Showing 3001 words to 6000 words out of 62424 words

Chapter 2 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2843

bayan ba'a sallame ku ba"


Ta ce "Kaidai bari mudai fa bamu yadda ba asibiti ba gaskiya duk da 'yar nan idan tazo tana nuna mana muna yadda amma ina baza mu taba yadda ba"

Alhaji ya budi baki zayi magana kenan yaga mutane sun shigo tare da Baffa cikin su harda limamin da kuma Sarkin Fulanin rigar, Baffa ya ce "Ga nan liman wannan kuma sarki ne yazo da kansa dan haka sadaki kawai zaka bada a daura ka tafi da matar ka." Alhaji ya kasa cewa komai, yayin da Inna da Hali suka yi cikin bukka.







_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/15, 7:17 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 5&6




Baffa ya dauko babban taburmar kaba ya shimfida suka zazzauna shikan Alhaji Ibrahim yana ta kallon ikon Allah.

Liman yayi gyaran Murya ya ce "Alhaji ina Waliyyinka? "


Kafin yayi magana Baffa ya ce "Ni zan wakilce shi, Allah gafarta Sarki kuma zai wakilci HALIMA"


Alhaji kan yana shiru, sai a lokacin ma yaji sunan ta.


Liman ya ce "Ina Sadakin"

Shiru Alhaji Ibrahim yayi yana tunanin wannan wani irin mutum ne zai bada ƴarsa a mutumin da bai sani ba, hakan yana nuna masa ƙauna ne ko tsabar yadda ne da yayi da shi, to ma idan ya aure ta ina zai kai ta, me zai cewa iyalen sa game da ita, ya sani Suna da fahimta kuma zasu fahimce shi to amma ay hakan bai dace ba.

Jin Muryan Baffa yayi ya ce "Alhaji kawo duk abin da ya sauwaka kawai kada ka damu"


Ya ce "Dubu goma ne a jikina Baffa barin je mota in dauko"

Ya ce "Dauko su"

Ya sa hannu a Aljihu ya ciro ya mika masa Baffa ya cire dubu biyar ya mika masa sauran ya ce "Biyar ma ya isa"

Mamaki Alhaji ya kuma yi, yana kallon su suka daura auren sa da Hali kan sadaki dubu biyar anan aka raba goro kowa sai farin ciki yake, shiko yara sa cikin farin ciki yake ko baƙin ciki wannan wani irin aure ne.


A hankali aka watse aka barshi a gurin ya rasa inda zaiyi, yana daga zaune yaga Hali ta fito Inna tana rike kullin kayan suna kuka, Baffa ya ce " To Hali kiyiwa Mijinki biyayya Allah ya kara lafiya Allah ya baku zaman lafiya, kuma kiyi wa Abokan zaman ki biyayya kinji"


Ya kalli Alhaji yace "Alhaji ga Halima Amanace a gurin ka Allah ya baku zaman lafiya"

Sai a lokacin Alhaji ya ce "Baffa a bari tukun zan dawo na dauke ta"

Ya ce "A'a Alhaji dauki matarka ku wuce kawai"


Alhaji zaiyi magana sai gani yayi Baffa ya dauki kullin kayan ya ce "Muje Alhaji kada dare ya muku"


Baida ta cewa haka ya bisu ita kuwa Hali makofta ne suka rakota har bakin mota yayin da Inna ta koma ciki tana kuka ita ma.


Baya ta shiga da kullin kayanta sai lokacin ne Alhaji Ibrahim ya ce "To Baffa na gode "


Ya ce "Kada ka damu Alhaji Allah ya kiyaye"


Ya ja motar ya fara tafiya yana sake sake cikin ransa yayin da ita kuwa take ta kuka marar sauti.

Suna Isa gida Yaran su uku lokacin Umar ma yazo suka zo har bakin motar suna masa oyoyo, koda suka ga Hali sai suka fara kallon ta tana kuka. Abubakar ya ce "Abba ka siyo mana Aunty ne"


Da yake baiji abin da ya fada ba, shi ya san ya masa maganar ta sigar tambaya ne yasa ya ce masa "eh"


Da gudu suka juya suna cewa Mama Suwaiba Abba ya siyo mana Aunty. Kallon su kawai yayi ya kada kai ya dauki faggon kayan nata ya ce "Ki daina kukan nan haka, mu shiga ciki "

Yana tafe tana binsa a baya har suka shiga falon ba kowa a falon ya ajiye kayan ya ce "Zauna ko"

Ta zauna can gefe guda a takure tana kuka, shi kuma ya shiga ya kira matan gidan suka fito Umma Aisha tana ganinta ta ce "To Alhaji ina ka samo mana bafulatana haka kuma kukan me take"


Zama yayi ya ce "Ku bata Abinci da ruwa kafin kuji wacece ita"

Usman yayi saurin miko mata Abincin da ya rage ya na cewa "ay anan zata zauna kuma ita zata na min wanka ko"


Mama Suwaiba Ta ce "Bana hana ku idan muna magana kuna zama a gurin ba"


Tuni suka watse suka koma gun wasan su.

Koda aka bata abincin bata wani ci sosai ba ta barshi dan bata ma saba da irin abincin ba, ko da ta saba ma baza ta iya cin ba. Saida ta zauna Alhaji Ibrahim ya fada musu komai game da yariyar sannan ya ce "To Ya kuke ganin ya dace ayi kenan yanzu"


Umma Aisha ta ce "Daki za'a gyara mata a sata a ciki ita ma ay a matsayin mu take yanzu"


Mama Suwaiba ta ce "Alhaji basai ka boye mana ba idan zakayi aure, ka fito fili ka fada mana kana son yin Aure kuma ka auri karamar yarinya kawai, taya za'ayi daga gaisuwa ubanta be sanka ba ya ce ya aura maka ita gaskiya wannan da sake"


Baidai ga yin magana ba Umma ta ce "Haba suwaiba mijin kuma kike karyatawa kuma a gaban sa kai gaskiya ban san ki da haka ba"

Ta ce "haba Yaya kina yanzu kin yadda da wannan zancen, idan zakayi auren ka ay bamu hana ka ba, amma bai dace kazo kana fadan irin wannan maganan, ba taya za'ay yarinya kamar wannan siyi wa yarsu haka nikan gaskiya ban yadda ba"



Alhaji zaiyi magana sai Umma ta dakatar da shi ta ce "Alhaji kaje ka huta a daki kaga a gajiye kake zamu ji da komai"

Ya ce "Amm..." ta dakatar da shi "Kada ka damu kaje kawai zanji da komai"


Ya kalli Hali da har lokacin kanta a sunkuye tana hawaye wannan lokacin ba kukan sai hawaye, ya ce "Ki sannan yarinyar tayi shiru haka dan Allah"


Yana gama fada ya tashi yayi dakinsa, ita kuwa kama hannun Hali tayi ta ce "Haba Halima kiyi shiru haka kukan nan ya Isa haka kanki zaiyi ciwo kuma gashi ba lafiya gare ki ba, kuje ki dan kwanta ki huta kafin Magrib tayi ko"


Ta miƙar da ita sukayi daki sannan ta ce "Idan kina da bukatar wani abu kiyi magana kinji, saida ta kwantar da ita sannan ta wuce dakin Mama Suwaiba ta same su ita da yaran duka a kan gado ta ce "Kuje falo zamuyi magana da Maman ku, "

Suka fita da gidunsu ta kalli Mama ta ce "Haba Maman yara me yasa kika yiwa mijinki haka kin sani bazai ji daɗi ba "

Ta ce "Haba Yaya yanzu ke kin yadda da wannan maganan tasa, ya za'ayi ace yarinya kamar wannan amma ace iyayen ta sun Mata hakan basa son ta ne ko me"


Ta ce "Ni na yadda da shi mijina bai taba min karya, kuma bana tunanin randa zai min karyan, wannan na dauke shi a matsayin jarabawa ce da Allah ya aiko mana da ita daga mu har shi, banda abinki wannan ay yarinya ce mu zamu bata tarbiyyan da ta dace, mu zamu lankwasa ta yadda mike so idan muka bata tarbiyya me kyau mu zamu ci riba idan kuma muka yi mata akasin haka, mu zamuyi kuka nan gaba dan haka ki cire wannan a ranki mu rungumeta hannu bibbiyu.


Ta ce "Yaya kenan nasan baya min karya amma wannan karan ban yadda ba"

Umma tayi murmushin karfin hali ta gano kishi ne ke damun ta, ita din ma haka to ba yadda ta iya haka ta danne zuciyarta tare da yiwa Allah tasbihi, amma ita ta kasa danne nata, amma haka tayi ta tausan ta har Mama Suwaiba taji kunyar Alhaji da kuma ƙaramar yarinyar haka taje ta bashi hakuri.


A dakin Umma Hali ta zauna tun tana kewan Innan ta har ta hakura saboda ta saba da su Abubakar Aunty suke ce mata sai Mama Suwaiba ta ce "Ummi zasuna kiran ta ay ita ma uwa ce" idan zasu shiga kicin tare suke shiga har ta koyi girkin zamani harma da wasu na gargajiyan biyayya sosai take musu tana ganin Mama Suwaiba zata yi abu ta ce "Mama kawo inyi, ko kuma idan Umma ne ta ce kawo inyi Umma, kullun idan yara zasu tafi makaranta ita take musu girki, Hali tayi kyau sosai ta zama yar gayu ita kanta idan ta kalli kanta a madubi tana ba kanta sha'awa ta zama ƴar gida ba inda bata sani ba a gidan kuma duk abin da taso take yi ba me mata magana, lokaci-lokaci takan yi tunani yanzu waɗannan kishiyoyinta ne, ita dai a rigagen da suka zauna idan anyi wa mace kishiya sun ringa bala'i kenan, sai daga baya ta gane ay kishiyoyin ma akwai masu ilimi, to ita da masu ilimin ta hadu.


Shekaranta daya da wata hudu a gidan Mama Suwaiba ta ce "Ya kamata mu dubo su Baffa Buba kaga tunda ka daukota bamu kara zuwa ba"

Umma ta ce "Gaskiya kika fada kan"

Ya ce "To sai ku shirya mana tafiyar kusa mana rana"


Umma ta kalli Hali ta ce "Ko dai bakya son zuwa ne Halima"


Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta ce "Ina so mana Umma"

Duka dariya suka mata Mama Suwaiba ta ce "Zanga randa zaki daina wannan kunyar taki, kuma muna dawowa zaki tare a dakin mijinki dan yanzu kan zaki iya karban miji"

Tana jin maganan Miji ta tashi ta ruga da gudu sai dakin Umma, duka dariya sukayi Mama Suwaiba ta ce "Alhaji wannan kunyar taka idan kuka tare sai kasha fama da ita"


Ya ce "Shi yasa nima nace ku kyale ta ba yanzu ba, sai ta kara girma "


Umma ta ce "Ayko muna dawowa zaku tare, hada mu dau hakki, Hali tana da jikin girma idan ta kara yaya, gwara ka tare da matar ka idan ma kasar zaku bari tare kuje can ku kare"


Ya ce "Naga Halama matan nan sun daina so na tunda suna nema su hada ni da bafulatana"


Mama Suwaiba ta ce "Son kenan akwai wani so ne da ya wuce wannan"


Su suka haɗa tafiyar tare da tsaraba, suka shirya suka tafi riga saidai Labari ya sha bam-bam dan gurin bukkar ba kowa ko bukkar ma babu, Hali tana ganin haka tasa kuka Umma ta ce "Ke me haka kika sani ko sun canza waje ne"

Ta ka'da kai cikin kuka ta ce "Wallahi Umma basu kada kai ba sun tashi ne sun tafi sun barni "


Alhaji Ibrahim ya ce "Ko sun tashi ay su sarki zasu san inda suka je "


Ta sake kada kai ta ce "Ba wanda zai sani baza su fada wa kowa ba kuma ma baza su san lokacin da zasu tashi "


Alhaji ya ce "Muje gun sarki", bayan an musu tarba ta musamman Sarki yake basu Mummunan Labari ya ce "Bayan tafiyan ku Mutanen ringan nan suka ringa tsegumi wai Buba ya siyar da Bilki yanzu gashi ya siyar da Hali, na tsawatar amma ina har saida taka idan an ganshi ake gudu wai ya siyar da yaransa ma balle su, abin da ya ishi Buba sai ya kaɗa shanun sa ya dauki matarsa suka bar rigar nan, da daɗewa ita Addan nata Bilki tazo ita ma tasha kukan ta har tana cewa da tasan da auren da baza'a taba yi wa ƴar uwanta irin wannan aure ba. Haka ta koma"


Hali ta ce, "To ka kaini gurin ta mana"


Ya ce "Garin da take Babban gari ne ko munje baza mu gano inda take ba tunda bamu sani ba"

Alhaji ya ce "wani gari ne"


Ya ce "Tana cikin birnin Kaduna"


Shiru Alhaji Ibrahim yayi yayin da Sautin kukan hali ke tashi Su Umma na lallashin ta.


Karshe haka suka dawo gida saidai sun bada Address kan cewa duk lokacin da Addan ta tazo a kawo ta, duk da sunsan baza ta zo ba tunda tasan ba Iyayen ta...




_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/15, 7:50 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_



*Wa shafi naki ne Mrs Basakkwace kiyi yadda kike so da shi in kinga dama ki hana kowa karantawa, Ina son ki Khadijatul kubra*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 7&8




Sunyi niyyar ta tare da Alhajin ganin tana cikin damuwa yasa suka kyale ta kuma suka yi ta kwantar mata da hankali suna bata baki kan cewa ko ta rasa iyayen ta ay tana da su, kuma suna sa ran ko wani lokaci Addan ta Bilki zata zo gare ta.


Saida ta kwantar da hankalinta sosai sannan suka gyara mata daki aka saka mata kaya sosai Mama Suwaiba ne tayi ta sata a kan hanya ta yadda zata kula da shimfiɗar mijinta, da farko taki ta ce ita a dakin Umma zata c gaba da zama saida suka nuna mata ɓacin ransu sannan ta amince, ta tare a ɗakinta, sun ce ta huta zasuna aikin gidan amma taki nan ma saida Mama Suwaiba ta mata da gaske sannan ta Amince, da hutun saidai ba satin ta guda taki ta fito tana yin aikin gidan badan sun so ba suka kyale ta, Sassafe idan ta tashi zata fara gyaran gidan sannan ta shiga kicin ta musu kumallo bata barin su suyi wani aikin sudai nasu Miji ya shiga dakin su, Alhaji Ibrahim yana lure da ita yana jin dadin kasancewarsa matarsa bata rage shi da komai ba, ko fushi taga yana yi sai tasan yadda tayi ta kwantar masa da hankali, da farko yana jin kunyar kasancewa tare da ita kasancewanta yarinya karama amma daga baya ya lura yarinyar ba irin wacce za a ji kunya bane, dan su Mama Suwaiba sun nuna mata koda zana jin kunyar kada ta ji kunyar mijinta.


Mama Sauda kuwa ganin Hali yariya ce ta fara shiga dan ta zugata saidai kuma bata samu nasara ba dan Umma da Mama Suwaiba sun ɗora ta akan turba me kyau karshe ma ce mata tayi "Kinga Mama Sauda Idan fa baki barni ba zan fada wa Umma da Mama su dau mataki a kanki"


Ta ce "Eyeh! Umma da Mama ma kike ce musu, niko me zaisa iyi wannan in kira kishiya ta Umma ko Mama"


Hali kuwa Murguɗa mata baki tare da jan wani dogon tsaki tayi ta tashi a gurin.


Haka ta hakura bata sake bi ta kansu.


Watanta biyar da tarewa Umma ta fahimci Hali ciki gare ta, saboda farin ciki bata iya boyewa ba ta fada wa yan gidan, tana ji kuwa Hali ta shige ɗaki ta kasa fitowa duka dariya suka yi har kowa yayi shiru Alhaji ya kasa rufe bakin ji yake kamar yau za'a fara masa haihuwa, Mama Suwaiba ta ce "To Alhaji rufe bakin mana"


Ya ce "Ohhh wai bakin a buɗe yake"


Tunda aka bayyana cikin take zaman ɗaki bata fitowa sai idan taga ba kowa a faron zata fito da dogon hijabinta tayi abin da zata yi ta koma, suna lure da ita hakan ma ya basu daman yin aikace-aikacen da ta hana su ne"


Idan ko ta fito taci karo da Umma ko Mama Suwaiba da gudunta zata koma ɗakin saidai suyi mata dariya kawai, su Abubakar ne bata jin kinyarsu kuma sukan shiga ɗakin har ta musu tatsuniya.


Cikin hakan ne cikin ta ya kai na haihuwa, tana zaune kan Sallaya bayan ta idar da Sallah isha Usman na zaune bakin gadon ta, yana jiran ta masa tatsuniya ta kalle shi ta ce "Usman yau bana jin dadi zan kwanta da wuri kuje kuyi karatu da Mama "

Ya ce "Nima anan zan kwana"


Ta ce "To Abubakar fa"


Ya ce "Ohonsa"


Tun tuni take jin maranta na murɗawa yanzu kuma taji tana jin bayan gida ta tashi zata naɗe sallayan sai ta koma ta durƙusa a gurin saboda wani azababben ciwon da koda uwarta ta haife ta bata taba yi ba.

Ta durƙusa tana salati, ganin Halin da take ciki ne yasa Usman ya fita da gudu yayi Falo dukan su suna falon ya ce "Ummi bata da lafiya kuzo kuga yadda take"


Kafin kowa ya tashi Abubakar yayi gaba da Gudu Umma ne ta jawo shi ta ce "Kada naga ka shiga ɗakin nan"


Suna shiga suka samu tana nishi ga zufa da ta hada ga kuma kwaton hijabinta, suka kamata zasu ɗagata tayi wani dogon Nishi sai ga Yarinya ta sulluɓota, tana fitowa ta zandara kuka da kara, da sauri Umma ta tare ta tana faɗin Alhamdulillah, Mama Suwaiba kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login