Showing 9001 words to 12000 words out of 62597 words
Chapter 4 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
kina so ki
fini ki danne ni,to Allah ya baki sa'a da nasara kamar kullum dai in kina neman wani taimako
kofa a bude take."
♡♡♡
Javed cike da farinciki ya yi Daliban barka da zuwa tare da jawabai masu ratsa zuciya.
,"Kar ku ga cewa wannan karatun da za kuyi kyauta ne kuyi tunanin wasa da damarku ina mai
tabbatar muka da cewa tamkar wasa da nasarorinku ne domin kuwa kasancewarku anan ma
kadai babbar nasara ce kuma jigo sannan bango ga rayuwarku,yadda duniya ta waye ko ince
take kan kara wayewa a komai yanzu Kimiya da fasaha ke aiki,ku rike maraicinsu ku bude
kwakwalanku da idanuwanku ku mai da hankali kan neman ilimi,shi zai zama madogara a gare
ku shi zai zam haske a gareku rayuwarku da ta ma al'ummar da ke tare da ku kamar yadda
A.Umar Farouq ya sheda maku nima a karshe ina mai yi muku fatan alkairi Ubangiji ya bamu
ikon amfana da juna."
Yana gama nashi jawabin shi ma ya bi Farouq ya barsu da sauran Lectures din.
Yana shiga Farouq ya mika masa wayarsa yana fadin,"Janinah ta kiraka."
Ajiye wayar ya yi yana,"rabo da rigimammiyar yarinyar nan yanzu zamu duba yadda tsarukan
lectures din zai kasance."
Farouq ya ce,"Okay."
System Javed ya bude suka shiga dubawa Farouq ya danyi masu gyaran abun da yake tunanin
za a gyara.
Sun jima sosai har suka yi sallar azahar suka idar suka ci abinci suna kan aikin sai wajen karfe
biyar kafin suka kammala.
Zasu tafi gida Farouq ya ce,"Mu bi ta inda zan siyawa Yan Mata iskirim dinta fa."
Javed ya ce,"wai kai yanzu biyewa hajiya Kaka za ka yi ina ita ina shan wani ice cream. "
Farouq ya ce,"Au shi ice-cream din an zabi wanda zasu sha ne? Ku bar tsohuwa ta ji dadin
rayuwarta please ni muje."
Aiko hakan aka yi sai da suka je THE ICE CREAM LAB, ya siyawa Kaka suma sun siya nasu
kafin suka dau hanyar gida.
Suna zuwa kuwa bangaren Hajiya Kaka suka fara wucewa.
Farouq na mika mata leda ta washe bakin nan da wawulonta tana,"Ah lallai yanzu ne na san na
yi miji dole inyi maka kwalliya ka ji dadi irin wacce na ke yiwa Mai Martaba Allah jikan rai sai kuji
yana "Uwar Gida Marurin Zuciya ganinki ke kara karfin zuciya." Wani lokacin fa inai wanka na yi
kwalliya sosai muna hada idanu sai fadawa sun rikesa domin tsabar farinciki sai ya fara kokarin
faduwa yana,"Ya Allah ni ko a aljanna ka bar mun ita,ita kadai nake so."
Dariya suka yi duka Javed ya ce,"Yana cen yana jiranki ai gashi kuma kin masa kishiya da
wani."
Kaka ta ce,"Yoo ai tun yana raye yake da kishiyoyi shiyasa yake dagewa ganin yafi kowa,shi fa
ba ruwansa da wata sarauta in yana gabana har rawa yake tirƙa mun irin wanda yan indian nan
suke."
Ta karasa maganar tana kwatantawa daga zaune.
Don Dariya Farouq da Javed na tsaye sai da suka zaune na.
Farouq ya ce,"Ah lallai Mai martaba ya iya diga soyayya dole nima in dage in kwace zuciyarki
ras."
Hajiya Kaka na kokarin bude Ice cream tana,"Aa fa sai dai abaka rabin zuciyar abar mai rabi
don in bani akwai matsala yana mutuwar rayuwar sona."
Ice cream dinta ta fara mamula da harce kamar abinci.
Javed ya ce,"Za a shiga salla ka ga in muka biyewa wannan Matar taka sai mu rasa."
Ficewa suka yi masallaci Hajiya Kaka an samu abun nema ko kallon inda suke batai ba har
suka fita daga bangaren nata.
A masallacin suka hadu da Abba Malik.
Bayan sun idar yake cewa,"Aiko inata so in zauna abani labarin Malaysia ashe kunje gaida
Madam lokacin ban dawo ba."
Javed ya ce,"Eh wallahi."
Abba Malik ya ce,"To yanzu ba kwa komai muje can mana sai mu ci abincin dare tare daga nan
sai mu yi hira abani labarai kasanni da son jin labari."
Murmushi suka yi duka.
Farouq ya ce,"Ba matsala Abba."
Bangarensan kuwa suka bi shi.
Bayan sun zauna a falo sai ga Momy Zulaihart matarsa ta fito.
Cike da fara'a take fadin,"Ah yau manyan baƙi garemu a gidanmu ashe to barkanku dai maraba
lale."
Gaisheta suka yi ta amsa cike da sakin fuska.
Abba Malik ya ce,"Nace bakon Malaysia yazo mu ci abinci tare mu yi hira ."
"Ya kamata dai kam yanzu bara insa akawo maku abincin in kun gama dole nima in zo in zauna
ayi hirar nan dani."
Ta fada cike da zolaya ta fice.
Bayan an kawo masu abinci sun ci sun koshi Abba Malik ya kalli Farouq ya ce,"Malam Umar ya
ka ga dan garin namu ne ko ince kauyen namu?"
Farouq ya ce,"Abba ai nan ya zarce kauye banyi tunanin zan ga hakan ba gaskiya garin ya
birge ni har ina cewa Javed na ji sha'awar gini anan sannan kuma yadda na ga ana ruruta
matsalar rashin tsaro a Nigeria nidai tunda na shigo ban alamar hakan anan ba."
Abba Malik ya ce,"mu kam gaskiya ba mu da matsalar rashin tsaro sam sam Shugaban dake
jan ragamar garin nan a tsaye yake ba a yadda da batun sace-sace ko hare-hare duk
abubuwan nan da ake a sauran garuruwan dake kewaye da Nigeria mu bama fuskanta domin a
kwanaki ma yan Ta'addan sun turo da takadda mai dauke da sakon suna son shigowa su karya
tarihi da ya kafa ya ce da su ba matsala yana jiransu su shigo,to karshe ma dai koda suka zo
garin basu ga Mokwa ba cikin garin nan din suka bi amman daji ya zame masu sai da suka yi
nisa har sun fada kanji tukun suka hango mokwa,Babban matsafi ne na karshe amman yana
taimakon al'ummarsa kuma yana karesu da tsafinsa a yanzu haka shekara biyu ke nan ba yana
fama da lalura bai da ishasshiyar lafiya magauta sun sanya masa hannu an hana shi zuwa
sallar idi a yadda aka sheda mana lallai muddin yaje zai iya rasa ransa kuma gaskiya ana
matukar kaunarsa al'umma na kukan rasashi domin duk ranar da ya bar duniya mun rasa adilin
shugaba a mokwa.
"Ikon Allah ke nan lallai yana da karfi sosai wannan shi ake kira shugaba mai sadaukarwa kuma
na lura yanayin garin nan sam babu yunwa ga dukkan alamu babu tsawallawa a kan kayan
hatsi."
Abba Malik ya yi murmushi,"Ai Mai Martaba bai yadda da batun rashin abinci ba ga al'ummarsa
ka ga ko boye kayan hatsin da ake a wasu jihohin? Mu nan ba a isa ba domin in ma kunyi za a
karba a rabawa al'umma shiyasa kowa yake taka tsantsan mussamman ma dake muna da
albarkar noma sosai."
Javed ne ya kalli agogon wayarsa ya ce,"Abba dare ya yi karfe sha É—aya da rabi gashi baku
gama ba."
Abba Malik ya ce,"Subhanallah lokaci na sauri kuje ku kwanta kam."
Farouq ya ce,"Gaskiya ban so a katse wannan tarihi ba amman dole watarana inzo in zauna a
ci gaba mun daga inda muka tsaya."
Murmushi Abba Malik ya yi ya ce,"Baka da matsala In sha Allah akwai shagali ma da za ayi na
al'ada kana nan ai zaka gani . "
Sallama suka yi masa kafin suka tafi.
♡♡♡Barci ya gama cin idanun Javed sallama shima yama Farouq ya wuce ya kwanta.
Shi ko Farouq Nafila ya yi kafin ya dauki system dinsa ya fara aiki,sai wajen karfe uku kafin ya
kwanta.
Asuba na yi kuwa da ya tashi yin sallah bai kwanta ba.
System din ya dauka ya shiga bincike....
[10/05, 8:50 am] Xayyeesherthul-humaerathí ¼í½‚: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! í ½í¸Š
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! í ½íºš*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-7
Jin alamar motsin mutum yasa Javed shiga dakin.
Yana shiga Farouq ya yi saurin kashe System din kafin ya karasa gabansa.
Ya daga kai yana binsa da kallo,Javed ya ce,"kai dai kam baka hutu inaga a kullum da kyar in
kana samun barcin awa uku zuwa huÉ—u."
Farouq ya yi murmushi,"Hutu ai ba nawa bane,akwai abubuwa masu mahimmanci da yawa da
nake kan gudanarwa kuma hankalina ba zai taɓa kwanciya ba har sai na ga tabbatuwarsu na
cimma nasara."
Javed ya yi dariya,"Ai kai kwaro ne Ga ka barawo ga ka adili kodayake ba ace da kai barawo ba
tunda kana kwamusowa al'umma hakkinsu ne da manya ƙasa suka danne, nima fa da zan iya
lamarin nan naka da na fara anan Nigeria wallahi don muma muna da azzaluman shugabbanni
da attajirai da suka danne dukiyoyin talakawa suna gina rayuwarsu da ta iyalansu."
Farouq ya ce,"Mai zai hana? Tsab zaka iya kuma zan baka gudunmawa wajen tabbatuwar
hakan,Duk da cewa ba hanyar kwarai nake bi ba wajen diban dokiyoyinsu ba amman kuma
hanyar kwarai nake bi da ita wajen tallafawa mabukata kuma na tabbatar da cewa Ubangiji zai
dubi zuciyata don haka ban taba jin dana-sani ko fatan dainawa ba,muddin numfashi bai bar
karakaina a jikina ba zan taba dainawa ba duk wani arzikin da bai taimakon al'umma ko yake
danne al'umma idona na zuwa kanshi sai na kwatar masu rabonsu sun amfana suma sun gina
rayuwarsu cikin aminci hakan ba karamin tallafawa yake ba wajen kawar da talauci a kasa ba
sai iya ka gwamnati ke da alhakin kula da al'umma ma muma muna da wannan nauyin muddin
ana son ci gaba a kowacce kasa."
Javed ya numfasa ya ce,"Gaskiya ne dukkanin bayanka kuma na gamsu da su sannan nima ina
bukatar ka daura ni akan hanya amman dai kasan nan ba malaysia ba ne abubuwanmu da
bambamci."
Farouq ya ce,"Yeah kuma ka ga ni kowanni mutum indai na taɓa masa dukiya ina tura masa
takaddar gargadi kan dalilin da yasa na diba tare da hujojjojina kuma ina basu tsari da dokoki
yadda zasuna tallafawa al'umma yadda na tsara ina biye da duk wani motsinsu ta yadda duk
wanda yaƙi aiwatar da abun da na bukata ina iya kara aikata masa mafiyin abun da na yi a
farko,to hakan yasa suke shakka suna kokarin bin tsarina ko iya hakanma babbar nasara da
galabace a gareni ìna sanya su yin alkairi ga al'umma ko da basu yi niya ni in samu lada suma
su samu kuma ubangiji ya kara buÉ—a musu to amman kuma kamar yadda ka fada Nigeria da
kamar malaysia zan danyi bincike mu ga yadda abun zai iya kasancewa."
Javed ya ce,"Yes My Boss da ana iya hallarta sata da nace wannan satar hallartacciya ce tunda
da nufin alkairi ake yinta."
Farouq ya yi murmushi.
Javed ya kara faÉ—in,"yanzu bara in barka ka ci gaba da aikinka kar in dameka."
Ya fada yana dariya ya fice.
Yana fita da sauri Farouq ya dago system dinsa ya kunna.
Wani page ya shiga wanda aka yi rubuta NIGER STATE/MOKWA
a kasa kuma GIDAN SARKIN AL'ADU.
Sauran rubutun da ya yi a kasan duk da programming language wanda sai cikakken Computer
scientist ne kadai zai iya fahimta.
Shiga ya dunga yi yana ta duba wasu abubuwa kafin daga karshe ya kulle wajen karfe bakwa
na safiya.
Cikin sauri ya karya domin 8 daidai zasu fara Lectures kuma Farouq ne farko.
Kafin ya gama Javed ya fito,yana gamawa suka fice ko Hajiya Kaka basu je sun gaida ba.
Kai tsaye lecture room Farouq ya nufa inda student duk sun hallara shi kadai ake jira.
Da tambayoyi ya fara masu kan binciken da yace su fara kan cybersecurity.
"Ko akwai wacce zata iya fadamun mene ne Cybersecurity atakaice?"
Kusan mutane biyar ne suka daga hannu ya tashi ta farkon ta ce,"Hanyoyin sanya tsaro ga
na'ura."
Sanyawa ya yi atafa mata kafin ya kara tada wata ma ta ce,"Yadda ake kula da kwamfuta
gudun samun hari."
Ita ma sawa ya yi aka tafa mata bayan sun zauna duka ya ce,"Ehto duk kunyi kokari yanzu
amman akwai bukatar cikakken bayani kowacce ta kunna system dinta ta login PDF dinmu na
Cybersecurity daman ai jiya ance an koya muku ko?"
Suka amsa da ,"Yes Sir."
Cike da zumudi dukkaninsu suka bude systems din suka shiga PDF din gwanin sha'awa.
Farouq ya ce,"Are we ready?"
Nan ma suka kara amsawa da ,"Yes Sir."
Cikin kwarewa Farouq ya fara jawabinsa.
Da farko shin mene ne CYBER SECURITY?
Cybersecurity shine tsaro na yanar gizo yana da alaƙa da kare kwamfutoci,hanyoyin
sadarwa,kiyaye bayanai ta hanyar shiga ba bisa ka'ida ba ko ba da izini ba,kawar da
hare-hare,lalacewa ko sata,kunshi fasahohi da hanyoyi tare da ƙa'idoji da aka tsara don kare
bayanai tare da tabbatar da ingancinsu,sirrinsu da samuwarsu. Wannan shi ne cikakken bayani dangane da Cybersecurity ina fatan kowa ya fahimta?
Sai da ya tabbatar da duk sun fahimta kafin ya ci gaba.
"Yanzu za mu wuce gaba,Akwai muhimman abubuwa na tsaro a yanar gizo da ya kamata ku
sani kamar su.
Network Security
Kare hanyoyin sadarwa.
Application Security
Sanya tsaro ga aikace-aikace da kubutar da su daga rauni.
Information Security
Kare ingancin da sirrin bayanai a dukkan na urori da hanyoyin sadarwa.
Endpoint Security
Tsaron na'ura guda dake samun damar shiga hanyoyin sadarwa na kamfani.
Cloud Security
Shi kuma shi ne tsaron gajimare wanda ake kare bayanai da aka ajje cikin yanayi na gajimare.
Sannan akwai
Disaster recovery
Incident response
Regulatory compliance wa innan kenan
Sannan ina so ku sani cewa tsaro na yanar gizo yana da matukar muhimmici a wannan rayuwar
yayin fa barazana ke ci gaba da wanzuwa yana da kyau ga murane da duk wasu kamfani ko
kungiyoyi da su kasance masu tsaurara tsaro da ka idoji masu karfi ga dukkan wani abu da ke
mallakinsu a yanar gizo." yana ka karasa wannan maganar ya ce,"ko akwai masu tambaya ko
abun da baku gane ba?"
Caraf wata ta daga hannu.
Ya bata damar tashi kafin ta ce,"Sir Amman a binciken dana fara na ga akwai yadda mutum ke
koyan yadda zai kai kutse ko hari ga wani shin ba za a koya mana bane."
Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Ke ko Meemah wa kikeson kaiwa hari tun yanzu? Za a koya
maku amman hakan ba wai yana nufin ku koya ku dunga cutar da mutane bane,za a koya muke
domin karin tsaurara tsaro tare da fahimtar tsaron da hanyoyin da ake iya bi don ruguzawa
amman ba don cutar da kowa ba,kuma ba mu zo bangaren ba tukunna muna tafe zamu zo In
Sha Allah amman a yau dai zamu tsaya anan."
Godiya Meemah ta yi masa cike da gamsuwa da bayanansa ta zauna.
Cikin jin dadi Farouq ya kammala masu lectures dinsa na ranar kafin ya fita.
Can yamma suna zaune da Javed ya kalli wayarsa ya ce,"Oga na manta fa in sheda ma yau
muna da zaman babban falo da dare duk ranar Friday haduwa ake aci abincin dare dukka
family a babban falon mai martaba sannan muna sanya kayan gargajiya a daren za aci abinci
tare ayi wasa da dariya in mutum na da matsala ko wata magana da yake son yi yana iya yi duk
a gun."
Farouq ya ce,"Ma sha Allah hakan ba karamin kara dankon zumunci zaiyi ba to yanzu har ni
zan iya shiga? Zanso in ganni cikinku ko zanji kwatankwacin yadda mutane suke jin yayin da
suka gansu cikin danginsu."
Javed ya ce,"Haba dai,ai ba kwatankwaci za ka ji komai zaka ji duk yadda kowa ke ji na sha
fada ma always feel like home please. "
Da hirar suka yi sallama da sauran Staffs din kafin suka tafi gidan.
Sai da akayi sallar isha suka nufi babban falo.
Suna zuwa kuwa kowa ya hallara hatta hajiya Kaka.
Tana ganin Farouq ta fara washe baki tana,"Mijin aiko yau inata nemanka."
Karasawa gabanta Farouq ya yi ya zauna yana,"aiko gani nan yan mata kaina kasa."
Duka suka fara dariya.
Mai Martaba ne ya yi gyaran murya da yasa dukkaninsu yin shiru.
Janinah da Kilishi suna ganin shigar Farouq suka fara kuskus.
Karshe dai Janinah ta tashi ta fita kafin ta dawo suna kallon juna suna sakin murmushi.
Abinci aka fara kawowa a ƙa ida jikoki maza faranti ɗaya ake masu su ma yara matan da
matan jikokin É—aya,na iyaye ma É—aya.
Mai martaba kuma shi da Abba Malik da Hajiya Kaka.
Hakan kuwa ya kasance.
Sannan a ƙa ida ba a surutu lokacin da ake cin abincin hakan yasa gabadaya falon ya yi shiru.
Suka yi bismillahi aka fara ci.
Tuwon shinkafa ne miyar wake wanda yana daya daga cikin abincinsu na gargajiya da suke ji
dashi.
Falo ya yi tsit
Kowa yana cin abincinsa cikin nutsuwa karaf cikin Farouq ya fara kugi.
Kallon kallo suka fara.
Ya make ya ci gaba da cin abincinsa.
Can da cikin ya yi masa wata irin murÉ—awa da kuka bai san lokacin da aguje ya tashi ba
yana.....
[12/05, 10:21 am] Xayyeesherthul-humaerathí ¼í½‚: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAÆŠINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA