Showing 42001 words to 45000 words out of 62424 words

Chapter 15 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2859

dangin ta, Lalle tayi Babban kuskure ta zaɓi aure akan dangin ta, miƙewa tayi tayi ɗakin Zalimu ta sameshi yana cin naman kaza, tuni yawonta ya tsinke, rabonta da ta ci shi tun tana gidan Alhaji, a ƙauye ma zabuwa suke ci, a nan ko sai da suga yana ci, ya kalleta ya ce "Ya dai damo sarkin haƙuri"


Ta ce "Dan Allah ina son kamin izini naje na duba ƴata Bilkisu tunda tayi aure banje ba, ina son naje naga ɗakinta"


Ya ce "Kinsan dai idan mutum zaiyi tafiya bana bada kuɗin mota, ƴaƴana ma saidai samarin su su basu, uwayen su kuwa ƴaƴansu ƴan mata suke samo musu, amma ke tunda baki da ƴa kuma na farko ne, zan je har tasha na biya miki kuɗin mota, kuma ay naga ke ɗin me haƙuri ce"


Ta ce "To Nagode"


Ya ce "Kije ki shirya gobe kije zan baki aika ma ki kaiwa Bilkisun dukda ban taɓa ganin ta ba"


Ta miƙe tana ƙara godiya, ya yago tsokar kazan ɗan ƙarami kamar wanda zai bawa ƙaramin yaro dake bayan uwarsa ya ce "Hungo gashi sa a bakin ki, naga yayunki ya tsinki" tasa hannu ta karba dan kar tayi laifi amma badan tana so ba, duk da tana kwadayinsa baza ta amsa ba dan bazata iya cin wannan abin ba, ay sai ya maƙale a haƙori.



*** *** ***



kwananta ɗaya a gidan ta zama ƴar gata, tana ɗan motsi kadan zakaji ance kina son wani abu ne, koda Alhaji Yusuf wato Daddy ya dawo shima yayi farin cikin ganin ta, ta saba da su sosai ga wasa da dariya.


Yanzu haka Sassafe aka haɗa mata ruwan wanka tayi wanka wani sabbi kaya tasa saida Maryam taga bata buƙatar komai sannan ta shiga wanka ita ma, tana kishingiɗe a bakin gado ta fito ta fara yin kwalliya ta ce "Muje mu karya to"

Suna shirin fita Aliyu ya shigo Maryam ta gaishe shi, ya amsa, ita ma ta gaishe shi ya amsa sannan ya sake kallonta ya ce "Zan fita me kike so a siyo miki"


Ta girgiza kai ta ce "Ba komai"


Maryam ta ce "To ni in faɗa"



Ya ce "Yanzu fa kema zaki tafi Makaranta ita kuma kiga fa halin da take ciki" ya sake kallonta ya ce "Baza ki faɗa ba ko"


Ta ce "Ba komai fa, bana buƙatar komai"


Ya ce "To idan kika haifo mana yaro da rowa ni da kene"

Maryam ta ce "Maida shi zamuyi"


Ita dai murmushi take tayi ya ce "To na tafi ni kumin Addu'a "



Maryam ta ce "Yaya yau da wuri zaka fita baka karya ba fa"


Ya ce "Momy ta haɗa min tea nasha kuma yau ina shari'a da wuri, kuma tana ta jiran ku"


Yana faɗa ya fita su kuma suka masa Addu'a haɗi da binsa a baya.



Koda suka je gun cin abincin ma ana ci ana barkwanci tun tana noƙewa har ta ware tana ɗan sa baki.



*** *** ***


Washe gari ta shirya kayanta Zalimu ya ɗauketa a mashin ya sata a mota sanna ya sake bata ɗari biyar a hannun ta.



Suna isa Gidan Su Umma tayi bayan sun gaisa ta ce "Zata je gidan Bilkisu, Umma ta nuna mata bata san komai ba, saidai kuma ta faɗa mata su Abubakar suna nan lafiya suna nan dawowa yau, dan sun gama karatunsu. Su ɗinma dan zasu dawo yasa ta faɗa musu.


Dan haka suka tashi, kai tsaye gidan su Alhaji suka wuce suna zuwa suka sami Alhaji duk ya rame ya zama abin tausayi, shi kuwa yana ganin su sai yaga kamar sun dawo ne, ko amsa musu gaisuwan baiyi ba ya ce "Kunga yadda Allah yayi da ni ko, Ba Bilkisu ba su Abubakar, Khadiyo ce kawai naji labarin ta, itama ta min Alƙawari zata zo ta ganni yau.


Umma ta ce "Su Abubakar suna nan dawowa yau daga Makaranta"


Da sauri ya ce "Addan fa"


Ta ce "Adda ita muka zo gani muma"


Ya ce "Bamusan inda take ba, munyi cikiya mun sa poton ta a gidan tv munyi cikiya amma shiru ba labari"



Ummi ta ce "Addan nawa ne, ta ɓata, ba ɓata tayi ba, kai kasan inda ka kaita kuma sai ka nemo min ƴata"


Ya ce "Ki saurare ni Hali"


Ya faɗa mata komai, ayko sai ta miƙe ta ce "Wallahi bazan yadda ba, sai kun nemo min ƴata, dan baka son ta shine zaka kore ta saboda matarka, "
Hango Mama Amarya tayi tana leƙen su ayko ta miƙe taje ta cakumeta tana cewa "Ina ƴata, ina kuka kaimin ita, sai na kulle ki, shima Umar din zan same shi"


Umma ne taje ta riƙeta taba bata baki.

Yamma kuwa nayi sai ga baƙin Saudiya, sun zama ƴan gayo kamar ba su ba, fatan su ta murje tayi kyau gwanin sha'awa, duk macen da ta gansu sai sun kyasa. Sunyi waya da Umma ta faɗa musu suzo gidan Baban su suna can, Suna zuwa suka ji Mummunan abu, nan fa wata bala'in ta tashi ba zancen hutu Usman ya ce "Muje gun Umar ɗin idan bai fito da Bilkisu ba Wallahi baza mu bar shi ba,"


Ummi ta ce "Nima Wallahi binku zanyi saina gwada masa abin da baiyi zato ba"


Shidai Alhaji kallon su kawai yake ta yi, Har suka bar gidan yayin da Umma kuma tana zaune a falon ta rasa abin da yake mata daɗi.




_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/4, 3:50 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 55-56




Suna isa gidan Baba suka shiga ciki suna parking ɗin mota shi kuma ya fito daga ɗakinsa na samartaka dan nan ya koma. Yana ganin su gaban sa ya faɗi, zai koma Usman ya ce "Ka tsaya kada ka koma ko ina, ka bamu ƙanwar mu, mu tafi da ita"


Shiru yayi yana kallon Ummi yana son ya gaishe da ita saidai ba fuskan hakan ta ce "Ina Addana"


Muryansa na rawa ya ce "Ummi kiyi haƙuri nima neman ta nake Wallahi, Abubuwa sun min yawa, Babana yaƙi min magana kuma ya saki Mamana saboda da ɓatan Bilkisu yanzu haka tana gidansu, nima bai san ina wannan gidan ba, da bazai barni in zauna, Kiyi haƙuri Ummi nima ba'a son raina na mata hakan ba"


Tausayin sa taji, Shiko Usman yayi kansa, Ummi ta riƙe shi ta ce "Ku kyale shi kawai mu tafi Addu'a zamu ci gaba da mata kawai"


Abubakar ya ce "Ummi ki kyale shi, dama can ina lura da shi tun Bilkisu tana ƙarama ya tsane baya son ganin ta, yanzu an aura masa ita yaga sai yadda yayi da ita shi yasa ya wulaƙanta ta, to kaje ka nemo mana ƴar uwar mu idan ba haka ba zan maka ka a kotu"


Ya ce "Zan tafi, zan shiga duniya neman ta bazan dawo ba, sai na sameta, na muku Alƙawari zan dawo muku da Bilkisu,"


Hanyar fita yayi kamar wani marar lafiya ya fita a get ɗin gidan ya fara tafiya da ƙafa.

Shiga mota suka yi suka koma gida.


*** *** ***


Tunda ya mata duka ya kulle gidan bai ƙara bi ta kanta ba, yana buɗe ƙofar ya ganta a kwance tana kuka hannunta ya kumbura. Ya kalleta ya ce "Tun ranan kina cin abinci dai ko"


Tace "Eh tea nake haɗawa, "


Zai wuce ta ce "Dan Allah hannuna, ka taimaka min"


Ya kalle ta ya bude mata baki saida yayi jini ya ce "Dama nasan halin da Bilkisu take ciki ne da zan iya tausayin ki, ban sani yanzu hala ma ta fiki shan wahala"


Ɗakin Bilkisu yayi yaga inda ya bar ɗakin haka yake, Takardan ya gani ya kuma karantawa, da sauri ya naɗe ta cikin ransa ya ce "Wato kaduna tayi, to Kaduna a ina, ya tambayi kansa saidai ba amsa. Rigar barcin ta ya ɗauka ya rungume yasa kuka, ya dade yana yin kuka sai kuma ya ɗauki wayarta haɗi da rigar ya fito yayi ɗakin sa da shi, kayansa ya bayan ya gama ya sa rigar barcin nata da wayarta yasa a ciki ya ɗauka yana zuwa Falo ya kalli Ruky ya ce "Ki tafi gun uwarki ta miki jinya idan na dawo kuma zamu ci gaba daga inda muka tsaya"


Ta tashi da hannu a kumbure tayi hanyar waje, shi kuma sai da ya kulle ko ina a gidan sannan ya fita, gidan Baba ya wuce ya kwana, washe gari sassafe yayi tasha ya shiga mota sai jihar Kaduna garin gomna.


A tashan kawo aka ɗauke shi, to gashi daiba kaduna amma baisan kowa ba kuma bai san inda zashi ba, sannan baisan ta ina Bilkisu take ba, Lalle yana da aiki a gaban sa.




*** *** ***


Gata kan Bilkisu ta same shi wannan yasa ta koma Bilkisunta na da, tana shagwabanta yadda take so, daɗi da ta samu Maryam ma ƴar shagwaɓan ce, haka suke haɗuwa suyi tayi.


Cikinta ya kai haihuwa tare da Momy suke zuwa awo, da yamma kuma Aliyu ya raka ta suyi ta zaga unguwar tasu a ƙafa.



kullun shi yake rakata randa Maryam take gida kuma ita ma ta bisu.


Yaukan ta dawo kenan suna zaune a ɗakin a ɗakin Maryam suna cin maƙulashen da suka siyo taji maranta ya kullu ta ɗan rintse ido, dama yau tunda Safe take jin ɗan ciwon mara, Maryam ta kalle ta ta ce "Ya dai, kodai abin yazo ne"


Ta ce "Haba an gaya miki wasan yara ne haihuwan"


Ji tayi ya sake murɗa mata wanda yafi na da ta kama gurin, sai kuma taji wani ciwon wannan karan abin dake bakinta ta fito da shi, saboda azaba, Aliyu da Maryam kuwa tashi sukayi da gudu suna rige-rigen kiran Mommy, ita ma da gudun tazo ta kama Bilkisu ta ce kalli Aliyu ta ce "Maza ɗauko mota muje asibiti haihuwa ne"


Kamata tayi suka fara takawa bakin ƙofa Bilkisu ta tsaya ta kasa ɗaga ƙafa ta ce "Mommy bazan iya tafiya ba, Mommy zan mutu, "


Mommy ta ce "Kina Addu'a ne kinji, insha Allah zaki haihu lafiya"

Jan ta Mommy ta kuma yi sai kuma Bilkisu ta durƙusa a gurin tayi wani nishi babba sai ga baby, da sauri Mommy ta tare sai a hannunta, sai ta kimu yin wani nishin da baikai wancan ba, saiga Mahaifa ta faɗo, Mommy ce tayi ta cewa "Alhamdulillah Allah mun gode maka"


Ita ta yanke cibi ta duba ta mace ce, ta sako kai ta ce da Maryam faɗawa yayanku ta haifi mace, da gudu taje ta same shi a cikin mota da yake jiransu ta faɗa murna gurin su ba'a magana.



Mommy ce ta gyara Baby da Uwar Baby sannan aka fito da babyn Falo, Aliyu ne ya amsa yana farin ciki sai washe baki yake yi, haka Umar ma, saida Bilkisu ta gama shirya wa sannan ta fito suka tafi asibiti, ko da aka je aka samu jaririya da uwarta duk lafiya sai ƴan gwaje-gwaje da aka musu sannan suka dawo.


Daddy ma yana dawowa ya sami Baby ya ɗauka yana ta murna, Aliyu kan cewa yayi "Mun samu ƙarin ƴan shagwaba a gida"


Daddy ya ce "Ita ma idan ta tashi taga iyayen ta suna yi yi zata ay"


Ita kan Bilkisu tana ɗaki abin ta.


Ashe gari da Sassafe Daddy ya shigo har ɗakin mai jegon ya same su duka a ɗakin Maryam ta shirya zata tafi Aliyu Kuma ya kalmashe ƙafa yana cin tuwon me jego Daddy ya kalle shi yace "Kai kuma yau anan kake karyawan "

Ya ce "To Mommy ta tare anan wai sai ta sallami me jego ni kuma zan tafi kuma yunwa nake ji"



Mommy ta ce "Shine ay nasa mata tuwon bata ci ba ta miƙa masa shi kuma da yake maye ne ay gashi ya cinye"


Ita ko Bilkisu kanta na sunkuye so take ta gaishe da Daddy amma yana ta surutu.


Daddy ya kalleta ya ce "To kuma ita da safen nan tuwo take ci"


Mommy ta ce " To ay shi zai kawo mata ruwan nono, bayan taci tuwon sai tasha tea "



Suna ta magana har Maryam da Aliyu suka tafi bayan sun tafin ne ya ce "Mommyn yara kin kira mutanen nan kin faɗa musu maganan haihuwan nan kuwa, kinga sai su faɗi sunan da za'a sawa yarinyar su"


Ta ce "Ay ko baza su ji ba ba wanda zaiji haihuwar, maganan suna kuma ga uwarta ta zaɓar mata"


Ya ce "Haba ya kamata a faɗa musu dai"



Ta ce "Alhaji yarinyar nan ta wulaƙanta a gurin su, sai aka samu ma uwarta bata kula da ita ba, ta barta kara zube, ka kyale su kawai "


Ya ce "To shikenan nima zan tafi idan kunyi shawaran sunan da za'a saka mata, da yamma idan Aliyu ya dawo sai ya mata huɗuba. "


Daddy yana fita Mommy ta ce "Kun taɓa shawaran sunan da za'a saka mata ne da Baban yarinyar nan"


Ta ce "Eh, Dama ya ce idan mace ne sunan mahaifiyarsa za'a sa, idan Namiji ne mahaifinsa"


Ta ce "Ya sunan Mahaifiyar tasa"

Ta ce "Sauda"


Ta ce "Sauda suna mai daraja ne, sunan Matar Annabi Muhammad (SAW) ta biyu kenan. "






_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/4, 8:44 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 57-58






Da yamma kuwa kuwa Aliyu naya dawo wa aka masa bayanin komai, ayko ya mata huɗuba da Suna NANA SAUDA.


Ranan suna kuwa bikin akayi sosai Aliyu ya yanka mata rago, anci ansha, Sauda da uwarta sun samu kyautuka daga wajen ƙaqayen Mommy da Abokan arziki, Haka Aliyu ma ba'a barshi a baya ba dan ya gayyato abokanan sa sun musu kyauta sosai, Maryam kan kamar ita ce mai jegon sai shiga take tana fitowa Sauda kuwa tasha jagwalgwalo a gurin ƙawayenta har kwalliya saida tasha.


Maryam ta ce "MAISUN Za'a na kiran ta saboda da sunan Uwarsa ce bai kamata ana kiran sunan ba"




*** *** ***



Tunda Ruky ta dawo gidan Alhaji bai kula su ba, an mata ɗauri amma abu yaƙi ko yaushe hannun a kunbure kullun cikin tsinewa Umar take kuma taci Alwashin sai ta rama abin da ya mata idan ya shigo hannunta.

Mama Amarya ke jinya. Duk kuɗinsu ya ƙare akan hannun kullun cikin kuka da hannun Ruky take. Shi kuwa Alhaji yanzu tunanin sa shine ya zaiyi ya dawo da Umma yana kunyar yi mata magana, gashi ita kuma takan kira ta gaishe shi lokaci-lokaci kuma takan kwantar masa da hankali, haka yaran nasa ma, sukan kwantar masa da hankali, duk abin da yake so suna bashi da yake ko wannen su yana aikinsa, duk kan lauyoyi ne masu zaman kansu kuma Albashinsu me tsoka ne, tunanin su yanzu inda Bilkisu take abin yana damun su a rayuwa.


Sun shigo a tare Cikin falon suka ga Alhaji ya zauna a kujera ya zuba tagumi, Sunyi magana amma shiru Usman yaje ya kama hannunsa yayi firgigit Abubakar ya ce "Tunanin Bilkisu kake ko"


Ya ce "Ba Bilkisu kadai ba, harda Umar ko ina ya shiga shima har yau shiru ba'a ganshi ba, ko yana lafiya, duk inda yake nasan shima yana cike da tunaninta duk da shi ya sata a wannan halin amma ay ba a hayyacin sa yake ba, Sai kuma tunanin Umman ku, ina son ta dawo ɗakinta amma kuma na rasa yadda zanyi in sanar da ita"


Usman yayi murmushi ya ce "Haba Abba ko mu yara baza muyi wannan ba, Umma fa taka ce, amma kace ta dawo kawai yanzu zaka ga ta dawo"


Ya ce "Ina jin kunyar yi mata magana ne ay, irin abin da na mata ay da kunya ace na dawo"


Abubakar ya ce "To Abba kada ka damu mu zamuyi maka komai, ay mu bama jin kunyar ta, Umma zata dawo ɗakinta, an bar wannan matsala ko"


Ya ɗaga kai, Abubakar ya ci gaba "Maganan Bilkisu da Umar kuma ka daina damun kanka, mudai muyi ci gaba da yi musu Addu'a, sannan kuma Abba ya zaka yi da wannan matar kasan dai baza ka ci gaba da zama da ita ba ko"

Ya ce "Talatuwa ta cuce ni ban san irin hukuncin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login