Showing 9001 words to 12000 words out of 62424 words

Chapter 4 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2845

zai fita ya tare shi ya ce "Abba dan Allah kayi hakuri ka daina ƙaurace mana bamu san abin da muka maka ba kake yi mana wannan horon"


Bilkisu tana daga ɗaki tana jin Muryar yayan ta ta fito ta kama hannun Alhaji ta ce, "Abba dan Allah ka dawo gare mu kada wata banzar... "

Maganan ta yanke sakamakon marin da ya bata har saida tayi taga-taga zata faɗi Abubakar ya tarota, ya nuna ta da yatsa ya ce "Ke har kin isa ki hana ni abin da nayi niyya to bari kiji daga ke har iyayen ki baku isa ba, Kuma nan da Sati biyu za'a ɗaura min aure da Talatuwa, duk cikin ku wanda baya son wannan aure ya bar gidan, gida ay nawa ne ba na wani ba"


Yana gama faɗa ya fita abin sa.

Abubakar kuwa yaja kanwarsa zuwa ɗakinsu yayita rarrashinta, dama me neman kuka an jefe shi da ɓawon gyaɗa.


Tun lokacin ba wanda ya ƙara tunƙaran sa, Sati biyun yana cika kuwa Aka daura aure, sai zuwa musu yayi da goro ya kira Umma da Ummi har daki ya ce "Yau an ɗaura min aure da Talatuwa Mama Ruky na kiraku daki ne na faɗa muku saboda naga yanzu ƴaƴan ku basu da kunya...


_Ayi hakuri da ɗan wannan wayar ba caji_



_*Mrs Aliyu ce*_



lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[5/18, 8:15 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 13&14




Umma tayi murmushin ƙarfin hali ta ce "Allah ya baku zaman lafiya Alhaji, kuma yaran mu ba suyi maka wani rashin kunya ba, idan kana tunanin haka ma to kayi haƙuri yarinta ne, muma ba munƙi auren bane, yadda matar take ne amma Allah ya bamu zaman lafiya"

Ya ce "Amin idan da gaske kike"

Ƙara kallon sa sukayi kamar masu nazarin wani abu, shi kuwa ba abin da ya dame shi harkokin gaban sa kawai yake yi.


Ba wanda ya kuma masa maganan shi ma baiyi maganar a kowa, baya ma zama dasu yayi wani taɗi da su, Sati biyu da yin hakan ya shigo bayan Isha ya same su duka a falo ya zauna Ummi miƙe ta kawo masa Abinci ko kallon abincin baiyi ba sai cewa yayi "Yau Talatuwa ta tare gidan ta ma zanje in kwana"

Umma ta ce "Ina ce anan zata tare"


Ya ce "A'a na kama mata haya kunsan ita da ƴarta ne "

Ta ce "To ay a gani na ɗakin Marigayiya ya isheta ita kuma Ƴar tata sa haɗu da su Bilkisu "

Ya ce "A'a ita ta ce tana son a ware wa ƴarta ɗaki ɗaya ne kinga ay ba gun zama a nan"

Umma ta ce "To Alhaji ay shikenan Allah ya baka ikon yin Adalci a tsakanin mu"


Ya miƙe yayi hanyar ƙofa Bilkisu zata yi magana Umma tasa ɗan yatsan ta a bakinta alamun tayi shiru.


Bayan ya tafi Abubakar ya ce "Umma me ke faruwa ne, kiga fa ko abincin da aka kawo masa ya ƙi ci"


Ta ce "Ina tunanin Sauri yake yi, muyi masa uzuri"


Bilkisu ta ce "Uzuri Umma, amma fa... "


Umma ta ce "Bana son dogon zance"

A ƙa'idar musulunci kwana uku yake a ɗakin bazawara amma Alhaji saida ya share sati bai shigo gidan ba, ranan da sati ya cika Ummi ta kalli Umma da take kusa da ita ta ce "Yaya anya Alhaji lafiyansa kuwa, idan Amaryarsa budurwa ce ya kamata ace yau ya dawo gare mu"


Umma ta ce "Haka ne, amma mu bashi uzuri"

Ta ce "Amma wani uzuri zamu bashi yanzu, ya kamata a ce ko a waya ne ya kira mu"


Ta ce "Mu sai mu kira muji ay"


Umma ta ɗauki waya ta latsa number sa bugu ɗaya aka ɗauka saidai maimakon taji muryan Alhaji sai taji wata ƙatuwar Murya har saida ta tsorata "Hello waye"

Ta ce "Dan Allah ina mai wayar"

Aka ce "Wai ke wace irin ƴar tasha ce zaki kira min miji kina kuma kuma tambayar ina yake"

Anan Umma ta gane Matarsa ce sai ta ce "Kiyi haƙuri ni uwar gidan sa ce"


Taja wani dogon tsaki ta ce "To ya shiga wanka sai ki bari idan ya fito, shashasha kawai"
Tana gama fada taji ɗif alamun an kashe wayar.


Umma ta bi wayar da Kallo yayin da Ummi kuma take kallon ta dan duk taji abin da suka yi.



Ummi ta ce "Yaya... Wannan wacce irin mace Alhaji ya auro? "



Ta ce "Allah kaɗai masani"

Suna jira suga ko ya kira shiru har suka shiga kowa ya kwanta, washe gari da safe ma shiru, har saida rana sai gashi ya shigo duka suka masa sannu da zuwa suka gaishe shi ya amsa zasu masa magana ya katse su ya ce "Me yasa dan kin kira ni Talatuwa ta ɗauka amma tsabar rashin hankali kika zage ta, me ta miki"


Ummi salati ta fara yi tana tafa hannu yayin da Umma kuma take kallonsa cikin mamaki dan ta kasa magana, shiko ya ci gaba "Dama tunda na ƙirƙiro wannan auren na lura bakwa so, kun ziga ƴaƴanku suna min rashin kunya kun ɓata min tarbiyyan ƴaƴa to bari kiji sai kisan yadda zaki yi Talatuwa zata dawo wannan gidan kuma ta zauna wanda bazai iya zaman gidan ba sai ya kama gaban sa"


Umma ta ce "Ita Talatuwan ne ta faɗa maka haka to na barta da Allah"

Ya ce "Nidai na faɗa da daddare zata zo ta zaɓi ɗakin da take so"


Umma ta ce "Allah ya kawo ta "

Baice komai ba ya fita, bayan ya fita Ummi ta kalleta ta ce "Yaya... "

Saboda ɓacin rai bata ce komai ba.



Da daddare kuwa suna zaune a falon su Abubakar suna ta cin Abinci ita ko Bilkisu ba cin abincin suke ba amma ta dame su tsokana ta taɓa wannan ta tsakuli wancan, Khadiyo kuma tana kwance tayi matashi da cinyar Umminta.


Ganin wata ƙatuwar mace suka yi ta shigo fuskarta ba alamar fara'a ba Sallama tana zazzaro ido sai wata matashiya a bayanta, ta saka wasu shegun kaya, rigane wanda duk rabin nononta a waje suke sai sket wanda aka tsaga shi har iya cinya, ita ɗin ma fuska a ɗaure, duk kan su sun zuba musu ido. Babbar macen tayi ciki zatayi hanyar kicin Usman ya miƙe ya sha gaban ta ya ce "Baiwar Allah lafiya zaki shigo mana gida kai tsaye kuma kin ganmu kina neman shiga inda ba'a baki izini ba, ko da yake yanzu ma ba'a baki izini ba"


Tayi masa wani kallo daga bisani ta kutuntumo ashar ta yaɓa masa sannan ta ce "To Bari uban naka ya shigo dan... " ta ƙara lailawo wata ashar ɗin ta yaɓa masa.

Bilkisu ta miƙe zatayi gurin su Umma ta tare ta sannan ta ja hannun Usman ta ce "Matar Abban ku ne shi ya turo ta, ta zaɓi ɗaki"


Bilkisu ta ce "To dan ya turo ta sai ta nemi ta ci mana mutunci ita ɗin wacece"


Ƴar matashiyar ta nuna Bilkisu da ɗan yatsa ta ce "Keeeee idan kina faɗa wa Mamana magana zan ci abu ta kazan ubanki"


Bilkisu ta ce "Ehhhh an saba zaman tasha dole a iya ashar"


Zuwa tayi ta kama Bilkisu da kokawa ganin haka Abubakar ya jawota ya kwaɗa mata mari, daga marin sai ta kwanta shame shame, ita kan Talatuwa ta kwala ihu tana cewa "Wayyo Alhaji zasu kashe min ƴata Ruky, "


Da sauri Alhaji ya shigo yaga Ruky kwance shame-shame.


_Ayi haƙuri da wannan ɗin ma mun samu matsalar wuta ne._

*Kuma dan Allah ku taya mu da Addu'a Allah ya tsayar da yajin aikin da ake a jihar mu ta Kaduna.*




_*Mrs Aliyu ce*_





lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/19, 8:35 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*_Gaskiya bana samun abin da nake so a gurin ku, wato comment da sharhi ko ba komai nima ina son insan cewa labarin yana shi kuma ana jin daɗin sa_*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 15-16




Ya ce "Wa ya mata hakan ita da waye"


Nan da nan Talatuwa ta sa kuka wiwi kamar ƙaramar yarinya cikin kuka ta ce "Daga shigowan mu suka kama yi mana faɗa har wacce yarinyar taka tazo tana dukanta suka haɗu da wannan yayan nata suka yi ta duka"


Ya ce "Na fa daɗe ina faɗa muku duk wanda bazai iya zama da su ba ya bar min gida na"

Bilkisu ta ce "Abba Wallahi ba haka aka yi ba"

Tana rufe baki taji ya buge mata baki, da Sauri Abubakar da Usman suka ce "Ahhh" ta tare suka rike ta Abubakar ya ce "Abba yanzu wannan matar har takai tasa kana dukan Bilkisu"


Shi ɗin ma mari yaji ya kwaɗa masa, Umma kan ɗakin ta tayi, ita ma Ummi ta shiga, Khadiyo tabi bayan ta, ya kalli Talatuwa ya ce "Ki zaɓi ɗakin da ya miki ita ma Ruky ta zaɓi nata ɗaki"


Ganin Inda Umma ta shiga yasa ta nuna ɗakin Umma ta ce "Shi take so, ita ko Ruky ta nuna ɗakin su Bilkisu"

Shiga yayi ɗakin ya sami Umma kwance ya ce "Ki tattara kayan ki ki koma ɗakin Suwaiba Amarya ta ce "Tana son ɗakin"

Umma ta miƙe ta fito falo ta kalli Talatuwa ta ce "Idan kina son zaman gidan nan ki shiga can dakin, sannan ƴarki ta haɗu a ɗakin yara ƴan matan amma ba wanda zai fita ya bar miki ɗaki"


Shiru tayi tana yiwa Alhaji wani kallo wanda kai idan kaga kallon kasan na umurni ne, shi ɗin ma kuma ya gane hakan yasa ya ce "Aisha yaushe muka fara musanyan yayu da ke"

Ta ce "Yau! Bazan taɓa barin ɗakina ba, kuma su Bilkisu ba inda zasu je"


Talatuwa ta ce "To Alhaji ni gaskiya ka sake ni, tunda naga alama Iyalenka sunfi ƙarfinka"


Abubakar ya ce "Ayko sai dai ya sake kin"

Da sauri Alhaji ya tunƙaro shi gadan-gadan da sauri Umma tasha gaban sa haɗi da cewa "Ba zai yuyu ina gani ka sake dukan min ƴaƴa ba "


Komawa yayi ya zauna yana huci, ita ko Umma ta kalli Bilkisu ta ce "Kije ki kwanta, " sannan ta kalli su Abubakar ta ce "Kuma ku shige ɗakin ku"


Duka suka fita daga falon sukayi ɗakin su ita ma Bilkisu tayi nata ɗakin. Umma ma juyawa tayi zata yi nata ɗaki sai ji tayi ya ce "Kada ki sake ki koma ɗakin nan, na gaya miki gida nawa ne, idan baza ki zauna a wancan ɗakin ba ki bar min gidan"


Ta juyo ta ce "Ba inda zanje, kuma ina ɗakina banga wanda ya isa ya fitar dani ba"

Talatuwa ta ce "Idan kana son in zauna a gidan nan to sai dai ka sake ta, dan idan ba haka ba ta bar min ɗaki"

Bilkisu tana daga ɗaki ta jiyo da sauri ta fito tayi ɗakin Ummi ta same ta kwance saidai ba barci take ba ta ce "Ummi dan Allah ki fito kada Abba ya aikata mummunan kuskure"


Ta ce "Menene"

Ta faɗa mata duk abin da taji, da sauri Ummi ta mike ta fito ta samu Talatuwa tana girgiza ƙugu Ummi ta ce "Haba baiwar Allah ya zaki zo ki samu mace a ɗakin mijinta amma kice dole ta fita, ay ina ga baki mata adalci ba"

Ta ɗago wa Ummi hannu ta ce "Banyi da ke ba, "


Ta dubi Alhaji da yayi shiru ya sunkuyar da kai ta ce "Malam ina jiranka fa"


Ya ɗago ya kalli Umma sanna ya kalli Talatuwa ya ce "Kinga fa ita ce Uwar gida na bazan iya ba"


Ta ce "Shikenan Ruky tashi mu koma cikin tasha"


Ya ce " Kada kije ko ina"


Ta ce "To ka sake ta"


Ya kalli Aisha sannan ya kauda kai gefe ya ce "Aisha kinƙi jin magana ta, To koje na sake ki saki ɗaya"

Ihu Bilkisu ta saka ta fita afalon tayi ɗakin yayyen ta tana kuka ta samu suna zaune sun haɗa kai da gwiwa, jin kukan ta yasa suka ɗago suna kallon ta tana cewa "Abba ya saki Umma"


Da sauri sukayi Falon suna zuwa suka durƙusa gaban sa, Suka kama gwiwarsa Abubakar ya fara magana "Haba Abba shekara nawa kuna tare da Umma amma wata zata raba ku"


Usman ya ce "Abba baka cikin hayyacin ka, meyasa zaka aikata haka yaushe ka haɗu da wannan mata"

Shidai kallon su kawai yake, Bilkisu kuwa tana ganin yadda Umma ta fito da Akwatin ta Ummi na kuka tana bata haƙuri akan kada ta tafi, ta kalli Talatuwa ta ce "Kema barin gidan nan zaki yi Wallahi "



Umma ta ce "Bilkisu bana son rashin kunya ku koma ɗakin ku, su Usman kuma ku tafi ɗaki, Ummin Yara ga yara ki ci gaba da hakuri da su"


Ta hango Khadiyo tana kuka can nesa ta je ta rungumeta ta ta ce "Kiyi shiru "


Suna gani Umma ta fita sannan ta ce "Kada su koma kada su biyo ta"

Kowa sai kuka yake, banda Talatuwa da ƴarta wanda suke jin kansu kamar a Aljanna, shiko Alhaji yayi shiru an kasa gane halin da yake ciki ma.


Sai da suka san Umma tayi nisa Bilkisu ta fara magana cikin kuka tana cewa "Wallahi gidan nan ba zaman Lafiya, Abba ka mayar da gidan ka filin yaƙi, dan baza mu taɓa yiwa wannan matar biyayya ba"


Abubakar ya ce "Gidanka yana cikin zaman lafiya ka tarwatsa shi, kana tunanin zamu dauke ta da mutunci ne, saboda ita ka kora mana mahaifiya, to yau itama sai ta bar gidan nan, ta koma can gidan hayan da ka kama mata idan ba haka ba zamu mata lahani.


Ummi ta rike hannun Abubakar ta ce "Bansan ka da haka na"

Bata ankara ba taga ana kokawa da Bilkisu da Ruky, yayin da Khadiyo ma ta shiga suka kwantar da Ruky ƙasa suna duka, gefe guda kuma Usman yayi kan Talatuwa da sandar moper a hannunsa.




_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/20, 7:08 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Alhamdulillah mun gode wa Allah da ya kawo mana ƙarshen wannan yajin aikin, muna ƙara godewa waɗanda suka mana Addu'o'i*


*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 17&18




Sa sauri Ummi taje ta sha gaban sa ta zaro idon ta ta ce "Usman kana hauka ne me kake da niyyar yi, "


Ganin haka yasa Talatuwa taje don ceton ƴarta, tana zuwa ta ɗago Khadiyo da hannu ɗaya ta wugar gefe kafin ta kai ga ɗago Bilkisu kuwa ta tashi ta arce da gudu, tana ɗago ƴarta tayi waje da ita daga bakin ƙofa ta ce "To Malam ay sai ka tashi mu tafi"


Miƙewa yayi baiyi magana ba su kuwa suna kallon sa ya fita.



Usman yaje ya ɗago Khadiyo ya ce " Sannu ko, baki ji ciwoba, ina yake miki ciwo"

Ta girgiza kai kwalla yana zuba mata ta ce "Banji ciwon komai na,"


Suna tunanin zai dawo shiru bai dawo ba ganin dare nayi yasa Ummi ta ce "Kowa yaje ya kwanta a ɗakin sa"


Duk da sunje sun kwanta ɗin ba wanda ya rintsa a cikin su, ko wannen su yana tunanin yaya zai raba wannan mata da mahaifinsu.


Da safe kowa ya shirya ya tafi inda zaije mazan duka suka yi gun sana'an su da yake suna hutu, matan kuma makaranta dan Bilkisu zata zana junior waec ne Yayin da Khadiyo tana primary 3.


Su Khadiyo suna riga tashi dan haka su aka fara tashi drivern da Abbansu ya ɗauka musu ya fara kai Khadiyo gida kafin nan daga bisani ya biya ya Bilkisu a get ya ajiye ta ta shigo falon kai tsaye ba tare da Sallama ba, ganin Talatuwa tayi kwance a tsakiyar falon sai Ruky tana zaune kan kujera tana danne-dannen waya.



Ruky ce ta fara magana ta ce "Malama lafiya zaki shigo mana gida ba Sallama ma"


Ta ce "Ay baku cancanci Sallama ba, tana gama faɗa ta wuce ɗakin su "


Talatuwa ta ce "Barta Ruky Bari uban ta ya shigo ni da uban ta zanyi, dan uwarta ma ta min kaɗan "


Shiga tayi ɗakin nata taga ya canja mata tana juyowa taga Ruky ta shigo ta ce "Malama fita min a ɗakina"


Yunwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login