Showing 36001 words to 39000 words out of 62424 words
Chapter 13 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt
take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
_*Dada Rabi Isah Musa Macen da take haɗa kan ƙannenta, Allah ya ƙara miki zaman lafiya keda mijinki ya albarkaci yaranki*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 47-48
Tsawa ta daka musu "Wannan wani irin iskancine, ke ƙaramar ƴar iska me na faɗa miki"
Bilkisu ta miƙe Umar ya tashi ya ce "Me haka zaki zo kina cika mana kunne"
Kallon su take sakaka sannan ta shigo jiki a sanyaye ta ce "Amma hakan kafin adalci kalli yadda kuke fa kasan bazan ji daɗi ba"
Ya ce "Wannan ɗin ba mata ta bace kike nufi ko me, ina da ikon yin komai da ita saboda mata ta ce dan haka ko ki zauna in raba muku kwana ko kuma ki koma inda kika fito"
Shiru tayi ta tashi tayi ɗakinta ta faɗa kan gado ta fasa kuka. Da dare yayi kuwa Bilkisu kwanciyarta tayi don tasan yau gun matarsa zai tafi, ga mamakin ta ta jishi yana buga ƙofa, ta miƙe taje ta buɗe ta ganshi Kafin tayi magana ya wuce ya kwanta a kan gado ta juyo ta ce "Ya Umar ba ga Ruky ta dawo ba, yakamata ka kwana a ɗakin ta ne"
Ya kalleta ba tare da ya ɗago ba ya ce "Aa kada ki min haka ki kyale ni a gurin ki, rabuwa ta da ke masifa ce, na saba da ke"
Ta girgiza kai ta ce "Haƙuri zaka yi kada Allah ya kama ka da laifi, ka tafi kada fushin Allah ya kama ka, tana da hakki a kanka, idan kaƙi zuwa gurin ta tabbas zamu haɗu da fushin Allah"
Tsaki yayi ya kwanta, ita ko taci gaba da masa nasiha karshe dai yaji jikinsa yayi sanyi ya miƙe yayi ɗakin Ruky ita kuma ta rufe ƙofa ta dawo ta kwanta, ji tayi ba daɗi ta saba da mijinta yanzu gashi zaije ya kwana a ɗakin wata, yanzu abin da yake mata haka shima zaiyi wa waccar, kuka ta fara yi wi-wi da taga ba mai iya lallashi ta share hawayen ta ta tashi tayi alola ta ɗauki Al-qur'ani mai girma ta fara karantawa da sautinta mai daɗi.
Lalle Al-qur'ani waraka ce domin taji wasai a zuciyar ta kuma da ta kwanta barci ya kwashe ta.
Koda yaje gun Ruky kuwa ta kama masifa, yana Yana jinta da yaji masifar ta ishe shi ne ya miƙe ya ce "Wai ke me ya same ki ne, me yasa kika fiya son ki, tunda na auro yarinyar nan ban taɓa bi ta kanta ba, ina ganin irin wulaƙancin da kike mata na sani sarai na kyale ki, yanzu dan na kasance da iya na lokacin ƙalilan shine kika damu kanki, to bari kiji Bilkisu mata ta ce, ba wanda ya isa ya raba mu, kuma zan raba muku kwana, kwana bibbiyu zannayi a ɗakin ko wannen ku idan baza ki zauna ba ga hanya nan"
Shiru tayi ta samu gu ta kwanta amma kuma taci Alwashin ɗaukan mataki.
*** *** ***
Kunna redia akayi aka kure vulum waƙar bori ke tashi a gidan, yayin da Zalimu yake taka rawa haɗi da buga ƙafa, ƴaƴansa ma suka shigo suna yi da buga ƙafa idan kuma akayi tsalle sai a buga ɗuwawu a ƙasa.
Ummi kuwa tana ɗaki tana ta cin tuwon haɗi da nadaman auren wannan mutumin, uwar gidan sa Shaga ce ta shigo ta ce "Kai Hali tsabar munafunci sai ki shige ɗaki kina kuka ga mai gidan mu yana raɓashewa baza ki fito mu taya shi ba"
Ta ce "Nikan bazan yi wannan shirmen ba"
Zalimu naji ya shigo ya ce "Kyaleta so take na sake ta ta koma gidan tsohon mijinta kuma ba yadda za'ayi na sake ta, bafulatanan banza kawai, ay duk Fulani munafukaine"
Ta tsakiyan da yake baffulatana ce ita ma ta ce "Ahhhh Zuminu ka daina sa munjaye, kada ka sake zagin mutane idan ba haka ba sai mu bada hamata iska"
Ya ce "To Tsaro nake ji, yanzun nan sai na ballaki na kaiki gidan ubanki su ɗaure ki samu sauƙi kuma dole ki dawo"
Ta nuna shi da yatsa ta ce "Wallahi ƙarya kake baka isa ba, " ya bata mari nan fa suka fara dambe yara kuwa suna ihu har da su ɗa da shewa, dukan su sunji jiki dan asabe ita ma mace mai ƙarfi, saidai tsirara da ya mata yara suna ta ihu, ganin haka Ummi ta fito tana rabiya ta kama Asabe tana son tura ta ɗaki dan jikin ta ba kaya Ita kuma ta ɗauki farantin silver zata rotsawa Zalimu sai aka yi rashin sa'a ta rotsawa Ummi.
Ummi ya kama gurin tayi ɗakin ta Zalimu kuwa ya ce "Maganin ki kenan ba shiga abin da ba ruwan ki ba"
*** *** ***
Haka Ruky ta haƙura ya raba musu kwana bibbiyu, duk lokacin da yake ɗakin Bilkisu takan sashi ibada da kanta take tashinsa ya wuce masallaci, baya taɓa rasa Sallah asuba yana yinta akan lokaci kuma, amma idan a ɗakin Ruky ne, wankan tsarkin ma sai zai fita yake yi sannan yayi Sallah asuba, girki kan Bilkisu ta yadda zata ringa yi sabo da Ruky bata iya komai ba, shi kansa idan yana ɗakin Bilkisu yafi sake wa, kuma yafi samun farin ciki.
Suna kwance kan gado ya kalleta cikin murmushi ya ce "Baby kwana biyu naga kina rama da yawa kuma bakya cikin kuzari kodai wani abu na damun ki ne"
Ta girgiza kai ta ce "Ba komai amma nima dai kwana biyu sai ina jin kasala Wallahi wataran da kyar nake gama aikin gidan nan ga tashin zuciya da rashin kuzari, amma ay ba komai bane canjin yanayi ne"
Ya sake kallonta da kyau sannan ya kalli kirjinta yayi murmushi ya ce "Eh tabbas canjin yanayi ne, gashi Allah ya nuna min kina ɓoye da ajiyata"
Ta ce "Me kenan "
Ya ce "Bayan ramar da na gani, kin kuma yin waji ja, kinyi haske musamman kuma kirjinki da ya cicciko wannan ya tabbatar min da kina da ciki"
Ta mike ta sauna ta ce "Jishi sai kace wani uwar mata ina kasan wannan kai kuma"
Ya ce "kin manta aiki na ne, bayan dabbobi da nake lura da su, ina lura da mutane, sai dai kuma aikina akan dabbobi ne, bama mu ba duk wanda ya ganki zai san kina da ciki idan kuma kina musu tashi muje a miki scaining"
Ta ce "Hmm nidai barci nake ji"
Murmushi yayi ya kyale ta sukayi barcin su.
Cikin ikon Allah kuwa sai gashi cikin ta yana girma, yana kaiwa wata huɗu ta fara jin motsi, ranan yana dawowa ko barin sa yaci abin ci ta kasa yi ta ce "Ya Umar Macijin ciki yana damuna, kaji yadda yake min zillo a ciki"
Dariya yayi ya ce "Ɗan nawa ne maciji, "
Ta ce "Ni gaskiya muje asibiti haka cikin yake, kasan inda yake min ne, zillo fa yake min"
Ya ce "To barin ci abinci"
Ta ce "A'a ka Bari sai mun dawo gaskiya"
Yayi dariya ya ce "Muje to"
Hijabinta ta ɗauko tasa suka tafi, suna zuwa aka mata gwaji aka tabbatar mata tana da ciki wata huɗu ta riƙe cikin ta kalli likitar ta ce "Wai ni ɗane a ciki na"
Likitan tayi murmushin ta ce "Ƙwarai kuwa ko kina mamaki ne"
Ta ce "Ikon Allah "
Shiko Umar bakin nan yaƙi rufuwa ya wangale 32 a waje, aka basu shawarwari suka koma gida, ita kan hannunta na cikin ta sai shafawa take, ita kaɗai tasan irin farin cikin da take ciki.
Ruky kuwa tana fahimtar cikin jikin Bilkisu da kuka tayi gun Mama Amarya tana faɗa mata yanzu Umar baya son ta ya raba musu kwana da Bilkisu yanzu kuma har ciki ya mata.
Mama Amarya ya ce "Kwantar da hankalin ki kinji zanyi wa boka bayanin komai idan yaso a zubar da cikin kowa ya huta,"
Ruky ta ce '"Nifa gaskiya ciki nake so nayi nima ko ta yaya, kinga yadda yake ji da ita ne, har fa kicin suke shiga tare"
Mama Amarya ta shirya tayi gun boka ta faɗa masa komai ya ce "Cikin nan bazai taɓa zubewa ba sai an haife shi, sai dai a sa ya tsane ta ita da cikin"
Mama Amarya ta ce "To shikenan duk ba damuwa zanje na amso kuɗi a gurin ta zan kawo maka"
Sai da suka gama shirin su na sharri sannan ta tafi.
*** *** ***
Tunda aka rotsamata farantin silver bata kuma shiga rabiya ba, idan an fara faɗan ma saidai ta koma ɗaki, tadai Addu'a take Allah ya rabata da wannan gidan. Idan ko ya tashi tsiyar sa, ya ce dan munafunci kuma sai ki zaunaa ɗaki.
Ta fito kenan zata shiga bayi sai ta juyo ana dambe a ɗakin Zuminu bata yi niyyar shiga ba sai ganin sai ganin wata mace tayi ta fito tana cewa "Wallahi sai ka biyani kuɗi na, kai ka ce zai sake ta kuma har yanzu shiru Wallahi sai ka biya ni"
Ya ce "Bazan biya ba na riga na miki aiki ay"
Ummi kuwa tunda ta juya ta kalli inda suke bata ce komai ba, ganin haka kuma yasa ya ringa zaginta wai tana gani ana ci masa mutumci tayi shiru.
Shirun ta kuma yi nan kuma ya ringa zazzaga mata masifa.
*** ***
A hankali cikin ta ya ta girma saidai wani abu da bata gane ba shine, Yanzu Umar ya canja mata ya daina rawan kai akan cikin nata, saidai kuma idan sha'awarsa ya tashi kai tsaye yake zuwa mata, batare da ƴan wasanni ba.
Wannan ma sai dare yayi ko ranan girkin ta ne yanzu ya koma gun Ruky idan da ranane da daddare kuka yaje ya kwana a ɗakinta.
Ruky tayi tayi ta sa ya daina kwana ɗakin Bilkisu amma yaƙi wannan yasa ta samu Mamanta ta ce "Boka yasa ya saki Bilkisu kawai, wannan karon tare suka tafi gun bokan, saida suka masa bayani Boka ya kalli Ruky yaga tayi kala yasa ya ce "Ta shigo ɗaki zan fara ɗanɗanata a cikin abin da zamuyi zan saka mata magani"
Mama Amarya ta ce "Haba kodai ni da muka saba amma ay hakan baiyi tsari ba kayi da ni ga kuma ƴata"
Ya ce "Akwai maganin da zan saka mata ne"
Mama Amarya ta kalli Ruky ta ce "Ku shiga "
Ruky ta ce "Haba Mama ji fa wani ƙazami da shi duk wari yake"
Ta ce "Ohon ki sai ki zauna kina ganinta da ciki"
Ta tashi ta shege ciki yayin da Mama Amarya take waje tana jira saida Suka ɗau wajen awa a ciki sannan suka fito, duk wanda yaga Ruky yasan taji jiki.
Ya fito yana lashe baki ya ce "Kuje ku yau ɗin nan zai saketa tabar gidan amma da sharaɗi kada tabar cikin garin bauchi idan kuwa ta bari komai zai lalace dan haka a kiyaye"
Mama Amarya ta ce "Idan ya sake ta ay gidan Sauda zata yi tana nan"
Suka tashi suka tafi suna farin ciki....
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[6/3, 6:54 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
_*Habiba Isah Musa Allah ya sauƙe ki lafiya*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 49-50
A gajiye ta dawo gida lokacin an fara kiran Magrib ita kuma da ƙaton cikinta tana jera musu abinci zata shige ciki ta ce "Ya Umar ana ta kiran Sallah fa"
Ya ce "Kin ɗauke ni bani da kunne ne ko me, ay naji"
Ita kan gun abincin ta kalla ta ce "Wallahi yunwa nake ji dama ashe na dawo a daidai an gama"
Ya ce "Barin zo in taya ki nima tun ɗazu aka cika min ciki da ƙamshi "
Ruky ta ce "A baki fa yau zaka bani kaji ko"
Ya ce "To duk abin da kiks ce hakan ay za'ayi"
Tana jinsu ta shige ɗakin tayi Sallah Magrib sannan tayi ƴan Addu'o'inta ta jira Isha nan ma tayi sid tayi shafa'i da wuturi sannan t fito, ganin sa tayi yayi matashi da cinyar Ruky kamar zata yi magana sai tayi shiru saboda yau a ɗakinta yake, ta wuce dan taci abinci taga babu komai ta kallesu ta ce "Ina sauran Abincin kuma"
Umar ya ce "Ruky ta ce in kaiwa Almajirai saboda bata son abinci ya kwana"
Ta kalle shi sai kuma ta kalli Ruky ta ce "Amma kuma ay kasan ni ban ci ba, kuma nice yakamata nasa a bawa Almajirai ba kai ita ba, saboda ni na dafa"
Ya ce "kina faɗa min kin dafa abinci to na bada sai ki yi bin da zakiyi "
Ruky ta miƙe ta ce "Idan kika ƙara magana yanzu zan bubbuge shegen cikin kin nan"
Ta ce "Zo ki buge ni tunda baki da hankali "
Ta tashi tayi kan Bilkisu da niyyar bugeta sai Bilkisu ta matsa da sauri Ruky ta bugu da dinning nan ta faɗi a gurin warwas, Umar yazo ya ɗaga itako Kicin ta shige ta haɗa tea ta dawo ɗaki tasha sannan ta sa doguwar rigar barcin ta ta kwanta.
Cikin barcinta taji ana buga ƙofa da ƙarfi ta miƙe cikin tsoro ta buɗe ta ga Umar ya ce "Baki da hankali kinga yanzu kinji wa Ruky ciwo amma da yake baki da hankali ko ki ce mata sannu"
Tsaki tayi zata tura ƙofan ya turo ya shiga Ruky ta biyo bayan sa ta ce "Ka tsaya kana kallon ta baza ka bubbuge ta"
Ya ce "Kyaleta tausayin ta nake ji saboda cikin nan".
Ta ce "Ina ruwan ka da ciki "
Bilkisu ta kalleta ta ce "Ki fita min a ɗaki idan ba so kike in miki duka ba, ku duba fa ƙarfe 12 saura yanzu amma kun hana ni barci ka ja matarka ku fita bana so idan ba haka ba a daren nan zan kira Baba ya min tsakani da ku, tunda baku da... "
Maganar ce ta katse sakamakon barin da ya bata daga bisani ya fara dukanta, da taga zai mata illah yasa ta fara ɗaukan kayan kan madubinta tana jifan sa da shi Yayin da Ruky ke gefe tana dariya, ganin bazata daina jifansa ba yasa ya fita ita kuma ta zauna a ƙasa ta kifa kanta a kan gado tana kuka, ba jimawa ya dawo jin muryansa tayi yana cewa "Ki tashi ki bar min gidana na Sake ki saki Uku "
Da sauri ta ɗago ta kalleshi taga yana miƙa mata takarda tasa hannu ta amsa ta duba ta gani ta kuma rushewa da kuka, ya jima a tsaye yana kallon ta tana kuka can ya ce "Ki tashi ki fita min a gida na"
Ta ɗago ta ce "Dare yayi sai da safe "
Ya ce "Safe! Karya kike yanzu zaki bar min gidana, ay bana ubanki bane"
Ta ce "Yanzu fa duba a gogo a daren nan zan fita"
Ji tayi ya fara zanata ta miƙe ta ɗaki kayan da ta cire ta cire rigar barcin ta sa ta a kan gado ta sa hijabi ta ta kalle shi ta ce "Umar baka cikin hayyacin ka, amma shawaran da zan baka ka kula da ibada'
Ta fita ta ga Ruky a falo tana dariya ta ce "Abi wani sarkin"
Tana fita tayi ta yafiya, ita kan tsabar takaici ma ko wayanta bata ɗauka ba balle kayanta. Da kyar ta samu Keke napep ta shiga ya kaita gidan Baba tayi buga ƙofa shiru, ta dade tana bugawa sannan Mama Sauda ta fito ta ganta ta ce "Lafiya "
Ta ce "Mama Ina Baba, Umar ya koreni daga gida"
Mungun kallo ta mata ta ce "To kuma sai kice min wani Baba dalla matsa min zan rufe gida, " tana rufe ƙofa ta ce "gwara da ya kore kin ma ay yanzu nasan na haifi ɗa"
Komawa tayi gun me Napep ɗin ta ce "Sun rufe ƙofa"
Ya ce "Yanzu ne dare yayi shi yasa ki kira wani a waya mana"
Ta ce "ba waya a hannuna ay"
Ya ciro waya ya ce "ga waya idan kin san number ki kira"
Ta haddace number Baba yasa tasa tayi ta kira shiru bai ɗauka ba, "
Me Napep ya ce "Ki masa saƙo kin san yanzu dare ne ba kowa yake son ɗaukan waya da daddare ba musammam baƙuwar number.
Ta tura text ta yi typing _"Baba gani a ƙofar gida ina cikin matsala, Baba dan Allah ka taimaka bani da gun zuwa kai kaɗai kake ƙaunata"_
Ta tura suko ɗan jima amma shiru bai fito ba, suka sake kira shiru, ƙarshe ma suka ji wayar a kashe
Me Napep din ya ce "Hajiya dan naga ke mace ce kuma ga ciki yasa na tsaya a gurin amma da yanzu ina gida "
Ta ce "Kayi haƙuri dan Allah ka kaini gidan mu"
Ya ce "Muje"
Suka tafi gidan Abba nan ko tana buga ƙofa Abba ya fito ya kalle ta ya ce "Kefa daga ina"
Ta ce "Abba dan Allah ka barni na kwana a gidan ka, ko a ɗakin su yaya ne zan kwana da safe zan tafi"
Jin muryan Mama Amarya tayi a bayan sa ta ce "To daga ina kuma, kinzo mana da cikin shege kice mana mu buɗe miki gida, Umar ya gane ba cikin sa bane kenan"
Ta ce "Wallahi Abba cikinsa