahi ai babu abun da ya fi karfin Ubangiji. " ya furta yana sakin murmushi.
Wani irin shiri da shaƙuwa ne ya fara wanzuwa tsakanin Farouq da Janinah domin indai zai
kasance a bangaren Hajiya Kaka to ita ma tana nan suna tare,har yana ƙara koya mata
abubuwa da dama.
Tun Javed da su Hajiya na mamaki har sun daina sun zubawa sarautar Allah ido.
Kilishi kuwa da ta fahimta tuni hankalinta ya tashi ta fara nemo kofar da zata shiga ta fita tasan
meke tsakanin Farouq da Janinah.
Zaune suke a falon Hajiya kaka su kadai Janinah da system dinta Farouq na mata bayani suna
wani abu,a fusace Kilishi ta shiga Part din tana fadin,"Wai ke Janinah ba cewa na yi a kira mun
ke ba? Kina nan kina shirme wani bare yafi danginki ko? Da ina jin labari ban gasgata ba ashe
da gaske dai hakan na faruwa?"
Kallonta Janinah ta yi kafin ta ce,"Aa Aunty Kilishi zasu fita ne yana sauri shiyasa na tsaya ya
karasa nuna mun abu sai in tawo,ki yi hakuri. "
Tsaki ta yi ta na karewa Farouq kallo sama da ƙasa kafin ta ce,"Wuce muje ki bar duk wani
shirmen abu anan."
Zata kara magana Farouq ya dakatar da ita da fadin,"ki je da dare in mun dawo ma karasa."
Yana karasa fadin Hakan Javed na shigowa.
"Yane Oga kun kammala?"
Farouq ya ce,"Eh mu je."
Wani irin kallo Kilishi ta bishi da shi zata fita,shi kuwa ya sake mata murmushi.
Suna zuwa part dinta ta fara balbale Janinah da fada.
"Kin san dai wannan ba muharraminki bane ko da har kike shige masa,saboda kin ga Arham bai
da rigima da tashin hankali yasa kike abun da ki ka ga dama ko? To in shi ya bar ki ni ba zan
bari ba,ba zai taba saɓuwa ba domin ni ba zan jure hakan ba dole ki fita a harkar bakon ban
daga yau yoo ma ban da rashin zuciya mutumin da ya wulakantakin yanzu zaki na kulawa ?
Daga yau na hana na taka miki birki kar inji kar in kuma."
Janinah ta ce,"Shin lamuran gidan nan sunyi tsamarin da har sai an zaba min wanda zan kula?
And batun Arham kuma na aure shi? Daga ke har shi baku da iko da ni a halin yanzu bare ma
ko na aureshi shi ke da iko dani ba ke ba."
Tsayawa Kilishi tayi tana kallon Janinah.
"Iyee? Janinah ni kike faÉ—awa hakan? ni ce nake magana kike mai da mun da martani a yau?
Kanwar
Mahaifinki kuma Mahaifiyar Mijin da zaki aura? Anya Wancen yaron bai yi miki wani abu ba
kuwa?"
Janinah ta ce,"Ya mun me? An fada miki kowa irinki ne mai bakar zuciya? Kuma wallahi ba
fashi sai na ci gaba da kulashi domin ina karuwa da kasancewa da shi fiye da ke da kike
daurani a hanya mara kyau,sannan batun aure kuma bar ganin cewa Mai Martaba ya amince in
na so babu musu zan iya kin auren ÆŠan naki ba yadda aka iya dani." Tana fadan hakan ta fice daga part din cikin sauri.
Cije yatsa Kilishi ta yi,"Lallai akwai matsala gagaruma,ba a banza na ji tsanar yaron nan,zai iya
hure mata kunne ma ta ce shi take so,shi zata aura ban da matsala da Mai Martaba amman
akwai bukatar in rufe kofar nan tun kafin ta bude tafi karfinmu dani fa shi."
Fita ta yi kai tsaye ta wuce Fadar Mai Martaba tana zuwa ta fashe masa da kuka gabansa kafin
ta ce komai.
Umartan yan zaman fadar ya yi da su basu waje zasu tattauna.
Bayan sun fita ya ce,"Lafiya dai? Mene ne ke faruwa?"
Kilishi ta ce,"Ina so ayi auren Janinah da Arham yanzu ba sai an jira ya kammala karatun
ba,domin na lura wancen bakon Javed din na daf da hure mata kunne na lura ma kamar
soyayya suke."
Tana fada Mai Martaba ya maimaita cike da firgici,"Soyayya? Janinah da bako? Soyayya fa."
Kilishi ta ce,"Kwarai kuwa,domin dalilin hakan yasa yanzu ta gama mun rashin kunya ta ci
mutuncina ta zageni ta fice abunta."
Mai Martaba ya ce,"Ah lallai abubuwan da yawa zaki ce mun,kin san cewa ban yarda da
kasancewar bakon nan a gidan nan ba? Domin jikina na bani cewa shi din wani tsaiko ne da zai
iya tona sirrinmu na shakarun da suka shuÉ—e kuma alamu ya nuna lallai shi jinin gidan nan ne
abun da ya fi tada mun da hankali ma kenan."
Zare Ido Kilishi ta yi tana,"Jinin gidan nan? Sirrin masarauta? na Mai Martaba da
Abdul-Rasheed tare?" Ta karasa maganar jiki a sanyaye zufa na keto mata.
Mai Martaba ya tashi yana kai da kawowa,"Kwarai kuwa,rabona da in samu barci cikin
kwanciyar hankali tun ranar da yaron nan ya iso cikin gidan nan."
Kilishi ta ce,"Innalillahi wa inna illahir raji'un mun shiga uku,to ma shi din wane ne?"
"Har yanzu mun gagara sani anata faman bincike amman amsar dayace yana da matukar tsari
da karfi sannan jinin gidan ne kuma jinin sarautar da ke jikinsa ma duk tafi tamu karfi."
Kilishi ta ce,"Ya illahil Alamina Allah gamu gareki yanzu dai asamu ayi gaggawar auren nan
kuma mu dukufa nemo hanyar da zai gagara aikata komai garemu."
Mai Martaba ya ce,"Babu matsala batun aure kam, zan yi masa gargadi na zahiri ma ki zuba ido
a daren yau daga shi har Janinan,amman kema kiyi naki kokarin abangarenki wajen ganin
munci nasara."
Kilishi ta girgiza kai.
"In sha Allah daga yanzu ma kuwa ina fita daga nan."
Tana tafiya tana sakawa a zuciya,"Kenan dai wannan yaron yana son dakile shirina nima in ko
hakan ne ba zan taɓa fari ya ci nasara ba,daukan mataki ya zam wajibi a gareni. "
♡♡♡♡Farouq sunata shirye-shiryensu na yaye dalibai
Javed kuwa soyayya ta yi zurfi tsakanin shi da Ameemah domin kullum suka tashi da kanshi
yake kaita gida kafin ya dawo su tafi da Farouq.
Misalin Karfe takwas na dare Mai Martaba ya sanar da cewa yana bukatar kowa a babban falo
kuma ya ce harda Farouq a wannan zaman.
Tunda Farouq ya ji ance harda jikinsa ya bashi cewa wannan zaman dominsa za ayi.
Suna zuwa kuwa kowa ya gama hallara saura su.
Neman waje suka yi suka zauna shi da Javed ana kallon kallon.....
[22/06, 5:39 pm] Xayyeesherthul-humaerathí ¼í½‚: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! í ½í¸Š
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda