Showing 27001 words to 30000 words out of 62424 words
Chapter 10 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt
tsorace ko wannen su yana muzurai da ido.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/28, 7:54 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
_Ƴan group ɗin *IHU BAYAN HARI* Ina jin daɗin sharhin ku, kuma ina Alfahari da ku ɗa bisa ɗari, Allah dai yabar ƙauna❤️❤️❤️❤️❤️_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 35-36
Ya ce "Dama abin da ua tsayar da ku kenan har kukai dare, shine zaku dawo kuci gaba a nan"
Bilkisu ta kalle Umar shima ya juyo suka haɗa ido Baba ya kuma daka musu tsawa "Baza ku min magana ba"
Murya na rawa Bilkisu Ta ce "Wallahi Baba ba abin da kake zargi bane, Shine fa... "
Ya kuma daka mata tsawa "Kefa nace zan miki aure kika ce A'a ke karatu kike so, a haka zaki karatun"
Kallon Umar ta sake yi, tana son yayi magana amma yaƙi yin maganan.
Baba ya sake cewa "Ku fito nan falo ina jiranku"
Ya fita ta sake kallon sa ta zubda ƙwalla ta ce "Dan Allah ka faɗi abin da kamin, ka faɗi gaskiya ya kyale mu, bana son wannan zargin"
Sauƙa yayi daga kan gadon ya fita a ɗaki ita ma tabi bayansa suka samu Baba zaune durƙusawa suka yi duka yayin da ita kuma take kallon Umar tana son yayi maganan.
Baba ya kalle shi, ya ce "Shashasha me yasa da kake son ta baza ka faɗa na muku aureba, sanin kanka ne zanfi kowa farin ciki idan kace kana son ta"
Lokacin yayi magana ya ce "Baba ba abin da kake zargi bane fa, ka tsaya na maka bayani"
Ya ce "Na yanke hukuncin nan da sati biyu za'a ɗaura muku aure, nasan kana da kuɗi ka haɗa ka kawo zan ƙara maka wani ka haɗa mata lefe, ni zan biya maka sadaki"
Jin muryan Mama Sauda suka yi a bayan su ta ce "Aure da Bilkisu Allah ya sauwaƙe ɗana ya aure wannan abar shi yasa na faɗa maka wannan karuwan zata lalata mana ɗa amma kaƙi ji gashi ta lalata shi... "
Bab ya ɗaga mata hannu ya ce "Ya ishe ni haka dan Allah, ita ce me lalata shi ko, shi da yake namiji, a ɗakin ta fa na ganshi, me ya kaishi banda lalata, ita kuma da yake sokuwa ce ta biye masa"
Mama Sauda ta ce "To maganan Aure ma ka janye dan yana da wacce yake so"
Ya ce "Ya faɗa min ne, ni wannan ido na ya gane min "
Ta ce "Ruky yake so, ƴar gidan matar yayan ka"
Ya kalli Umar ya ce "Faɗa min da gaske Ruky kake so"
Ya ce "Eh Abba kuma ita ma tana da Saurayi a ƙauye sunan sa Tsammani "
Ya kalle ta yana neman ƙarin bayani ta ɗaga kai alamun eh
Baba ya ce "To ba ruwana da wani Tsammani ko Ruky abin da na yanke kenan, kuma kada na sake ganin ka kayi ƙofar ɗakinta, haka kama kada na sake gani ko ƙofar ɗakinsa kin kalla, idan kunyi auren kuje can ku ƙarata"
Bilkisu ta ce "Baba kayi haƙuri"
Ya ce "kije ki haɗa min lipton "
Ta tashi jiki na ƙwari tayi kicin, shi kuma ya fita shima jikinsa ba kwari.
Duk kan su ba wanda yayi barci, itakan kuka ta kwana tana yi, dan tana ganin idan aka musu aure da Umar zai iya kashe ta, dan Umar mungu ne, akan ta auri Umar gwara ta auri Tsammani ta ƙwammace taje a ta uku, kuma ta zauna a ƙauyen.
Baba kuwa Samun Alhaji yayi da maganan auren Umar da Bilkisu, sannan ya faɗa masa abin da ya gani da idon sa"
Alhaji ya nisa ya ce "Hakan da kayi yayi daidai "
Tsangwama gurin Mama Sauda ya ƙaru, kullum tana mata gargaɗin idan ta yadda aka ɗaura auren nan ita da jin daɗin duniya sun har ta mutu. "
Yauma tazo ta same ta a kicin tana tsaka da aiki ta ce "To karuwa kin faɗa an fasa auren ko"
Shiru tayi Mama Sauda ta kuma matsowa ta ce "Malama kina jina fa"
Ta ce "Haba Mama nima bana son Ya Umar Wallahi ina da masoya da yawa, Wallahi da ina da daman hana wa da na hana, ke ya kamata ki hana Mama"
Ta ce "To shikenan mu zuba ni da ke, kuma ina mai tabbatar miki Umar na Ruky ne"
Shiru tayi saidai zuciyar a cunkushe take da baƙin ciki, tana neman a lallashe ta tunawa tayi da yayyen ta sai kuma ta fashe da kuka cikin kuka tana cewa, shi yasa nace zan biku, gashi ba mai iya lallashi na, yanzu da ina tare da ku da hakan bata faru ba"
Saita tayi kuka da kanta ta share hawayen ta, bayan ta gama aikin tayi wanka ta shirya Abba na dawowa ta same shi ta ce "Abba yau ina son naje gidan su Umma na gano ta"
Ya ce "To Sai kin dawo idan kinje sai ki faɗa mata zancen auren naku, na aika wa Ummin ki ma, saidai tace baza ta samu zuwa ba saboda ita ma jiya tayi aure"
kudi ya ciro ys bata ya ce "Gashi sai ki samu abin hawa ko"
Ta amsa ta ce "Nagode "
Tana sauƙa a keke napep ta shiga a ƙofar ɗaki taga Umma tana ganinta ko Sallama bata yi ba ta fashe da kuka ta faɗa jikin ta, Umma kuwa ta ce "Ohhh ni Aishatu, me yake so ya faru ne haka"
Bubbuga bayanta ta ringa yi tana lallashi, dama abin da taje buƙata kenan dan haka tayi shiru, ganin tayi shirun ta ce "Adda faɗa min me ke faruwa ne"
Labari ta bata tun bayan Tafiyan Yayyen ta har zuwanta gidan su Umar da wannan aure da ake so a ɗaura.
Umma ta ce "Kiyi haƙuri ayi auren kinji, ita kuma Umminki, ki kyaleta taje tayi ta auren bazaa ƙara aika mata bama, Yanzu yakai ace tayi hankali ay, amma mace kamar ba hankali, ace za'ayi auren ƴarki amma kice ke jiya kika yi aure, ki kyaleta ay kina da mu, kuma zan kira Adda Bilkisu, takwaranki nasan zata zo ay, Idan zaki koma zamu je tare sai na roƙe shi ya bar min ke ana gobe ɗaurin auren sai ki koma, dan baza a barki haka ba ay, za'ay miki gyaran jiki.
Kusan Magrib suka sauƙa a gidan suna isa kuwa sukayi sa'a yana nan, bayan sun gaisa ne "Umma ta roƙi alfarmar a bar mata Bilkisu ana gobe ɗaurin auren sai ta dawo da ita"
Nan da nan Baba ya amince sannan yayi wa Bilkisu kyautar kuɗi suka koma.
Adda Bilkisu kuwa ana faɗa mata maganan auren da auren Ƙanwar ta, Adda ta ce "Nikan ma ban san auren ya mutu ba ma balle nasan da wani aure da zata yi, kyale ta, nima bazan kula ta ba ma, tayi ta zaman ta a can kauyen,"
Washe gari kuwa ta turo kuɗi ta ce da Umma ayi abin da ya dace na gyara amarya kafin ta zo. Hakan tundaga lokacin aka fara gyara Bilkisu.
Su Mama Amarya kuwa suna jin maganan auren hankalin su ya tashi aynun dan haka suka yi gun Boka, boka kuwa ya amshi kuɗin sa dan ya yi musu aiki.
Kullun Ruky kuwa tana manne da waya suna waya da Umar, tana masa kukan a fasa wannan aure, shima ya ce "Ba son ransa bane kuma ya faɗa mata koda anyi bazai taɓa haɗa gado da ita ba, saboda ya tsaneta.
Da wannan furucin nasa take murna.
Ana saura kwana Uku Adda Bilkisu ta iso tare da yaranta Aliyu da Maryam.
Aliyun da zaikai sa'an angon ya kalle ta ya ce "Amarya kenan yaushe rabon in ganki, tin kina yarinya, kinga yadda kika girma kuwa wai kece zakiyi aure, amma taki aka sa miki ko"
Ta ce "Eh takin da aka saka maka ka girma shi aka saka min, kaima idan kana da zuciya kayi auren mana"
Dariya Maryam tayi ta ce "Kamar ko kinsan a gida abin da Mommy da Daddy suke masa magana akai kenan"
Bilkisu ta ce "Tuzuru kawai"
Ya ce "Dan nazo bikinki kike ce min tuzuru"
Adda Bilkisu tasa baki ta ce "Ay gaskiya ne"
Ranan juma'a aka ɗaura Auren Umar Jafar Hamza da da kuma Amaryansa Bilkisu Ibrahim Hamza. Koda na gano Baba cikin fararan kayansa yana farin ciki dan yafi kowa murna da wannan haɗin saɓanin ango da Amarya da suke baƙin cikin wannan auren.
Adda Bilkisu tasa Takwaran tata a gaba ta ce "Bilkisu ki saurareni da kyau, naji labarin komai tsakanin ki da mijinki, bawai baya sonki ba, to kiyi haƙuri, kuma ko auren soyayyar kikayi haƙurin ne shine ya dace da ke, balle irin auren ki. Kiyi masa biyayya, banda ƙwiya ki kasance me tsabta a gidan ki, kada ki bar gidan ki da ƙazanta ki kula da kayan mijinki, idan kuna kai wanki ne, kada kina haɗawa da ƙananan kayansa, ke zaki na wankewa, kada ki damu da wani cin mutunci da tsangwama a gurin sa, aure ibadane, Allah zai baki lada, yanzu Allah ya ɗaga martabar ki da darajarki saboda aure, kiyi masa biyayya iya iyawanki, maganan girki kuwa, kada ki bar mijinki yana cin abinci a waje, kin kasance ko yaushe kina canja masa abinci da abinsha, ki kula da tsabtar jikinsa da na shimfiɗarsa ki lura da yadda zakina tashinsa daga barci idan idan ya kama dole sai ya tashin. Kiyi haƙuri, ki riƙe Addu'a Kada kiyi sakaci da shi, domin ita Addu'a makamin mumini ne. "
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/28, 9:12 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 37-38
Ita ko Bilkisu kuka take tayi tasan idan aka bar amanarta a gurin Umar tabbas sai yaga bayan ta, ita kan kwanan ta ne ya kusa ƙare wa domin Umar mungu ne.
Da kan ta Adda Bilkisu ta kira Umar yazo da kan sa ya same ta bayan ya gaishe ta, ta ce "Kaji tsoron Allah Umar, nasan Bilkisu ba tsabin ka bace baka son ta, an muku auren dole ne, Bilkisu Amana ce a gurinka, duk da baka sonta, yanzu maganan ƙiyayya babu ita tunda ta zama matarka abokiyar rayuwarka, saboda haka ka riƙe Amana kayi haƙuri da abin da ya faru a baya ka fuskanci gaba, yarinya ce mai haƙuri zaka iya tanƙwarata ta inda kake so, Kai zaka bata tarbiyyan da kake so, domin duk tarbiyyan da ka bata tabbas naka zata bi ta watsar da ta gida saboda haka ina roƙon ka kayi haƙuri ka manta da komai ka rungumi matar"
Ya ce "To Nagode insha Allahu baza a samu matsala daga ɓangare na ba"
Taji daɗi amsar da ya bata sosai, saidai kuma abin da bata sani ba duk abin da ta faɗa masa ya shiga ta kunnen dama ne ya fita ta kunnen hagu, tunanin sa yadda zai hukunta Bilkisu idan ta tare a gidansa a matsayin mata, gidan da ya jima yana gina shi yana mafarkin sun shige shi shida Ruky Uwar ƴaƴansa, sai kuma ace wata mazinaciyar yarinya ce, zata Shiga yarinyar da ya tsana tun tana yarinya yanzu ace ita ce abokiyar rayuwan sa, Ina ay bazai yuyu ba.
Da daddare Su Umma da Adda Bilkisu suka kaita, Nasiha suka sake mata suka tafi suka barta tana kuka, ita ba kukan rabuwa da gida take ba, kukan yadda zata zauna da mijin da aka aura mata take, bata san da wani sabon salon muguntar zai shigo ba, hala yau saboda haushin an aura masa ita da wuƙa zai shigo ya yanka ta, ya tona rami ya bunne.
Tana cikin haka kuwa taji motsin shigowa a falo gabanta ya faɗi ta sauƙo da kafafunta ƙasa da suke kan gado tana ji ya buɗe ɗayan ɗakin ya shige. Takai kusan minti talatin a haka, ganin bai shigo yasa ta shiga bayi ta watsa ruwa tasa kayan barcin ta ta kwanta barci ya kwashe ta.
Shi kuwa yana shigowa ɗakinsa yayi ya watsa ruwa yayi kwanciyar da, dan ma Baba ya matsa masa sai yazo ne amma da ba abinda zai kawo shi wannan gida. Waya ya ɗauko ya kira masoyiyarsa Ruky suka raba dare suna hiransu. Saidai duk da haka bai makara ba, ya tashi yayi alolo ya fito zai nufi masallaci ya kalli ƙofarta, ta murɗa ƙofar ta buɗe ya hangeta a kan gado tana ta shaƙar barcinta hankalinta kwance doguwar rigar barcin ta ɗaga cinyoyin duk a waje sai sheƙi suke, gashi dama sunsha gyara, ya daɗe a gurin yana kallon cinyoyinta ya yin da yakai kirjin ta ya hango rabin kirjin a waje, ji yayi kamar yaje ya cire rigar duka, ji yayi an shiga Sallah da sauri yaje jikin gadon yana cewa "Ke! Ke!! Ke!!!"
Da yaga bata motsa ba ya buga mata duka a cinya, da sauri ta tashi tana sosawa ta kalle shi, ya ce "Kin barni ina ta tashin ki, to lokacin Sallah yayi idan kinyi niyya sai ki tashi idan kuma Sallah ɗin ma bakya yi Zina kika sa a gaba to, dan da kin saba d Sallah ma da ba sai an tashe ki ba"
Yana gama faɗa ya fita, ta sauƙo daga kan gadon tayi bayi tana hawaye ta shiga bayi tayi alola tazo tayi Sallah, yana dawowa ya leƙa ɗakin ya ganta a kan sallaya alamar ta idar tana Addu'o'i ne, ɗakin sa ya shige yayi kwanciyarsa.
Ita kuwa bayan ta gama ta ɗan kwanta, can ta tuna da shawarwarin Mommy (Adda Bilkisu)
Ta miƙe tayi kicin komai ansa ba abin da babu dan haka ta fara shirya kumallo, da yake ƙwararriya ce, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama, ta gyara komai, ko ina fes falon ma ta sake gyarawa dukda dama a gyare yake. Ta shiga ɗakinta nan ma ta gyara sannan ta faɗa bayi tayi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa ta fito, ta ɗebi abinci taci. Da ta gama ta wanke abin da ta ɓata ta dawo falo tayi zaman ta, tana kallo. Tana tsaka da kallo ya fito da alama wanka yayi dan ƙananan kayane a jikin sa, ya hangi dinning table a cike yayi gurin ba tare da ya ce komai ba, ita ɗin ma bata ce masa ba. Buɗe-buɗe ya fara yi sannan kuma ya zauna ya fara ci, yana cikin ci ya kalle ta ya ce "kin gyara ko ina a gidan nan amma saboda raini bazaki gyara ɗaki na ba".
Tashi tayi ba tare da ta ce "Komai ba ta shige ɗakin ta fara gyarawa cikin ƙanƙanin lokaci ta gama da yake ɗakin ba wani ɓaci yayi ba, ɗayan ɗakin ta shiga nan kan baya buƙatar gyara saboda ba'a kwanta a ciki ba ma.
*** *** ***
Ruky tayi gun Mama Amarya tana kuka Mama Amarya ta kalle ta ta ce "To menene kuma"
Ta ce "Nidai gaskiya ina son ayi auren mu da Umar da wuri dan kada wannan shegiyar yarinyar ta mallake min shi"
Mama Amarya ta ce "Ta ina zata mallake shin, basai ya sake mata fuska ba"
Ruky ta ce "Kinsan shi wawa ne, zaije ya buɗe ciki yayi ta cin girkin ta, taje ta masa barbaɗe a ciki ya ci ya fara son ta"
Mama Amarya ta ce "Zamu je gun bokan ay zan sake masa bayani, kinsan Baban sa ne baya so, idan Boka ya tura masa abin a zuciya shikenan ba yadda suka iya dole ki aure shi kuma ki zama ƴar gaban goshi a lokacin kuma zaki ci uban shegiyar yarinyar kafin ki koreta ta bar gidan domin Umar naki ne ke ɗaya"
*** *** ***
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya baya mata magana saidai yazo ya samu abinci ya cika cikin sa, idan yana buƙatar wani abu kuma zai mata magana cikin gatsali, yanzu idan da sabo ta saba da halin sa, baya damun ta, ita dai tunda ba dukanta zaiyi ba da sauki, kusan kullun sai Baba ya kira ta sun gaisa kuma ya tambayeta idan da matsala ta ce babu
Ko yaushe idan yana gidan yana maƙake da waya a kunnensa suna soyewa da Ruky yana faɗa mata irin son da yake mata.
Ita ko wannan baya damunta sam.
Ya rasa inda zaiyi Babansa ya yarda ya auri Rukynsa. Shiko