Showing 3001 words to 6000 words out of 62597 words

Chapter 2 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf

24 Jul 2025

2372

daga shugabbanin har sarakun nan."

"Ma sha Allah yanzu wani hotel din zaka kaini?"
Javed ya ce,"Hotel kuma? Haba dai ai a gidanmu zaka zauna har ma na sanar an shirya
tarbarka."

Farouq ya ce,"anya ni dai ban cika son takurawa mutane ba."
Javed ya yi murmushi,"ba takura bane ai kasa aranka gidanmu tamkar na ka kaima haka kuma
nima duk sanda zan je Malaysia zan dauka kamar a gidanmu nake."
Murmushi shi ma Farouq ya yi ya ce,"Shikenan na gode Allah ya bar zumunci."

Daidai wani gatafaren gidan saurauta suka tsaya ana kokarin bude masu.
Tun daga wajen gidan za asan cewa zai amsa cikakken kowani suna da gidan sarauta ke
amsawa.

Farouq yana daga kanshi sama yaga an rubuta shedar MASARAUTAR SARKIN AL'ADU ma
sha Allah ya furta a zahiri ya yin da aka bude masu gate din.
Janinah na hango motar Javed ta fito da sauri tana jira ya karasa parking ta masa magana.
Yana fitowa kuwa ya yi saurin komawa bangaren da Farouq yake ya bude masa kofa.....
[04/05, 10:15 pm] Xayyeesherthul-humaerath🍂: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! 😊
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! 🚚*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-3

Janinah na kokarin tawowa inda suke Farouq na fitowa daga cikin motar.

Kansa na kasa ita kuma tana kallon wayarta da kira ya shigo ciki.
Da saura ta dauka tana fadin,"Mammah Mi da nan (ina nan),Okay to me bedabo (gani nan
zuwa)."
Ta karasa maganar tana juyawa cikin sauri.
Farouq ya karewa gidan kallo kafin ya kalli Javed ya ce,"Ma sha Allah nidai tunda nazo ina ta
cin karo abubuwan ban mamaki da sha'awa ban da mara kunyar yarinyar da na ci karo da ita
ban ga wani abun rashin jin dadi ba a garin nan mussamman cikin mokwa ni anya ni ba zan
nemi waje inyi gini ba kuwa ina zuwa ina dan hutawa." Dariya Javed ya yi ya ce,"aiko da na ji dadi abokina dan malaysia garinmu ya birgesa ya yi
gida."
Farouq ya ce ,"aikuwa dai na ji inaso gaskiya. "

"Ubangiji ya tabbatar mana,yanzu mu shiga ciki ko?" Javed ya fada.
Wani irin faduwar gaba Farouq ya ji zuciyarsa na bugawa cikin sauri sauri.
Nemawa kansa nutsuwa ya yi cikin ransa ya fara karanto,
"Allahumma inni a'uzu bika min al-khwaf."
Ajiyar zuciya ya yi na karfin hali kafin ya amsawa Javed da ,"Okay mu je."
Daidai kofar da zasu shiga fadar Sarkin Al'adu suka ci karo da wani dattijo.
,"Ah Javed bakon naka har ya iso ne?"
Javed ya amsa da murmushi,"Eh wallahi Abba."
Dagowan da Farouq zaiyi suka haÉ—a ido da Abba wata irin yanayi dukanninsu suka shiga
wanda basu san dalili ba kallon kallo suka tsaya yiwa juna na tsawon second talatin Farouq ne
ya yi karfin halin kashe shirun da fadin,"Barka da warka Abba ina wuni fatan mun sameku
lafiya."
Murmushi Abba ya yi kafin ya ce,"lafiya lau,Alhamdulillahi barkanka da zuwa,Allah ya yi albarka
ko."
Farouq da Javed suka amsa da Amin.
Abba ya wuce yana fadin,"ina da meeting bara inje sai na dawo ma yi hira."
Ya karasa maganar yana fita da sauri.

Javed ya ce,"wannan shine Alhaji Abdulmalik wanda yake kanin mahaifina mutum mai kirki da
son mutane dan gaye ajin farko duk da kasancewar yana rayuwa cikin gidan sarauta kuma
yana da gadon sarauta hakan sam bai dameshi ba,hasalima yafi son sanya kananun kaya fiye
da manya kamar yadda ka ganshi a yanzu,yana nuna mana soyayya da kauna fiye da zato
wanda in ba an fada ba kai kace shine mahaifinmu mussamman bangaren karatu duk wanda
zai taso cikin wannan gidan sai ya yi iya bakin kokarin wajen tabbatar da cewa ya samu
ingataccen ilimi kuma shi Allah bai bashi haihuwa ba har yanzu kuma baya taɓa nuna

damuwarsa ga hakan ya kan ce ai gamu mun ishesa."

Farouq ya yi murmushi kafin ya ce,"aiko gashi tamkar sabon saurayi baya tsufa. "
Javed ya yi dariya,"ina zai tsufa kullum mutum na cikin ado har yanzu mata rububi suke akansa
a yadda aka bamu labari tun yana matashin saurayi mata ke binsa kuma har yanzu ma basu
daina ba yana da farin jini sosai don ko ni da nake matashin saurayi Abba Malik yafi ni kwarjini
da farin jini agun yan mata."
Dariya Farouq ya yi.
Suna ci gaba da shiga cikin fadar suna ci gaba da tattaunawa har suka shiga inda sarkin al'adu
yake.
Shigarsu dakin tun kafin Sarki ya dago jikinsa ya bashi wata alama da ya gagara fahimta
aranshi dai yasan cewa dole wani babban al'amari ne yake shirin faruwa ko kuma ya riga ya
faru.
Durkusawa duka suka yi suka gaisar da shi.
Ya amsa cikin izza da isa irin ta sarauta idanunsa na kan Farouq duk da cewa javed ya sanar
da shi cewa daga malaysia bakon nasa zai zo.
Har sai da suka fice idanunsa suka bar kan Farouq aran mai martaba ya fadin,"gashi da
yanayin turawa amman babu shakka jikinsa akwai jinin sarauta duk yadda akayi acen
malaysian ma suna da sarauta."

Suna fita Javed Ya ce,"shi kuma wannan shi ne mahaifina Alhaji Abdul-Raheem wanda yake
shine Sarkin Al'adu na garin mokwa kuma ya gaji sarautar ne tun daga wajen kakanninmu shi
mutum ne da bai da sakewa da mutane kuma mai tsaurarran ra ayi da kafiya inya furta abu
baya so aja da shi ko kadan baya wasa da al'adu sannan yana da kokarin kiyaye duk wani
mutunci da martabar wannan gida duk wanda ya yi kokarin kawo tsaiko cikinsa ko waye shi sai
ya yi kokarin dakilewa domin ya kan ce martaba da kimar gidan nan tana da mahimmanci a
gareshi tamkar rayuwarsa zai iya rabuwa da kowa kuma zai iya ɓatawa da kowa akan martaba
da kimar gidan nan in kana neman asali kuma cikakken dan gargajiya to ka samu mai
martaba."

Farouq ya ce,"ai kuwa kasan yawanci haka masu sarauta ke da tsauri sosai."
Javed ya yi ajiyar zuciya,"e kam Amman fa Mai martaba ya yi yawa gaskiya. "

Falon Hajiya Kaka suka je suka gaisheta.
Kasa dauke idanunta akan Farouq ta yi tana ji aranta wani da ta sani ne amman kuma ta
gagara tunawa hakan yasa kau da kai kawai ta ce
,"Ah anzo mun da sabon mijine"
Ta faÉ—a cike da tsokana.
Farouq ya ce,"ai kuwa ga sabon miji kin samu amman ni ina da kishi sai dai a saki dukka
sauran abar ni ni kadai."
Dariya hajiya kaka ta yi ta ce,"anyi an gama don kasan daman ni nafi gane fararen fata irinmu
tuni zan basu yellown kati na saki dari ba É—aya."

Duka suka kyalkyale da dariya.
Hajiya kaka ta ce,"waiji lafiya? (Ka zo lafiya)"

Farouq ya ce,"to fa inda matar zata kada mijin kenan ai ba jin yaren naku nake ba."
Hajiya kaka ta ce," aiko tunda kake da mata banufuya dole ka koyi nupanci."


Farouq ya ce,"anyi an gama daga yau yanzu ma."


Dariya hajiya kaka ta yi ta ce,"ince kun gama gaishe gaishen ku samu kuci abinci gashi cen
nasa an haÉ—a muku."
Javed ya ce,"ehto ba mu gama ba amman daman su nake ya ci abinci anan muyi sallar magrib
tukun sai mu karasa sauran."
Hajiya Kaka ta ce,"ya kyautu kan gwanda hanjin sabon mijina ya fara daukan girki ban so ya
wahala kun sanmu a zamaninmu mun san salon rike miji."
Dariya suka yi duka kafin suka tashi suka koma bangaren da aka jera masu abincin suka fara
ci.
Suna cikin ci Javed ya ce,"wannan ita ce hajiya kaka mahaifiyar mai martaba da Abba Malik da
Kuma Kilishi Hajiya Khaleesa ita kaÉ—ai ta rage mana a fannin kakanni kamar yadda ka gani
dattijuwace mai faran faran da mutane ga fara'a da wasa da dariya tana matukar kaunar
jikokinta sosai sannan ita ma ba baya ba wajen ado duk da cewa ta tsufa zan iya ce maka
gadon Abba malik ta yi a fagen tsafta da son ado da kuma son jama'a."
Farouq ya ce,"gaskiya kam har na ji ina kaunarta da ma ace ni ne nake da kaka kamarta da na
ji dadin rayuwa sosai."

Javed ya ce,"umm yanzu ma kasa aranka tamkar ita din jinin kace na tabbatar da cewa kuma
Hajiya kaka zata sa kaji hakan aranka domin kowa nata ne kuma babu bambamci."

Bayan sun gama cin abincin suka yi sallah Javed ya ce," To yar tsohuwa mun gode da abinci
bara mu karasa gaishe gaishe bako ya samu ya huta."
Hajiya kaka ta ce,"aa fa ka daina cemun yar tsohuwar nan kar sabon mijina ya fara guduna yan
mata zaka na cewa. "
Da dariya Farouq ya ce,"ai ni kallon budurwa yar shekara sha shida nake miki ki rabo da shi yan
matana."
Hajiya kaka tayi dariya ,"yawwa mijin kirki to sai da safe ko a huta gajiya lafiya."
Da amin suka amsa kafin suka fice suna dariya.

Bangaren mahaifiyar Javed suka wuce.
Ita ma ta tarbesu cike da sakin fuska tare da yiwa Farouq maraba da zuwa.
Javed ya ce,"wannan ita ce mahaifiyata ita ma dai mace ce mai son mutane da son kyautatawa
al'umma mu hudu ta haifa nine na uku akwai yayuna maza guda biyu Ya Jamaal da Junaid duk
sunyi aure suna cikin gidan nan suna rayuwa da yaransu sai ni da kuma kanwata É—aya tilo

Janinah da ta kasance m081030807q7inmu,mahaifiyata tana matukar bin umarni da dokikin mai
martaba domin ko gyaran murya ya yi tasan me yake nufi inko yace mata kar ayi abu to bazata
taba aikata wannan abun ba ko da kuwa ranta naso in yace kawai ta bi babu makawa."

Farouq ya ce,"Ma sha Allah."
Daga nan suka wuce bangaren Matar Abba Malik ita ma ta karbesu cike da fara'a.
Suna fita Farouq ya ce,"lallai ita ma matar nan tana yanayi da mijinta naga ita ma tana son
mutane sosai."
Javed ya ce,"ai Aunty Heedaya ba ruwanta kam wallahi rayuwarta so simple kamar Abba
Malik."

Bangaren Kilishi Khaleesa suka shiga tana zaune ta cikin izza da isa ta harde kafa kan kujera.
Suna sallama amman karewa Farouq kallo take wani irin kallon banza da rashin isa.
Yatsina fuska ta yi ta kalli Javed shi kuma wannan fa daga ina?
Kafin Javed ya bude baki zaiyi magana kenan sai ga muryar Janinah sun fito ita da Arham tana
fadin,"Aunty Kilishi mun dawo."
[05/05, 6:26 pm] Xayyeesherthul-humaerath🍂: *CENTURE*

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath

The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.

*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*

ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs! 😊
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials

- Home decor
- Sleeping dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! 🚚*
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*

PAGE-4

Hada ido suka yi da Farouq cikin sauri ta karasa inda yake tana nuna shi da yatsa.
"Kai ne?,sai kuma ta yi wani Murmushin mugunta ta kalli Javed ta ce Yah Javed wannan shi ne
bakon naka kenan maddallah ma sha Allah. "
Kilishi ta ce."Au shi ne bakon? Yo ni na ga mutum ne ai gashi nan dai shi ba bature ba kuma ba
fulani ba."
Ta karasa maganar tana yatsina fuska.
Javed ya ce,"shi ne mun zo gaisheki ne daman."
Farouq ya ce,"ina wuni? Fatan mun sameku lafiya."

Kanta na gefe ta ce,"Alhamdulillahi yadda kake gani muna lafiya. "
Javed ya kalli Farouq,"mu je ko."
Da haka suka fice.
Ita ko Janinah binsu take da kallo a zuciyarta tana jin dadin cewa babu shakka zata rama marin
da ta dau alwashin ramawa.
Kilishi ce ta lura da yadda ta ke wani irin tunani fuska kuma cike fal da annashuwa ta
zurngureta.
"Ke lafiya kuwa? Ban gane ba."
Gyara zama Janinah ta yi tana fadin,"ai tsuntsu ne daga sama gashasshe har gida Aunty Kilishi
wannan shi ne wanda na baki labari ya mareni a minna

Na ji dadin ganinsa sosai a gidan nan domin zan samu damar aikata masa abun da yafi mari
ma in ninka abun da ya mun.
Lallai sai yasan da cewa ya tabo jin sarauta."
Kilishi ta gyara zama.
"No wonder na ga ni bai wani mun ba sam sam bai kwanta mun gashi nan dai abu kamar ba
mutum ba aiko na daure miki gindi kiyi masa yadda kikeso zan tayaki ina bayanki dari bisa dari."
Arham ya ce,"Ayyah Momy ke kike kara daurewa Janinah gindi tana abun da ba kyau na
tabbatar da cewa in an bincika wannan tsiwar taki kika masa har ya mareki kuma fa shi ba dan

kasar nan bane ba."
Janinah ta ce,"Kai Yah Arham ai kullum daman ni mai laifi ce kuma wallahi ni dai sai na rama ba
fashi."
Kilishi ta ce,"Au kai kafi so ana taba mu muna bari? Ai nafiso mutane ko da sunan wani a gidan
nan suka ji su razana bare kuma ganinsa da har za ayi tunanin aikata mana wani shirme ba
ruwana da shi dan kasar waje ne inma dan kasar cikine muna daidai da shi sai ya san waya
taba." Dariya Janinah ta yi tana rungume Kilishi ,"shiyasa nake kaunarki wallahi Momy."
Arham kam saboda takaici tashi ya yi ya bar dakin.
Su kuwa suka shiga kitsa abun da za su aikatawa Farouq.

Suna fita Javed ya kaisa bangaren Jamaal da junaid sai da suka gaishesu da matansu kafin
suka koma bangaren Javed din.
Suna shiga Farouq ya numfasa ya ce,"lallai masarautar nan da girma take."
Javed ya ce,"ba laifi kam gaskiya kuma haka akwai bangaren yan uwa da ba mu karasa
ba,yawwa kuma ina so in baka hakuri duk da cewa na san hakan daman zai iya faruwa wacce
muka je bangarenta ita ce Aunty Kilishi ita ce yar auta agun hajiya Kaka tana zaune da mijinta
da yaranta su uku a cikin masarautar nan Arham shine babba wanda muka ganshi da Janinah
kuma su ake shirin hadawa aure sauran mata biyu kuma Ameemah da Amnah suna school a
minna Aunty Kilishi bata fiye son mutane ba mussamman bare tana jin cewa a kullum ita sama
take da kowa kuma tafi karfin kowa zan iya cewa bata dadin sha ani sam sam gaskiya shiyasa
banyi mamakin tarbar da ta yi mana ba."

Farouq ya yi murmushi ya ce,"Ayyah ba komai ai daman kowa da yanayinsa kuma baza a taba
taruwa a zama daya ba."

Javed ya ce,"haka ne kam,yanzu barin barka ka huta ka samu barci zuwa gobe da safe sai mu
tattauna."

Farouq ya ce,"alright thank you so much ."

Javed ya ce,"kar ka damu an zama daya ai duk abun da kakeso na sha akwai a fridge snacks
ma gasu can nasa an hada a dinning in kuma akwai wani abu da kake da bukata let me know
sai da safe. "

"Okay Allah ya tashe mu lafiya."
Javed ya fada.

Dake bangaren nasa babba ne bed room biyu ne da falo ya shiga dayan ya bar Farouq a
dayan.

Sai da Farouq ya yi sallar Isha kafin ya dauki waya ya kira Maah.
Cike da zumudi ta amsa kiran tana fadin,"Yan nigeria fatan an isa lafiya? Ina ta tunaninka ina so

in kira sai kuma nace kila baka samu nutsuwa ba kar in takura maka."
Farouq ya ce,"Wallahi kuwa na dan jima da isa ma kawai zaman ne ban samu ba sai yanzun
fatan kina lafiya?"

"Lafiya lau,ka dai ci abinci ko? Kuma ina fatan babu wata matsala."
Maah ta fada.
Farouq ya ce,"ina lafiya lau kuma na ci abinci na koshi sosai kuma babu wata matsala."

"Ma sha Allah Alhamdulillahi haka na ke son ji,ka tabbatar kana kula mun da kanka ka ji Dan
albarka kuma kar ana wasa da sallah da azkar duk da cewa na san ba ka wasa da ibada sam
sam amman a kara rikewa da kyau,ina nan ina tayaka da addua da fatan nasara,Ubangiji ya
tsare mun kai ya kare mun kai daga sharrin mutum da aljan aduk inda za ka kasance."
Farouq ya ce,"Amin amin ya Allah Maahnah Adduarki da fatan alkairinki da ke biye dani a
kullum ba zai taɓa bawa wasu damar cutar dani ba,ina alfahari da kasancewarki mahaifiya a
gareni,Ubangiji ya kara miki lafiya da nisan kwana kuma ibada In sha Allah ina turbar da kika
daurani babu wasa ko kadan."
Maah ta yi ajiyar numfashi kafin ta ce,"Yawwa Darling kuma kuma ana barci da wuri ban cewa
za a kwana akan Internet. "

Dariya Farouq ya yi ya ce,"Okay Maah I love you,Gudnight."

Maah ta amsa da,"I love you to Nighty Night Byee."

Kafin suka katse wayar.

Shiga Group dinsu ya yi na 5stars
Suka yi masa sannu da hanya kafin sai ga kiran Zeeyter ya shigo wayarsa.
Ta ce,"Friend bro ya ake ciki ne? Fatan ka sauka lafiya."
Farouq ya ce,"lafiya lau gimbiyata,kamar ko kinsan ina tunanin kiranki kenan."
Zeeyter ta ce,"aiko gashi na rigaka,ya ake ciki ne akwai alamun nasara kuwa?"

Farouq ya ce,"Ehto ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login