Showing 60001 words to 62424 words out of 62424 words

Chapter 21 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2839

na tsane bazan kuma sake auren ka a karo na na biyu ba, yanzu kai ba dai-dai kake dani ba, dan haka Ruky ita ce dai-dai da kai, amma ni bazan taɓa auren ka ba, don bana son ka"


Ji yay daga bayan sa ance to kaj bata sonka bani ita mu tafi.


Wannan mutumin ne ya matso gurin, Umar ya ce "Dan ta ce bata sona ba Lalle bane in baka ita tare zamu tafi saboda ƙanwata ce "


Ta ce "Ba abin da ya haɗa ni da kai malam kyale ni na tafi gun habibina"


Ya ce "Ba inda zaki je tare zamuje gida"


Ganin hawaye tayi a idon yana gangarowa ta tausaya masa amma tasa hannu a kirjinsa ta ture shi sukayi gun motar mutumin ya buɗe mata mota ta shiga shima ya shiga, basu tafi ba sai suka kunna wutar motar ya ɗauko ice cream ta amsa tana sha shima ya fara Umar yana hangosu yana jin zuciyar sa tana masa wani iri, koda ta juya taga alaman yana hangosu sai ta kashe wuta, suka ci gaba da sha a hakan can kuma Umar yaga sun tada motar suntafi ya bisu a baya, saidai maimakon suyi hanyar gida sai kuma yaga sun yi wata hanya.



Ce mata yayi muje gidana nima tunda na raka ki ko,

Ta ce "A'a ni gida zamuje "

Nan ko ya ce "Dole ta bishi suka "


Ta ce "To zata fita shine fa suka dara kokawa dashi, koda taga motar Umar da gudu sai ta sauƙe glass ɗin tana ɗaga masa hannu shi kuma yana ganin haka ya ƙara wuta a motar ya iso ra gefen ta ya ɗago mata hannu ta ce "Dan Allah ka taimake ni "


Ganin haka yasa ɗan iskan ya ɗaga glass ɗin har yana matse mata hannu ya kulle ko ina. Sannan ya ƙara gudu a motar sa, Umar ma gudu ya ƙara a motar ya bisu, wani get suka zo suka tsaya dan a buɗe get ana buɗewa motar ta shige Umar ma ya samu nasaran shiga, motar tana tsayawa Umar ya tsaida tasa ya fito yayi gun motar Bilkisu tana fitowa tayi gun Umar ta ɓoye a bayansa shi kuma yaja hannunta yana son yayi da ita cikin mota, sai gani yayi mutumin ya fito da bindiga a hannunsa ya saita shi ya ce "Ko shiga cikin gidana ko yanzun nan na harbe shi kuma dole ki shiga dan yau sai na ɗanɗani zumarki"


Ta fara jan hannun ta da ya rike a hankali Umar ya ce "Shiga zaki yi"


Ta ɗaga masa kai Ya ce "Ba inda zaki je"


Ta girgiza kai. Ya ce "ki tsaya anan kada ki matsa ko ina"



Komawa mota yayi kamar zai tafi ya barta a gurin ya ɗauko wata powder da ake watsawa dabbobi dan su hankalinsu ya ɓace yayi gaban da mota yana zuwa ya watsa masa ya dawo gun Bilkisu ta shige mota suka bar gidan. Suna zuwa gida ya tsaya tana son masa magana amma sam yaƙi bata fuska, zata fita ya ce "Kince bakya sona ko, nagode kuma insha Allahu bazan ƙara miki magana akan son da nake miki ba, nima na haƙura amma ki sani idan zuciya ta ta fashe kece sanadi"


Kallonsa take yi ba tare da ta ce komai ba, ya ce "Jeki kawai, kuma idan hukuncin da kike min bai isa ba a shirye nake da na ci gaba da ɗauka"


A hankali ta fita a motar saida yaga shigarta gida sannan ya bar ƙofar gidan.


Tana shiga ta samu Ummi da Umma suna ta hira, ɗakinta tayi tayi alola sannan tasa kayan barcin ta taje ta ɗauko Haidar ta yi musu Addu'a suka kwanta.

A haka dai ƴan biki suka watse Umar kuwa bai sake kiranta koda a waya ba, rashin kiran nata ya dame ta. Gashi bata da daman tambayar kowa, Maisun ce take tambayarta ina Daddynta bata ganin sa kwana biyu, sai ta ce bata san inda yake ba.



Sati guda kenan ba Umar ba labarin sa dan haka ta shirya ita da Maisun da Haidar ba wanda ya sani ta tafi gidan Baba tana zuwa Baba ta samu ta gaishe shi ta amsa ta kalli gidan ta ce "Baba yaushe Mama zata dawo ne"


Ya ce "Ba rana, bazan dawo da ita ba"


Ta ce "Kai Baba kayi haƙuri dan Allah ka dawo da ita mana gidan ba daɗi ba mata Wallahi "



Ta ce "Bilkisu da bakin ki kike cewa haka"



Ta ce "Eh Baba Mama tayi nadama kuma yanzu zata bi umurnin ka"



Ya ce "To shikenan zan duba, munje anyi maganan Ummin ki da Abbanki ba jibi za'a ɗaura auren su"


Ta ce "Nikan ban sani ba ma"


Maisun ce ta ce "Baba Ina Daddy na ne"


Ya ce "Kyale Daddyn ki yana can bashi da lafiya nayi-nayi da shi muje asibiti amma taƙi zuwa sai dirkawa kansa Alluran dabbobi yake"


Bilkisu ta ce "To kuma Baba ba'a hana shi ba kada ta masa illa fa"



Ya ce "Taurin kai gare shi, kuma baza ta masa illa ba"


Ta ce "Barin je na duba shi"



Suka tashi suka bar Haidai a hannunsa ta tura ƙofar ta jita a buɗe ta shiga ciki ta ganshi a kwance a kan gado ta je ta zauna a bakin gadon Maisun kuma ta hau gadon kusan kansa ta ce "Daddy meke damunka ne"

Ya ce "Ba komai"



Bilkisu ta ce "Me yasa kaƙi zuwa asibiti"


Ya ce "Taya zanje asibiti bayan kece maganin nawa"








_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/12, 5:45 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Last Page 79-80




Ta ce "Hmm ni kuma to gani ay"

Ya ce "Ba wai ganin ki kawai nake buƙata Idan na ganki ban bakya sona fa, kinfi son wani a kaina"


Ta girgiza kai ta ce "Nikan bana son kowa, bani da wani sama da kai, yanzu na gane bani da wanda ya fika"


Ya tashi a hankali



Ta ce "Kwanta kawai basai ka tashi ba, barin gyara maka ɗakin kalli yadda ɗakin ya dawo" nan fa ta fara gyara masa ɗakin yana kallonta saida ta gama tazo ta haɗa masa ruwan mai zafi a bayi ya shiga ya ya fara wanka ita kuma ta gyara gadon ta cire zanin gadon ta saka masa wani, yana fitowa ta fita taje cikin falon ta haɗa masa tea mai kauri ta kawo masa, duba tayi taga akwai kayan abinci, nan fa ta fara shirin girki, cikin lokaci kaɗan ta gama. A kula ta sa ta kai masa ta zuba masa plate ya amsa ya kalli abinci ya kalleta yayi murmushi ya ce "Nayi missing ɗin abincinki gaskiya "


Ta ce "Gashi yanzu ay sai kaci"

Ya ce "Tare zamu ci amma"


Cokali tasa suka fara ci tare har Maisun ma.

Sai yamma tabar gidan ta koma gida da daddare kuwa suka yi waya sosai ita kanta tasan tayi sake da yayi zuciya da kuma waye zai maye mata gurbin Aliyu, tasan duk duniya Umar ne zai maye mata gurbin sa, zai zame mata mijin marainiyya.



Bayan kwana biyu aka ɗaura auren Abba da Ummi Baba ma ya maida Mama Sauda ɗakinta tayi nadama sosai yanzu biyayya take masa sau da ƙafa, bayan nan ne kuma aka fara maganan Auren Bilkisu da Umar, sai aka haɗa da Usman da Husaina, Mommy ce tace "Bilkisu tazo kaduna dan ta gyara ta"


Umma kuwa tasa ta yaye Haidar da yake yakai shekara ɗaya kuma ya saba da su sosai, ta ce baza ta tafi da su ba daga baya a kai mata su.


Tuni Umar ya sama wa Maisun Makaranta taci gaba da zuwa.


Kaduna taje Mommy ta mata gyara na musammam ta ƙara komawa yarinya ɗanya shataf.


Ana saura kwana biyu ne biki suka zo da Mommy.


Ranan tana zuwa kuwa ba ɓata lokaci aka ɗaura auren Bilkisu da Umar, washe gari kuma aka ɗaura auren Usman da Husaina. Anyi shagarin biki sosai inda Amare da angwaye suka tare a ɗakunan su. Ha biki ya watse kowa yana sam barka.



Maryam ne dai na aci moriyar bikin da ita don tana da tsohon ciki da ƙyar take tafiya saidai tana zaune ne.



Bayan bikin ne da kwana huɗu ta haifi ɗanta namiji, Ranan Suna kuwa yaci sunan Abba ana kiransa da Ajman.



BAYAN SHEKARA BAKWAI



Yaran Bilkisu Shida Maisun ta farko da take shekara goma sha ɗaya sai Haidar da yake sha takwas sai Ibrahim da ake ce masa Khalil shekaran sa shida Sai Halimatu mai sunan Ummi d ake kiranta Ummita ita shekaranta huɗu sai kuma ƴan biyunta Mata shekaransu biyu Aisha da Suwaiba shekaransu Biyu sai ƙaraminsu da take goyo wato Jafar.


Abubakar yaransa huɗu Ibrahim sai Yusuf sai jafar sai ƙaraminsu Aliyu, shikan baida mace ko ɗaya kuma yana son ya samu saidai nan gaba.



Usman shima yaransa biyar na farkon Aisha da Halimatu ƴan biyu ne sai kuma Ibrahim sai kuma Maimunatu da Aliyu suma ƴan biyu ne.


Sai Khadiyo ita kuma tana da yara biyu yaranta biyu Suwaiba sai kuma Halimatu.




Family ne ya haɗu ko yaushe cikin farin ciki suke da ƙaunar juna.


Bilkisu ta zama likita Umar ya buɗe mata asibiti inda shi kuma ya buɗe asibitin dabbobi kusa da nata asibitin.



Ya tashi kenan da yamma yabar likitocin dabbobi a ciki ya shiga asibitin Bilkisu office ɗinta ya shiga kai tsaye da Jafar a hannunsa tana ganinsa ta ce "Haba Abeey ya zaka ɗauko min shi ban gama ba"


Ya ce "Yana ta wahalar da Ummi da yawa shi yasa na taho da shi nasan kema kin gama ko sai muje gida"


Wata Nurse ce ta shigo ta gaisheta ta ce "Madam wata ce me HIV tana jiranki tun tuni "


Ta ce "Kiyi mata abin da ya dace kinga Mai gidana yazo sai gobe kuma"


Ya ce "Kije ki duba ta mana daga nan sai mu tafi ko"


Ta ce "To barin shirya daga nan na tafi ko"


Ta kalli Nurse ɗin ta ce "Kice mata ta ɗan jirani ina zuwa"


Ta fita ita ko ta Amshi Jafar ta fara bashi Nono saida yasha ya ƙoshi sannan ta miƙa masa ta shirya sannan suka fito, gaba tayi tabar Umar a baya tana zuwa gurin taga Ruky da hannu ɗaya, ɗayan hannun an yake shi, kallon mamaki take mata ita ko Ruky ta ce "Bilkisu me kika zo yi asibitin nan, dan Allah kije ki kira min wannan likitan tazo ta duba ni ta bani shawarwari "



Nurse ɗin ta ce"Ay ita ce Likitan "


Ruky ta fara kuka Bilkisu ta ce "Tsaya yi shiru muje in duba ki"


Umar ne ya ƙaraso gurin ya kalle ta ita ma kallon sa tayi ta ce "Umar "

Ya sake kallon ta ya ce "Sannunki"


Kuka ta kuma fashewa dashi ya juyo ya ce "Kukan me kike yi"


Ta ce "Umar bani da kowa ka taimake ni Mamata Tayi mutuwar wulaƙanci a ƙarƙashin gada ba wanda ya iya binneta sai ruwa ne ya tafi da ita, kuma HIV ne ya kashe ta, abin baƙin ciki ma wanda ya saka mata shi ya saka min"



Ya ce "To yanzu me kike so in miki"


Ta ce "Ka maida aurena da kai"


Kallon banza ya mata ya kuma kallon Bilkisu ya ce "Baby bata shirya ki duba ta ba muje gida kawai"

Bilkisu ta ce "Ki kalle ki fa toma kina da ciwo muna da lafiya shine zamu aure ki, Allah ya kiyaye baki ma yi nadama ba, idan zaki zo muje in duba ki kizo idan baza ku zo ba kuma ina da Abin yi, mijina yana jira na"


Ta taka a hankali tabi bayan Bilkisu suka shiga ta mata ƴan gwaje-gwaje ta fito ta rubuta mata magunguna sannan ta bata shawarwari, suka fito, Ruky ta kalli Umar ta ce "To dan Allah ko Sadakan ɗari biyar ne ka ɗan bani"


Bilkisu ta ciro kuɗi dubu biyar ta miƙa masa suka tafi Ruky sai kallon su take tana cije leɓe. Da hannunta ɗaya.



Da daddare ko duk yaran suna nan Maisun tana koyawa Ummita Home work Haidar kuma yana koyawa Khalil, gefe kuma ƴan biyu ne suke da damun Bilkisu da Umar Jafar kuma yana ta barcin sa.



Can da aka gama Home work ɗin Ummita ta shigo da gudu ta faɗa kan Umar sai Khalil ya biyo ta ta tashi ta tsallaka Jafar tayi jikin bango Umar ya riƙe Khalil ya ce "Me ta maka"


Ya ce "Bata jin magana kullun sai tana ce min mai ƙaton kai"


Ya ce "Kayi haƙuri, ke kuma idan kina masa rashin kunya zan sa yana zane ki"


Bilkisu ta ƙwalawa Maisun kira ta amsa tazo ta ce "Yaran nan sunyi Sallah isha kuwa"


Ta ce "Eh"


Ta kalle su ta ce "To kunyi wa Abban ku Aliyu Addu'a "


Khalil ya ce "Nidai nayi amma Ummita bata yi ba ina kallonta"


Nan fa Ummita ta fasa kuka ta ce "Wallahi ina yi kullun har a makaranta kuma in ƙarya ne Allah na kallon mu"


Bilkisu ta ce "To kuje ku duka Auntyn ku ta gyara muku shimfiɗa ku kwanta ga ƴan biyu ma kuma ku bisu"

Duka suka tafi da gudun su.

Umar ya bisu da kallo yana musu Addu'a ya ce " duk cikin Haidar baida rigima"


Ta ce "Ba ruwansa amma idan suka masa bai iya duka ba dan Ummita tafi shan wahala saboda tana da tsiwa"


Ya ce "Ummita ay ko Maisun bata bari ba "


Ta ce "yawwa kaga Maisun tana tausaya mata amma Haidar idan ya kamata da bugu ko"


Ya ce "Allah dai ya shirya mana su ya musu Albarka"


Ta ce "Amin"




ALHAMDULILLAH



INA GODIYA GA ALLA MAI KOWA DA KOMAI DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LABARI MAI SUNA *BILKISU* ABIN DA MUKA FAƊA DAIDAI ALLAH YA BAMU LADA WANDA MUKAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MANA.




Sai kuma mun haɗu a sabon littafina Mai zuwa insha Allah wato ma suna *A MASARAUTATA*



NAGODE🥰🥰





_*Mrs Aliyu ce*_





lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login