Showing 48001 words to 51000 words out of 62597 words
Chapter 17 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
da mutum ya aikata na zunubi daga ranar da ya musulunta duk an shafe
zunubansa ya dawo tamkar jariri sabuwar haihuwa.
Ka ga wannan ma wata falala ce da wanda aka haifa cikin musulunci ba shi da ita. "
Haka kuma ya ƙara da fadin,"
2. نع يبأ ةريره يضر الله هنع :لاق
لاق لوسر الله :ﷺW
نم" ملسأ نم لهأ ةيلهاجلا مث نسح ،همالسإ مل ذخاؤي امب لمع يف ،ةيلهاجلا نمو داع يف ةيلهاجلا ذخ
ُأ
لوألاب ".رخآلاو
هاور يراخبلا E6924F ملسمو E120F
Ma'ana: Wanda ya musulunta daga jahiliyya, kuma ya kyautata Musuluncinsa , ba za a hukunta
shi da abin da ya aikata a baya ba.
Sannan
3. نع يبأ ةريره يضر الله هنع :لاق
لاق لوسر الله :ﷺW
سانلا" نداعم نداعمك بهذلا ،ةضفلاو مهرايخ يف ةيلهاجلا مهرايخ يف مالسإلا اذإ ".اوهقف
هاور ملسم E2638F
Ma'ana: Mutane kamar ma'adanai ne — kamar zinariya da azurfa. Zaɓaɓɓunsu a jahiliyya, su
ne zaɓaɓɓunsu a Musulunci — idan sun samu fahimta.
Ina fatan cewa ka fahimci cewa tubabbu ba sa daga cikin makaskanta a wajen Ubangiji kuma
duk wanda ya ƙarbi baƙuncinsu yana da alfarma mai girma wajen Ubangiji saɓanin wanda ya yi
kokarin hura masu wutar komawa cikin duhun da suka tsira daga shi.
Ka yiwa kanka adalci ka fito daga rayuwar duhun da kake ciki domin a halin yanzu kai ne
babban kafiri na hakik.....
Kafin ya karasa Mai Martaba ya yi wata kara yan umartar Dakaranshi da su kama Farouq su kai
shi daƙin duhu.
"Za ka san wa ka kira da kafiri,za ka yi danasin kasancewar ka a duniyar nan ma gabadaya ba
kasar nan ba kuma zaka fadamun kai waye."
Yarima Rasheed ya karasa yana fadin,"Ba wanda ya isa ya hukunta shi don ya fadi gaskiyar
kuma kowanni Ɗa ba zai taɓa zuba idanu ana ciwa iyayensa mutunci ba."
Mai Martaba ya ce,"Ni ke da iko a wannan masarautar kowa na ciki wanda zai shigo da zai fita
karkashina yake,don haka ba wanda ya isa ya ja dani."
Yarima Rasheed ya daga hannu zai kaiwa Mai Martaba mari Baba Malam ya dakatar da shi da
fadin,"Aa a yanzu shi ke da karfin iko ka da ka jawa kanka matsala."
Wani irin kafirin Murmushi Mai Martaba ya yi yana fadin,"Ai da ka barshi, da ka barshi yau da
zaiyi bankwana da hannunshi."
Ya kalli Dakaran cikin dagun murya ya ce ,"Ku Dauke shi....
[01/07, 7:20 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-29
Haka suka cinciɓi Farouq tamkar wani daurin kaya,kai tsaye basu direshi a ko ina ba sai ɗakin
duhu,daƙin da ya kasance babu ko hanya bare alamun haske;babu abun da mutum yake iya
hanga sai dai duhu,buɗe ido da akasinsa duk ɗaya a wannan daƙin.
Bayan sun shigar da shi Hajiya Kaka ta kalli Mai Martaba ta ce,"Kar ka manta fa wannan Yaron
jinin kane,bai kamata ka aikata hakan ba."
"Ba jinina bane,domin ni ba zan haɗa jini da Kafirai ba,sannan in an bibiyama a yawon
banzansu aka samo shi."
Mai Martaba na faɗan hakan ya yi tafiyarsa.
Yarima Rasheed ya rike Hannun Hajiya Kaka kafin ya ce,"Kar ki damu Hajiya,ka da duk abun
da zai yi ya dameki domin ya aikata mafiyin hakan ma sannan na tabbatar da cewa bai isa ya
yiwa Farouq komai ba,duk abun da ya sameshi to sai dai in har ubangiji ne ya kudurta hakan."
Tsaki Kilishi ta yi ta ce,"Wa inda suke cikin addini na gaskiya kuma suke bin Ubangiji sune kadai
Ubangiji ya ke karesu amman wa inda suka dau wata hanyar daban kam ai sai kallo,ba su ma
fara ganin komai ba."
Wani irin mummunan kallo Abba Malik ya bita da shi yana fadin,"Ki san me zaina fitowa daga
bakinki domin ba da sa'o'inki kike ba."
Binsa da kallo ita ma tayi sama da ƙasa kafin ta ce,"Ina ji da kaina fiye da yadda kake ji da
kanka kuma da sannu zaka zam bawana anan zan ga ko akwai batun sa'anni."
Tana fadan hakan ita ma ta fice kai tsaye ta yi bangarenta.
Gabadaya ficewa suka yi jiki a sanyaye Janinah kuwa mai za ta yi ban da kuka,da gudu ta
karasa jikin Hajiya Kaka ta rungumeta tana,"Yah Farouq,mutuwa ake a dakin nan Hajiya Kaka
kisa a fito da shi,in ba haka ba wallahi mutuwa zaiyi,zai mutu."
Shafa bayanta Hajiya Kaka ta yi kafin ta ce mata,"Ba zai mutu ba In sha Allah Janinah ki yi
haƙuri. "
***Mai Martaba na shiga Part dinnan ya kira dakarai ya kara sheda masu cewa a sanya tsaro a
dakin duhun nan sannan ka da a bashi abinci ko da kuwa ruwa ne,duk wani guri da zai iya
samun sassauci ko na yin numfashine a ƙara rufewa domin yana so nan da kwana biyu zuwa
uku kawai ace ya mutu ne a cikin dakin yadda babu mai tuhumarsa sai dai ayi hakuri don dole.
Daga nan suna tafiya kuma ya kira Moli,a tattaunawarsu Moli ke sheda masa cewa ashe lokacin
da Mariam ta zo Nigeria ma tana dauke da cikin Farouq domin ba ta hanyar aure aka sameshi
ba sannan kuma Yarima Rasheed bai aureta ba har rana ita yau,hasali ma rabonsu da ganin
juna tun ranar da ta bar nigeria. Ya kara da cewa,"Na sha wuya matuka kafin na samo wa innan bayanan suma din sai da na
hada da aiki da Jinnun wajen Baba Malam,ka san su da taurin kai iya abun da na samu ke nan."
Kai da kawowa Mai Martaba ya fara yi kafin ya fara wata irin dariyar mugunta,"Oh ya tabbata
dai yaron ma Ɗan shege ne,ba a haifesa da aure ba amman har yake so ya yi takara dani,oh ta
zo ma gidan sauki ai kenan wannan mummunan fanten da ke kewaye da shi ma ai kadai ya isa
ya hana shi samun sarauta wannan ko da ma na barshi a raye ai rayuwarshi bata da wani
cikakken amfani Ɗan Shege har ya shiga gonata?"
Ya ci gaba da kyalkyale dariya.
Moli ne ya dakatar da shi yana,"Amman akwai matsala fa,akwai alamun allura na daf da tono
garma."
Take ya dakata da dariyar cikin damuwa ya ce,"Aa! allurar nan ba zata taɓa iya tono wannan
garmar ba, domin kuwa ramin da na binne mai zurfe ne kuma garmar tana da matukar kwari."
Jan Numfashi Moli ya yi kafin ya ce,"Hmm ina tabbatar maka da cewa ka yi kokarin kara rufe
wannan garmar da kyau."
Mai Martaba ya ce,"Na fahimci inda ka dosa,babu wannan matsalar shikenan na san me zan
yi."
Yarima Rasheed kuwa tunda suka bar Dakin Hajiya Kaka suna tare da Baba Malam,da Abba
Malik har ma da Javed domin hankalin Javed ya matukar tashi,shi babbar damuwarsa a san
yadda za ayi a fito da Farouq.
Suna ta tattaunawa,Yarima Rasheed ne ya dunga rarrashinsa kan cewa duk abun da ya faru
Ubangiji ne ya kudurta kuma hakan ne daidai.
Da haka suka rabu kowa ya je ya kwanta,Asalin Part din Yarima Rasheed da ke kulle Abba
Malik yasa aka bude masa suka shiga da ke ana yawan gyarawa babu datti baki anan suke
sauka.
Shi kuwa Farouq tunda aka sanya shi cikin dakin ban da adduoi babu abun da yake karantawa
hakan yasa tun yana jin firgici da tsaro har ya samu nutsuwa.
Sai a lokacin ya tuna da cewa rabonsa da abinci tun safe,hanjin cikinsa suka fara
cakudewa,suna har gitsewa tare da karo da juna.
Har dare ya yi bai ma sani ba,kuma ya kasa ko da runtsa ido ne tsabar yunwa.
Tsakiyan dare wajen karfe biyu ya jiyo sautin murya na masa magana.
"Yaah Farouq,ga abinci,ka karba ka ci." Daga jin muryar za ka fahimci cewa mai maganar ta
sha kuka kuma tana cikin yanayi na matukar damuwa.
Mamaki abun ya basa ya ce,"Janinah, ke ce?"
Cikin muryar kuka ta ce,"Eh."
Haske ta kunna tana miƙa masa dake ta saman ginin ta haura ta fasa wani ɓari.
Yana karɓa ta ji sautin takun mutane an fito da gudu ana kunna haske.
"Zai gudu......
[05/07, 8:37 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-30
Mannewa ta yi ta cikin wani lungu ta ɓuya,su ka gama haske-haskensu ba su ganta ba,hakan
yasa suka leƙa dakin suka hango shi zaune idanunshi a rufe,hakan yasa su ajiyar zuciya,Ɗaya
cikinsu ya ce,"Kila ma Mage ce ta wuce muka zata mutum ne."
"Da alama kam." Suka amsa da hakan kafin kowannensu ya ci gaba da tsayuwa inda
yake,daman barci ne ya ɗan kwashesu.
☆☆☆Gari ya waye
Misalin karfe Goma Yarima Rasheed ya fito daga bangarensa cikin shigar sarauta,kai tsaye
wajen Hajiya Kaka ya fara nuna ya gaidata tasa mi shi albarka kafin ya nufi fadar Mai
Martaba,Yana shiga ganinsa cikin yanayi na shigar sarauta ya firgita Mai Martaba ba tare da ya
ankare ba ya tashi yana sakin baki. Murmushi Yarima Rasheed ya yi ya ce,"Ka yi mamaki ko? Kadan ma ka gani,na zo in jadadda
maka cewa yadda kake da karfin iko a gidan nan haka nima nake da shi duk da cewa a yanzu
ka fini amman da sannu za ka dawo tafi kafafuna,kar ka damu batun tsare Ɗana da ka yi ba zan
ja da kai ba,domin ko ba komai kana matsayin uba ne gareshi sannan kuma shugabansa a
wannan masarauta,abun da nake so ka sani shine iko,mulki,izza da duk wasu dokokinka ba za
su taɓa aiki ko tasiri akaina ba,inma ka manta yanzu ka tuna ko da ace bani bane mafi
cancantar zamtowa Sarkin Al'adu to matsayin Ɗan Sarkin da nake ba za ka iya kawarwa
ba,bare ma dukka biyun suna nan kuma sun dawo."
Kasa furta komai Mai Martaba ya yi,shi ko Yareema Rasheed ya na gama faɗan abun da ke
ransa ya fice daga cikin fadar,Baba Malam da Manager suka bi biyansa,dukkanin Hadimai da
ma'aikata gidan suna ganinsa suka fara cincirindon durkusawa suna miƙa masa gaisuwa,bakin
gate kuwa tun kafin su ƙarasa aka yi gaggawar buɗewa ana rusuna masa. Har suka shiga mota suka fice daga gidan.
Kai tsaye gidan Hakimin Mokwa suka je wato mai wakiltar Sarkin Bida.
Sun yi gaisuwar mutunci,Baba Malam ya gabatar da Yarima Rasheed gareshi,ya ji dadin
ganinsa matuka kafin daga bisa suka wuce Bida.
Dake tun daren jiya Yarima Rasheed ya shirya zama da Sarkin ta hanyar tura masa saƙo kuma
ya aminta kasancewar daman yana yawan tura kayan tallafi ga mabuƙata zuwa ga
fadar,shiyasa ko da ya nemi ganin Sarki bai samu tsaiko ba.
Suna tafiya suna hira,motarsu na shiga cikin garin Bida Yarima Rasheed ya tamkar an caka
masa wani abu a tsakiyar kansa,wata irin ƙara ya sake yana dafa kansa can kuma sai ya fara
karanto,"Innalillahi wa inna illahir raji'un,Hasbunallahu wa ni'imal wakil."
Tsaida motar suka yi gefe duka suna tambayar ko lafiya ganin yadda lokaci guda jikinsa ya dau
zafi ga kuma wata irin zufa da ke keto masa.
Manager ya ce,"Sir ko dai za mu nemi asibiti mafi kusa ne?"
Girgiza masa kai ya yi alamar aa ya ci gaba da Adduoinsa can kuwa ya ji ya dawo daidai kafin
ya ce,"Mu tafi ba komai In sha Allah. "
Baba Malam kallonsa kawai ya yi yana murmushi ba tare da ya ce komai ba.
Masarautar suka nufa
Sai da aka kaisu wani ɗaki suka huta,suka ci abinci suka yi sallah kafin aka kai su Fadar Mai
Martaba.
Suna shiga idanun Mai Martaba akan Yarima Rasheed,Murmushi ya yi ya miƙa masa hannu
yana su gaisa yana faɗin,"Yarima Rasheed."
Girgiza kai Yarima Rasheed ya yi cikin yanayin mamaki ya ce,"Ka sanni kenan? Kai ba ka
manta dani ba Yallaɓai?."
Murmushi ya yi kara yi kafin ya ce,"Ko da ace za a iya yiwa kowa na garin niger katanga da
wasu lamura ai ban jin cewa za a iya yi mun,ina yaronka? fatan yana lafiya?"
Nan fa Yarima Rasheed ya ƙara rikicewa.
."Shi ma ka san shi ke nan? to taya?" Ya karasa maganar yana kallon Baba Malam.
Baba Malam ya ce,"Ka kwantar da hankalinka kamar ka manta gabanwa kake zaune? Sarkin
Bida ne ai babu wani abu daga gareshi na mamaki domin karfin ikonsa ya zarce tunanin
dukkanin mai tunani. "
Mai martaba ya yi murmushi kafin ya ce,"Na san Farouq Ɗanka ne,kuma na jima da zaman jiran
zuwansa domin shi ne kadai zai iya saita Sarautar gidan Al'adun mokwa ta dawo kan
tsari,aranar da na fara ganinshi aka tabbatar mun da cewa shine hakan yasa na dauki rawani
da ya kasance sak wanda mahaifinka ke sanya ma na ba shi,afakaice saƙo ne na bayar da ɗan
uwanka domin ya gyara zama kan cewa zalincinsa ya kusa zuwa karshe."
Yarima Rasheed ya ce,"Ka san da cewa Abdul-Raheem shi ne ya kashe mahaifinmu mai
martaba?"
Gyara zama ya yi kafin ya ce,"Babu shakka na sani."
"To amman ka yi shiru kuma?"
Yarima Rasheed ya faɗa.
"Ban da iko da karfin fitowa kai tsaye da batun duk da cewa zan iya daukan mataki da
kaina,amman aa,na tabbatar da cewa akwai wannan ranar kuma ita nake ta jira, Yaronka ya fi
mu dukka wannan karfin."
Mai Martaba ya faɗa.
Yarima Rasheed ya ce,"To amman kuma yanzu yana nan a kulle ya kulle shi a dakin duhu."
Mai Martaba ya girgiza kai,"Ba zai iya yi mishi komai ba,kasancewarsa a dakin duhu ko fitarsa
ba zai ragesa da komai ba sai dai ma ya kara fahimtar rayuwa da karfin iko, kuma zai fito cikin
lafiya In sha Allah."
Yarima Rasheed ya ce,"Allah yasa mu dace."
"Ameen,amman ni na jima da gano dacewarma,yanzu kawai ku koma sannan ku tanadi duk
wata hujja da kuke da ita,sannan kar ku bari ya fahimci komai a kowanni lokaci zan iya zuwa
daga yau zan shirya fara shirya komai domin duk da kasancewarsa ƙaramin matsubbaci akwai
bukatar shiri akansa,in ba hakan ba sai asamu matsala."
"Ma sha Allah mun gode kwarai sosai Ranka Yadade Allah ya kara girma da sutura."
Baba Malam ya fada.
Yarima Rasheed ya ce,"Allah ya kara tsawon kwana da lafiya mai albarka muna godiya kwarai."
Mai Martaba ya ce,"Kar ku damu,amman dai ku daina tafiya babu tsaro,yanzu ma zan baku
jami'in tsaro daya ya biku gwanda adunga kiyayewa domin Abdul-Raheem ya wuce duk inda
kuke zato."
Da haka suka yi sallama,ya sa aka basu jami'in tsaro daya ya shigar motar kafin suka dauki
hanyar komawa mokwa.
Suna isa gidan Baba Malam suka fara sauka,aka ajiyeshi sannan Yarima Rasheed yasa
manager da ya sa a kawo masu kayan abinci da duk wani abu da yake da bukata shi da
iyalansa, ya umarci jami'in tsaron da ya koma sannan shi kuma ya dau mota ya koma gidan
al'adu.
☆☆☆Mai Martaba ya Sarkin Al'adu ya kasa zaune ya kasa tsaye,
Kai da kawowa yake, ita ma Kilishi a bangarenta kai da kawowa take kawai.
Da ta kasa hakura afusace kawai ta shiga Bangaren Mai Martaba domin ya kasa zaman Fadar
tun da Yarima Rasheed ya zo ya fada masa maganganun nan ya gagara gane komai.
Tana shiga ta