Showing 15001 words to 18000 words out of 62597 words
Chapter 6 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
gwiwa irin ta yau ba,na gode sosai Oga ashe kai fa
ka shahara ta ko wanni fanni daga yau za a fara wasan In sha Allah. "
Farouq ya ce,"Yawwa wai Janinah bata School ne na kullum tana gida."
Javed ya ce,"Eheen ai a ƙa'idar gidan Maza ne kadai ke da ikon yin karatun jami'a mace na
gama sakandari aure ake yi mata kawai ita ma yanzu Arham kawai take jira ya kammala
digirinsa sai ayi masu aure amman ta samu ta yi School dinnan ta samu training akan computer
shi ma hakan sai da Abba Malik yasa baki da kyar Mai martaba ya amince shi ma na wata uku
kacal ta yi acewarsa karatun ba wani amfani zai mata ba domin a gida zata zauna ta haihu ta
kula da yaranta."
Farouq ya ce,"Huh Abubuwan da yawa ashe amman kuma shekararta nawa ne ma wai?"
Javed ya ce,"wannan shekarar zata cika 17."
"Ikon Allah baya karewa,amman ko da an bari ita ma ta dan kara karatun zai fi ko da bangaren
computer dinne anan ko shekara ta yi."
Farouq ya fada.
Murmushi Javed ya yi ya ce,"Hmm ba ka san gidanmu bane har yanzu."
Alamar shigowar kira Farouq ya gani.
Yana dubawa ya ga Zoe ce murmushi ya sake a zahiri kafin ya dauki wayar.
"Our Own pilot yau an tuna dani ke nan."
Gajeran tsaki Zoe ta yi kafin ta ce,"Ba wani nan,wato kana Nigeria ba labari sai da mu ka yi
magana da Khalil ya ke shedamun kana Nigeria ."
Farouq ya ce,"Eh wallahi a lokacin i try to reach you but bana samun ki seems you're off and
ban san wani da zan iya tuntuɓa ba."
Zoe ta ce,"Oh Yeah I have been bedridden for two weeks So wayoyina duk suna kashe."
"Subhanallah yanzu ya jikin to? Fatan dai ya yi sauki."
Cewar Farouq.
Zoe ta ce,"Eh har ma na koma kan aiki."
Farouq ya ce,"Ma sha Allah yanzu yaushe zamu hadu? Zaki shigo ta Nigeria ne?"
Zoe ta ce,"E to bana ce ba amman zan duba jadawalina daman ina so ka dan seta mun wani
abu a system dina amman dai za muyi magana zuwa dare ma I will chat u."
Farouq ya ce,"Okay Byee."
Javed na kallonsa tunda ya fara wayar har ya gama.
"Oga ko dai Madam ce wannan irin shauki tunda ka ga kiran fa kaketa murmushi har yanzu."
Farouq na dariya ya ce,"Nop wannan kawatace fa ai ni ban da Madam duk wacce ta nuna tana
yina kawai binta na ke."
Javed ya ce,"Kowa darling kenan amman ni dai duk da haka wannan fa kila ta dabance."
Murmushi kawai Farouq ya yi ba tare da ya ce masa komai ba.
[14/05, 12:35 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-10
Suna tashi zasu tafi gida kamar yadda Farouq ya faɗa bai fasa ba sai da ya yi wa Hajiya Kaka
siyayyar ta, har da shawarman kuwa sannan suka tafi.
Suna zuwa ya bata, sosai ta ji daɗi ta karɓa tare da saka masa albarka har ma da ɗan taka
rawar ta daga zaune.
Sun sha hira sosai don a part ɗin nata ma suka ci abinci, suna cikin cin abincin ta ke cewa.
"Bikin Sallar Gani fa ya zo, muna daf da tafiya Bida, don an fara shirye-shiryen tafiyar, ka ga
idan na tafi zan yi kewar ka domin muna yin kusan sati a can. "
Da mamaki ya ce. "Mene kuma bikin sallar gan
Hajiya Kaka ta ce. "Biki ne na Al'ada da ake shiryawa kowacce shekara acn gidan Baban Mai
martaba da ke Bida, dukkanin mu za mu tafi can har sai an kammala shagalin kafin mu dawo
nan mu yi namu."
Farouq ya ce. "Ai ko nima zan je don ina son ganin al'adunku na gargajiya sosai abubuwan
suna birge ni."
Haɗa ido Javed da Hajiya kaka suka yi domin sun tuna cewa Mai Martaba ya haramta masa
kasancewa a cikin su a koma mene ne.
Gudun ka da maganar ta ja Javed ya yi saurin katsewa tare da faɗin. "Oga dare fa ya yi
maganarku kai da matar nan taka ba karewa za ta yi ba, kawai ka zo mu tafi Please. "
Dariya Hajiya Kaka ta yi ta ce. "Kai dai ka faɗi gaskiya kishi kake ya zo ya ƙwace maka mata, yo
kai ma da za ka riƙa shigowa da baƙar leda ai da mun sasanta ko da rabin igiya ɗaya ne in
barma."
Dariya suka yi Farouq ya tashi yana. "Na jima da fahimtar sa ai, karki damu 'yan matana ni
kaɗai ma na ishe ki."
Dariya suka yi duka kafin nan suka yi mata sallama suka fice.
Suna zuwa ɓangaren Javed suka baje a falo.
Farouq ya ce. "Yawwa gobe Sunday za mu fita yawo dai in ga gari ko? Mussamman river niger,
ina so na gane wa idona, na ji an ce Mungo Park ne ya fara gano rafin ko?'
"A'a Gaskiya, asalin waɗanda suka fara gano rafin Richard Leander ce da kuma John Leander
kwai dai..."
Kafin Javed ya ƙarasa magana wayarsa ta yi ƙara, yana dubawa ya ga kiran mai Martaba ne ke
kiransa.
Tashi ya yi da sauri ya na. "Mai Martaba ne ya ke kira na, bari na je na ji."
Ya ƙarasa maganar yana amsa wayar tare da ficewa.
Numfasawa Farouq ya yi a zahiri ya ce. "Bikin Sallar Gani, tabbas duk yadda za a yi sai na
kasance a wannan shagalin, zan iya samun wani bayanin na san."
Ya kai ƙarshen maganar yana ɗaga kai sama.
Kamar wanda aka tsikara ya miƙe tare da shigewa bedroom, waya ya fara yi wanda ba mai jiyo
abin da ya ke fadi daga shi sai wa inda yake wayar da su, ya kwashe kusan awa guda yana
wayar kafin ya katse ya koma kan System.
♡♡♡♡♡
Ƙarfe huɗu na yamma dukkanin su sun yi wanka sun shirya, sun yi kyau matuƙa.
Farouq sanye yake da ƙananun kaya kamar yadda ya saba saka wa, yayin da Javed ya shirya
cikin manyan kaya domin ba sosai mai martaba ya ke son ganinsu sun yi shigar ƙananun kaya
ba.
Kai tsaye River Niger suka nufa.
Javed ne ke driving din su suna tafe suna hira har suka isa.
Cike da mamaki Farouq da ya ga wasu manyan motoci na tafiya ya ce. "To su kuma waɗannan
manyan motocin fa?"
Ya yi magana tare da kallon Javed.
"Suna dawowa daga gabas da kuma kudu ne, don nan din shi ya zama kamar meeting point
ɗin su, don ko lokacin da ka turo taimakon nan da na baka labari, ai a nan aka yi hatsarin.
Da yake yawanci 'yan cirani suna ƙyashin biyan kuɗin mota, shi ne suke raɓuwa gefen manyan
motocin da ke ɗauko mai (petrol) wanda ƙarshe duk kusan a nan suke rasa rayukansu, babban
abun takaicin kuma 'yan road safety ɗin maimakon su kula su riƙa hanawa, to da an basu ɗan
cin hanci shikenan bakinsu ya yi shiru."
"Lallai suna wasa da rayukansu sosai, Allah ya kyauta! Gashi kuma hanyar na bukatar gyara
sosai." Farooq ya faɗa cikin sassanyar muryar jimami.
Kallon sa Javed ya yi kafin ya ce. "Sauƙin ta ma yanzu an dawo da tollgate, ka san shi yana
taimakawa sosai da kuɗin harajin da suke bayarwa, ana amfani da shi wajen gyaran titin da
tabbatuwar hanya bisa tsari har ma da tattalin arziki."
Kasancewar babu nisa sosai ba su jima ba suka isa.
Suna zuwa wajen kuwa Farouq ya ce. "Ya Subhanallahi! Ai kogin ya fi kyau ma a zahiri fiye da
yadda ake Misalta shi da kuma hotunansa da ake ɗauka."
Javed ya ce. "Haka ne kam to ka ga wannan shine kogin Nijar yana da matukar muhimmanci ga
rayuwar dukkanin al'ummar Jihar Niger da Nigeria da ma tarihin yankin, a matsayin jigo. Kogin
yana da tasiri sosai a cikin al'adunmu, yana bayar da gudummawa wajen ci gaban tattalin arziki
ta fannin noman hatsi da kuma kamun kifaye. Wannan yana nuna cewa kogin ba kawai wani
jigon ruwa ba ne, har ma yana da tasiri a cikin rayuwar yau da kullum na al'ummomin da ke
zaune a gefensa.
Batun Mungo Park kuma yana daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi binciken Kogin
Nijar. Mungo Park ya kasance ɗaya daga cikin masu bincike da suka bayar da gudummawa
wajen gano ingancin kogin da alfanunsa, amman ba shi ne farkon wanda ya fara ganowa ba
Richard Leander da John Leander suna daga cikin waɗanda suka yi fice wajen bincike da
nazarin kogin, suna bayar da muhimman bayanai game da tasirin kogin a cikin al'umma kuma
sune wa inda suka fara gano kogin.
Dukansu, Richard da John Leander, an binne su a kusa da kogin don nuna girmamawa da
ƙoƙarin su wajen tabbatar da ingancin kogin da kuma alfanunsa ga al'umma. Wannan yana
nuna yadda kogin ya zama wani muhimmin ɓangare na tarihin al'ummar Niger, tare da bayar da
gudummawa ga al'adun gargajiya da zamantakewar al'umma.
Sarakuna da Al'ummomi baya ga Richard da John Leander, akwai sarakuna da sauran
al'ummomi da suka yi fice a cikin tarihin kogin. Waɗannan mutane sun taka rawa wajen tabbatar
da cewa kogin yana ci gaba da zama jigon rayuwa da al'adu a yankin. Kogin Nijar yana da
matukar tasiri a cikin al'ummomin da ke kewaye da shi, yana zama tushen rayuwa da ci gaban
al'umma.
A taƙaice, Kogin Nijar yana da matukar muhimmanci ga al'ummar Jihar Niger , yana bayar da
gudummawa ga al'adunmu da ci gaban tattalin arziki, tare da kasancewa jigo a cikin tarihinmu."
Farouq ya ce,"Maddalla! Amman ya nake ganin kamar electric power Station?" ya faɗa yana
ƙarasawa ta wajen.
Dariya Javed ya yi kafin ya ce.
"Ah lallai kana wasa da mu ,ba ka san cewa mu ke da tushen wutar lantarki ba? Mu ke bawa
Nigeria kaf wutar lantarki, mu ke da electricity Hydro Electric power station kenan yana samar
da wurar lantarki da ya kai 760 megawatts (MW) wanda ya taimaka wajen samar da wutar a
ƙasar nan tun cikin shekarun da aka gina ta a 1960s sannan tana da matakai biyu na bada
wuta da kuma tasiri wajen rage katsewar wutar a Nigeria."
Farouq ya ce,"Ni na isa inyi wasa da ku ni fa son garin nan na ku kara shigata yake a kullum
wallahi."
Suka ci gaba da magana suna tafiya.
Wasu mata suka gani sunata wanke ƙasa akan carpet.
Farouq ya ƙarasa gabansu da sauri yana,"Wannan fa me suke yi?"
Kafin Javed ya yi magana ɗaya daga cikin matan ne ta ɗaga kai ta kalli Farouq ta ce. "Zinare
muke cirewa." Ta karasa maganar tana nuna masa yadda suke amfani da chemical suna
cirewa.
Bude baki Farouq ya yi yama rasa abun cewa sai.
"Wow!"
Muryarta ta katse masa mamakin nasa ya ji ta na faɗin. "Ka ga yadda a ke gasawa ma."
Ta faɗa tana sakawa a abun gashin kafin ta ce. "A can sama kuma akwai inda ake narkawa in
kana so za mu je in nuna maka."
Javed ya katse su da fadin,"Aa ba mu da ishasshen lokacin yammata, ya kamata mu koma
gida ai dai ka ga wannan ka kara yarda mu ɗin mu ne."
Farouq ya ce. "Gaskiya kam wannan lamuran naku ko ƙasashen waje albarka."
Godiya suka yiwa matan Farouq ya yi masu kyautar kudi kafin suka juya Javed ya ce. "Ai ko
gonar Mai Martaba akwai wa inda suka zo suka ce sunga zinare amman ya hana su sam har
cewa suka yi ko nawa ne zai saida zasu iya siya amma ya ƙi amincewa wai gonar gadonsu ce."
"Amman ko da Mai Martaba ya sa ana yi masa aikin ya buɗe ƙaramin kamfani karkashinsa da
za a samu alfanu sosai, don wannan babbar dama ce domin haɓaka arziƙin gidan." Farouq ya
faɗa
Javed ya ce.
"To ka san shi da kafiya da tsayawa a kan batunsa, 'yan uwansa ma basu isa su ce ba bare
kuma mu, lamarin mai martaba sai dai kallo."
Da wannan hirar suka shiga mota, suna cikin tafiya motar ta samu matsala ta tsaya ga dare ya
yi gashi gari ya haɗe da hadari kan kace miye ruwa ya kece kamar da bakin ƙwarya.
Ganin ruwan bai da shirin tsayawa ga shi dare ya yi haka dukkaninsu suka fita a motar domin
nemo bakanike,
sunyi neman duniya sun rasa saboda ruwa kowa ya tafi gida kuma dama dare ya yi gashi ba a
wajen da mutane su ke wulgawa sosai suke ba.
Can tunanin Zeeyter ne yazowa Farouq ya kirata ya faɗa mata abun da ke faruwa.
Ta kirashi video call ita da Haiydar suka ga yanayin motar, da yake Allah ya taimaka Javed na
dauke da box ɗin kayan gyara a motar, nan Zeeyter ta saka yi ɗauko tana faɗa masa abun da
zai yi shi ma Haiydar na taimaka masu har suka samu suka gyara motar da ƙyar.
Sai wajen ƙarfe ɗayan dare kafin suka koma Gidan Sarkin Al'adu, suna shiga Javed ya kalli
agogon hannunsa zuciyarsa ta yi wani irin mummunan faduwa domin ya san a ƙa'idar gidan ba
a wuce karfe goma a waje gashi yau shine har ƙarfe ɗaya, sosai jikinsa ya yi sanyi mussamman
da ya hango wuta a falon Mai Martaba. Yana gama Parking suka fitowa gabaɗaya a jiƙe ruwa na bin jikinsu.
Ɗaya daga cikin dogaran Mai Martaba ne ya ƙaraso garesu da sauri yana faɗin.
"Ranka Ya Dade Mai Martaba da Jama'ar gida suna jiranku a babban falo."
Kallon Farouq ya yi cikin dauriya da ƙarfin hali ya ce. "Oga kai ka tafi ɗaki sai na...
Kafin ya karasa dogarin ya katse shi da faɗin. "A'a ai ance dukkaninku ake son gani Ranka
yaɗaɗe."
Nan fa zuciyar Javed ta fara bugawa cikin sauri.
Muryarsa na rawa ya amsa da ,"Okay." Kallon Farouq ya yi yana ,"Mu je Oga."
Suna shiga suka ga Mai Martaba tsaye,Hajiya Kaka,Mammah,Kilishi,Abba Malik,Janinah da
kowa.
Kafin Javed ya ankare sai jin saukar mari ya yi a kumatunsa.
[17/05, 5:28 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAGE-11
Zai kara masa wani da sauri Abba Malik ya tare gaban Javed yana,"Ayi masa afwa Yaya."
Dakatar da shi ya yi da hannu alamun ya matsa ba ruwansa.
Matsawa gefe Abba Malik ya yi yana kallon ikon Allah.
Mai Martaba ya kalli Javed cike da tuhuwa ya fara jera masa tambayoyi,"Ba ka da hankali ne?
na ce ba ka da hankali ne? ko kuwa ka samu taɓuwar hankalin da ya mantar da kai cewa kai
ahalin wannan gidan ne?"
Javed bai iya cewa komai kansa na ƙasa.
Cikin dagun Murya Mai Martaba ya ce,"Za ka bani amsa ko kuwa?"
Cike da firgici Javed ya durkusar da gwiwarsa ƙasa yana,"Ayi mini afwa Mai Martaba akasi aka
samu motata ta lalace a hanya." Ya faɗa muryarsa na rawa.
Mai Martaba ya ce,"Amman ka fi kowa sanin doka da tsarin wannan masarautar ko? Daga Yan
Uwana har Yayunka da na haifa babu wanda ya