Showing 18001 words to 21000 words out of 62424 words

Chapter 7 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2844

kuma ma Abba ko na yi abin da kake zargi bai kamata ka kore ni ba, sabo da ni mace ce, Addu'a zaka min, dan Allah Abba ka duba min kada ka kore ni"


Tayi shiru hawaye ɗaya na bin ɗa ga majina, haka shima.


Ganin maganganun zaiyi tasiri yasa Mama Amarya ta ce "Dama haka karuwai suke akwai iya tsara magana "


Wani mungun kallo Bilkisu ta mata ta ce "Kada ki kara sa min baki idan ina magana da mahaifina"


Kallonta yayi ya nuna mata hanya ya ce "Fita min a gida"

Ta ce "Abba kayi haƙuri dan Allah kada ka... "



Ya bata mari ya sa ƙafa ya hankaɗata waje ta fito falo ta bugu da kujera a goshinta sai jini, ta dawo ta kama ƙafarsa tana kuka ta na cewa "Abba goshina ya fashe ka kaini asibiti"


Ya sake hankaɗata ta faɗi ta kuma tashi ta ce "Abba ba inda zanje ka taimaka min"


Ya kama hannunta yayi da ita waje ya hankaɗata, ta faɗi tana miƙewa ta sake biyo shi tana cewa Abba bansan inda zanje ba, ya tokare tada ƙafa a cikin ta, ta sake ƙoƙarin tashi ta koma saidai kuma ya rufe kofar har ya haɗa mata da babbar yatsarta na hannun daman ta, ta jingina da jikin get ɗin ta ci gaba da kuka jini na zuba daga goshinta, can kamar wanda aka tsikara ta miƙe ta fara tafiya tabar unguwar tana tafiya tana kuka, dare yayi sosai ba mutane a hanya taga ƴan sanda da motar su, tana isowa gurin ɗaya ya ce "Daga ina kike"

cikin kuka ta ce "Abbana ne ya kore ni daga gidanmu shine zanje gidan Ƙaninsa"


Ɗaya ya ce "Me kika yi"


Ta ce "Wai yana zargin ni karuwa ce ina kawo maza gida kuma Wallahi ba haka bane"

Ogan su ya fito a mota ya kama goshin ta ya ce "Sannu ko kina zubar da jini da yawa muje cikin mota ki huta sannan muje asibiti"

Ta bishi suka shiga cikin motar tare, ya kwantar mata da kujera ya ce ta kwanta, ta kwanta, sai jinshi tayi yana shafa mata wuya da sauri ta miƙe ta kalle shi, sai ji tayi ya ce "Baby tsaya mana ba wanda zai ganmu, muna gamawa zamu je in kaiki asibiti, kuma muje ki kaini in kama Baban ki"


Ta girgiza kai tace "Kayi haƙuri dan Allah ni...


Ji tayi ya rungumeta ya rike ta yana ƙoƙorin cire mata rigar barcin da ta saka. Ita ko duk ƙarfin ta ya ƙare.





_Ayi haƙuri da wannan_





_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 27-28





Ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba wajen kokawa dashi, ankwa ta gani a gefe ta dauka ta buga masa a goshin sa, jin zafin gurin yasa ya sake ta, ita kuma tayi sauri ta buɗe mota ta fita da gudu, gudu take tsulawa duk da gidan da nisa bata iya tsayawa ba saida taje bakin get ɗin gidan Baba Jafaru, jiri ta fara ji amma duk da haka ta buga ƙofa da ƙarfi, tayi ta bugawa.



Umar kuwa cikin barcin sa yaji ana buga ƙofar da ƙarfi kuma anƙi a daina, tsaki yayi ya miƙe ya ɗauki wata ƴar ƙaramar wuƙa ya fito yaje jikin get ɗin yayi magana da ya ce "Waye"


Ba magana sai nishi da ake, ga duk kan alamu nishin mace ce dan haka ya buɗe ya kalle ta ya ce "Bilkisu su, kece,? me ya faru da ke,? Wa ya ji miki wannan raunin? "


Bata iya amsawa ba sai raɓawa tayi ta jikin sa zata wuce, jiri ya kwasheta zata faɗi ya tare ta, daga nan kuma numfashin ya ɗauke, jijjiga ta ya ringa yi amma shiru, ya kalli jikin ta duk jini, ga irin kayan dake jikin ta, kayan barci ne, riga da wando, daga shi ba komai a jikin nata danko bra babu balle ƴar singlet, ɗaukanta yayi kamar jaririya yayi ɗakin sa da ita ya ajiyeta kan gado, ya duba agogo ƙarfe 1:45am ya sake kallon ta, a fili ya ce "To me ya fito da yarinyar nan cikin dare a cikin wannan yanayin, kodai wani ne ya mata fyaɗe"


Kasancewan sa likitan dabbobi kuma likitan dabbobi suna iya duba mutane, sannan yana da kayan aiki na mutane yasa ya ɗauko ya fara mata dressing din goshin ta da ta bugu sannan ya mata Allura a hannun ta, ya goge mata jinin dake fuskarta ya ɗaga rigar yana goge wanda ya gangaro cikin ta ya fara kaiwa zuwa kirjinsa yaji yanayin shi na neman sauyawa, dan haka ya bari, ya jawo bargo ya rufe ta, ya zauna a bakin gadon ya ɗauki waya ya kira number Baba Jafar, kasancewa dare ne saida ya kira shi kusan sau uku sannan ya ɗauka ya ce "Lafiya kuwa"


Ya ce "Lafiya ba lau ba, Bilkisu ce"


Ya ce "Wace Bilkisun kuma me ya same ta"

Ya ce "Ban sani ba, gata nan dai a ɗakina cikin mummunan yanayi"


Da sauri ya tashi ya buɗe ƙofa yana zuwa ɗakin Umar yaga abuɗe kai tsye ya shiga shima ya zauna a bakin gadon ya kalleta ya ce "Ta zubar da jini da yawa ɗauke ta muje asibiti"


Kayansa ya saka sannan ya janye bargon ya ɗauke ta, lokacin Baba ya je ya sanar da Mama Sauda ita ko tana ji ta koma ta kwanta abin ta abin ta, bai bi ta kanta ba yaje ya tada mota Umar ya shiga baya rungume da ita, saidai ba ƙaramin dauriya yayi ba kasancewan yadda gaba ki ɗaya yana yin sa ya sauya, har idonsa ya fara canja kala, Tunawa yayi Ruky irin yadda take masa, tana yawan nuna masa suran jikinta sannan tana yawan mannewa a jikin sa, bata taɓa birge shi ko bashi sha'awa ba, saiga ƴar ƙaramar yarinyar nan tana neman dagula masa lissafi, lallai da Bilkisu ce take masa hakan da ta jima da saka masa tarko.


Suna isa aka karɓe ta hannu bibbiyu, jinin ta aka fara gwadawa dan a duba ko yayi ƙasa, sun samu yayi ƙasa sosai amma kuma ba sai an ƙara mata ba, idan tana shan kayan ƙarin jini ma ya wadatar, Allura suka sake mata, sannan suka ce idan ta farfaɗo zasu iya komawa gida da safe dan an riga an gama mata komai tun a gida.



Ganin yadda likitan ke kallon ta yasa Umar yaja mayafi ya rife mata jikinta ya watsawa likitan kallo, tuni likitan ya kama hanya ya fita. Baba waje ya fita, shiko Umar ya zauna a kujera a ɗakin daga baya ya kifa kansa a bakin gadon barci ya kwashe shi.



*** *** ***


Tuni Umma ta haɗa musu komai da taimakon Allah sannan ƴan uwan ta suka haɗa musu komai suka tafi Saudi Arabian Karatu, kuma ta ci Alwashin baza ta taɓa faɗawa kowa a cikin dangin mahaifinsu cewa tasan inda suke ba, bata barsu haka nan ba ta dage da musu Addu'a Allah yasa su samu abin da suka je nema, so take ƴaƴan nata suma su tsayu da ƙafan su, saidai wasu su nemi taimako a gun su badai suje neman taimako wani guri ba, ta gargaɗe su idan suka je, in sun samu sana'a kada su zauna haka suna yin sana'a ɗin ma.


*** **** ***


Ana kiran Sallah Asuba ta farka ta tashi ta zauna tana dube-dube taga Mutum ya kifa kai a tunaninta Abubakar ne yasa tasa hannu a kansa a hankali ta ce "Yaya Ina kuka yafi kuka barni ina ta shan wahala, dan Allah yaya ku tafi dani inda kuke, yana jinta bai ɗago ba, sai ta kama hannun sa, wani yarrrr yaji a jikinsa yayi saurin janyewa ya ɗago suka haɗa ido da sauri ta ɗan matsa baya ta fara tunowa da abin da ya faru, ta lumshe idon ta wasu hawaye masu zafi suka sauƙo, ya ce "Kukan me kike kuma, me ya fito dake daga gida cikin daren nan"



Shiru tayi sai kuka da take yi, yayi ta tambaya amma shiru ba magana, fita yayi ya shigo da Baba shima yayi ta tambaya amma ta shiru, ya ce "To yanzu daga nan muje gidan naku muji ko menene"


Lokacin tayi magana ta ce "Dan Allah idan munje ka bashi haƙuri na zauna bana son barin gidan mu"


Ya ce "To menene ya fito da ke"


Faɗa masa komai tayi bata ɓoye ba, har yadda suka yi da ƴan sanda.


Shiru yayi can kuma ya ce "Muje gidan muji"


Fita suka yi ta bisu a baya ta rungume hannunta a ƙirji saboda yanayin inda take, Tunda ta faɗi wannan magana Umar sai hararanta yake wannan ya tabbatar mata bai yadda da ita ba kenan.


Suna zuwa ta shiga ɗakinta ta cire kayan barcin nata tasa doguwar riga sannan ta fito lokacin kuma taga Alhaji da Baba suna magana tana zuwa ta durƙusa gefe ta ce "Abba kayi haƙuri dan Allah na tuba bazan ƙara ba, kada kace zaka kore ni"


Mungun kallo ya watsa mata sannan ya nuna mata hanyar fita, Baba ya ce "Kinga abin da kika ja wa kanki ko, idan aure kike so me yasa baza ki faɗa ba"


Ta kalle shi ta ce "Baba kaima ka yadda kenan dan Allah kada kumin mummunan zato"



Alhaji ya ce "Kai ka shigo da ita saboda haka ka Fita min da ita idan ba haka ba zan saɓa maka"


Ya ce "Haba Yaya ay hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yar, hukuncin da ka mata ma ya isheta ishara, kuma ga duk kan Alamu tayi nadama, kayi haƙuri ka kyale ta"


Ya nuna shi da yatsa ya ce "Ku fitar min daga gida, ay kana da gida ka kaita gidan ka mana"


Miƙe wa yayi ya tashi ya ce "Muje Bilkisu "


Ta bishi a baya Umar ma ya miƙe sai hararanta yake.



Suna zuwa gida a falo ta zauna, ya shiga ciki ya kira Sauda suka fito tare ita ma ta zauna a kan kujera Baba ya ce "Bilkisu zata zauna a gidan nan na ɗan wani lokaci kafin ta koma gidan su"



Miƙewa tayi ta ce "Wallahi bazai yuyu ba baza ta zauna ba ta koma can gidan su, ay naji abin da ya faru, wato ubanta ya kore ta saboda tana kawo kwartaye gida ni ta zauna min tana kawo min, kuma ma ay Ina da ɗa zata ɓata min tarbiyyan yaro"


Shima miƙewa yayi ya ce "Gidan ki ko gidana, dole Bilkisu ta zauna a gidan nan kuma idan naga dama ta dawo kenan. "






_*Mrs Aliyu ce*_





lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 29-30





Ɗaki ta wuce fuuuuuuu Baba ya kalli Umar ya ce "Gobe kaje ka ɗauko mata kayanta "


Baice komai shima ya fita, ya kalli Bilkisu yadda ta takure guri ɗaya tana zubar da hawaye tausayinta ne ya kama shi Ya ce "Kiyi haƙuri kuma kiji tsoron Allah ki tuba gare shi, sannan ki dage da ibada, idan kina buƙatan wani abu ko menene shi ki faɗa min, ko ki faɗa wa yayanki Umar kinji ko"


Bata da zaɓi sai dai ta amsa masa, haka kuwa ta ɗaga kai.


Ya nuna mata ɗaki ya ce "Wannan ɗakin baƙine ki shiga ciki idan an kawo miki kayan naki ki ajiye a ciki, tashi ki shiga ciki"


Tana hawaye ta ce "To Nagode Baba Allah ya... " Ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu da ce wa "Ya isa haka tashi ki je"


Ta miƙe ta take ta zauna a ƙasa kusa da katifar ta fara rera kuka, cikin kuka tana cewa "Ya Allah gani gare ka." Sai kalmar take ta maimaitawa, ta jima a zaune a gurin tana kuka da taji ya ishe ta sai yayi shiru tana ajiyar zuciya, turo ƙofa taga anyi ta kalli ƙofa taga Umar ne ya cillo mata akwatin kayan ta ya haɗi mata akan ƙafarta taji zafi dan haka ta kama gurin tana sosawa tana sake kallon sa, kamar zai fita sai kuma ya juyo ya zauna kusa da ita a bakin katifar, ya kama tsolon gashin kanta ya ja, tasa hannu takai yayin da idon ta yayi jajur, ya ce "Da nasan abin da kika aikata kenan lokacin da kika suma da na kaiki daji cikin dare nan"


Ta ce "Da zafi fa, dan Allah ka sake ni"


Sake ja yayi ya ce "Wawiya mazinaciya, kamarki ƙaramar yarinya kinsan kinsan kawo kwarto ɗakinki dana ay an faɗa akwai karuwan da suke zama gidan iyayen su"


Maganan sa ta ishe ta dan haka ta ce "Ni ba karuwa bace amma ka sani, wacce kake neman aure wato Ruky a ita zaka faɗawa haka, dan tun lokacin da su Yayana suka bar gidan ɗakin ya koma jahannaman ta, dan kullun sai ta kawo kwarto, nasan da wannan kuma Mama Amarya ta sani, Ina tausaya maka idan ka auri Ruky domin ka auri cikekkiyar karuwa wanda ta ajiye ɗaki a cikin gidan su," ta nuna masa yatsa manuniya ta ce "Ya kamata kasan wannan, ni ba mazinaciya bace ka adana kalaman ka zasu maka amfani lokacin da kasan waceece mazinaciya"



Tunda ta fara magana yake kallon bakinta, kamar zai yadda sai kuma ya ce "Ohhh so kike ki rabani da Ruky ta, to ƙarya kike, Ruky wayayyiya ce, ban taɓa kamata da wani saurayi ba, kefa har ya tsallaka gidan ubanki, ya tsallaka falo ya shige ɗakin ki, amma ki sani idan kika ce zaki haka a nan sai mun karya ki"


Sa hannu tayi a kirjinsa ta ture shi ya faɗa kan katifa, saboda zafin da take ji a kanta dan yaƙi ya sake mata gashi, da sauri ya shige bayi ta kulle kanta a ciki. Tashi yayi ya zauna da yaga bata da niyyar fitowa ya miƙe ya fita abin sa.


Yana fita ta fito ta kama kanta da yake ta mata ciwo, ta ce "Allah ya isa tsakani da wanda ya min sharri, Allah ka saka min tun a duniya ma"


Mama Sauda ce ta shigo ɗakin ta kalleta ta ce "To Tsinanniya ay hutawa zaki yi da kika zo gidan ba dan haka ki fito ki fara aikin gida"



Ta tashi ta ta fito tayi kicin duk yayi kaca-kaca kamar ba'a taɓa shara na, kwanuka kuwa duk kudaje nabi, wanke wanken yafi ƙarfin a yi shi a cikin kicin ɗin dan plates dun sunyi yawa ga datti da yawa, ta ringa kwasa tana kaiwa bakin pampo da yake ta baya saida ta gama kwashewa ta gyara kicin din tas, ta goge ko ina, sannan ta dawo kan wanke-wanken ta fara yi, tana cikin yi ne Baba ya shigo ya kalle ta ya ce "Bilkisu baza ki huta ba, kika kama aiki, ko da yake nasan Sauda ce ta saki barin je in sameta"


Da Sauri ta ce "Aa fa Baba ba ita bace nice nazo ina yi da kaina, ita kan ma bata sani ba, kaga ay wanke-wanken ba yawa"


Ya ce "Da yawa mana, da kinsan kwana nawa aka tara wanke-wanken nan da kin riƙe baki, Sauda ƙazamar mace ce, koda yake tana yarinya ma bata da tsafta balle yanzu,"


Ita dai Bilkisu shiru tayi dan bata son ma maganan, ganin haka yasa ya shige ciki. Saida tayi komai ta gyara gidan tas sannan ta koma ɗakinta ta sake gyarawa tayi wanka.


Tun Sassafe ta tashi ta fara gyare-gyaren gidan saida ta gama tayi wanka ta koma ta kwanta, bata daɗe da kwanciya ba taji an turo ƙofa, Sauda ta ce "Baza kiyi mana abin karyawa bane?"



Ta ce "Zanyi dama ina jiran ki tashi ne ki faɗi abin da za'ayi"


Ta ƙarazo ta kama kunnenta ta ce "Daga yau, Ina tashi in samu kin gama shiryawan komai idan ba haka ba na lahira sai ya fiki jin daɗi"


Cikin ranta ta ce "Na lahira kan akwai masu jin daɗi, amma bama fatan in kasance ta ɗayan ɓagaren.


Wucewa tayi kicin ta fara abin karin kumallo cikin ƙanƙanin lokaci ta gama, ruwan tea ta dafa sai Arish da ta soya da kwai sai farfesun naman rago da ta ɗumama, sannan ta kuma girka abinci dan dai kada tayi laifi.


Tazo ta jera komai akan dinning sannan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login