Showing 24001 words to 27000 words out of 62597 words
Chapter 9 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
dai ai ba ya fada mana sarauta ba mu da aka haifemu ciki."
Kilishi ta ce,"Sosai fa ni ba zan taba yarda da cewa shi jinin sarauta bane ma yanzu haka
tsafinsa ya yi kawai daman yan kasar wajen nan suma ance ba baya ba wajen tsafi musamman
su turawan nan."
Abba Malik ne ya yi gyaran murya kafin suka yi shiru
Su Mammah,Aunty Heedaya,Yah Jamal da Junaid tare da matansu duk suna gun ana cin abinci
ba masu jawabi da Kilishi da Janinah.
Meeting na gaggawa Sarkin Bida ya kira suka shiga kan lamarin Farouq.
Sarki ya ce,"Shin wane ne shi wannan din? Sannan a tawagar wa yake?"
Mai Martaba Sarkin Al'adu ya ce,"Ranka Ya dade, Gidana ya sauka a mokwa,Abokine ga Ɗan
wajena Javed sun wani program ne na koyarda dalibai marasa karfi da galihu kimiya a kyauta."
Mai Martaba ya numfasa ya ce,"Ma sha Allah ta kwana gidan sauki ai,hakan ya yi amman a kira
mun shi yaron naka ina so in masa wasu tambayoyi."
Sanyawa aka yi aka kira Javed aka masa tambayoyi akan Farouq duk ya sanar da su komai
kafin aka bashi izini ya fita.
Hakimin Mokwa mai wakiltar Sarki ya ce,"Lallai Ranka ya dade akwai lamari babba tattare da
wannan yaron bisa alamu kuma yana tare da manya domin kafin mu iso nan na yi kokarin
bincikar lamarinsa amman sam ba dama na gagara gano komai illa abu ɗaya da nake da
yaƙinin cewa zuwansa alkairi ne garemu a garin mokwa da ma jahar niger gabadaya ɗayan
bangaren kuma bana ce komai ba, amman babu shakka alkairi ne a tattare da shi."
Mai Martaba ya ce,"Tabbas nima na lura da hakan kuma na ji dadin hakan akwai iko da kudirar
ubangiji da yake tafe da bayyanarwa,sannan ga dukkan alamu shi kan shi bai san shi waye ba
don haka ina fatan kafin ya bar kasar nan ubangiji yasa mu amfanesa fiye da zatonmu sannan
ina bada umarnin cewa duk wani abu da yake da bukata abarshi ya aiwatar muddin bai saɓawa
tsari da dokokinmu ba,anyi biki wanda ba a taɓa yin irinsa ba kuma da kyar in akwai yiwuwar
samun ci gaba na gobe a yau komai za a karƙesa domin kuwa ruwan nan shine komai kuma
yana dauke da manufofi masu yawa."
Shi dai Sarkin Al'adun Mokwa yana jinsu amman aransa ji yake kamar ya fitar da Farouq ta karfi
a kasar ma gabadaya,tsantsar tsanar yaron yake ji har cikin rainsa.
Da haka suka tashi a zaman ana jinjina kasancewar Farouq bisa ga abubuwan al'ajabi da ya
faru.
Har cikin dare ruwa bai dauke ba kuma Farouq bai farka ba sannan Mai Martaba Sarkin Al'adu
bai iya barci ba,zagaye daki yake yana tafiya yana tunani karshe ya dauko wata kwarya yana
karanto wasu abubuwa yana juya hannunsa.
Wani abu ne ya fara hadewa yana yin mulmule,dariyar mugunta ya fara yana kara hadewa,can
kuma abun ya tarwatse.
Take ya firgice ya tashi tsaye yana wasu irin sambatu ,"Ya za ku mun haka? Ku barni inyi aikina
ku barniiiiiii bana son dakatarwa bana so na ce bana sooooo."
Ya karasa yana ajiyewa tare da kara daura hannunsa yana ci gaba da juyawa,kara fara
mulmulewa ya yi yana daf da hadewa ya kara tarwatsewa.
Dafe kansa ya yi yana sakin wani dogon tsaki.
"Wannan ba zai yi ba,babu shakka akwai wata kuma dole sai ya yiwu ba makawa."
Ya karasa yana kyalkyale dariya.
Hannunsa yasa ya bude yana tsaye wani irin haske ya fara fitowa.
Janyo hasken ya fara yi da hannunsa ya yazo tafi hannunsa kafin ya zuba shi cikin kwaryar da
ke gabansa.
Yana sawa hasken ya juye ya dawo wani irin abu shi ba mutum ba shi ba dabba ba,a tsaye
yake tamkar mutum amman da ƙahon doki da kuma kafar kufoto.
Dariya suka fara daga shi har mutum da ke ciki.
Cikin wata irin murya ya ce,"Kai har akwai wani abu zai razana ka? Hahhhhhhhh kar ka bani
kunya kar kace mun ba za ka iya ba,domin ba wanda ya isa ya ja da kai,sai dai wani bangare
amman ba dai bangarenmu ba sau dai mu razanar ba dai a razanar da mu ba, kuma sai dai mu
mu aiwatar yanzu haka ma na yi ture hahhhhhh."
Biye masa da dariyar Mai Martaba ya yi suna ta yi ba kakkautawa tamkar zararro.
Karfe uku daidai kamar an tsikare Farouq ya miki tsilif
[25/05, 3:29 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-15
Ji ya yi kansa yana wani irin sarawa tamkar ana zare masa wani abu,cikin kankanin lokaci kuma
ɗakin ya kaure da wani hamshakin baƙin hayaki.
Rike kan nasa ya yi sosai don ji ya yi tamkar kan na kokarin ficewa daga gangar jikinsa,cike da
karfin hali ya fara karanto adduar neman tsari da kariya "Allahumma inni a’udhu bika min zawāli
ni’matika, wa tahawwuli ‘āfiyatika, wa fuja’ati niqmatika, wa jamī’i saḫaṭika."
Yana cikin karantawa daidai lokacin da Maah ta idar da sallar walha karfe goma 10am na safe
kenan a cen malaysia.
Zama ta yi akan sallayarta tana yi masa addua ,"Allahumma inni as’aluka liwaladiyya khayra
hadhihi d-dunya wa khayra al-akhirah. Allahumma ihfazhu bi ‘aynika allati la tanam, waj‘alhu
min man tuhibbu wa tardha, wa wafqhu fī ‘ilmihi wa ‘amalihi, waj‘alhu min aṣ-ṣāliḥīn al-mufliḥīn,
wa qihish-sharra kullahu, dhāhirahu wa bāṭinahu, wa ij‘alhu min man yanshuru l-khayr. (Ya Allah, ina roƙonka alheri na duniya da alheri na lahira ga ɗana.
Ka tsare shi da idonka wanda baya bacci.
Ka sanya shi cikin waɗanda Kake so kuma Kake yarda da su.
Ka ba shi nasara cikin ilimi da aikatawa.
Ka sanya shi cikin masu gaskiya da masu rabauta.
Ka kare shi daga kowanne irin sharri, na fili da na ɓoye.
Ka sanya shi cikin waɗanda ke yada alheri)."
A hankali ya fara jin azabar na raguwa sannan hayaƙin da ya sarƙafeshi na washewa.
Ajiyar zuciya ya yi a zahiri yana faɗin,"Alhamdulillah."
Ya karasa faɗin ya tashi,Toilet ya nufa ya yi ya dauro alwala ya zo ya fara nafila,yana idarwa ya
yi karatun Qur'ani sannan ya kara jero adduoi a kan sallayar wani irin barci mai dauke da ni'ima
ya kwashe shi nan take a wajen.
Maah kuwa tunda ta zauna ta fara karanto masu adduoi sai da ta kwashe awa guda kafin ta
tashi.
Farouq kuwa sai sallar asuba ya farka,yana idar da sallar Maah ya fara kira.
"Fatan dai kana lafiya,na ji muryarka a sanyaye ko dai ka samu mahaifin naka ne,in dai da wata
matsala ka dawo gida ka ji,ni ina sonka,ban gaji da ganinka ba,ina son ka ci gaba da rayuwa,na
san cewa wa innan mutanen mugayene basa da imani sam a zuciyarsu,suna da son kan su fiye
da komai kuma.....
Katseta Farouq ya yi,"Maaah ina lafiya fa,kawai kewarki na yi na ji ina son jin muryarki kuma mu
nan yanzu muka idar da sallar asuba."
Maah ta ce,"Ai sai ka ce mun shagwaɓarka ce ta motsa,indai kana cikin koshin lafiya ai
shikenan Alhamdulillahi. "
Murmushi Farouq ya yi,"Umm indai adduarki na tare dani ai na san da cewa ba wani abu da zai
taɓa samuna sai dai in har yana cikin kaddarata kuma kasancewarsa cikin kaddarar tawa ma
adduarki zata iya sanyawa ya zo mun da sauki."
"Sosai kam Yaron kirki shiyasa kai ma nake maka tuni a kullum kan cewa kar kana wasa da
azkar domin wasa da azkar tamkar wasa da rayuwane."
Farouq ya yi dariya ,"Kin ga ko yaronki ba ya yi wasa da rayuwarsa ba."
"Ma sha Allah To Allah ya yi albarka ka ga yanzu bara inje in duba abin da zanci na lunch
yunwa nake ji."
Farouq ya taɓe baki,"Uhum to ba ki ce kina sona."
"Rigima kai kasan ba wanda nake so a duniya fiye da kai ai,Ina Sonka ina kaunarka kuma ina
kewarka,Ubangiji ya kara tsaremun kai a duk inda zaka kasance."
Cike da fara'a Farouq ya amsa,"Amin Maahnah Byebyee nima ina sonki."
Katse wayar suka yi duka suna dariya.
Ruwan sama fa a Bida bai da shirin daukewa har wannan lokacin hakan yasa ma yawanci a
masaukinsu sukai sallah sai daidaikunsu ne suka fita da lema zuwa masallacin.
Javed na zaune yana kallon Farouq har suka gama waya da Maah.
Ya ce,"Oga nikam kun burgeni kamar ba da mamanka ka ke waya ba,ji yadda kuke tsokanar
juna kuna dariya? Kodayake daman ku yan kasashen waje kuna da wannan wayewar."
Farouq ya ce,"Mahna ai ni ita ce Aboki kuma Ƙawata ta farko a rayuwa ko acen ma wasu gani
suke ni ƙaninta ne ba ɗanta ba ganin yadda muka shaƙu ta kan cemun in bata jani a jiki ba wa
zata ja? Ni kadai ne gareta kuma ta hakane kawai zata iya zame mun garkuwa yadda ba zan
taɓa shakkar fada mata damuwata ba."
Javed ya numfasa,"Hmm mu kam dai ai saidai gaisuwane kawai tsakaninmu da Mammah wai a
hakanma mu tana iya dan kulamu ni da Janinah sabanin Jamal da Junaid da suke manya bare
akai batun kuma Mai Martaba shi kam ai ba sai anyi magana. "
Murmushi Farouq ya yi ya tashi yana daga labule,"Wai har yanzu ruwan nan bai dauke ba?"
Javed ya bi bayansa,"Gashi kuwa kana gani,yauwa ni ka tuna mun ma,ruwan nan fa akwai
alamun cewa ta dalilinka ya sauko,shin kana da wata sarauta ne a bangaren dangin mahaifinka
ko mahaifiyarka?"
Farouq ya ce,"Ubangiji dai ya saukar da ni'imarsa, batun sarauta kuma Mahaifiyata ta taɓa
fadamun cewa mahaifina yana da sarauta sannan kuma ita ma mahaifinta na da sarauta
amman ni ba wani abu da na sani dangane da sarauta tunda ban taso ciki ba."
Javed ya kallesa cike da mamaki,"Ba ka taso ciki ba kamar ya?"
Murmushi Farouq ya yi,"Ba zaka gane komai ba a yanzu amman in lokaci ya yi zaka sani."
Shiru Javed ya yi ba don ya so hakan ba sai don ya lura cewa Farouq baya son zancen.
"Bara inje in karbo mana abun karyawa don na fara jin yunwa wallahi. " Javed ya fada.
Farouq ya ce,"Okay Food Master ka tuna mun da Abokina mijin kawata Haiydar.
Dariya Javed ya yi ya fita yana,"Ai abinci abin so ne."
Dukkaninsu a ɗaki suka wuni ranar Farouq ya riga ya bar system dinsa a hotel ba damar aiki
haka ya fita suka koma bangaren su Hajiya Kaka suka dunga hira.
Suna haɗa ido da kilishi ko Janinah sai dai su galla masa harara,shi kuwa da murmushi yake
binsu wanda hakan ke matukar baƙanta masu rai.
Yanata dannawa Hajiya Kaka kafa tana jin dadi tana bashi labarai.
"Rabon da akwana a wuni ana ruwa irin wannan tun zamanin da muke yan mata ban mantawa
kamar ranar da aka naɗa mai martaba Kakanku ne sarautar Sarkin Al'adu wato sai da aka
kwana biyu cur ana tsala wannan ruwa kuma shi ma a irin wannan lokacin fa da ba damuna ba
to sai kuma yanzu kusan shekara hamsin rata Allah shi kadai ya barwa kansa sani Kakata
lokacin ta fadamun cewa irin hakan na faruwane kawai yayinda wani abun al'ajabi ke daf da
shirin faruwa."
Cike da zolaya Farouq ya ce,"To kika sani ma ko abun al'ajabin na aurena da ke ne."
Dariya Hajiya Kaka ta yi ta ce,"Kuma fa hakanne."
Farouq zai yi magana kenan suka ji gyaran murya.
Mai Martaba Sarkin Al'adun mokwa ne......
[25/05, 3:29 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-16
Suna haɗa ido da Farouq ya yi saurin kawarwa shi kuwa Farouq ƙara kura masa idanun ya yi
yana kallonsa shi ksnshi ba tare da ya san dalilin haka ba.
Shi ko Mai Martaba sam yaƙi bari su haɗa ido.
Gaishesa Farouq ya yi.
Kansa na gefe ya amsa yana neman waje ya zauna, bayan sauran sun gama gaidashi ya gaida
Hajiya Kaka ya ce ,"Ina ganin ku kasance cikin shiri zamu koma gida domin an kammala
wannan bikin da saukar ruwan nan,in Allah yasa ya dauke zuwa gobe za mu wuce mokwa da
sassafe."
Hajiya kaka ta ce,"Ni ko ina sai munyi mako guda, ka san fa ina son zaman bida sosai."
Cikin tsawaita magana Mai Martaba ya ce,"A wannan yanayin ba zamu iya zama ba,ina da
muhimman abubuwan da ya kamata in gudunar a gida."
Yana gama maganar ya tashi ya fice ba tare da sauraron kowa ba.
Dare ya yi an kawo masu abinci sai da suka ci kafin Javed da Farouq suka koma Dakinsu.
Farouq ya ce,"Ji nake a takure fa,ina bukatar System dita gaskiya i have alot of work to
cover,anya zan iya hak'uri daren yau kuwa? Gaskiya zan fita."
Javed ya ce,"Oga da dai ka yi hakuri wannan ruwan ka ga har yanzu da dan saura tunda ya
fara raguwa da ka bari zuwa safiya kila ya dauke duka sai muje ka dauko kafin mu wuce
mokwa."
Farouq ya ce,"Ai inna tafi acen zan zauna ka ga daman ba tare zamu tafi ba inna kammala
abun da zanyi zanzo daga baya nima. "
Javed ya ce,"Ina? Ai umarni daga sama gun Mai Martaba babba ya ce tare zamu koma domin
an sanar da shi cewa kai bakon mune."
Farouq ya kalleshi,"Koma yane dai ni ina bukatar System dina a daren nan akwai bayanan da
ya kamata in shigar."
"Alright yanzu mu je hotel din in rakaka ka dauko sai mu dawo tare barain samo mana rigar
ruwa incase."
Hakan ne ya kasance suka tafi tare Farouq ya dauko System dinsa da sauran kayan kafin su ka
koma cikin masarautar Bida.
Suna komawa kuwa ajiyar numfasa Farouq ya yi yana cire rigar ladan ruwan da suka sa.
"Ma sha Allah jin System dinnan nake tamkar wani bangare na rayuwata,kodayake kundin
rayuwar tawa ma dukka ai yana ciki."
Dariya Javed ya yi,"Lallai kam ai na ga alamu kai computer ka sai Allah. "
Zama ya yi ya bude ya shiga fara dube-dube da aikinsa,kari gani ya yi lallai an kara kokarin
kaiwa na'urar tasa hari,Security Alert ya bayyana kan cewa System din na kokarin fuskar
hacking abun da ya kara bashi mamaki shi ne da ya duba location din ya kara nuna masa nan
masarautar ta bida kamar yadda ya nuna masa masarautar mokwa lokacin da suke cen. "Ke nan koma wane ne yana tare dani anan ma,to wane ne ya ke bibiyata haka? Me yake son
sani? Alamu ya nuna akwai wanda ya san shirina ke nan? Lallai akwai bukatar na yi taka
tsantsan domin gano ainihin abun da nake son ganowa kafin in kai ga matakin karshe ga
dukkan alamu akwai mai son kawo mini tsaiko,to amman ai bana jin cewa akwai wanda ya
fahimci inda na dosa."
Ya karasa faɗa aransa ya yin da ya tashi tsaye yana kaiwa da kawowa,a lokacin shi kam Javed
ya jima da lulawa duniyar barci.
Farouq ya numfasa kafin ya ce,"Whatever na san ba za a taba iya samun abun da ake nema
ba,amman babbar matsalata shi ne insa wake yin wannan kokarin sannan kuma mene ne dalilin
hakan? Ko ma ta yane dai dole