Showing 33001 words to 36000 words out of 62424 words
Chapter 12 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt
_*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 43-44
Tashi tayi ta zauna tana kallon sa, gani tayi ya hau gadon ya rungumeta ta matsa can gefe jikin bango, ya kuma matsawa ta fara kuka ta ce "Dan Allah kada ka dake ni kaga ban maka komai ba"
Ya ce cikin wata irin murya, "ke dalla ba dukan ki zanyi ba"
Gani tayi yana ƙokarin cire mata riga nan fa suka fara kokawa tana son kwatan kanta, duk da bata da ilimin sanin wannan harka yanayinsa ya tabbatar mata da halin da yake ciki kuma tasan me zai mata, hakan yasa tayi saurin barin ɗakin, ya riƙota suna kokawa, da yake ƙarfin su ba ɗaya ba, yasa ya iya rabata da kayan jikinta. Ganin zaici nasara a kanta yasa ta fara kuka tana cewa cikin kuka "Dan Allah kayi haƙuri kada ka min komai "
Harara ya mata, ya ce "Kin manta ni waye a gurinki, da baza ki yadda da ni ba, ohhh kin fi son ki yadda da mazan banza a kaina. "
Yo wa kanta ya kuma yi ta dunƙule hannu ta masa naushi a idonsa ya kama gurin ya kwanta kan gado taja bargo ta rufe jikinta zata fita, ganin halin da yake ciki yasa ta dawo tana cewa "Dan Allah kayi haƙuri Wallahi ban sani bane"
Sake riƙeta yayi ya matse ya ce "Kin bawa wasu ma balle ni, har kina ƙoƙarin ji min ciwo"
Kokawa ce ta barke tsakanin su saidai kuma yaci nasa a kan ta, inda take ta kuka da yaƙushi harda su cizo amma Umar ya jure, saboda yadda yaji Bilkisu a cike tam, cikekkiyar budurwa, jikinta kuwa ga ƙamshi ga kuma ni'ima mai sawa mai gida farin ciki, bai taɓa tunanin haka zai samu Bilkisu ba, bai taba sanin ana iya samun irin wannan ni'imar a jikin mace ba, gaskiya ya cuci kansa, kuma ya cuci Bilkisu.
Ko da ya samu nutsuwa ya juya yaga yadda take zubar da hawaye, shima ji yayi hawayen na zuba a idonsa ya jawota ya rungumeta yana bubbuga bayanta, kukan ta ne ya tsaya jin yana bubbuga mata baya, alamun yana rarrashinta miƙewa tayi daga jikinsa ta koma gefe tana cewa "Allah ya isa tsakani da kai, bazan taɓa yafe maka ba"
Hannunta ya kama ya ce "Haƙiƙa na cancanci duk wani hukuncin da zaki min kuma zan ɗauka, nayi miki mummunan zato kin faɗa min ke ba mazinaciya bace amma naƙi yadda yau na tabbatar da hakan fizge hannunta tayi ta sauƙa zata tafi nan taji baza ta iya tafiya ba ta koma ta kwanta ta kuma fashewa da wani sabon kukan.
Bayi ya shiga ya haɗa mata ruwan ɗumin da dettol ya dawo ya sa hannu ya ɗauke ta kamar jaririya, tana wutsil-wutsil da ƙafa haka ya kaita ya tsomata a ciki tana dukansa da zaginsa amma haka ya dannata a ciki, da taji daɗin ruwan sai ta zauna sau uku yana canja mata, sannan ya fita ya barta, ita kuma tayi wankan tsarki a ranta tana ƙara tsine masa.
Taba fitowa taga ya canja zanin gado ya shimfiɗa wani sabo, ya ɗauki zanin gadon a hannun sa yana son ya shiga bayida shi yana kallon ta, ita kuma sai hararansa take, ya shiga cikin bayin, ita kuma ta shafa mai tasa wani kayan barcin ta kwanta, gani tayi ya fito da zanin gadon da ya wanke a hannunsa ya fita da shi, yana fita ta rufe ƙofa tasa key ta dawo tayi kwanciyarta.
.
Shi kuwa yana shanyawa ya dawo ɗakin amma yaji a rufe ya bubbuga shirubata buɗe ba haka ya haƙura ya koma ɗakinsa, yana jin farin ciki yana ziyartarsa .
Daga bisani kuma ya ringa murmushi yana zubda kwalla. a haka barci ya kwashe shi.
Kiran sallahr farko ta tashi, ta shiga bayi a hankali ta sake yin tsarki da ruwan zafin ta sake jin daɗi, sannan tayi Alola tayi raka'atainil fajr sannan tayi tayin Addu'o'i har aka kira Sallah tayi Sallah asuba. Nan ma tayi ta ƴan Addu'o'inta. Sannan ta kwanta a gurin barci ya kwashe ta.
Sai ƙarfe 10:15am ta tashi fitowa tayi falo taji ƙamshin girki na tashi alamun ana girki, shiga tayi kicin ɗin ta ganshi yayi kaca-kaca da kicin ɗin wai yana haɗa kumallo, komawa tayi ya jawota ya rungumeta ya ce "Nasan har yanzu kina fushi da ni ko"
Haushi ya bata ta kama hannunsa tana son ta raba shi da jikinta amma ina. Zamowa yayi ƙasa ya durƙusa ya rungume ƙafafunta ya ce "Kiyi haƙuri dan Allah kada ki azabtar dani, ki yafe min nasan na miki mummunan zato a baya na alaƙanta ki da abin da baki aikata ba, Har ga Allah Ina sonki, to abinda yasa nake miki hakan saboda abin da aka ce kinyi ne, wanda a yanzu nasan ƙazafi aka miki, ki taho gare ni, muyi rayuwar ma'aurata" kallon sa take yayin da ta hango hawaye daga cikin idon sa yana zuba da sauri itama ta durƙusa tana share masa hawayen shi kuma ya rungumeta yana bubbuga bayanta yayin da shi kuma yake sake zubar da hawayensa.
Tunani kala-kala fal cikin ranta, wai ita ce Umar ke lallashi har yake zubar da hawaye akan ta. Ɗagowa tayi ya riƙeta ya ce "Ina kuma zaki je? "
Ta ce "Zanje na haɗa mana kumallo"
Ya ce "Na gama mana komai ay, saidai in baza ki iya ci ba"
Ta miƙe zata tafi ya ce "Ina zaki je"
Ta ce "Wanka zanyi"
Ya ce "To je ki kiyi barin ƙarasa"
Ba musu ya tafi tana zuwa ta faɗa kan gado daɗi ne taji a ranta wai ita Umar ke tattali, dama can ashe yana son ta, saboda ƙazafin da aka mata ne yasa ya tsane ta, yau dai ya san wacece ita, yasan cewa bata taɓa yin zina ba, inko son da yake mata gaskiya ne to lallai ita ma zata rungumi mijinta.
Sai da ta gama tunaninta ta shiga tayi wanka, yau kan sai ta tsinci kanta da tsara kwalliya kamar zata je gasar sarauniyar kyau, Atamfa koriya ta saka ɗinkin riga da sket aka yi, ta ɗaura ɗan kwanlin ta ɗaurin zamani, tayi kyau matuƙa, ta fito tayi kicin ɗin taga yana ta gyarawa, ya juyo ya kalle ta ya isa gurinta ya kama hannunta ya ce "Kinyi kyau sosai"
Murmushi tayi ta ce "Ka fini kyau ay"
Ya ce "Kalle ni fa yadda nayi datti fa"
Ta ce "Kaje kayi wanka zan ƙarasa"
Ya ce "Nagode, "
Ya shige ɗakinsa ita kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta gama gyara kicin ɗin ta haɗa da falo da kuma ɗakin ta, ta shiga ɗakin sa taga ya shirya da shadda ɗinkin kaftan ya saka hula yana gyara sajen sa a gaban madubi. Ta ce "Zaka fita ne kuma"
Ya kalle ta ya ce "Wannan kwalliya duk naki ne, ba inda zanje yau"
Gyara ɗakin ta fara yi yayin da ya taya ta, bayan sun gama ne suka je dan su karya, A baki ya ringa bata abincin tana ci saida ta ƙoshi shima ya ci.
Yini suka yi suna Soyayya a gidan, Idan lokacin Sallah yayi ita da kanta take cewa yaje masallaci.
Ƙarfe biyar ya ce "Ta shirya suje su gaida Baba"
Ta shirya tsab suka shiga mota suka yi gidan Baba, a yana parking ta fito ya ce "Ina zaki je, ki jira ni"
Ta jira ya rufe motar yazo ya riƙe mata hannu suka shiga falon tare, Baba suka tarar a falo yana ganin su ya washe baki, Mama Sauda ta fito daga kicin tana ganinsu a haka ta ɗaure fuska tana musu wani kallo, Bilkisu na ganin haka tayi ƙoƙarin ƙwace hannunta yayin da shi kuma ya damƙe hannun.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/2, 7:12 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
_*Allah ya jiƙanki Dada Wasila Isah Musa, yau shekara karanki goma kenan da tafiya, Allah yasa kin huta, Allah yasa kina cikin rahman sa, yayi wa ƴaƴanki Albarka, Munyi kewanki Dada Wasila"*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 45-46
Baba ya lura da hakan yasa shima ya mata wani kallo wanda yasa ta koma ba shiri, ya kalle su ya ce "To Kun tsaya min a kai ku zauna mana"
Murmushi suka yi duka suka zauna a ƙasa suna, gaishe shi, bayan sun gaisa ne Baba ya kalli Umar ya ce "Ina kuka bar Rukayyan"
Umar ya ce "Tayi tafiya ay"
Ya ce "Ina taje kuma"
Kai tsaye ya ce "Ban san inda taje ba ta ce dai sati guda zata yi"
Baba ya kalle shi ya ce "wani irin aure kake haka har matarka tayi tafiya amma baka san inda taje ba"
Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi Baba ya ce "Baka cikin hayyacin ka Umar, ya za'ayi ka saki mace tayi abin da take so"
Faɗa yayi ta masa sosai sannan ya ce "Idan kun koma gida ka buga mata waya ta dawo ko ta faɗa maka inda take"
Ya ce "To Baba"
Ya kalli Bilkisu ya ce "Bilkisu yaya kuna zaune lafiya dai ko"
Ta ce "Lafiya lau Baba"
Ya ce "Baki da wata matsala ko "
Ta ce "Ba komai "
Ya ce "Masha Allah mun gode Allah, kuje ku gaida Maman naku"
Suka tashi a tare suka yi kicin ɗin Suna zuwa Mama Sauda ta harare su duka ta ce "Wannan wani irin karuwanci ne, a gida na zaku na yin haka, wato ki nuna wa mutane ke cikekkiyar Karuwa ce yasa kika wani riƙe masa hannu kai kuma da yake wani hotiho ne ka biye mata, ay dama na faɗa lalata min ɗa zaki yi"
Ta fizge hannunta daga nasa zata koma Umar ya tare ta ya ce "Haba Mama nifa bana son kina faɗan haka, Bilkisu fa ƴarki ce ki daina faɗa mata wannan sunan kinsan ba daɗi"
Ta ce "Ƙarya ne ko ba da kwarko aka kama ta ba, ohhhh ka ta mantar da kai ko, saboda ta barbaɗe ka kasha kunu ko, kasha a shayi, kaci a abin ci ko, to ko har abada sunan nan bazai canja na"
Fashewa tayi da kuka ta koma falo shi kuma ya biyo ta Maman tana kiransa amma ko ya juyo.
Baba miƙewa yayi ganin tana kuka ya taro ta, ya kama hannun ta ya zaunar da ita kan kujera ya kalli Umar da yake tahowa ya ce "Menene kuma"
Umar ya ce "Ita da Mama ce "
Shiga yayi Umar kuma yazo yana bata haƙuri ta sigar lallashi.
Yana zuwa ya sami Mama Sauda ya ringa zazzaga mata faɗa amma tayi shiru ko a jikin ta, ya koma gun su ya samu Umar ɗin yana lallashin ta, ya ce "Ɗauki matarka ku tafi gida ka lallasheta"
Ya miƙe ita ma ta miƙe suka tafi Baba ma ya raka su har gurin mota yana bata haƙuri.
Har gida suka je tana kuka, shiko sai faman lallashi yake daga bisani ya kifata a jikin sa yana bubbuga bayanta, jin an kira Sallah Magrib yasa ta tsaida kukan ta ce "Ka tafi masallaci nima zanyi Sallah "
Ya ɗan karyar da wuya ya ce "Amma baza ki rufe min ƙofar ki ba"
Ta ce "Eh amma saidai idan kaje kada ka dawo, ka tsaya kaji wa'azi zuwa Isha idan anyi Sallah Isha ka dawo"
Ya ce "To amma kada nazo na samu kina wannan kukan kiyi haƙuri ".
Ta ce "Komai ya wuce ba damuwa"
Ya ce "Ina son ki nuna min ya wuce ɗin ta hanyar tanada min kanki"
Murmushi tayi haɗi da shigewa ciki don yin alola.
Shima fita yayi zuciyarsa cike da tunanin matarsa.
*** *** ***
"Gaskiya Abin da kake baya dacewa wannan ay bokanci ne"
Ya daka mata tsawa "Ke kin isa ki hana ni abin da nasa a gaba ne, wannan sana'an da kike kallo dashi nake samo muku tuwon da kuka raina, kuma tun kafin kizo gidan nan ake yin ta idan baza ki iya gani ba kiyi gaba"
Ummi ta ce "Ni gaskiya nake faɗa maka"
Ya ce "Hali ki kiyaye ni da irin wannan maganan banzan naki"
Ummi kenan da mijin da ta aura, da bincike dama ta aure shi matansa biyu ita ce ta uku, sai daga baya ta gane halisa, wato Ɗan bori ne, kuma boka, kullun daga safiya zuwa yamma mataye ne suke zuwa masa suna faɗan masa sirrinsu, yana basu magani ta hanya marar kyau, ko a wulaƙanta kishiya ko wani ɗan uwa, mazan ma ba'a barsu a baya Musamman ƙananan ƴan siyasa sai su fake da sunan a musu Addu'a. Wasu suna dacewa wasu kuwa saidai suyi ta ɓata kuɗin su.
Duk samun kuɗin da ake yi abinci ɗaya ake ci a gidansa Safe rana dare, wato tuwon masara da miyar kuka, daga su har yaran tuwon ya ishe su suna ci ne kawai da haƙuri, ga gidan ba tarbiyya yara basa ganin girman babban sai iyayen su, suma manyan basu kama girman su ba, haka zaka ji yaro ya kutuntumawa kishiyar uwarsa ashar kuma uwarsa baza ta ce komai ba haka uban ba.
Sassa Shida ne a gidan, Sassa na farko shine na asalin mai gidan wanda tun asali shine silar taɓarɓarewan gidan, yaran sa bakwai biyar maza biyu mata, matan sunyi auren su, mazan kuwa kowa yayi aure ya kama sassan sa, Zalimu shine babba shine kuma mijin su Ummi matansa uku, wanda shima bai kama girman sa ba, haka zai cire riga yayi dambe da matan ƙannen sa, saidai yaran gidan suna tsoron sa sosai. Sai na biyun su shine Sallau shi direban mota ne yana ɗaukan fasinja zuwa gari gari, akwaishi da aure-aure yanzu haka dai matans uku. Shima bai kama girman sa ba. Sai na ukun su, shima direban ne ne, shi da daman sa, matan sa biyu, sai kuma na huɗu hadi shiko matan sa ɗaya, sai ɗan autan su da baiyi auren ba, shima da sassansa sai dai akwai shi da lalata yaran mutane, har na gidan bai kyale ba, idan aka akayi magana maman ta ce ay yaran su suka kai kan su.
Ummi tayi nadaman auren wannan mutumi ga gida ba tarbiyya haka ƙaramin yaro zaiyi ta zaginta.
*** *** ***
Rayuwa me daɗi suke a gidan ta saba da shi shima ya saba da ita sosai, idan ya tafi gurin aiki Allah-Allah yake ya dawo ya kasance da Matarsa.
Satin Ruky biyu ba ita sukan sun man ta da wata aba wai Ruky sai dai lokaci-lokaci yakan tuna ta yakan ce ko ina ta shiga, saidai ya raya a ransa idan har ta dawo dole su ya raba musu kwana don bazai iya rayuwa ba Bilkisu da take sanyaya masa zuciya ba.
*** *** ***
Mama Amarya ne ta ɗaga waya ta kira Ruky tana ɗagawa ta kutuntumo mata ashar "Dan abu kazan ubanki kina ina ne"
Ta ce "Haba Mama ina tare da sabon kamu ne dai, kinga yadda yake sakar min kuɗi ne,"
Ta ce "To Boka ya ce asirinmu yana gab da karyewa dan haka kiyi sauri ki dawo kuma, ki dawo da kuɗi sosai dan za'a bawa boka"
Ta ce "To shikenan ina nan dawowa kada ki damu Mama Umar nawa ne ni ɗaya.
*** *** ***
Ya dawo a gajiye saidai yana ganin matar tasa yaji ba wata gajiya, wanka yayi yasa ƙananan kaya T-shirt da dango three quater yazo ya ci abinci bayan ya gama ta haɗa kayan ya bita ya taya ta suka wanke tare da sake gyara gidan, ko ina fes da ƙamshi, yana zaune a tsakiyar falo tazo ta kwanta tayi matashi da cinyarsa ya shafi fuskanta, suna a haka suna hira cikin nushaɗi Ruky ta shigo idon ta ya kai kansu tuni kayan hannun ta suka zube yayin da wayarta ta tarwatse, lokacin suka juyo duka suka ganta...
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/2, 7:45 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude