Showing 45001 words to 48000 words out of 62424 words
Chapter 16 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt
zan mata ba ay"
Abubakar ya ce "Kayi haƙuri Abba ka daina sa wannan a ranka"
Yayi murmushi ya ce "To yaushe Aishan nawa zata dawo"
Dariya suka yi Abubakar ya ce "Kwanan nan ka zuba ido ka gani"
*** *** ***
Umar dai an zama ƴan gari a tashan kawo dan kuwa yanzu an sanshi, ya zama ɗan dako, duk wanda zaiyi tafiya yana zuwa tasha harda Umar yana cikin masu ɗauka masa kaya ya kaishi motar garin da zaije, ya cire girman kai, kuma duk aikin da ya samu na ƙarfi zaiyi a biya shi lada, wani abokinsa ya kira shi ya ce "Akwai wani Mai gidana da yake son a masa fiɗa gobe sunan matarsa zai yanka rago, ko ka iya"
Ya ce "Allah ya kai mu goben "
Ya ce "Amin"
Washe gari kuwa suka shirya abokin sa sale ya kaishi gidan, cikin ƙanƙanin lokaci ya gama fiɗan, aka biya shi sanna aka basu nama. Sun shirya zasu tafi kenan Umar ya hango tinkiya zata haihu tana ta kuka, amma haihuwar ta gagara. Zuwa yayi gurin Sale ya ce "Me zaka yi "
Baice komai ba yaje ya kama kunkumin tinkiyar da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma yana shafa mata baya a hankali sai kuma gashi ta haihu. Mai gidan yana kallonsa ya matso ya ce "Malam Umar ya akayi haka, duk haihuwan da wannan dabbar zata yi sai ta sha wahala sosai"
Umar ya ce "Ay abin da na karanta kenan"
Ya ce "Ahhh dama kuwa a zango inda ake siyar da dabbobi ana neman likitan dabbobi ya kamata muje can kana musu magani ana biyan ka"
Ya ce "To Alhaji na gode"
Ya ce "Gobe sai kazo in kaika ko"
Ya ce "To nagode"
*** *** ***
Tana yin arba'in Aliyu ya nema mata makaranta ta fara zuwa, dama bata yi waec ba yanzu ko sai da tayi sannan, da yake har yanzu akwai ƙwaƙwalwan tana nan tana ja.
Maisun kan gun Mommy take barin ta har taje ta dawo.
Watan ta biyar tayi girma tayi wayo tana gane kowa musamman Mommy da yake tafi zama a gunta. Barci ke rabasu da Mommy
*** *** ***
Ba ɓata lokaci aka maida auren Alhaji da Aisha ranan da ta dawo kuwa Mama Amarya taso tayi bala'i amma da taga baxa ta ci riba ba, sai ta kyale taji da jinyar hannun ƴarta.
Farin cikin su ya fara dawowa dan Khadiyo ma tana zuwa lokaci-lokaci
Sun dawo kenan suka ga ɗakin su a buɗe sunyi mamaki da suka samu a buɗe. Usman yana shiga ya yi karo da mutum ya ce "waye kuma anan"
Abubakar ya ƙarasa ya kunna wutar ɗakin haske ya gauraya a ɗakin sa ganin Ruky suka yi daga ita sai towel a jikin ta, ta kama towel ɗin tana neman cirewa da hannu me lafiyan, Abubakar ya ce "Me haka ne me kike nema"
Ta ce "Na mallaka muku kaina kyauta kuyi abin da kuke so da ni, Idan ma kwana kuke so nayi ma zanyi koda ku biyu ne zan iya ɗauka"
Usman ya kwaɗa mata mari ya jawota ya cillo ta waje ta faɗi a kan hannunta me ciwon tasa kuka ya biyo ta ya ce "Idan muna neman matan banza ke kin isa mu neme ki, du be ki fa yadda kika dawo me zamu samu a jikin ki ƴar iska irin ki"
Ta ce "Wallahi sai na maka sharrin da baza ka manta da ni ba"
Ta tashi da kyar tana jin zafin hannun tayi ciki tana kuka Alhaji ta gani a falon ta ce "Kaga su Usman sun min fyaɗe"
Ya kalli ta ya ce "Sun maki fyaɗe ko kin musu fyaɗe, lalata min yara kike so kiyi ko yaya"
Mama Amarya ta fito da kukan ta tana cewa "nikan na gaji da wannan wulaƙancin gwara a Sallame ni nida ƴa ta"
Ya ce "To kuje na sake ki, ku bar min gidana, nima ay na huta, kuma ƴaƴana sun huta, maganan Bilkisu kuma ina nan kan bakata, duk lokacin da ta dawo sai kun fuskanci hukunci, dan ina ji a jikina ƴata zata dawo.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/6, 9:05 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 59-60
Shiru suka yi duka Ruky ne tazo da hannun ta ce "Abba dan Allah ka barni na zauna a nan ɗin kaga ni ƴarka ce, kuma ma ni ban maka komai ba"
Ya ce "Ƴata a ina, ni ban haife ki ba, ki tashi ki bi uwarki, to ma kin taɓa ce min Abba tunda kike, sai yanzu wai Abba, ki bar min gida ko insa yarana suyi kaca-kaca dake. "
Mama Amarya ta turo baki ta ce "Muje Ay in shi ya sake ki Umar bai sake ki ba, sai mu tafi gidan sa, mu zauna kafin ya dawo kuma"
Ruky ta ce "Mama ni ba inda zanje gwara ma ki bashi haƙuri muci gaba da zama"
Jawo Ruky tayi ta ce a hankali "Ke banza ce, yaushe zan bari in bar gidan nan, ay ni da shi mutu karaba, kizo muje kisa ido ki gani, ba akwai boka ba, kamar yadda Aisha ta bar gidan nan a wancan lokacin yanzu zata barshi, su ma yaran sake barin gidan zasuyi"
Basu ankara ba, sai jin muryan Usman sukayi ya ce "gwara ma ku sami wajen zama dan a wannan lokacin ƙarya ne boka yayi nasara a kan mu, idan kuma kunga ba haka ba, GA FILI GA DOKI"
Abubakar ya ce "Saura sukuwa"
Jan Ruky Mama Amarya tayi feeeeee sai waje.
*** *** ***
Kwanci Tashi babu wuya a gurin Allah yau Maryam ta zama cikekkiyar lauya, sannan kuma a ranan ne Maisun ta cika shekara biyu Bilkisu da Aliyu ne suka haɗa musu walima sosai anci ansha, saidai Aliyu ya lura da Bilkisu kamar hankalinta baya jikin ta, sauri sauri take taga halama fita take son yi ba da sanin kowa ba, mamaki yaji sosai, Lalle idan haka ne, akwai mai hure mata kunne"
Yana gani tayi wa Maisun wayo ta zame, ta gudu, cikin gidan tayi, can sai gata ta fito da basket cike da abinci tayi hanyar waje da shi, da sauri ya bita ya shiga mota ya bita, Makarantansu yaga tayi ana sauƙeta ta shiga ciki gani yayi ta miƙa wa wani ɗalibi amma kuma ya manyanta Abincin ya matsa ya laɓe ta jikin bango inda basa ganin sa, buɗe abincin yayi ya ce "Nagode miki, yanzu sai muje gida ko"
Ta ce "Ni bazan bika gidan ka ba gaskiya, shi yasa nace mu haɗu a nan"
Ya ce "Lalle na lura bakya sona Bilkisu, tunda baza ki iya kai min ziyara gidana ba"
Ta ce "Kai da na gayyacenka walimar ƴar uwata kaje ne, ay tilasta min kayi sai dai na kawo maka abinci, haka na kawo maka a ɓoye ba wanda ya sani, amma kuma yanzu kace in bika gidan ka kuma ba kowa, gaskiya bazai yuyu ba"
Murmushi yayi ya ce "To shikenan mu shiga ciki sai ki juye min abincin, akwai kula na a ciki ko "
Ba wani tunani ta shige ciki zai bita a baya Aliyu yayi saurin bayyana a gurin daidai lokacin kuma yaga wannan mutumin Aliyu ya ce "Kaine kuma dai"
Bilkisu tayi saurin juyowa da taga Aliyu ta zaro ido, Aliyu ya ce "Har yanzu baki da wayo, akwai kuruciya a tare da ke, da har zaki biye wa namiji ya ce ki shiga office ɗinsa amma ki shiga, Ina tunaninki yake, Ya yaudare ki da maganan so yana nema ya lalata ki"
Ta ce "Ya lalata ni kuma"
Ya daka mata tsawa ya ce "Ɗauki abincin ki shiga mota mu tafi gida"
Ta tsaya tana kallonsa hannun ta ya kama ya jata feee yayi da ita cikin mota da ya wugata ya dawo ya ɗauki basket ɗin abinci ya nuna shi da yatsa ya ce "Ƙaryan ka Wallahi, kuma Wallahi na sake ganin ka da wata ƴar uwata sai nayi ƙaranka"
Ya dawo ya shiga motar ya ja suka yi gida, suna zuwa Maisun ta taho da gudu tayi gunsa ya ɗaga ta sama suna suna ta dariya.
Ita ko gimbiyar shigewa tayi ciki rai a bace, ɗakinsu ta shiga ta kwanta a kan gado ba jimawa sai gashi ya biyo ta ya zauna bakin gadon ya ce "Wai dan na raba ki da ɗan iskan nan kike fushi"
Shiru tayi ta kuma juyawa ya ce "Kinsan wanene wannan mutumin kuwa? Shine fa yaso ya yaudari Maryam, aikin sa kenan ya yaudari ƴan mata ya ringa lalata da su, a wancan lokacin badan Allah Ya kawo ni ba da ya lalata "
Ta juyo ta ce "To bashi ɗin bane baka sanshi ba"
Ya ce "Dole kice haka saboda kina sonsa"
Sake juyawa tayi ya kalli Maisun ya ce "Kije gun Mommy kiyi wasa ko"
Ta tafi da ɗan gudunta ya ce "Kiyi haƙuri banso ranki ya ɓaci, Amma ina son kisan wanene Jabir. Wata rana na ɗauki wayar Maryam sai naga Chat ɗinsu wai bashi da lafiya ta kai masa abinci ɗakinsa, a da taƙi daga baya sai ta amince saboda nacin da take masa, koda na bincika sai naga a ranan zata kai masa girkin, saida ta gama na bita, ta shiga ta same shi a kwance, saidai kuma tana shiga yaje ya rufe ƙofa da ƙyar na samu na balla ƙofar na shiga naga suna kokawa yana neman keta mata mutunci, ki gwada tambayan Maryam waye Jabir. "
Yana gama faɗa ya fita cikin damuwa yana jin ɗaci a cikin zuciyar sa.
Da suka kwanta kuwa da Maryam Bilkisu ta kalli Maryam ta ce "Waye Jabir"
Maryam ta ce "Badai ɗan iskan nan kike tambaya ta ba, na tsane shi, badan Ya Aliyu ba da tuni bani da wata amfani a duniyar nan"
Bilkisu ta ɗauki wayarta ta nuna mata potonsa ta ce "Wannan shine"
Ta ce "Shine Wallahi munafuki mai fuska biyu"
Bilkisu ta bata labarin komai yadda suka yi da Aliyu, Maryam ta ce "Ki godewa Allah sannan Ya Aliyu, amma ina son infaɗa miki wani sirrin da Ya Aliyu ya ɓoye, sannan ina so kiyi tunani akan maganata, kada ki ɗauketa da wani manufa"
Bilkisu ta ɗaga kai, Maryam ta ci gaba "Ya Aliyu yana Sonki, yana son ki zama matarsa, ni kadai nasan wannan, tunda kika haifi Maisun nake fama dashi ya faɗa miki yaƙi, wai yafi so ki gane da kanki, ke kuma kinki ganewa, kiyi tunani mai kyau zaki gane maganata"
Tana gama faɗa ta juya dan yin barci.
Ita ko Bilkisu ta shiga kogin tunani, tabbas ta fahimci hakan, amma sai tayi tunanin saboda ita ɗin ƴar uwarsa ce, tabbas idan ta samu Aliyu a matsayin miji ta more.
Wayanta ta ɗauka ta shiga whatsapp ta ganshi online.
Ta tura masa saƙo "Kayi haƙuri"
Ba jimawa ta turo mata da amsa "Da kika min me"
"Da na kasa fahimtar ka, kuma na fahimci wanene Jabir na rabuda shi har abada"
"To kina da wani saurayinne sai ki fito da shi na aurar da ke tunda naga alama auren kike so"
"Hmm babu kowa "
"To akwai wani wanda yake son auren ki ko zaki iya manage da shi tunda baki da kowa "
"Eh to ya ya kawo kansa idan naga yamin shikenan"
"Kina son yazo ɗakin ki yanzu"
Daɗi ya kamata dan ta fahimci akan ta yake magana amma sai ta tura masa "Ay dare yayi ko zaka bari wan gardi ya shiga maka ɗakin ƙannen ka"
"Kedai kawai kice yazo ki gani zaki gan shi"
"To yazo amma idan bai min ba kada yaji haushi dan na fatattake shi"
"Ki fito falo yanzu zaizo"
"Allah ya bashi sa'a"
Amin"
Tashi tayi tasa hijabi kan Kayan barcinta ta fito ta zauna a falon.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/7, 8:29 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 61-62
Tana zaune taga ya shigo kallo ɗaya ta masa ta kauda kai ya zauna a ɗaya daga cikin kujeran ya ce "Ina Maisun ta ke"
Ta ce "Suna barci ita da Maryam"
Ya ce "Ke kin zo nan jiran masoyinki ko"
Ta ce "To ba kai kace nazo na jira shi ba"
Ya ce "To ay gashi yazo shi, ko zai samu karɓuwa"
Shiru tayi tana kallonsa ya ce "Kinyi shiru kina kallona ko ban samu karɓuwa bane"
Rufe fuskanta da tafukan hannayenta tayi, shiko murmushi yayi ganin ya samu nasara a kanta, saidai yana son ta tabbatar masa da bakinta, dan haka Ya ce "Ban samu karɓuwa ba kenan, ko da yake dama kina ce min tuzuru, ina ga ba yadda za'a yi ki auri Tuzuru iri nah"
Da sauri ta ce "Nifa ba haka bane"
Ya ce "To yaya ne"
Ta ce "Kaga ni bazawara ce, ina tunanin kada Mommy da Daddy suce baza ka auri bazawara ba, kana saurayin da baka taɓa aure ba"
Ya ce "Wannan duk ba hujja bace Mommy da Daddy zasu fi kowa farin ciki idan hakan ta faru, sai dai idan kece bakya sona ko kina da wani wanda ya fini"
Ta ce "Ni bani da kowa"
Ya ce "To baki sona kenan "
Ta ce "Nifa ban ce haka ba"
Ya ce "To ki faɗa min mana "
Ta ce "To kaje zan faɗa maka a a chat"
Ya ce "Kinyi Alƙawari "
Ta ce "Nayi"
Ya ce "Idan kuma banga komaiba, to nasan banyi bane, kuma bazan iya barci ba"
Ya ce "Zaka ga saƙona"
Tayi ɗaki tana zuwa ta samu wayarta ta mutu, ta kunna taga taƙi kawowa tasa a chaji.
Shiko gogan naka da taji ta shiru ya tura mata saƙo "Yanzu nasan matsayina a gurin hala kina da wani ne wanda kike so amma ba damuwa zan zamo me haƙuri akan rashinki"
Yana tura mata ya kashe wayarsa, ya kwanta, sam barci ya gagari idon sa, yasan ya samu nasara a kanta amma yana tunanin me ya hanata yi masa saƙon.
Wayar tana ɗan yin chaji ta kunna saƙonsa ya shigo tana karantawa, tayi kira shi a waya amma a kashe ta tura saƙo shiru, kwanciya tayi tana ta juyi, ta kasa jurewa, da sauri ta tashi ta ɗauki dogon hijabinta har ƙasa tasa tayi ɗakinsa, daga nesa ta hango wutan ɗakin a kunne alamun baiyi barci ba, tana zuwa jikin ɗakin tayi bugu ɗaya, daga ciki ya ce "Waye"
A hankali ta ce "Bilkisu ce, waya ta ce fa ta mutu ba chaji shine nasa chajin, ina buɗewa naga saƙonka Wallahi ba haka bane, ni bani da kowa, kuma dama nayi niyyar in faɗa maka ne fa"
Wani daɗi yaji yana murmushi ya tashi ya buɗe ƙofar, ya ce "To shigo ki faɗa min"
Ta shigo ya nuna mata kujera alamun ta zauna, ta zauna ya ce "To faɗa min"
Ta ce "Ka buɗe wayanka zan faɗa maka"
Ya ce "Aa ni anan nake so"
Ta ce "To Ina sonka"
Murmushin jin daɗi yayi ya ce "Ɗan ƙara faɗa inji"
Ta sake faɗa ta miƙe tayi bakin ƙofa ta sake maimaitawa sai kuma ta kwasa da gudu ya biyo ta a bakin ƙofa ya tsaya saida yaga shiganta ciki sannan ya rufe ƙofa ya koma ciki yana ta hamdala wa ubangijinsa.
Ita kuwa tana shiga ta ɗauki wayarta saida ta tura masa kalaman Soyayya sannan ta kwanta saidai barci sam yaƙi ziyartar idanun nata (Allah Sarki Mu mata bamu iya faɗawa Soyayya ba, har na tuna lokacin da na faɗa soyayyar Baban Mufeed Wallahi bana barci ko cin abinci, da naje makaranta ma karatuna ya gagara, kullun tunanin sa nake, ni kawai so nake na ganshi)
Washe gari kowa ya fito da shirin sa, Maryam dama ba ko ina zata je ba, amma ta shirya su ita da Maisun Mommy ma da Daddy duk sun shirya, shima yazo a shirye suka zauna duka dan karyawa, ya kasa sa komai a bakinsa yana jiran yaga ta fito amma shiru, Mommy ta lura da shi ta ce "Wai kaikan baza ka fita bane"
Ya ce "Zan fita"
Ta ce "To naga ne kaƙi ka maida hankali kaci abincin ka"
Ya ce "Bana jin cin komai ne ma fa yau
Barin wuce kawai "
Har ya kai bakin ƙofa ya juyo ya ce "Maisun Ina Mommyn ki"
Cikin tsamin bakinta ta ce "Tun tuni ana ta tashinta taƙi tashi, sai barci take, sai ta tashi ma ta sake faɗuwa"
Ya ce "Muje in ganta ko bata da lafiya ne"
Ta wuce ya bita a