Showing 21001 words to 24000 words out of 62424 words

Chapter 8 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2846

gyara kicin din sai da ko ina ya koma tas sannan taje ta sake yin wanka ta shirya kanta ta zauna bakin katifar. Bata daɗe ba, Baba ya turo ƙofa ya ce "Kizo mu ci abinci mana"


Ta ce " To" hijabi tasa ta fito


Ta fito ta same su duka sun zauna tana zuwa ta gaida Baba sannan ta gaida Umar, Mama Sauda kan ta riga ta gaidata dukda amsawantan masifa ce"


Baba ya ce "Yau ƴata ce zata zuba mana abinci"


Ta tashi ta ɗauki plate ta zuba wa Baba sannan ta ɗauka ta zuba na Mama sauda ta ce "Aa barshi, ta miƙawa Umar, "

Baba yayi mata wani kallo ita kuma sai ta kauda kai ta ce "Ina da hannu ay zan zuba da kaina"


Baice komai ba, sai ya kalli Bilkisu yaga ta zuba nata kaɗan ya ce "Ayko sai kin zuba da yawa, ji yadda kika sa nawa da na Yayanki ke kuma naki kaɗan"


Ya amshi plate din ya sake zuba mata d yawa ya haɗa mata tea ya tura mata kwai da Arish ya ce "Ko kina son bread ne, dan mu idan mun samu wannan bama hadawa da shi saidai wannan yayan naki ne sai yaci, kinga idan zaki ci kuny biyu"


Ta ce "Aa Baba nima bana ci"


suka fara cin Abinci Mama Sauda ma ta zuba nata tana ci tana harare-harare duk Baba yana lure da ita, duka abincin ya ƙare, Umar ya buɗe kulan Abincin yaga wayam, ya ce "Wai ya ƙare ne"

Baba yayi dariya, yace "Bilkisu yau kinsa munyi ɗurin Abincin da bamu taba yi a gidan nan ba"


Ya kalli Sauda da take ta ɗurawa ya ce "Ga Mamanki ma sai Ɗurawa take tayi"


Miƙewa tayi ta tashi tayi ɗaki, shi kuma Umar ya dauki sauran na Maman yasa a nashi plate din yana ci,


Baba ya ce "Allah ya miki Albarka, yanzu ni nasan mijinki zaiyi alfahari da ke, kota ta wajen girki, balle ma ba tanan kaɗai kika tsaya ba, kalli gidan nan yadda ya sauya a zuwanki jiya-jiya nan, kafin mu samu abinci irin haka a gidan nan tun Mamanku tana Amarya, mun gode Allah ya miki Albarka Bilkisu, Allah ya kare ki daga sharri mutum da Aljan"


Ta ce "Amin Nagode Baba"


Umar ya gama zai tashi da kofin tea a hannunsa Baba ya ce "Zo ka bata tukuici Malam, ka cika ciki ka tashi zaka yi gaba"

Ya ce "Ba wani daɗi fa abincin yayi ba, na cinye ne kada ayi asaransa"

Baba ya ce "Ƙarya kake, ruwan tea da bread kadai kake sha a gidan nan, ko anyi abinci baka ci saidai ka barshi ya bushe anan, amma yau har ragowan na wani ka cinye, kafi kowa ci, anan, Ni mamakin ma da nayi, da naji tea din yana wani kalan ƙamshi, na kasa barinsa duk da na ƙoshi"


Umar kan shiru yayi ya fita abinsa, Baba ya ce "To yau kada kiyi abincin rana da shi"


Yayi murmushi ya ce "Ashe ko ita baza ta ci ba"


Nasiha Baba ya mata, sannan ya ce "Zan fita koda abin da kike son na siyo miki"


Ta ce "Ba komai, Allah ya tsare Allah ya dawo mana da kai lafiya"


Ya ce " Amin"


Shiga ɗakin Mama Sauda yayi, can ya fito ya fita, Motarsa tana fita Mama Sauda ta fito ta same ta tana haɗa plate zata wanke. Ta ce "Kinzo kin sa mijina ya fara faɗa min magana ko to bari kiji idan ya sake faɗa min magana sai na karya ki Wawiya, kuma kije ki gyara min ɗaki da na mijina"


Ta koma, Umar ya shigo rankwashinta ya fara yi sanna ya wuga mata key ya ce "Kije ki gyara min ɗaki yanzun nan, kuma akwai ƙananan kayana a bayi ki wanke min su tas, saura in dawo in samu bakiyi ba, ko inzo in samu kin kawo min kwarto ɗaki"


Ɗauka key ɗin tayi ta ajiye a kan table ɗin tayi ɗakin Mama Sauda tana shiga saida gabanta ya faɗi ganin yadda ɗakin yayi kaca-kaca kamar ba ɗakin mace ba, nan ta shiga gyarawa da tazo shara kuwa kamar tana share bola, tana shiga bayi dan ta wanke saida ta toshe hancin ta dan wari, saida ta ɗauki dogon lokaci tana gyarawa sannan ta gama, ta shiga ɗakin Baba, nan ma yayi datti amma baikai na Mama Sauda ba nan kan bata sha wani wahala wajen gyaransa ba, Ɗakin Umar kan gyaran kaɗan ne, kana shiga zaka san me ɗakin yana da tsafta, dan komai nashi a kintse, haka bayin ma, under weres din ne ma ya ɗan tara da yawa, ta wanke su, ta shanya sannan ta rufe ɗakin ta fito da makullin.


tana fito wa ta ɗora tuwon semonvita da miyar ɗanyen kuɓewa sai bushashshen kifi da tasa a ciki, gida ya buɗe da kamshi.


Bayan ta gama komai tayi wanka bata yi wani kwalliya ba tasa kayanta ta fito ta je, ta kwaso kayan, harda goge su tayi, wai dan yaji daɗi ya yaba mata ya daina ci mata fuska. Tana gamawa ta koma ɗakin ta, ta kwanta, barci ya fara daukanta, bata jima da yin barcin ba, aka kira Sallah la'asar ta tashi taje ta ƙara kintsa Falon da gurin cin abincin, dan tana fashin Sallah, ta zauna, Umar ne ya fara shigowa yana zuwa ya nufi gun abinci da kansa ya zuba ya fara ci, sannan yasha kunun ayan da ta haɗa, ya tashi kenan zai tafi Baba ya shigo tayi masa sannu ya miƙa mata leda yace "Gashi naki ne"


Ta masa godiya ta ajiye, ya shiga ɗakin MAMA Sauda can ya fito ya samu Umar Zaune lokacin ya gama ci ya zauna a falo yana kurɓan kunun aya. Ya ce "Nima a zuba min ko"


Ta zuba masa ta kawo masa tsakiyan falo ya fara ci yana santi, saida ya gama ya ce "Ki huta da daddare wannan sauran ya ishe mu"

Fita yayi ya barta da Umar shi ɗaya ta miƙe taje ta dauki tuwon guda ɗaya ta zuba miya a plate din da Baba ya ci, ta wuce ɗakinta, ta zauna ta fara ci kenan Umar ya shigo ya ce "Bani key"


Ta sa hannu ta miƙa masa, saida ya kama hannun ya matse mata sannan amshi key ɗin, ta ce "Allah ya isa na"

Ya ce "Barin dawo ki faɗa min awa kike jan Allah ya isa"


Tuwon ta taci gaba da ci, a ranta tana cewa "Ka dawo duk abin da zaka min ka min, idan duka ne, na saba sha ba kashe ni zaiyi ba"

_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 31-32



Yana shiga yaji ɗakin sa ya bada wani daddaɗan Ƙamshi mai sanyawa zuciya farinciki, ko ina ya shiga ƙamshi har bayin komai ta ajiye shi a ma'adanan sa, kamar dama tasan yanayin ɗakin, yaji daɗi kan kan har zaka iya ganewa a fuskarsa idan ka shiga sai dai idan ya tuna yarinyar da ta masa wannan abin irin halinta sai ya fara haushi, kuma yaji ya tsane ta, ya tsani yarinyar da ta bada kanta a waje, kyamar ta yake yi koda ta matso kusa da shi, saidai ita wannan ba inda zai da ita saboda Babansa, sake jin haushin da kyamarta yaji, ya fara duba ɗakin yana son yaga wani abin kushewa yaje ya kusheta, shi yasan ba abin kushewa, tayi abin da za'a yaba mata, kuma ƙarya take ya yaba ɗin.


*** *** ***


Mama Amarya kuwa tayi nadama da tasa aka kori Bilkisu gashi yanzu aikin gidan ya caɓe mata, dama Ruky ba taya take ba saidai tayi wanka tasa ƙananan kayanta ta fita abin ta, yanzun kan ma abin nata ya daɗa gaba, dan har ɗaki take shigar da saurayin ta suyi abin da zasuyi su fito, gidan duk a lalace shiko uban gayyar ba abin da ya dame shi, baya neman yaransa, ko Khadiyo baisan inda takeba amma kuma baya ko neman ta, yana musu kallon masu takura masa a rayuwa, yanzu Mama Amarya ce da ƴarta a cikin ransa ko ɗan uwansa baya son yana raɓansa, baida wani dangi da ya wuce Mama Amarya da ɗiya. Ta dawo kenan da ƙananan kaya a jikin ta, sai nishi take saboda yadda kayan ya matse ta. Ta zauna akan kujera ta fito da kuɗin ta tana ƙirgawa Mama Amarya ta matso ta ce "Wannan fa a ina kika samu"


Ta ce "Wallahi Wani shegen Alhaji na haɗu da shi mai sakin kuɗi Mama kinga kuɗin da ya bani"



Mama Amarya ta ce "Shege yaga kyakykyawan mace, kinga dama muna neman kuɗin da zamu kaiwa boka akan maganan auren ku da Umar, muna son mu jawo hankalin Uwarsa ma, kinga saida yardan ta za'ayi komai ko"


Turo baki Ruky tayi ta ce "Haba Mama ba kina da kuɗi ba, ki tambayi mijinki ya baki mana, ni a dan wannan kuɗin nawa za'a sawa ido ni gaskiya A'a bazan yadda ba"

Mama Amarya ta wafci kuɗin ta ce "Duk abin da ake ba akan ki ake ba zaki ce a bar miki kuɗin ki"


Kai hannu Ruky tayi zata wufta suka fara kokawa har wasu daga cikin kuɗin suka yage, nan fa Ruky ta buga tsalle ta ce "Wallahi sai kin biyani kuɗi na"


Mama Amarya "Ruky me zaki da kuɗi haka ne"


Nan fa Ruky tayi ta yi masifa wa uwarta karshe dai uwar ta fara rarrashin ta sannan ta ce zata biya ta.



*** *** ***


Aikin gidan sam baya damun ta, abin dake damun ta bazai wuce tsangwaman Umar da Uwarsa ba, suma idan Baba yana nan basa mata, watan ta kusan biyu a gidan, yanzu tunanin Ummin ta take ko a wani hali take ciki, tana son taje ta duba ta ganta.

Baba kuwa ya gane tana cikin damuwa dan haka ya kira ta falo ta zauna a gefen ƙafan sa Ya ce "Bilkisu lafiya na ganki bakya walwala me ya faru ne faɗa min"


Ta ce "Ina son in je inga Ummi ne"

Ya ce "Shine baza ki faɗa min ba, gobe lahadi ki shirya sai yayanki Umar ya kaiki, ay kinsan inda take ko? "


Ta ce "Nasan bazai wuce tana gidan Sarki ba"


Ya ce "To shikenan Umar zai kaiki, ya baro ki a can kiyi kwana biyu sai ya ɗauko ki, kuma zaki fara zuwa makaranta ki zana jarabawa, bayan kin zana idan kina da tsayayye sai ki fitar kiyi auren ki, in yaso sai kici gaba da makarantan a ɗakin mijinki"



Shiru tayi idanuwanta ya ciko da kwalla, ganin haka yasa ya ce "Faɗi abin dake ranki"


Ta ce "Baba kayi haƙuri ni nafi son makarantan abar maganan auren nan, ni bana kula kowa ma"



Ya ce " Shikenan dai, goben ki shirya ko, ki rubuta me da me za'a kai mata sai a siyo mata"


Ta ce "To Nagode Baba "


Washe gari Sassafe ta shirya ta haɗa da tsaraba ta fito, tana tsaye, Baba ma ya fito ganin Umar bai fito ba yasa Baba ya ce "Shiga ciki ki masa magana"


Ta shiga saboda gan ɗoki ko Sallama bata yi ba ta faɗa ciki, ganin sa tayi da towel a ƙugunsa yana tsane ruwan jikin sa da ɗan ƙarami, ta juya ta bashi baya ta ce "Baba ya ce "Ka fito mu tafi"


Bata san yana matsowa ba sai ji tayi an kamo mata hannayen ta ta baya ya banƙaro ta ya kai fuskarsa daidai kunnen ta ya ce "Ke wace irin daƙiƙiya ce baza ki sallama ba, ko kwartancin naki ne ya motsa"

Tana ƙoƙarin ta kwace hannunta amma ta kasa. Ya riƙe hannun nata da hannu ɗaya, ya nuna ta da yatsa ya ce "Saura idan munje kije ki samo kwarto ƙauye"

Jin haushin maganan sa yasa ta tofa masa miyau a fuskar sa, ya sake ta ya ce "Ke! "


Zata gudu ya kuma kamota ya haɗata da kirjin sa, ta kalle shi cikin ido ta ce "Wannan wani irin iskanci ne, "


Ya ce "Saikin lashe ƙazantar da kika zuba min "


Kokawa suka fara, gaba ɗaya ta canja masa yanayi a jikin sa dan ji yayi kamar tana masa cakulkuli a jiki, baida wani ƙarfi a jikin sa, hannu tasa a kirjin sa ta tura shi kan gado, da sauri ta fita, shiko gunda tasa hannu ya kama yana jin zuciyar sa tana wani irin bugu wanda bai san ko na menene ba. Ido ya lumshe ya miƙe da kyar ya fara shiryawa.


Da ta fito kuwa Baba ya ce "Ina yake"

Ta ce "Yana shiryawa"


Ba jimawa ya fito, Baba ya saka mata kayanta a mota ta shiga shima ya shiga gurin driver Baba ya musu Allah ya kiyaye, sun fara tafiya zasu fita a get ɗin Ya ce "Bari mu fita a cikin gari, zaki san kin zuba min ƙazantarki a fuskata"


Shiru ta masa ita dai burinta ya kaita gun Ummin ta





_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/27, 9:21 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 33-34






Hanya suka ɗauka sai dai kirjinta na dukan uku-uku, sun shiga cikin daji saidai ga mamakin ta ko tsayawa ma baiyi ba har suka sauƙa akan titi inda zasu ɗauki hanyar rugan, suna isa ta nuna masa gidan Sarkin Fulani a ƙofar gidan yayi parking, ya ce "Allah yasa ma baza a ganta a gidan ba, kije ki duba "



Bata ce komai ba ta fita a motar ta shiga gidan da Sallamartar, ta gaida mutanen gidan bayan sun gama gaisawa ta ce " Inna neman Ummina"


Ɗaya daga cikin matar ta ce "Wacece kuma wannan"

Ta ce Hali

Wata daga ciki ta ce "Kodai kece Balki"


Ta ce "Eh nice"


Ta ce "Bari a kira miki ita ko"


Ta mike ta shiga wani ɗakin saiga Ummi ta fito daga qani ƴar bukka, Bilkisu taje da gudu ta rungumeta sai kuma ta saki kuka mai ban tausayi, cikin kuka tana cewa "Haba Ummi, tun da kika tafi ko ko waiwaye mu kiga halin da muke ciki amma kika ki, kinsan irin ƙalubalen da muka fuskanta ne, Haba Ummi me yasa"


Share mata hawaye ummi tayi tayi ta jata zasu yi ɗaki sai kuma ta ce "Tare da Ya Umar fa muke yana waje"


Ta ce "Je ki shigo da shi"


Ta fita yana ganin fuskar ta duk hawaye yayi Dariya ya ce "Allah ya amshi Addu'a ta"


Ta ce "Ta ce ka shigo ciki"


Bata masa magana ba ta ɗauki kayanta da tsarabar da Baba ya mata, tayi gaba ya bita a baya saida suka je soron gidan ya tare ta, ya ce kawo akwatin munafuka, salon muje Ummi ki taji haushi na barki da kaya da yawa"


Cikin ranta ta ce "Ay ba munafuki irin ka,"


Ya fizga harda sauran kayan, ita ko kamar zata yi dariya dan Abin ma dariya ya bata, tayi gaba ba tare da komai ba, shi kuma ya rike kayan.

Suna shiga Suka samu Ummi ta shimfiɗa musu tabarmar kaba, suka zauna, ta kawo musu ruwa da madara, suka sha, nan akayi ya gaisawa da shi, Ummi taji dadin yadda taga Umar yana kula da Bilkisu, wanda sabanin da da yake hantaranta. Bayan ya ɗan huta, ya ce "Ummi ni zan koma, kwana biyu zata yi, zan dawo in ɗauke ta"

Ta ce "To Umar nagode idan kaje ka gaida min kowa da kowa, kayi wa Baban ka godiya "


Bayan ya shiga mota kuwa aka kawo masa ƙwan zabi da kuma madaran shanu, bayan kowa ya koma Bilkisu zata shige Umar ya kirata, ta koma da baya taje, yayi mata alama ta buɗe ta shigo, ta buɗe ta shiga ta zauna, ya riƙe mata kunne ya ce "Saura kuma kije ki bawa wani ɗan ƙauye kanki ko kuma idan nazo ɗaukanki nazo na samu baki shirya ba, sai kin yaba wa aya zaƙinta"


Saida ta fita sannan ta ce "Ina ruwan ka, idan na nawa wani kaina ɗin ma ay ba kai nabawa ba, kuma jikina ne ba jikinka ba, kuma ay bani nasa kazo ka ɗauken ba idan kaga dama ma kada kazo, ni ina ruwana tunda ina tare da uwata"


Buɗe murfin ƙofa yayi zai fito sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login