Showing 51001 words to 54000 words out of 62424 words

Chapter 18 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2851

muyi jinyar ka"




*** ****




Cikin haka ne cikin Bilkisu ya fara girma yakai wata shida kula gun Aliyu ba irin wanda bai bata ganin mai wankin su ya tafi gida yasa Take yi da kanta, shi kuma yaga kamar tana wahala yasa ya fara nema musu mai wanki, da bai samu ba yayi magana wa Daddy, Daddy ya ce "To shikenan zanyi magana da wani yaro Umar sai ya samo muku"


Alhaji kuwa ya ɗaga waya ya kira Umar ya ce "Kazo gida ina son ganin ka"



Umar ya ce "To an gama Alhaji"


Sai yamma Umar ya samu zuwa gidan, a gurin adana motoci Daddy ya same shi, bayan sun gaisa ne ya ce "Akwai ɗana Aliyu yana neman mai wanki shine nace zan maka magana ka idan za'a samu a gurin ka sai ka samo masa"




Ya ce "Ay ba komai Alhaji idan wankin ya taru zan na zuwa ina musu"


Ya ce "Da yawa fa, ga nashi ga na matarsa da ƴarsu fa"


Ya ce "Ba komai Alhaji ay zan iya"


Ya ce "To shikenan zan masa magana sai kaje can gidan nasa"


Daddy ya ɗaga waya ya kira Aliyu Suna gama magana Daddy ya kalli Umar ya ce "To zaka same shi a gida wai, amma aikin bazaiyi yawa ba ga wanda kake yi a zango"



Umar ya ce "Ba damuwa Alhaji "



Kwatanta masa gidan yayi tare da bashi number n Aliyun akan idan yaje ya kira shi.


Yana zuwa kuwa ya kira shi bayan sun gasa ya ce "Nine wanda Aka ce nazo zan muku wanki"


Aliyu ya ce "To gani nan fito wa ma"


Aliyu yana zuwa da ya kalle shi ya ce "Amma fa kamar na sanka"



Umar yayi murmushi ya ce "Kama ne kawai Alhaji ni ba ɗan garin nan bane ma"


Ya ce "To shikenan yanzu zaka fara ne ko sai gobe"


Ya ce "Yanzu zan fara goben idan nazo sai na goge muku ko"



Umar ya shiga ciki ya ɗauko kayan harda matarsa da na Maisun da sabulu da omo ya bashi.


Kayan Aliyu ya fara wankewa sannan ya fara na matar, saidai a duk lokacin da ya ɗaga rigar ta ko wani abu nata, sai yaji wani ƙamshi wanda ada ya saba jinsa wanda yanzu ya ƙaurace ma hancinsa.



Tun yana tunanin ina ya san wannan ƙamshin har ya tuna wannan ƙamshin irin na Bilkisu ne, cikin ransa ya ce "Lalle Hajiya ma ma'abociya ƙamshi ce irin Bilkisuna"



Yana wanke kayan yana nishaɗi har har ya gama.



Da yake ana iska wasu sun bushe ya naɗe su.

Yana naɗewa ne aka dawo da Maisun daga Makarantar Islamiyya tana zuwa ta wajen ta ce "Sannu da aiki"


Ya ce "Yawwa ƴar lele kece ashe kin tuna ni kuwa"



Tayi shiru kamar me tunani ta ce "Na tuna ka, kaine na ganka ranan auren Daddyna"



Ya ce "Eh nice ranan baki faɗa min sunan ki ba, ya sunan ki"


Ta ce "Maisun Amma a makaranta ana kirana da SAUDAT UMAR"


Yace "Da kyau sunan Mama ta ce ke ashe, kuma suna ƴata idan na haihu"










_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/10, 5:25 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 67-68




Zata ƙara magana ya ce "Ki shiga ciki kada Mommynki ta ga baki shigo ba ko"

Ta ce "To"


Ta fara tafiya shiko yana kallon ta har ta shiga ciki, Kaunar yarinyar yaji ta shiga ransa, tunawa yayi da Bilkisu da cikin ta tuni ƙwalla ya fara zubo masa yasa Babbar yatsar s ya ɗan share ya ci gaba da abin da yake.


Washe gari kuwa ya dawo ya fara guga duk da an wanke kayan amma ƙamshin Bilkisu yake yana gogewa yana jin wani iri a zuciyar sa, kai gaskiya bazai jure wannan aikin ba, yana tayar masa da hankali da yawa, saida ya goge duka sannan ya kwasa, dan Mai gidan ya ce "Idan ya gama ya kawo masa falo"



Falon yayi yayi Sallama Aliyu yazo ya buɗe masa ƙofa ya amshi kayan ya ce "Ka shigo Matar gidan tana son ganin ka don wata rana koda bana nan idan kazo sai ta baka ko"


Ya ce "To Yallabai"


Har zai juya ya ce "Nawa ne kuɗin da zan baka, ko sai wata zan na baka"


Ya ce "Duk yadda ka yanke Alhaji "


Ya ce "To nawa zan na baka, gwara dai a ringa biyanka a lokacin da kayi aikin ko"


Ya ce "To na gode"


Ya shigo ciki, ya zauna a ƙasan kafen, abin mamaki ƙamshin falon ma irin na Bilkisu ne, lumshe idonsa yayi yana jin daɗin ƙamshin.


Shiko Aliyu shiga yayin ciki ya ajiye kayan ya kalle ta da take kishingiɗe ya ce "Kisa hijabinki kizo ki ganshi ko"

Ta ce "To"


Ta ɗauki hijabinta tasa ta biyo bayansa Aliyu ya zauna idon Umar ko yana rintse yaji muryan Aliyu ya ce "Malam Umar ga iyalina zuwa"


Ya buɗe idonsa kenan daidai lokacin ita kuma ta iso tsakiyar falon da sauri ya miƙe yana nunata da yatsa, ita kuwa bayan Aliyu tayi da gudu ta cakume shi.



Aliyu ya daka masa tsawa "Me haɗinka da Matata"


Muryan Umar na rawa ya ce "Bil... Ki... Su"



Aliyu ya juyo ya kalli Bilkisu da ta riƙe shi ta baya yaga sai hawaye ke zuba ya kamata ya dawo da Ita gaban sa ya ce "Faɗa min waye shi"


Cikin kuka ta ce "Umar ne fa, ka kawo shi gidan mu dan Allah ka kore shi bana son ganin sa na tsane shi, ganinsa yana sa in shiga tashin hankali, ka kore shi, ni kayan da ya wanke ma bana so a fitar da su"


Ya ce "Wai kina nufin Umar Mahaifin Maisun"



Ta ce "Bana so kana haɗa shi da Maisun, Maisun bata da wani uba da ya wuce kai"


Umar kan ƙafafunsa rawa suka fara yana kuka daga bisani kuma ya durƙusa akan gwiwarsa cikin kuka ya ce "Ku saurare ni dan Allah, Bilkisu ki tsaya zan faɗa miki ba yin kaina bane"


Aliyu ya zaunar da ita kan kujera yaje ya kama kafaɗan Umar ya ce "Haba kana namiji kana kuka ya isa ka daina kukan haka "


Ya ce cikin kuka "Dole nayi kuka na rasa Bilkisu yanzu ta min nisa nidai roƙona gare ta, ta taimaka tazo muje gida domin nayi Alƙawari bazan taɓa komawa gida ba tare da ita"


Da sauri Bilkisu ta miƙe ta ce cikin ɗaga murya "Baka da hankali ne, ko ka haukace ne, Ina da auren zan bika, ko da yake dama da alamun hauka a tare da kai"


Hannunsa ya haɗa yana sake roƙonta ta ce "Ka tashi ka bar min gidana, Ya Aliyu ka kore shi bana son ganin sa, na tsani ganinsa a rayuwata"



Aliyu kan da yaga tana faman haukace masa yasa yaja Umar suka fita waje, saida suka je gun mota ya ce "Umar ya akai haka, me yasa kayi mata haka a wancan lokacin"


Ya ce "Wallahi ba yin kaina bane bana cikin hayyacina"


Ya ce "Ya aka yi haka to"


Umar ya bashi labari tun farkon auren su da Bilkisu har izuwa inda ya koreta haɗi da saki.

Aliyu ya ce "Kayi haƙuri dan Allah ka tsaya a nan barin je na lallasheta "


Umar ya ce "Yanzu dama Maisun ƴata ce"


Ya ce "Eh ƴarka ce "


Hawaye ne suka ci gaba da zarya a idonsa, shiko Aliyu ya shiga ciki ya sameta zaune akan kujera tana huci kamar taga Umar ɗin a gabanta, Yazo ya durƙusa a kan gwiwarsa yasa hannu kan cinyarsa ya ce "Haba My Billy ban sanki da haka ba, ki manta da baya ki fuskanci gaba, Umar ɗan uwanki ne, bai kamata ki masa haka ba, duk da ya miki kuskure a baya ay ba yin kan sa bane, baya cikin hayyacin sa, Asiri suka masa. "



Ta ce "Asiri, to Ƙarya yake Ay tun tuni dama ya tsane ni, tun ina ƙarama yake tsangwama ta, tare da cin zali na, Shine fa musabbabin da yasa Babansa ya mana aure saboda shi ɗin ɗan Iska ne"



Aliyu zai sake magana ta ce "Dakata Malam wai me yasa kake bin bayan sa, dan ba a kai yayi ba"


Murmushi yayi ya ce "Ke kina masifar ma bata miki kyau Wallahi ki canja masifa ba taki bace"


Haushi ne ya kamata tayi fuuuu ta wuce ɗaki ta jawo ƙofar ta rufe.



Kallonta yayi kawai ya fito gun Umar ya buɗe masa mota ya shiga, shima ya shiga gun driver yaja suka yi gidan Daddy.


Har Falo Aliyu ya shiga da shi ya samu Mommy tana falo amma Daddy baya nan




Mommy tana kallonsa ta miƙe ta ce "Wannan kamar Umar"


Aliyu ya ce "Eh shine ashe dai zaki gane shi"


Da sauri ta tashi tsaye ta nuna hanyar waje da hannunta ta ce "Fitar min dashi daga gida, me tazo ya min kuma"


Aliyu ya ƙarasa ya kama hannun ta ya ce "Haba Mommy ki saurara kiji mana ba yin kansa bane fa"


Ta ce "Tun muna saida juna da ka ka fitar min da wannan azzalumin daga gida "


Ta daka masa tsawa tare da nuna shi da yatsa "Kai! Fitar min daga gida tunda ba gidan uban ka bane"


Da sauri Umar ya fita waje, yana fita ita ma tayi ɗakinta tabar Aliyu a tsaye a gurin.



Fitowa yayi ya samu Umar a jikin mota yana kuka yaje ya tsaya gefen sa ya fara kiran Daddy ya faɗa masa komai game da Umar, Daddy ya ce "To Ku jirani gani nan zuwa"


Suna tsaye a gurin sai ga Daddy ya shigo da motar sa, yana kallon Umar ya ce "Ashe kai ɗin ma na gida ne, to Bismillah ku shigo ciki"


Suka ƙarasa amma Umar ya kasa shiga saida Aliyu ya kama hannunsa suka shiga tare. A ƙasa suka zauna dukan su. Daddy ya shiga ɗakin Mommy Nasiha yayi ta masa da nuna masa Umar ba a hayyacin sa yake ba lokacin da ya aikata wannan kuskuren har ya sauƙo, suka fito tare suka zauna a kan kujera ta ce "To Yanzu dai kaga Bilkisu tana da aure ya kenan za'ayi"


Daddy ya ce "Yanzu dai maganan ɓoye-ɓoye ya ƙare gobe da safe zamu shirya duka mu tafi Bauchi har ita Bilkisun "


Mommy ta kalle shi ya ce "Eh, idan yaso daga baya ta dawo ɗakin mijinta, amma banga dalilin da yasa zamuna ɓoye yarinya mutane suna cikin damuwa ba"



Shiru tayi bata ce komai ba, ya kalli Aliyu ya ce "Ka kaishi ɗakinka ya yi abin da ya dace, gobe mu ɗau hanyar Bauchi"



Ya ce "Tukun na ma yaje yayi aski ko, dube shi yadda ya tara gashi "
Shidai Umar yana shiru abinsa.



Aliyu ne ya kaishi aski sannan ya kawoshi gida yayi wanka, Aliyu ya bashi kayan sa sabbi yasa sannan ya kawo masa abinci.



Bayan nan ya koma gida gun Gimbiyar tasa, A faro ya ganta fuskan nan a ɗaure yazo ya zauna gefenta ya kama hannunta ya ce "Kina fushi dani ko, kiyi haƙuri ki sake min fuska dan fushinki masifa ce a gare ni"


Kuka ta fasa cikin kuka ta ce "Ba ka nuna min ka fi son Umar akaina ba, kuma Umar ɗin da ya cuce ni"


Ya ce "Wa ya faɗa miki, Lalle har yanzu baki san yadda nake ji da ke ba, yanxu dai mubar wannan zancen Daddy ya ce "Gobe zamu je Bauchi dukan mu "


Hararansa tayi ta ce "Ni ba inda zanje"



Ya ce "Baki son ganin su Ya Abubakar ko"


Shiru tayi can kuma ta juyo da jikinta gurinsa ta ce "Ehhhh haka ne, su ya Abubakar suna nan, amma badan su ba ba inda zani "



Da yamma kuwa saiga Mommy, Daddy, Maryam da Umar, Bilkisu ta musu tarɓa ta Musamman ta gaida su Amma Umar ko kallon sa bata yi ba. Daddy ya fara magana ya ce "To Bilkisu abin da nake so da ke, kiyi haƙuri ki manta da komai gobe zamuje Bauchi gun iyayen ki"


Ta sunkuyar da kai ta ce "To Daddy duk abin da ka ce haka za'a yi"



Maisun ce ta fito da yake yau Alhamis ba Islamiyya tana ganin su ta faɗa jikin Daddy tana gaishe shi, Daddy ya nuna mata Umar ya ce "Ga can Daddynki kije ki gaishe shi"


Kallon sa ta ringa yi can ta ce "Daddy na kuma, wannan fa me wanki ne, " Ta nuna Aliyu ta ce "Nika ga Daddy na nan" sai kuma ta faɗa jikinsa.



Kunya ce ta kama Aliyu sai ya janye ta ya ce "Maisun wannan ma Daddyn ki ne kije ki gaishe shi"


Ta je ta hau jikinsa ta ce "Shine tun tuni baka zuwa sai yanzu"


Shidai Umar yana Shiru ba Magana. Sai daɗi da yake ji ƴarsa na jikin sa.





Washe gari Sassafe suka ɗauki mota ɗaya Aliyu ne ke jan mota, sai Bilkisu a gaba, Daddy da Mommy kuma suna can baya, sai Maryam da Umar riƙe da Maisun sune a bayan su Aliyu, wato tsakiya kenan.






_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/10, 7:24 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 69-70




Aliyu ya iya gudu a mota, wai dan ma Daddy yana masa magana, wannan yasa suka isa da wuri. Gidan Abba suka yi da Umma ce kawai a gidan sai Khadiyo da tazo dama Umma tasan da zuwan su taji komai, Khadiyon ɗin ne bata sani ba, tana ganin Bilkisu ta je da gudu ta rungumeta sai kuma tasa kuka tana cewa Aunty ina kika shiga ne mukai ta neman ki, kinsan jalin da muka shiga kuwa?"


Zama suka yi Umma da Khadiyo suka kawo musu abinci da Abinsha, kafin su gama kuwa Umma ta kira Abba, Baba, Abubakar da Usman. Ita kan Bilkisu sam ta kasa cin Abincin ma tana cewa da Umma ita yayyenta.


Ba jimawa suka Baba ya shigo gidan yana ganin Bilkisu yaje ya zauna gefenta ya kama hannunta ya ce "Bilkisu! Kece haka ina kika shiga"


Murmushi kawai yake take tayi. Ana ta gaishe shi ko ya kula shidai ta Bilkisun yake kawai sai daga baya ne suka gaisa Umar kuwa ya matso ta jikin ƙafar sa ya ce "Baba Tun tuni ina ta gaishe ka baka amsa min ba"



Shiru ya masa baice komai ba Bilkisu kuwa tana lure da haka.


Can saiga Abubakar da Usman ayko bata bari sun ƙaraso ba ta tashi da gudu taje ta rungume su Aliyu kan yana ta cewa " Ahhhh"


Mommy ta masa ido alamun ya bari a hankali ya ce "Mommy Cikin ta fa take gudu"


Ta ce "Wai a kanka aka fara ciki ne"


Yayi shiru.


Sun daɗe ruƙe da juna suna murna sannan suka saki juna suka fara gaisawa da jama'a Usman ya kalli Maisun ya ce "Wannan ce ƴarmu "


Ta ce "eh"


Ya ɗauke ta suka fito waje ay bata iya zama ba ta bisu Aliyu ma ya tashi ya bita a baya Ɗakin su Abubakar yaga sun shiga ya bisu zama suka yi shima ya zauna ya ce "Baki ci Abinci ba fa ina kallon ki, dan Allah kizo kici kada ki zauna da yunwa"


Ta kalle shi ta ce "Ayya Yayana, ni na ƙoshi ma da naga ƴan uwa na"


Usman ya ce "Kodai shine mijin yanzun"


Kafin ta amsa Aliyu ya amsa da "Eh yayan mu"



Dariya suka yi duka Abubakar ya ce "Harda saurin Amsawa "


Aliyu ya ce "To na kawo miki Abincin nan"


Ta ce "A'a"


Abubakar ya ce "Khadiyo zata kawo mana zamu ci anan ma, Kaima nasan baka ci da yawa ba tunda taƙi ci"


Suna haka kuwa Khadiyo ta shigo da Abincin, tare suka ci duka har Aliyun ma.



A falo kuwa Baba ne yake maida Maganan yadda akayi da irin cin Amanar da Umar yayi"


Alhaji Yusuf ya ce "Ka daina faɗan haka fa ka dubi ɗanka tunda ka shigo nan yake baka haƙuri baza ka haƙura ba"


Ya ce "Nifa na riga na Sallama wannan ɗan a duniya dan haka yaje kawai, bani da wani ɗa "


Abba ne ya shigo Falon shima gaisuwar akai tayi Umar ya gaida Abba ya Amsa ya ce "Kai dai baka da dattaku Umar sai ka wuce ka tafi baza'a a ganka ba kaƙi dawowa gida ina hankalin naka yake"


Ya matso ya ce "Abba kayi haƙuri "


Baba ya ce "Yanzu ma komawa inda ya fito zaiyi"


Abba ya ce "Ba ya dawo maka da ƴarka ba. To ka kyale shi kuma ya isa haka"


Bayan sun gama suka shigo duka Bilkisu ta faɗa jikin Abbanta tana murna ya ce "ni dai ɗaga ni ay dama kin watsar damu kin yaye mu"


Ta ce "Ay haƙuri Abbana bazan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login