Showing 30001 words to 33000 words out of 62597 words
Chapter 11 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
cin abincin naka zuwa bayan la'asar zamu shirya za a fara
bikin in ka gama sai mu dau rawanin mukai a naɗa maka a ajiye sai sawa kawai."
Farouq ya girgiza kai yana fara kai luma abunsa.
Gida anata shige da fice ana gyare-gyare da girki girki da ma shirye-shirye domin duk da gidan
cike yake da adon gargajiya da sarauta na yau ya bambamta da kullum domin an kara tsara
komai cikin ƙawa.
Misalin Karfe Hudu daidai an fara taro kowa da kowa na gidan sun hallarci farfajiyan filin da ake
taron hatta mai martaba anata raye-rayen da kaɗe-kaɗen gargajiya illa Farouq da Javed da
suketa fama da rawani da kyar aka samu aka daidaita ya zauna.
Shigar sarautar ba ƙaramin kyau ta yi Farouq ba wanda ya zarce misali domin kuwa ba zai taɓa
misaltuwa.
Javed ya ce,"Ya Subhanallah Oga ka ganka kuwa? Yoo ni ko sarki ban taba ganin yayi kyau
cikin kayan nan kamar yadda ka yi ba,gaskiya tsaya inyi ma hoto tukunna in samu da na status
a tiktok kuwa na san sai ka kaini viral ba makawa. "
Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Kai dai baka da dama."
Hotuna Javed ya dunga yi masa,ya masu selfie tare sannan suka fita.
Jinin sarauta,izza da kamala,ƙasaita da duk wani shauƙi na sarauta sun gama bayyana ga
takun Farouq,wani yanayi ya riski kansa na jin tsantsar ƙasaita da ba zai iya kaucewa hakan ba.
Cikin izza suke tafiya har suka isa farfajiyar taron,sheƙen da rawanin kansa da zobensa da suke
shi ya fara aikawa da al'ummar wajen saƙon isarsa.
Kallon kallo aka fara yi yinyin da idannun kowa ya koma kansa.
Abba Malik na bude baki,"Abdul............"
Tsintar kansa da kasa ƙarasa sunan ya yi yana jin tamkar wani dutse ya maƙale masa a wuya.
Hajiya kaka kuwa kwakwalwarta ce ta fara dawo mata da rayuwar baya,tana so ta gano wani
abu amman lamarin ya citura,dafe kanta ta yi tana,"Ina yake....ina yakeee."
Kilishi kuwa zare idanu ta yi cike da mamaki," lallai wannan ba mutum bane."
Ta furta a zahiri ba tare da ta sani ba.
Wani irin kallo mai martaba ya bisa da shi yana zare idanuwa "Zargi na ya tabbata zai juyar
masu da tunani zai dawo da su,zasu fahimta,zasu tuna,baka isa ba,wallahi baka isa ba."
Ya karasa maganar ya ciro wani gari ya fesa.
Hajiya kaka na kokarin faɗuwa kenan Farouq ya yi saurin karasawa ya tareta,"Amarya ta ga
angonta ya yi kyau ta tsure harda shirin faduwa. "
Ya fada cikin sigar tsokana.
Lamura sun ci gaba da tafiya amman gabadaya zuciyoyin Mai Martaba,Abba Malik,Kilishi da
Kaka cike take fal da damuwa kuma a cunkushe mussamman Hajiya Kaka da Abba Malik da
abun yafi daurewa kai.
Mutane sai zuwa suke ana hoto da Farouq yadda ake damuwa da yin hoto da Sarkin Al'adu
wannan karan ko ta shi ma ba ayi gabaɗaya rububi ake akan Farouq kowa burinsa ya yi hoto
da shi kuma mussamman da yake labarinsa ya baza gari kan abun da ya faru a Bida sai nuna
shi ake ana ai shine ance dan baiwa ne.
Wani tsoho ne tukuf ya karasa inda Farouq yake ya shafa fuskarshi kafin ya ce,"Kai ne kadai
zaka kawo karshen zalinci kai ne zai ka fito da tsagwaran gaskiya,ina rokon ubangiji da ya yi
maka albarka kuma ya tsare ka da tsarewarsa tare da kariyarsa sannan ya maka lulluɓi da
albarkarSa."
Farouq ya amsa da Ameen duk da cewa bai gama fuskantar abun da tsohon ke faɗa ba.
Hannu yasa a aljihunsa ya ciro wani dumin kudi ya miƙawa tsohon ya karba yana kara sa mishi
albarka sannan ya tafi.
Janinah sai cizon yatsa take tana takaici,"shi wai wannan kowa sonshi yake ne? Sai kace Aljani
Mtswwww. "
Ta ja tsaki tana kallonsa.
Suna hada sai ta galla masa harara.
Shi ko da murmushi yake binta.
An yi shagali anci an sha an watse.
Farouq ya bazu a social media yan nigeria mussamman mata sai reposting ake da ga Asalin
Mijin Novel ya bayyana har da masu rubuta wasikar soyayya,lamura dai kala kala,suna zaune a
falon Hajiya Kaka da dare Javed sai dariya yake yana nuna masu,"Oga ka baza capacity fa ka
tashi kan yan matan nigeria ko ina aka bude lamarinka ke trending
tiktok,Instagram,Twitter,Facebook har WhatsApp status kawai kaine harda me cewa ita in ba kai
ba ba zata yi aure ba harta mutu. "
Caraf Hajiya Kaka ta taɓe baki tana faɗin,"Aiko dai saidai ta mutu ko ince su mutu ma don dai
wannan kam nawa ne ni kadai,ko ba haka ba Mijin?" Ta fada tana kallon Farouq.
Daga mata gira ya yi yana,"Sosai ma Amaryata Yan matana ai daga ke ba ƙari ke ɗaya ce."
Janinah ma da taga abun yaƙi karewa ko ina ta bude shi ke yawo tuni taje tana nunawa
Kilishi,wani yanayi da bata saba riskarta ciki ba ta ganta,"Aunty Kilishi kin ga ko ina fa hoton
wancen banzan bakon ne."
Kawar da kai Kilishi ta yi tana,"Kin ga Janinah kije da safe zamuyi magana yanzu kaina na
ciwo."
Ba yadda Janinah ta iya haka ta fita amman zuciyarta cike fal da tarin tambayoyi domin bata
taɓa ganin Kilishi a yanayi na damuwa kamar na yau ba.
Dakinta ta wuce ta kwanta abunta.
Shi kuwa Mai Martaba Moli ya gayyato cikin fushi da ɓacin rai yana yi mishi magana,"Shin ka ga
rawanin da ya sanya? Ka ga rawanin da ke kanshi? Ka ga yadda siffarsa ta kasance a cikin
kayan nan? Ka kasa gano mun shi wane ne tawagarka ma sun kasa,kenan yafi karfinku? Anya
ma mutum ne kuwa? Na ce anya ma mutum ne kuwa? Na fara tantama wannan ba mutum
bane,kuna gani za a gaba bayana,kuna gani karshena zaizo."
Ya fada yana buga bango.
Dariyar muguntar da Moli ya saba ya yi kafin ya tsagaita ya ce,"Kai Abdul-Raheem Hattara dai
na ce hattara dai,wannan yaron mutum ne kamarka na fadama na sake fada ma mutum ne
kamarka kusancinsa ga ubangiji ne mai girma sannan lamarinsa dauke yake da matukar
sarƙaƙiya aiki akansa muke ba dare ba rana wanda sanadinsa har wani cikin yarana ya samu
matsala,ba shi bane wanda kake tunani domin ba zai taɓa zama shi ba don ya sa wannan
rawanin in zaka kwantar da hankalinka ka kwantar."
Cikin fushi mai martaba ya ce,"lamarin ya kai ni makura kuma cikin daren nan zan dauki
matakin da kuku kasa dauka."
Dariya Moli ya fara yana,"Ka dauka,ka gwada dauka za ka kai kanka ga tona ramin da ka birni."
Ya ci gaba da dariya kafin ya ɓace.
Dare ya yi,kowa ya tafi daki sunyi barci.
Karfe Ɗaya Daidai Farouq na zaune gaban System sai ji ya yi ana taɓa kofarsa.
Zura key aka yi aka bude aka shige,wani mutum ne dauke da wata doguwar bakar riga data
rufeshi daga sama har ƙasa.
,“Lā ilāha illā anta subhānaka innī kuntu mina-ẓ-ẓālimīn.” Farouq ya furta cike da firgici.
Daga abun da ke fuskarsa ya yi,ya bude.
Suna haɗa ido ya ga mai martaba ne.
Wani irin faduwar gaba ya ji yana ja da baya.
Mai martaba ya ce,"Kai wane ne? Ka fadamun kai wane ne?"
Farouq ya ce,"Ni ba kowa bane kuma nima ban san ni wane ne ba."
Cikin Fushi Mai Martaba ya zaro wuƙa yana shaƙo Farouq,"Ka faɗa mun kai wane ne ko in
kasheka."
Cikin daurayi Farouq ya ce,"Sai dai in ka kashenin bare kuma ba ka isa ka kasheni ba har sai in
kwanana ya kare."
Kara sa masa wukar ya yi akan wuya yana,"Ba zaka fada ba kenan? Zan iya kasheka yanzu in
kashe banza anan ba tare da kowa ya sani ba,amman a halin yanzu nafi son insan kai wane ne
sannan kuma ina Umartarka da safiyar gobe ka shirya ka bar kasar nan tun kafin ni da kaina
ɓatar da kai."
Farouq ya ce,"Kai ya kamata in tambaya ni wane ne,sannan kuma baka isa ka ɓatar dani ba in
kana hakan kana cin nasara to ka gwada akaina ka ga ko zaka ci."
Shaƙesa ya yi yana kokarin daba masa wukar Farouq ya yi saurin kaucewa ya kwantar da shi
yana karbar wukar shima yasa mishi kan wuyansa yana,"Ni ba zan kasheka ba,amman zanyi
ma illar da sai ka ji cewa dama mutuwar kayi,kuma ina umartarka da ka bar dakin nan tun kafin
in tarama jama'a,sannan kasa aranka ba zan taɓa barin gidan nan ba sai aiwatar da kudirina."
Murya na rawa Mai Martaba ya ce,"Daga sai in fita to don Allah ka barni karka tada kowa."
Daga shi Farouq ya yi da wukar a wuyansa har sai da ya hankadeshi waje kafin ya kulle kofarsa
ya jefar da wuƙar gefe.
Ficewa daga masarautar Mai Martaba ya yi cikin daren ya shiga wani daji yana tone tone.
Shi ko Farouq ajiyar zuciya ya yi ya koma ya ci gaba da aikinsa da yaga ma ba zai iya ba
karshe kwanciya ya yi.
Yana fara barcin babu wanda yake mafarki illa wannan tsohon da ya yi masa addua da yamma.
Kasa hakuri ya yi karfe hudun asuba ya je dakin Javed ya tasheshi.
"Lafiya Oga?"
Javed ya fada.
Farouq ya ce,"Lafiya lau,kasan gidan wannan tsohon da ya yi mini addua dazu?"
Javed ya ce,"E kwarai a cikin gari yake."
Farouq ya ce,"To muna idar da sallar asuba zaka rakani Don Allah ."
Javed na washe barcin da ke idonsa ya ce,"Lafiya kuwa?"
Farouq ya ce,"Lafiya lau ina so in kara masa abun da na basa ne."
,"To kuma shine da asuba bazamu bari sai safiya ba?"
Farouq ya ce,"E ba zan iya hakura ba mafarkinsa nake."
Suna yin sallar asuba kuwa suka fice daga masarautar.
Wani ķaramin gidan laka ne da duk ya gama jin jiki ya rurrushe duk an yi ciko da leda.
Javed ya ce,"ga gidan nan....
[31/05, 9:21 am] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-19
kallon Gidan Farouq ya yi yana,"To ka ɗan taimaka ka yi muna sallama da shi mana."
Javed zai yi magana kenan sai ga Tsohon ya dumfaro inda suke,ga dukkan alamu daga
masallaci yake,tsoho ne tukuf da kyar yake tafiya da sanda.
"Ah Javed kune? Ince dai lafiya?"
Javed ya kalli Farouq ya ce,"Lafiya lau Baba Bakonane ke son ganinka ya ce sai mun zo yanzu
na yi na yi ya bari sai safiya yaƙi."
Wani matsakaicin Murmushi ya yi ya ce,"Daman nasan za a rina,Ɗan samari sannunka ko
zamu ƙarasa soro ne?"
Farouq ya ce,"E gaskiya zan so hakan,yanzu kai Javed ka koma gida kar a fahimci bama nan in
mun gama da Baba zan tawo."
Javed ya kallesa yana,"Okay to amman dai zaka gane hanyar ko?"
"In sha Allah. " Farouq ya fada.
Baba ma ya ce,"ko bai gane ba ai na rako shi."
Tafiya Javed ya yi ya barsu,suka shige zauren gidan sannan suka zauna kan taburma.
Baba ya ce,"Mene ne tafe da kai yaro?"
Gyara zama Farouq ya yi da kyau kafin ya ce,"Cikin mafarkina ya nuna mini cewa kana dauke
da hasken da zaka fiddani daga duhun da nake ciki in daina lalube sannan kuma zuciyata ta
ƙara gasgata mun hakan ya yin da ruhina ya aminta da cewa lallai akwai abun da ka sani game
dani." Numfasawa Baba ya yi kafin ya ce,"Ina mahaifinka?fatan yana cikin ƙoshin lafiya?"
Daga kai Farouq ya yi yana yiwa Baba kallon rashin fahimta cike da tuhuma.
"Mahaifina? Shi ne abun da nake nema Baba,kuma shi ne nake jin cewa kana da masaniya
akan inda yake domin har yanzu na gagara gasgata shin wane ne mahaifina cikin gidan
masarautar al'adu,Mai Martaba ko Abba Malik? Sam babu mahaifina ciki,shi na zo nema
amman na lura da cewa tamkar babu shi ma a duniya da tarihin masarautar abun da na riska ya
bambamta da abun da mahaifiyata ta sanar mini."
Baba ya ce,"Na ji mamaki matuka da kace mahaifinka ka zo nema,domin a tunanina mahaifinka
ne ya turoka domin daukar fansa indai hakan ya tabbata abun da kake fada to tabbas lamarin
da girma yake."
Farouq ya ce,"Babu shakka Mahaifiyata bata ƙara sa mahaifina a idanunta ba tun daga ranar da
ya kaita filin jirgi domin komawa ƙasarta har kawo yanzu da nake zaune a gabanka."
Girgiza kai Baba ya yi kafin ya ce,"Gatan da zanyi maka bai zarce ace in baka tarihin abun da
na sani ba domin kila a ciki zaka samu hasken da kake da buƙata."
Gyara zama Farouq ya yi yana fuskantar Baba
" Nine Malami na farko ga gidan sarkin al'adu tun lokacin da Kakanku ke raye Mai Martaba
Abdul-Alim,ni ke bincike da shige da fice kan duk wani abu na tsaro da tsafi dake guduna cikin
masarautar domin kuwa ni amintacce ne kuma amini ga Mai Martaba hakan yasa na san komai
shige da ficen wannan gidan,Mahaifinka su biyu Allah ya fara bawa mai martaba da shi da ɗan
uwansa Abdul-Raheem wanda ya kasance sarkin al'adu na yanzu kasancewar kakarku ta yi
jinkirin haihuwa an sha shige da fice kafin zuwansu duniya wanda har kai ga dukkanin su ana
haifarsu muka fara duba taurarin rayuwarsu akaron farko Maihafinka Abdul-Rasheed da yake
babba manuniya ta nuna cewa shine ya cancanci gadar sarautar kakanku domin shi ne ya gado
kyawawan dabi'u irin nasa saɓanin Hussaini Abdul-Raheem
Dukkaninsu sun taso cikin gata da soyayya matuka ya yin da suka fara girma sun kammala
karatuk sakandare sai Mahaifinka ya buƙaci da a turasu ƙasar waje domin yin karatu a bangare
kimiya wato na'ura,
A lokacin an haifi Baffanku Abdul-Malik da Khaleesa
Mai Martaba ya amince da hakan amman sai dai inda gizo ke tsaƙar shine Abdul-Raheem sam
karatun baya gabanshi saboda zaɓin Abdul-Rasheed ne ba na shi,baya karatun kuma ba ya
maida hankali illa sanyawa mahaifinka karar tsana da ya yi ganin cewa Mai Martaba na matukar
ji da shi da kyawawan dabi'unsa.
Har ya kai ga Abdul-Raheem kullum yana cikin shiga da rayuwa irinta sarauta tsangwama da
kyarar mutane kuwa ba a magana duk da cewa mai martaba na kokarin tsawatar masa amman
ba hakan ke sawa ya daina ba sai dai ya rage aikatawa a gaban idanunshi,shi kuwa Mahaifinka
tamkar ba ɗan gidan sarauta ba,rayuwa yake daidai data kowa cike da girmamawa.
Karshe Abdul-Raheem daga zuwa hutu yaƙi komawa makaranta ya zauna a fada,shi kuwa
Abdul-Rasheed sai da ya kai wani babban mataki da ba zan iya cewa mene ne ba tunda ba
bokon muka yi ba amman dai bana mantawa dawowarshi an shirya shagali mai girma na
tarɓarsa wanda bikine da ba a taba yin irinsa ba a tarihin mokwa inda ya haɗa manyan
sarakuna na nigeria da kewaye wannan bikinma ba ƙaramin tadawa Abdul-Raheem hankali ya
yi ba domin kuwa gagara boye hassadarsa ya yi ban mancewa har tsoron shi mahaifinka ya
fara ji ya dakesa ya bigesa kuma ya kwace masa abubuwa amman mahaifinka bai taɓa faɗa ba
ita kuwa kakarku data fahimci hakan sai ta sanya aka raba masu ɗaki amman duk da hakan bai
tsira ba
ana cikin hakan ya samu aiki a kasar Netherlands inda ya koma cen na tsawon shekara uku cif
ina kyautata zaton cewa anan ne ya haɗu da mahaifiyarka suka fara soyayya wanda har
tsautsayi ya gifta tsakani akai yi cikinka ba tare da aure ba,ganin hakan ya sa mahaifinka
dawowa gida da ita bayan ta musulunta iyayenta sun gujeta kan cewa zai aureta inta haihu,bai
sanar da kowa cewa tana dauke da ciki ba illa ni kadai domin a lokacin kakanku na jinya
kwance babu lafiya rai a hannun Allah.
Hakan yasa Abdul-Raheem ne ke kula da duk lamura na masarautar kuma daman abun da
yake da buri kenan.
Zuwan mahaifinka da mahaifiyarka ya ce sam ba za a shigan masu da kafura cikin ahali ba su
ba za su abun kunya ba,a lokacin Khaleesa duk da tana da ƙarancin shekaru amman ta bawa
Abdul-Raheem goyon baya sosai domin tare suka yi shige da ficen da don dole sai aka sa
mahaifinka ya nemawa mahaifiyarka tikitin gaggawa na komawa kasarau domin kuwa lamarinta
har sai da ya kai ga mai martaba babban sarki na bida ya shiga ciki lamura dai marasa dadi
sosai cike da tozarci da cin mutunci duk yadda na so domin kwantar da lamarin abun ya cutura
sai da na zam ɗan kallo,
Bayan mahaifiyarka ta koma ba jimawa Allah ya dauki ran mai martaba ya yin da aka fara shiri
gadan gadan domin naɗa Abdul-Rasheed nan fa Abdul-Raheem ya