Showing 57001 words to 60000 words out of 62597 words
Chapter 20 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
yi mata tsawa da fadin,"Hattara dai,ba ayiwa Mai Martaba
kakkausan lafazi."
Dakatar da shi ya yi da hannu yana,"Bar ta barta ta fadi dukkanin abun da ke ranta."
Ci gaba da magana Maah ta yi,"Irinka ne masu cirewa mutane kwaɗayin zama cikin
musulunci,irinka ne ke sawa adunga yi wa musulunci da musulmai mummunan zato da kallon
da bai dace ba,irin kane masu dasawa mutane shakku akan musulunci,da ace zuciyata ba ta
gama aminta da rayuwar musulunci akan shi ne rayuwar gaskiya ba da tuni ka jima da sawa in
koma ruwa,na tabbatar da cewa Allah na gani kuma yana ji ba zai taɓa barinka haka ba domin
shi ba azzalumin bawansa bane."
Dariya ya yi kafin ya ce,"Babu shakka na ji dadin zuwanki nan domin kema zaki shiga sahu,wa
innan jami'an tsaron kuma kun san sarai baku da ikon taɓani ka dakatar dani domin ina da mulki
a hannu har sai Mai Martaba sarkin bida ya amince don haka zaku iya tafiya ku barni in aiwatar
da muradaina ko kuma kuma ku shiga sahu."
Xavier ya ce,"In su yan nigeria ne ni ba dan nigeria bane sannan zan iya aiwatar da komai da
na yi akanka ba tare da an dakatar dani ba laifukanka suna da yawan gaske ya kamata ace a
yanzu kana kokarin nemawa kanka mafita ne."
"Mafita? Mafita? Ai indai Sarauta na hannuna to babu wata matsala da zan rasa mafitarta."
Karasa maganar ya yi yana yana gyara bindigar da ke hannunsa ta baya.
Karfe biyar in asuba kenan daidai.
Sautin kiɗan sanarwar zuwan Sarkin Bida ya jiyo wanda hakan ne yasa shi gaggawar jefar da
bindigar baya.
Sarkin Bida da tawagarsa tare da Hakimin Mokwa ne suka shiga gidan.
Mai Martaba na ganinsu ya fara kame-kame.
Da sauri yaje ya taro Mai Martaba yana fadin,"Ranka Ya dade barka da zuwa,lafiya? Da asubar
nan."
Murmushi ya yi kafin ya ce,"Lafiyar ke nan."
Ya karasa ya zauna sai da ya karewa kowa kallo kafin ya ce kalli Yarima Rasheed ya ce,"Wato
abun da ke faruwa ke nan?"
Kafin Yarima Rasheed ya amsa karaf Mai Martaba ya ce,"Ranka Yadade wallahi wasu yan ta
ad....
Kafin ya karasa ya dakatar da shi da hannu kafin ya ce,"Ku fara cire masa rawanin da ke
kansa."
Nan fa Mai Martaba ya kara ruɗewa sanyi ake amman shi zufa yake yana daga riga yana fiffita.
Sai da aka warware masa tas kafin Mai Martaba Sarkin Bida ya ce,"Daga yau kai ba sarkin
al'adu bane,kuma ba zaka kara kasancewa wani sarko ko mai sarauta ba domin kuwa ka riga
da aikata abun da zai rabaka da sarauta tun farko."
Abdul-Raheem ya ce,"Ranka Yadade ni ban aikata komai ba sai dai in sharri ake so ayi mini
kuma nasan wannan aikin Rasheed ne yana bakinciki dani tun muna yara kuma yanzu ma yana
so ya kwace mun sarauta."
Mai Martaba Sarkin Bida ya bada umarni aje a shigo da wani.
Aiko Abdul-Raheem na ganinsa ya razana bai san sanda ya furta ba,"Dr Imam."
Suna kallon kallo.
Murmushi Sarkin Bida ya yi kafin ya ce,"Yanzu ka gasgata abun da nake nufi ko? DR Imam ya
sheda mini komai yadda ya tallafa maka ku ka yi sanadin kashe Marigayi Mai Martaba Sarkin
Al'adu wato mahaifinka wanda a karshe ka bashi kudi mai yawa da sharadin zai bar nigeria
kuma hakan ne ya kasance,munyi bincike mun gano inda yake kuma ya kara tabbatar mana da
komai don haka baka cancanci zama sarki ba,daman asalin sarauta ta Abdul-Rasheed ce ka yi
masa kurciya Allah ya dawo da shi don haka shi zai amshi abunsa."
Kasa magana ya yi yana wani irin huci.
Yarima Rasheed ya ce,"Amman Mai Martaba ina neman wata alfarma ni daman ko ada cen
bana da sha'awar sarauta da ace baiyi saurin aikata hakan ba ma ni zan iya bar masa amman
yanzu in ba damuwa abarwa Farouq madadina."
Ka da bakin Abdul-Raheem ya ce,"SHEGEN? Wanda aka haifa ba ta aure ba?"
dukansu sai suka fara kallon-kallo......
*Yau har page biyu kuka samu,Gaskiya na ci kyauta *
*CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-35
Mai Martaba Sarkin Bida ya kalli Yarima Rasheed ya ce,"Hakane?"
Girgiza masa kai ya yi alamar E.
Numfasawa Sarkin Bida ya yi kafin ya ce,"To ka ga indai hakane kuwa Ɗanka bai da hurumin
gadon sarauta sai dai kai din ko kuma aba wani."
Khalil ne ya katse su da fadin,"Ranka Yadade ina so inyi magana in an bani dama duk da cewa
bana ɗaya daga cikin ahalin wannan gida."
Sarkin Bida ya ce,"Ba matsala Bismillah za ka iya magana."
Khalil ya ce,"Duk da kasancewar gadon sarauta ta haramta ga Farouq amman za a iya bashi
rikon kwarya na sati ɗaya ko ƙasa da hakan domin tabbatar da komai ya yi daidai daga nan in
ma mahaifinsan ne zai karɓa ko wani sai abada amman na tabbatar da cewa in dai Farouq ya
kasance a kujerar nan ko da na kwana ɗaya ne abubuwa da dama zasu setu."
Gyaɗa kai Sarkin Bida ya yi alamun ya ji dadin jawabin Khalil ka fin ya ce,"Babu shakka na ji
dadin hakan domin ko ni jikina ya jima da bani cewa shi kadai ne zai iya gyara gurɓacewar da
masarautar nan ta yi kuma ina goyon bayan hakan ya yi sarauta na sati ɗaya sannan bisa
adalci an bar masa zaɓin kan wanda ya dace domin ba don akasin da aka samu ba shi ne mafi
cancantar jogarar masarautar gabadaya."
Karaf Kilishi ta ce,"Haba Ranka Yadade nima fa ya kamata ayi mini adalci ga Ɗana nan Arham
shi ya fi kowa cancanta tunda dai nima jinin gidan ce ai sai adunga duban hakki kar a tauyewa
kowa."
Wani irin kallo Sarkin Bida ya bita da shi kafin ya ce,"Ki yi mini shiru kin taɓa ganin in da mace
ta gaji sarauta ne? Bare ke kanki ma mai laifi ce ina nan dawowa kanki ba wai kin ga anyi shiru
ba,ai ina sane da cewa komai tare kuke aikatawa."
Abdul-Raheem ya ce,"Kwarai kuwa Ranka Yadade wallahi da ita munafuka da ita muke shirya
komai."
Tsiru-tsiru Kilishi ta yi kafin ta ce,"Wallahi karya ne,ni dai na san akwai sa hananuna ayiwa
Rasheed Kurciya amman wallahi babu hanuna a kashe Marigayi Mai Martaba. "
Kuka Hajiya Kaka ta fara tana fadin,"Amman ku dai na yi asarar haihuwarku na yi dana sani kun
cutar dani kun cutar da zuciyata Abdul-Raheem saboda kawai abun duniya ka kashe
mahaifinka kuma kuka haɗa baki kuka cutar da Ɗan uwanka,Allah na tuba ka yafeni da laifin da
na yi ka bani wa innan 'Ya'Ya marasa tausayi."
Sarkin Bida ya ce,"Ki yi hakuri Hajiya Allah ya riga da ya kaddara hakan sai dai kawai su dinne
suka zam sanadi Kilishi indai Rasheed ya yafe mata shikenan shi ko Abdul-Raheem dole a
hukunta shi bisa ga kisan da ya yi."
Durkusawa Kilishi ta yi gaban Yarima Rasheed tana kuka,"Ya kai Ɗan Uwana ka yafe mun
wallahi Abdul-Raheem ne ya kwaɗaita mun son sarauta kan cewa in mun koraka wata duniyar
ni da shi zamuyi abun da muke so ka yafe mini Don Allah na tuba."
Murmushi Yarima Rasheed ya yi ya ce,"Ki tashi Allah ma muna yi masa laifi kuma yana yafe
mana."
Nan ta fara yi masa godiya domin tasan cewa indai aka ce za a hukuntata to kiyamarta ta tsaya.
Sarkin Bida ya ce,"Ba zan bar nan gurin ba har sai na naɗa Umar a matsayin Sarkin Al'adu na
sati guda don haka adauko mun rawanin da na bashi. "
Cikin hanzari Javed ya je ya dauko,take kuwa aka naɗawa Farouq rawanin yayin da duk wani
abu da ke rayuwa cikin gidan al'adu ya dawo karkashinsa.
Wani irin baƙin ciki ne ya tokare Abdul-Raheem a zuciya wanda ya kasa riƙewa take ya zama
tamkar zautacce sai wasu irin sambatu yake yi.
Sarkin Bida ya tambayi Farouq,"Shin kana da wata bukata da kake so ayi ma?"
Farouq ya ce,"Eh domin ina so kar atafi da Tsohon Mai Martaba a kasheshi inda hali abar mana
shi asanya shi a dakin tsaro ganin cewa ya riga da ya zauce wannan ma kadak wata ishara ce
da kuma hukuncin ubangiji. "
Jinjina kai Sarkin Bida ya yi kafin ya ce,"E to a hakikanin gaskiya dai babu hukuncin da ya dace
dashi a yanzu fiye da na kisa kamar yadda Allah ya umarta amman kuma kamar yadda kace kai
ma kasancewarsa zautacce sakaya ce ta Ubangiji,ba zan musa maka ba domin ko a hakan aka
barshi ya riga da ya gama yin asara don haka zaka iya ajiyeshi kamar yadda kake so."
Hakan kuwa akayi dakarai ne suka daukeshi suka sa shi dakin ajiya yanata sambatu da wasu
tsalle tsalle da kyar suka kulle kofar suka fito.
Mai Martaba Sarkin Bida ya gama miƙa ragamar komai a hannun Farouq kafin ya bar cikin
garin Mokwa.
Suna tafiya Farouq yasa aka kiya Wani babban Doctor ya zo duka ya dubasu aka wankewa wa
inda suka ji rauni gurin sannan aka yi masu allurau aka basu magunguna.
Zahra,Zeeyter,Zoe da Deejerh ne suka shiga gyaran gidan tsaf da kansu ko da Janinah ta ce
zata tayasu ƙi suka yi suka ce bata da lafiya, sai da suka gyara gidan tsaf ko ina ya yi kalkal
suka baɗe da turaren wuta.
Dakin Mai Martaba Abdul-Raheem Su Farouq suka nufa sai da suka cire dukkanin wani abu da
ya shafi tsafi suka zubar duk wani abu suna cirewa Abdul-Raheem yake ƙara ficewa a
hayyacinsa.
Tafiya Xavier ya yi kasancewar an fada masa cewa an fara gano wa inda suke zargi da kisan
Baba Malam da kuma binsu Farouq zasu kashe.
Jamaal,Junaid da Javed suna biye da su Farouq suma suna tayasu aikin.
Bayan sun kammala an seta komai Farouq ya kira meeting din gaggawa da duk wasu
ma'aikatan gidan ya faɗa masu sabon tsarinsa,sunji dadi matuka domin babu takura da tsanani
kamar irin na Abdul-Raheem hakan yasa kowa ya tashi yana cikin farinciki.
BAYAN KWANA UKU
Masu bincike nata bincike,Farouq ya gama seta komai da gyara komai da ke wakana a gidan
ya kira zama kan kowa ya faɗa in akwai abun da yake da muraɗi.
Javed ne ya fara magana kan cewa yana so ya auri Meemah yasan cewa ba a aminta da auren
wa inda ba jinin sarauta ba bai sani ba ko za a lamunce masa.
Tuni Farouq ya ce,"Wannan tsarin da ne,a yanzu kowa na da damar zabar matar da zai aure
muddin ta kamata don haka Abba Malik ya je ya nemo maka auren da kake so."
Javed ya yi farinciki da jin hakan sosai sai kuma Janinah ta ce,"Ayi hakuri kar aga kamar na yi
rashin kunya,amman na lura kamar an manta da batun nawa auren ko?"
Dariya suka yi duka.
Farouq ya ce,"Haba dai waye ma ya isa da mantawa da batun auren Kanwata,yanzu me
kikeso? Kuma wa kike so ki aura?"
Kunya ta ji ta rufe ido ta ce,"Uhumm Arham mana amman daman cen muna son junanmu kawai
tunanin su Auntu Kilishi da Mai Martaba ne yasa na ke ja baya kuma ni ina so ci gaba da
karatu. "
Farouq ya kalli Arham ya ce,"To Oga ka ji fa na san daman kai ma kana son abarka to amman
shin ka yarda da cewa zaka barta ta ci gaba da karatunta? Domin ni na jima da yi mata wannan
alƙawarin. "
Arham ya ce,"Ranka Yadade ai karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu zan
ji dadi nima in ta yi karatun don haka babu wata matsala ta bangarena."
Yarima Rasheed ne ya ce,"Ma sha Allah gaskiya na ji dadin hakan kunga yanzu ke nan muna
da shirin bukukkuna har biyu to saura kai ma babban Yaya a fito da mata ko."
Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Tukunna dai amman In sha Allah Very Soon."
Karaf Hajiya Kaka ta ce,"Aa fa ni baza amun kishiya ba ni kadai na isheshi ehee."
Dariya Farouq ya yi ya ce,"Yawwa shikenan ma fada masu yan matana."
Sun sha hira sosai tukun suka watse.
Dake bangare guda aka bawa 5stars Farouq na shiga ya tarar da Zoe zaune ta ƙura idanu
gaban tv tana kallon Dr.Zakir Naik yana lectures akan Rahamar da ke cikin musulunci.
Zama ya yi kusa da ita yana,"Ah Madam sannu da kallo."
"Welcome Sir,an gama zaman fadar ne?"
Ya gyaɗa mata kai.
Murmushi ta yi ta juyo tana kallonsa kamar zata yi magana kuma sai ta fara wasa da zoɓen da
ke hannunta da Farouq ya lura tana son yin magana sai ya juya shi ma yana kallonta suna
kallon kallo.
Daidai lokacin Zeeyter ta fito daga daƙi kenan ta gansu Murmushi ta yi tayi masu gyaran murya.
Suka ankare kafin ta koma ta kulle kofa.
Farouq ya ce,"Kamar kina son yin magana ne."
Girgiza kai ta yi alamar e sai ta kara da,"Amman ina jin nauyin fada saboda addininku."
Farouq ya ce,"Saboda Addininmu kuma? Aa ni dai yanzu fada muji."
Zoe ta ce,"Ina so in fada amman ina tsoro saboda ance wai ku musulmai kuna wulaƙanta mata
indai sune suka fara... sai kuma ta yi shiru.
Farouq ya ce,"ki faɗa mana,indai sune suka fara me?"
Sunkuyar da kai ta yi ta ce,"Suka fara cewa suna sonku kuma suna so ku auresu."
Farouq ya kalleta cikin ido kafin ya ce,"Kina Sona?"
Ta girgiza kai.
Murmushi ya yi ya gyara zama kafin ya ce,"Da farko dai ba haka bane abun da kika ji mutane
na faɗa kan cewa wai in mace ce ta fara cewa tana son namiji yana wulaƙantata domin mu a
addinin musulunci ma ana daraja mata sosai fiye da zatonki sannan ko Manzo Allah S.A.W
matarsa ta farko ita ta fara neman cewa ya aureta kin ga kuwa ba haram bane hasali ma tamkar
sunnah hakan yake garemu a karshe kuma ina miki albishir da cewa nima sonki kuma zan
aureki."
Don farinciki Zoe bata san lokacin da ta rugume Farouq ba ƙaƙam tana wani irin lumshe idanu.
Janye jikinsa ya yi yana,"Ki bari a Nigeria ba a cika haka ba fa yanzu sai a mana wata fassarar."
Dariya ta ce,"Oh Sorry amman da ni da nake so inyi kissing dinka ma."
Farouq ya ce,"wannan sai bayan aure."
Zoe ta ce,"Tom sannan kuma akwai abu na biyu Ina so in musulunta tun ba yau ba,kuma tun
da ka fara koyamun sallar nan kusan kullum sai na yi da dare amman matsalar shine ban iya
karatun ciki ba duk da cewa iya ba ina koyan wasu da adduoi kuma ina da Application din
Deen Body da kuma true ilm ina karuwa da su sosai"
Farouq ya ce,"Babu matsala,nine mijinki kuma nine malaminki zan koyar da ke komai kuma
anjima zamuje masallaci a musuluntar da ke,amman ina fatan ba za mu samu matsala agun
family dinki ba ko?"
Zoe ta ce,"Kasan babana da Maman sun mutu,Auntyna kuma bata da matsala sai dai na sanar
da ita ma kan cewa ina so in musulunta kuma in aureka,ta amince mun ita ce ma ta bani goyon
baya ta ce ita bazata hanani bin addinin da yafi kwanta mun arai ba kuma tana tare dani
akomai."
Farouq ya ce,"Ma sha Allah,amman ina so ki bani labarin dalilin da yasa kika ji cewa kina son
shiga musulunci."
Zoe ta gyara zama kafin ta ce,"Ina yawan bibiyar islaminc lectures a Deen Body da true Ilm
sannan na yi bincike akai sosai wanda na fahimci abubuwa masu yawa."
Ta tsawaita da maganar kafin ta ci gaba da fadin,"Musulunci shi ne addinin da ya koya mana
cewa rayuwa ba wai kawai duniya bace, amma wata hanya ce zuwa ga babban sakamako
Aljanna.
Kuma a Musulunci mace tana da matsayi na musamman sosai. Allah ya ɗaga matsayin uwa har
ya ce ‘Aljanna na karkashin ƙafafun iyaye mata.’ Kowane Musulmi yana ganin mace a matsayin
gata da amana, ba wani kayan wasa ko raini ba.
Kuma a duk lokacin da wani ke cikin damuwa ko tashin hankali, akwai adduoi masu yawa da
aka tanada da mutum na karantawa zai samu nutsuwa.
Musulunci ya koya cewa: ‘Kada ki taɓa ganin ke ba ki da amfani. Kina da daraja a idanun
mahallici, kuma yana so ki dawo gare Shi domin ya cika zuciyarki da natsuwa da