Showing 54001 words to 57000 words out of 62424 words

Chapter 19 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2852

kuma ba"

Magana Aka ci gaba da maidawa aka yafi juna amma sam Baba yaƙi ya saurari Umar.


Baba ya ce "Kai me yasa kake da taurin kaine haka"


Alhaji Yusuf ya ce "Shine nima na gani ay"


Abba ya ce "Ka ganshi tun yana ƙarami akwai kafiya da taurin kai"


Ganin Umar yadda yake kuka yasa gaba ki ɗaya zuciyar ta ya tsinke, Namiji kamar wannan amma yayi ta kuka haka, dan haka ta matsa kusa da Baba ta ce "Baba kayi haƙuri ka yafe masa ni na yafe masa, idan saboda ni kaƙi yafewa kayi haƙuri Baba"



Baba yayi shiru yana kallon ta Can kuma ya ce "Kin manta abin da ya miki ko"


Ta ce "Baba ka manta da komai kaima dan Allah "



Ya ce "To shikenan Allah ya yafe mana gaba ki ɗaya"


Wani sanyi Umar yaji a ransa ya ce "Nagode Ƙanwata Allah ya sauƙe ki lafiya "



Abubakar kan tun da ya shigo yake lure da Maryam da duk da ake magana bata sa baki ba, tayi shiru Maisun na jikinta, Miƙewa yayi ya kira Bilkisu ta taso suna zuwa ya tarar da Usman yana waya suka zauna ya ce "Wacece waccar ƴar budurwan da kuka zo tare"


Ta ce "Wai Maryam, Ƙanwar Mijina ce"



Ya ja hancin ta ya ce "Baki da kunyar cewa mijinki a gaba na, ko da yake naga mijin ma ba kunya gare shi ba, Ita Maryam ɗin An mata miji ne"



Ta ce "A'a amma kasan baza ta rasa masoya ba"


Ya ce "To idan so samu ne a sani a ciki"


Da sauri Usman ya kashe wayar ya miƙe ya ce "Tab amma ko yau ga abin Al'ajabi"


Bilkisu ta ce "Dan ya ce yana sonta "



Ya ce "Ay baki san wani abu ba, shifa a rayuwan sa bai taɓa yin budurwa ba, ga ƴan mata sai bibiyansa suke amma duk yaƙi su har ana cewa Aljana ce ta aure shi"


Ya ce "Ni kawai banga abin da zaisa ina ɓata lokacina bane kawai, wannan ɗin ma idan ta nuna min tana da wanda take so zan barta"


Bilkisu ta ce "Ayko baza'ayi haka ba, idan Maryam ne kamar ka same ta"



Ya ce "Yawwa My sister Nagode miki"


Usman ya ce "Su sabon shiga fa an faɗa"


Abubakar ya ce "Tashi ka gyara mana ɗakin yanzu za'a kira min ita"


Ta ce "Kaga kuwa ita ma Barrister ce"


Ya kama hannunta ya ce "Dan Allah fa! Kai kashe wayan nan kazo ka gyara mana ɗaki yanzu zata zo"



Usman ya miƙe ya ce "Kaga ni fita ma zanyi bazan gyara ɗaki saboda mace ba"


Bilkisu ta ce "Yi shirun ka Yaya ni barin gyara "


Gyarawa tayi sannan ta shiga ta kira Maryam suka shigo tare, Abubakar kan harda canja kaya yasa kaftan ya saka hula. Maryam kan zama tayi a can gefe Bilkisu kuma ta miƙe zata tafi Maryam zata bita Ta juyo ta ce "Magana za kuyi dai"



ita ko Bilkisu ta koma ciki ta samu wai su Mommy zasu koma sun yanke shawaran zasu bar Bilkisu da Maisun su kwana biyu. Bilkisu ta ce "Mommy abar Maryam ma dan Allah"


Ta ce "Idan zata zauna sai a barta tunda ay bata da aikin komai"



Ita ko Bilkisu tayi hakan ne dan su samu su daidaita kansu da yayan nata.


Tuni Maryam da Abubakar suka daidaita kansu. Ita kan ya burge ta, koda ta shigo Mommy ta ce "Maryam zaki zauna idan yayanki yazo sai ku tafi tare ne ko zaki bimu"


Ta ce "Zan zauna Mommy "



Ta ce "To"


Da yake sunyi Sallar Azhar yasa suka shirya tafiya, Mommy ta kira Bilkisu gefe ta ce "Idan Umar ya ce zai karɓi ƴarsa ki bashi kayansa, sai a turo masa kayan ta daga nan'


Ta ce "Mommy kuma... "



Ta katseta ", Kiyi haƙuri idan yace yana buƙata ki bashi amma idan bai buƙata ba shikenan"


Ta ce "To"


Aliyu kan baiso barin matar sa ba, amma ba yadda ya iya haka suka tafi.



Da yamma kuwa ƙarfe biyar saiga Mama Sauda duk ta rame kamar ba Mama Sauda mai ji da kanta ba. Tans zuwa ta rungume Bilkisu tana cewa "Ki yafe min dan Allah Bilkisu, ganin Umar na kallonsa yasa Bilkisu ta ce "Haba Mama ni ƴarki ce ay kada ki damu komai ya wuce"


Umar kuwa matsowa yayi Bilkisu ta ce "Mama Yaya yana magana"


Tana ganin sa rungumeshi tayi tasa kuka tana cewa "Ina ka shiga ne, nayi rashin Baban ka gashi kaima nayi rashinka"


Rarrashinta ya ringa yi har saida tayi shiru.


Bilkisu dai taga gata duk inda ta matsa Bilkisu Shiko Umar yana maƙale da Maisun, Sauda ma da tazo har goya ta sai da tayi, tana mamaki halarci irin na Bilkisu da ta iya sa Sunanta bata yi tunanin irin cutar da suka mata ba.


Da daddare kuwa ɗakin su Abubakar suka tafi duka, Bilkisu, Usman Khadiyo da Umar riƙe da ƴarsa Abubakar kan janye maryam yayi suka tafi Ɗakin Umma.



Hira sukayi ta sha kamar daga Sama saiga Ruky ta shigo har ɗakin, kowa ya juyo yana kallon ta.


_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/10, 6:15 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 71-72




Umar ne ya ɗaure fuska ya ce "Kefa me ya fawo ki"


Ta ce "Nazo ne ka mu tafi gida"


Ya waro ido "Gidan wa"


Ta ce "Naji labarin dama ance ka samo Bilkisu kuma da auren ta, to tunda tayi aurenta ba shikenan sai mu ci gaba da zama ba tunda dama baka sake ni ba"



Ya ce "wa ya ce Miki zaki koma gida na, ƙarya kike ay, aurenki kuma sa ke kaina kije na Sake ki, kada na ƙara ganin kina bibiyata, Kinci darajan Ƙanwata Bilkisu amma badan haka ba... " ya yarfar hannunsa.



Komawa tayi kamar zata tafi sai kuma ta dawo ta ce "Umar dan Allah kayi haƙuri"


Usman ya ce "Wai kai ka kira yarinyar nan ne da baza ta bar nan ba"


Umar ya ce "Saina balla ɗayan hannun ya kuma lalacewa tukun na"



Usman ya miƙe tuni tabar gurin.


Kwanan su biyu Aliyu yazo ya ɗauke su, Umar kan yayi wa Maisun hidima da yawa yayi mata siyayya kuma bai nuna alamun zai amshe ta bama.


Saida suka biya suka gaida Zalimu mijin Ummi tukun dan tin da yayi hatsarin nan kasancewan ba asibiti aka kaishi ba, daga baya aka gane dama ya samu matsala a haƙarƙarinsa, kuma gurin yana damunsa sosai.


Ummi ji tayi kamar kada ta rabu da ƴar tata amma ya zata yi dole suka rabu da Alƙawarin zasu dawo mata idan ta haihu.


Daga nan suka ɗau hanya suka koma Kaduna saidai sunyi dare sosai dan ma Aliyun yana gudu sosai a mota.



A gidan Maryam ta kwana saida Washe gari ta koma gida.



Cikinta yakai wata takwas lokacin kuwa ansan da Maganan Abubakar da Maryam dan har an sa musu rana nan da wata biyar.



Aliyu yana zaune ita kuwa tayi matashi da cinyarsa wayan sa ne yayi ƙara ta ɗauka ta miƙa masa dan bata son ya motsa dan taji daɗin kwanciyar.



Ya duba yaga Mommy ce ya ɗaga da Sallama daga can ta ce "Ina Bilkisu ne ana ta kiranta bata ɗaga waya ba"


Ya ce "Wayar tana ɗaki ne, ita gata a falo"


Ta ce "To saidai haƙuri Mijin Umminku ne Zalimu ya rasu"


Ya ce "Innalillahi wa Inna'ilaihir raju'un Allah ya jikansa da rahma"



Mommy ta amsa "Amin, Daddynku ya ce Gobe zamuje ya kace kai"



Ya ce "Mommy makarantan Maisun fa"


Ta ce "Nima nayi tunanin haka to amma zata zauna da Maryam, zamu barta a gida.


Ya ce "To Allah ya kaimu goben, amma Maryam nan zata zo ko"


Ta ce "Eh"


Sukayi Sallama suka kashe wayar ya kalli Bilkisu ya ce "Wai Mijin Ummi ne ya rasu"


Ta tashi zaune ta ce "Allah sarki Ummi, Allah ya jiƙan Baba Zalimu"


Ya ce "Amin"


Washe gari tun Sassafe sukayi shirin su dan sai zasu dawo a ranan ne shi yasa ma ko kaya basu ɗauka ba, Bilkisu kan jikin t ne yayi sanyi duk bata jin ƙarfin jikinta ya kalleta ya ce "Yaya dai,?

Ta ce "Ni Wallahi duk bana jin daɗin tafiyar nan Yaya dama a fasa ba yanzu ba"

Ya ce "A'a taya za'a fasa kuma, gaisuwa ne idan munyi sai mu dawo"



Ta kama hannunsa tasa a daidai zuciyar ta ta ce "Yaya taɓa ƙirjina kaji sai wani bugawa yake Wallahi kamar wani abu zai same ka"


Ya ce "Kina min Addu'a ba abin da zai same ni Insha Allahu"


Ta ce "Yaya dan Allah kada ka rabu dani duk wuya duk daɗi ka kasance dani"


Rungumeta ya yayi ya sa kanta bisa kirjinsa ya ce "Wa ya ce miki zan rabuda ke, mai raba mu da ke sai mutuwa "

Daidai lokacin suka ji horn alamun su Daddy sun zo, ya je ɗakin Maisun yaga tana barci ya mata kiss a kumatu sannan suka fito Maryam ta fito ta shiga ciki tana ɗaga musu hannu, Aliyu shine mai jan motar sai Bilkisu a gefen sa sai kuma Daddy da Mommy a bayan su.


Nan fa suka ɗau hanya, basu ɓata lokaci ba suka isa saboda gudun da suka sha.

Nan fa suka yi mata gaisuwa tare da mutanen gidan Aliyu da Daddy waje suka koma yayin da Mommy da Bilkisu kuma suke ciki tare da Umma dan ita ma tazo da Abba shine ya koma. Suna zaune saiga Mama Sauda ita ma tazo, duk tana rame zanin jikin ta maa koɗe yake. Bilkisu ta ce "Mama Ciwo kika yi ne"


Ta ce "Bilkisu kenan ay dama ciwo nayi da yafi, zama rayuwan gidan da nake babu daɗi kwata-kwata ga Baban Umar ya ce gwara yayi aure da ya maida ni"


Ta ce "To banda abin Baba ma tinda ba auren zaiyi ba ya maida ki mana"


Ta ce "Nikan ma na haƙura idan na samu miji aure zanyi, saidai yanzu mazajen yanzun ne sai a hankali duk wanda zaizo saidai yazo da maganan iskanci"



Tausayin taji ta ce "Kada ki damu Mama za kira Babam A waya muyi magana insha Allahu zaki koma"


ƙarfe biyu daidai na rana suka ce zasu koma zuwa Isha ay sun isa, Suka yi wa Ummi Sallama sannan Bilkisu ta ce "Zata zo ta zauna mata idan ta haihu tunda anan zata yi takaba "


Haka sukayi Sallama wa mutane suka ɗau hanya kuma. Nan fa ya fara gudun nasa Daddy ya ce "Ka daina gudun nan mana, ɗazu ma naso na maka magana kai idan baka yi gudu ba baka jin daɗi"


Nan ya rage Daddy kuma ya ci gaba "Tafiyan nan mu muka sa kanmu ba wani ya samu ba dan me to zaka damu kanka sai kayi gudu"


Haka sukayi ta tafiya a hankali har sukay dare a hanya, A pambegua suka yi sallah Isha sannan suka ci gaba da tafiya. Ji yayi motar tayi shiru ya juya yaga Mommy da Daddy duk suna barci ita ma Bilkisu tayi barci, ya ɗora hannunsa ɗaya akan cikin yaji yadda babyn yake ta motsi kamar zai faso cikin nata. Murmushi yayi ya kunna ƙira'ar Karatun Al-qur'ani Mai girma cikin suratu Yusuf an yi yana bi a hankali, sautin kaɗan yasa shi yasa basu tashi ba, ya kuma ƙara gudu a motar hannunsa ɗaya nakan cikin Bilkisu yana jin yadda Babyn ke motsi.



Bai ankara ba yaga an hasko shi alamun motar ta biyo ta hannun da yake, yaso jan burki dan kaucewa motar gaban sa, ashe bayansa kuma akwai wata motar nan fa motar bayan nasa ta bugi motarsa ya da murɗa sitiyari yayi cikin daji tuni motar tayi daji ta bugi wani ƙaton dutse.


Tun lokacin da abin ya fara Mommy, Daddy da Bilkisu suka farka sukayi ta salati, saidai lokacin da Motar ta bugi dutsen Daddy ne ya ci gaba da Addu'a, kafin kace me sauran motacin sun tsaya suka kawo agaji, da kyar Daddy ya samu ya fito sai ya zaga gun Bilkisu ya kamata ya fito da ita, ya kwantar da ita, sauran jama'an kuwa suka fito da Aliyu da Mommy da ko motsi basa yi.


Kafin ka ce motar Ambulance tazo nan da nan aka kwashe su Daddy ma ya shiga aka ƙarasa asibiti da su, Tin a cikin motar aka fara da Bilkisu kasancewan ta me ciki, sannan suka fara da Mommy da Aliyu, a cikin Motar Mommy ta farfaɗo, Aliyu da Bilkisu kuwa shiru, emergency aka yi da su duka, Mommy kan taƙi yadda su mata komai burin ta taga Bilkisu da Aliyu sun farka, haka suka gyaleta sai can dare ne Bilkisu ta farka ita ɗin ma tashi tayi tayi tana cewa Ina mijinta.


Aka hana ta shiga gurin sa nan fa ta fara kuka Mommy na lallashi. Aliyu yaji jiki da yawa dan ma likitan kwararrune kusan asuba ya farfaɗo.



Wani likita ne ya fito ya ce "Alhamdulillah mun samu nasara ya farfaɗo zaku iya ganin sa, sannan ku fito kuma kuna buƙatan a duba ku".



Rige-rigen shiga suka yi suna shiga ya miƙo wa Bilkisu hannu yazo ta kama ya kalli Ummi ya ce "Ummi ki kula min da takwaranki dan Allah, bana son ta shiga cikin damuwa bayan babu ni"


Bilkisu ta ce "Me haka ka daina min wannan magana dan Allah"



Mommy ta ce "Zaka samu lafiya in Allah ya yarda"


Ya kauda kansa ya ce "Daddy ka yafe min, Mommy ki yafen min, Bilkisu kema ki yafe min"


Daddy ya ce "Mun yafe maka, amma ya isa surutu n"


Ya kauda kai yayi kalmar shahada sai kuma rai yayi halin sa.


Innalillahi wa Inna'ilaihir raju'un " likitan dake bayansu ya faɗa tare da matsowa ya rufe masa fuska da mayafin dake jikinsa..



😭😭😭😭😭 So Sad😭😭😭😭😭


_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/11, 4:25 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 73-74





Daddy baya ya juya ya kalli ƙofa ji yayi jikinsa ya ɗau zafi, Mommy kuwa tuni ta fara kuka tana salati. Bilkisu kan shiru tayi sai ji tayi numfashinta na neman ɗaukewa ƙafafuwanta sun kasa ɗaukanta, koda Daddy ya juyo yaga halin da take ciki yazo ya kama kafaɗanta ya girgiza kai a hankali ya ce "Addu'a zakiyi"


Bai ankara ba ta faɗi ƙasa ko motsi bata yi. Da sauri Mommy tayi kanta cikin kuka tana cewa kada kumin biyu dan Allah ki tashi. Zuwa akayi aka ɗauketa aka yi da ita wani ɗakin.


Shiko Masallaci ya wuce don yaji ana kiran Sallah asuba amma saida yasa aka rufe ɗakin. Bayan ya dawo ne ya leƙa ɗakin da Bilkisu take ya samu Mommy ta idar da Sallah tana Addu'a tana kuka. Ita ma ta farfaɗo tana yin Sallah saidai ko alamar hawaye babu a fuskar ta.



Tausayin su yaji ya koma ya ringa kiran ƴan uwa da abokan Arziki yana faɗa musu. Tuni aka zo aka ɗauki gawa likitocin sukayi sukayi akan Mommy da Bilkisu su zauna amma suka ƙi.


Gidan Daddy aka wuce da gawar Su Mommy ma can aka wuce da su. Daddy ya tura aje gidan Aliyu a ɗauko Maryam da Maisun.


Tana zaune kan sallaya tana tunanin abin da ya hana su dawowa jiya taji ana buga ƙofa ta tashi cikin tsoro saida ta leƙa ta ƴar kafa taga Driver ne ta buɗe ya kalleta ya ce "Alhaji ya ce kuzo na kaiku gida keda Maisun"

Ta ce "Sun dawo ne"


Ya ce "Eh "


Ta ce "To barin shirya Maisun sai a ajiyeta a makaranta "


Ya ce "Hajiya kizo kawai mu tafi ki ɗauko ta a haka muje"


Ta ce "Lafiya kuwa"

Ya ce "Lafiya lau kizo muje Hajiya "


Ta koma ciki ta ɗauko Maisun ta fito jikin mota taga yana kuka ta ce"Na tambayeka lafiya kace lafiya me yasa baza ka faɗa min ba, me ya faru da Daddy na"

Ya fito ya buɗe motar ta shiga da Maisun a hannun ta ya ja mota suka tafi.


Suna zuwa taga ƙofar gidan cike da jama'a wasu suna ta alola. Makara ta hango ana shiga da ita, wannan ya tabbatar mata mutuwa aka mata, ta sauƙe Maisun ta taka da ƙafarta ta fito tana ratsawa cikin mutane sai kunnen ta ya jiyo mata wani yana cewa "Allah sarki Aliyu mutumin kirki ne, Allah ya jiƙan shi"


Da gudu ta ƙarasa shiga ciki tana kuka tana zuwa falon ta tarar har an shirya shi an saka shi a cikin Makaran da aka shigo da shi. Faɗawa tayi jikin gawar tana kuka Daddy ya riƙota ya tiƙe hannun Maisun da take bayanta yayi da ita ciki inda su Mommy suke.

Tana zuwa ta rungume su tana kuka, saidai Bilkisu kan ba magana, ko kwakkwaran motsi bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login