Showing 57001 words to 60000 words out of 62424 words

Chapter 20 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2854

yi. Mommy ne ta jamota jikinta ita ma Maryam tana ta gefenta.


Ana fita dashi saida maza suka gama wucewa Mommy taja Bilkisu suka je suka masa Sallah Maza suka ɗauke shi suka yi da shi gidan sa na gaskiya.


Koda suka dawo Bilkisu kan shiru ko an gaisheta bata amsawa Maryam da Mommy kan ita suka fi tausayawa, sun san su kansu basu ji raɗaɗin da take ji a zuciyar ta.


Azhar kuwa ƴan Bauchi suka iso harda Umar da Mama Sauda. Bayan sun gaisa sunci Abinci. Sai Mommy take faɗa musu halin da Bilkisu take ciki gashi ko abinci bata iya haɗiya Abubakar ya miƙe yayi ɗakin maryam da yake anan akace masa take ya buɗe ƙofar ya ganta ta jingina da gado idonta na kallon sama tana jin motsinsa ta ɗago ta kalleshi sai ta kawar da kanta gefe. Ya durƙusa ya kama hannunta ya ce "Kina da ilimi kina da hankali da tunani, ya kamata ace kin bar ma Allah komai kin rungume ƙaddara, mijinki lokacin sa ne yayi, munsani kina son sa shima yana sonki amma ki sani son da kuke yiwa junan ku bashi zai hana Allah ya barshi ba, ki rungumi ƙaddara kina yiwa mijinki Addu'a, dan yanzu abin da yake buƙata kenan a gurin ki, ke baki son ya dinga Alfahari da kene, nasan akwai raɗaɗi amma ba yadda zamuyi haka zamu rungumi ƙaddara mu masa Addu'a"


Wasu hawaye ne masu ɗumi suka fito mata yasa hannu ya share mata ya ce "Barin ce Maryam ta haɗa miki tea ko"


Ta girgiza kai alamun A'a


Zaiyi magana sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi ta ɗora kanta a jikinsa ta ci gaba da rera kukanta cikin kukan kuwa tana cewa "Allah ya jiƙan ka Ya Aliyu, nayi rashin miji na gari Allah yasa halinka na gari ya bika"

Hannu yasa a kanta yana jin kukan nata zuciyar sa tana masa wani iri.


Saida ta kusan yin awa tana kuka sannan ya fara rarrashinta yana bata haƙuri da kyar ta iya sayawa da kukan nata sannan ta janye jikinta ta koma kan kafet ta kwanta hawaye na ci gaba da zuba mata.


Tashi Yayi ya yi magana wa Maryam ta haɗo tea sannan ya kai mata, ya ɗagota yana bata a hankali tana sha, saidai ko rabi bata yi ba ta miƙe ta shiga bayi ta ringa amayo shi saida ta amar da shi tas ta dawo ta sa wani sabon kukan ta ce "Bana son cin komai Yaya ka kyale dan Allah baka san yadda nake ji ba"


Ya ajiye kofin tea ɗin yana mata nasiha saidai tana jinsa ne kawai amma bata ɗaukan komai.


Haka sukayi ta fama da ita bata cin komai ko taci ma sai ta amayar da shi, sai ran da akayi uku ne abincin ya fara zama a cikinta, ta rame sosai sai ɗan talin cikin da yake da girma, kasancewar ita ɗin mai Addu'a ce kuma ƴan uwanta suna mata yasa ta ɗan fara samun sauƙi a zuciyarta har take ɗan magana idan taji ana yi ko ansata a ciki.

Ranan ukun kuwa duka suka tafi dama su Abba tun a ranan suka koma, lokacin ne kuma jama'a suka watse sai masu zuwa gaisuwa. Mommy kuwa ita take yawan kwantar mata da hankali a kullun haka Maryam ma, yanzu kan hankalinta ya kwanta saidai tana tunanin sa kaɗan-kaɗan lokaci-lokaci Abubakar yana kiranta suna gaisawa ya kuma mata nasiha, haka Umminta ma.


Rayuwa kenan Yau Aliyu ya cika kwana arba'in an masa Addu'a sosai yau kuma Bilkisu ta tashi da naƙuda. Mommy ce ta kaita asibiti. Tasha wahala sosai amma duk wahalan da take bai hana ta yiwa mijinta Addu'a ba, taba cikin wahala amma bakin ta na motsi tana roƙa masa rahman ubangiji. Awanta 6 tana abu ɗaya sai kusan Magrib ta haifi ɗanta namiji. Suna gyara shi suka miƙo mata ayko tana ganin fuskarsa sai taga fuskar Aliyu a fuskar yaron hawaye ta ringa yi, Mommy ce ta shigo tana hamdala ko da taga tana kuka ta ce "Lafiya "


Ta miƙa mata shu ta ce "Mommy kalli fuskansa ki gani"


Mommy tana amsan sa ta ce "Wannan ay ba abin da ya bar Aliyu, lokacin da na haife shi inda kika san wannan "


Hawaye ta ci gaba da yi, Mommy ta dafa kafadar ta ta ce "Ki ci gaba da masa Addu'a kedai Allah ya baki ladan takabarki"




_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/11, 9:04 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 75-76







"Amin" ta ce ta ci gaba da share hawayen ta



Basu wani jima a asibitin ba aka sallame su suka dawo gida. Tuni gida ya cika da ƴan barka kowa ya ganshi sai ya ce wannan ay Aliyu ne ya dawo, dan kamannin su ɗaya da uban sa.


Kwana uku da haihuwan Umma da yaranta suka zo Mommy ta ce "Yawwa tunda ga iyayensa ma sai kuzo kuyi masa huɗuba, nace Daddyn ku yayi masa ya ce saidai ku kuzo kuyi"


Usman ya ce "Wannan Ay Babansa yayo kawai a saka masa sunan Babansa"


Umma ta ce "A'a uwarsa da taji wahalan haihuwan ita zata zaɓa masa suna ku sai kuyi masa huɗuba"


Bilkisu ta ce "Nima Aliyun nake so a saka masa"


Abubakar ne ya masa huɗuba da suna ALIYU bayan ya gama ya miƙa mata ya ce "Allah ya raya Aliyu"


Tayi murmushi ta ce "Haidar za'ana kiransa"



Ranan Suna kuwa sai ga Umar yazo da Akwatuna biyu ɗaya cike da kayan Haidar ɗayan kuma Kayan uwar haidar sai kuma na Yayar Haidar Wato Maisun da ya saka mata riguna masu tsada guda huɗu.


Ana kawo kayan aka buɗe ana sam barka da kayan ita ko Bilkisu ta ɗaure fuska Umma ta kalle ta ta ce "Menene wai".


Ta ce "Nikan gaskiya a mayar masa da kayan sa, ay ba'a ce masa tsirara zamu zauna ba"


Umma ta ce "Ba inda za'a mayar dole ki amsa tunda ya baki"


Ta ce "Na yadda na ƴarsa za'a amsa, amma nawa da na Haidar kan mayar masa zamuyi"


Umma ce tayi ta mata wani kallo da ta fahimci kallon da take mata ne ta ce "Umma kinsan waye Umar Wallahi wata rana zai iya mana gori, ni kuma yanzu bazan ɗau wulaƙancinsa gwara a mayar kawai"


Umma ta ce "Wai yarinyar nan yaushe kika fara rashin kunya ne"


Shiru Bilkisu tayi Umma kuma ta ringa mata faɗa ƙarshe kuma ta ce "Zai shigo nan ganin Haidar saura ki masa wani rashin kunyan kuma".


Shiru ta kuma yi bata ce komai. Can kuwa saiga Umar ya shigo Umma ce ta miƙa masa Haidar sannan ta miƙe ta fita, ya tsura wa yaron ido sai kuma ya kalle ta yayi murmushi ya ce "Kamar babansa ne yayi kaki"


Bata ce masa komai ba shima shirun yayi yana rungume da yaron can kuma ya fara mutsu-mutsu kamar zaiyi kuka ta matso ta ce "Ni bani ɗana zan bashi Nono"

Ya miƙa mata ya ce "To ay nima ɗana ne"


Baki ta turo masa ya ce "To kafin ki koreni barin tafi"

Ya miƙe zai fita kenan ta ce "Yawwa barin faɗa maka wani abu, ni da ɗana baza mu taɓa zama tsirara ba dan haka daga yau bana son ka sake aiko mana da wani abu naka bama so, kada kaga dan ubansa ya mutu kayi tunanin zamuyi maraici"


Dawowa yayi ya zauna ya ce "Banga laifinki ba dan kin faɗi haka saboda na cancanci haka daga gurinki, amma ki sani ko Aliyu yana raye zanyi wannan, balle yanzu da baya raye, kuma ay ina ganin shima Haidar ɗin ma ɗana ne"


Ta ce "Ba abin da ya haɗa ka da Haidar, kada ka sake haɗa kanka da shi"



Kuka Haidar ya fara yi Umar ya kalle shi ya ce "To ki bashi Nono mana"


Harara ta galla masa ta ce "To kuma a gabanka zan bashi Nonon ko Iskancin da kamin da ne shine zaka min yanzu"


Tuni ya fita bai sake magana ba. Ita kuma ta fara bashi Nonon.


Washe gari Abubakar da Umar suka tafi Usman kan tunda ya haɗu da Husaina ya ce sai Umma zata tafi su tafi tare.


Tunda yake da ƴan matan sa bai taɓa samun wacce ta kwanta masa ba irin Husaina, yarinyar akwai nutsuwa da kamun kai wannan yasa tunda yazo garin ya liƙe mata.


Saida suka sake kwana biyu da Umma sannan suma suka tafi suka bar mai jego da ɗanta da kuma kyautukan su.


Kula sosai Mommy take basu ita kanta Bilkisu har ƴar kiba ta fara yi Haidar kuwa zuwa kwana Arba'in yayi girma da shi ya fara gane uwarsa.



Watan Haidar uku aka fara Shirye-Shiryen bikin Abubakar da Maryam yanzu hankalinta ya kwanta sosai har ƙiba tayi ga Haidar ma da yayi girma abinsa sai wayo. Umar ne yanzu ke yawan damunta da waya yana ce mata yaushe zata dawo, ita ko banda wulaƙanci ba abin da take masa, duk da ita ɗin ma tana son ta dawo amma saboda tsana da take masa ta kwammace ta zauna, shi kuma marar zuciya yaƙi ya daina damun ta.


Yauma ta gaji da aiki sosai tazo ta kwanta Haidar yayi barci wayanta tayi ƙara ta duba taga number Usman ne murmushi tayi ta ɗaga, sai jin muryan Umar tayi, tsaki tayi ta ce "Wai kai wani irin marar zuciya ne Umar"


Ya ce "Ohh yanzu ba ko ɗan yayan ma tunda kika haihu kika canja "

Ta ce "Ay baka cancanci na kira ka yaya ba Yaya ada kenan"

Ya ce " Nima bana son Yayan gwara ma Umar ɗin ya fi min daɗi dan idan kika kira sai naji kinfi kowa iya kira"



Ta ce "Ni barci nake ji ka kyale ni in kwanta, Umar kana damu na da yawa me yasa baka da zuciya ne"


Murmushi yayi kamar tana gurin ya ce "Ina da zuciya amma bazan taɓa yin zuciya dake ba ƙanwata, ko kashe ni kika yi na dawo bazan taɓa zuciya da ke ba, duk abin da kika min kin isa kiyi ne ke ɗin ta daban ce a zuciyata, fatana ki amince ki dawo Bauchi ina ganin fuskar ki kullun koda zagina zaki nayi, balle kuma baki taɓa zagina ba"


Ta ce "Ayko idan baka kyale ni ba zan iya zaginka"

Ya ce "Wallahi ko Al-qur'ani zan iya dafawa baza ki iya zagina ba, wannan ba halin ki bane, kuma koda kin zage ni ba abin da zai canja"


Mtswwww tsaki taja yasan zata kashe yasa ya ce "Mu kwana lafiya Gimbiya "



Wayan ta jefar gefe tayi Addu'a ta shagawa yaran sannan ta kwanta.


Rana bata ƙarya saidai uwar ɗiya taji kunya, Yaudai aka ɗaura auren Abubakar Ibrahim da Maryam Yusuf, Bilkisu kan ta kasance kamar ita ce Amaryar Haidar ma Ummi ce ta riƙe shi, da yake ita ma tazo akan idan za'a kai Amarya sai su tafi can tare, ita ma taci kwalliyarta da yake dama can Yarinya ce yasa yarintar ta ta sake fitowa a fili, idan ka ganta zaka rantse da Allah ba ita ta haifi Bilkisu ba sai dai ace ita ce Uwar Haidar da yake ita take riƙonsa sai kuma akayi sa'a yaron bai ƙita ba, duk da yana ɗan taɓa ƙyiwar.




Bayan ɗaurin Auren walima aka yi aka yi wa'azi sosai akan zaman aure da kuma tarbiyyan yara.


Washe gari kuwa da Safe aka tafi kai Amarya su Umar su suka kawo motocin Maisun kuwa tana ganinsa ta liƙe masa Bilkisu ta kwashi kayansu da yawa saboda anyi hutun makaranta dan tana sa ran zata daɗe a can kafin ta dawo amma idan taga Umar ya takura mata dawowa zata yi ta kyale shi.


Umar kan yana ganin kayan da ya ɗauka yaji daɗi a ransa. Matsawa yayi ta gefen ta ya ce "Zo ga mota ko Gimbiyar "
Hararansa tayi tayi motar da Ummi ta shiga dan Haidar na hannunta, Maisun kuma ta zauna gun Uban ta.


Suna Isa ana kiran Sallah dan haka kowa ya fara shirin yin Sallah. Bayan anyi Sallah aka fara gaishe-gaishe, Ummi kan da kanta taje gaida Abba koda ya kalle ta, sai ya kalli Umma ya ce "Ina ga fa bayan wannan bikin za'ayi nawa bikin"


Ta ce "Biki kuma na me"


Ya ce "Aure zanyi mana"

Umma ta ɗaure fuska ta ce "Wani aure Alhaji kana nan tsofai-tsofai da kai gashi ka fara tara jikoki"


Ya kalli Ummi ya ce "Haba Aisha ina kallon wannan ƴar fulanin in barta, ay kawai ki yadda asha biki"


Ummi ta sunkuyar da kai tana murmushi ta ce "Kaji Alhaji sai kace wasu yara wai za'a sha biki"...


_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/12, 8:21 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 77-78





Umma ta ce "Ahh idan ay ita ce ko baka ce ba zan aura maka ita ni zan biya Sadakin ma"


Shirin zuwa Diner aka fara da yake Bilkisu a ɗakinta na da ta sauƙa tayi kwalliya sosai ta shirya tsaf tayi kyau matuƙa wani tsadadden leshi ta saka sannan ta ɗauki Haidar ta fara bashi nono tuni barci ya ɗauke shi, ɗakin Umma taje ta kwantar dashi a gefen Maisun sai jin Sallamar Umar tayi a ɗakin gaishe su yayi ita kuma ta fita ta koma ɗakinta, ko da ta fito binta yayi har ɗakin ya sameta a zaune a bakin gado shi kuma ya zauna a kujeran dake ɗakin ya ce "Da kika gudu ma na biyo ki"


Tsaki taja ta tashi zata fita ya riƙe hannunta ya ce "Ina zaki kuma"


Hararan sa tayi ta ce "In da ka aike ni dalla sake ni nikan"


Ya kuma damƙe hannun ya ce "Tunda kin shirya muje ga mota can mu tafi Diner ɗin ko"


Ta ce "Akwai wanda zai ɗauke ni"


Ya ce "Wa kike da shi bayan ni"

Ta ce "Masoya da yawa"



"Duk a bayana suke Wallahi basu kaini sonki ba"


Ta ce "Allah zan maka ihun kwarto, mema ya kawoka cikin ɗakina, sai in maka ihu ince kana son ka cire min kaya"


Ya ce "Wannan ba halin ki bane, da zaki hakan ma da ns gode miki kinga sai ayi na wancan karan"


Fizge hannunta taje yi suka fara kokawa ta samu hannun sa ta gantsara masa cizo har saida ta cire fatar da sauri ya sake hannun yana yarfar da hannu ta fito waje ya biyo ta ta samu ana ta tafiya motan Usman ta hango tana zuwa taga Husaina a gabab mota ta ce, "Malama yaushe kika zo ban sani ba"


Ta ce"Tare aka kawo amarya dani"


Ta ce "Shine ban sani ba"


Ta kalli Usman t ce "Shi ay ya sani"


Ta ce "Saura naku ay"


Sai ji tayi daga bayanta ance "Namu dai, ƙarya yake yana ƙanina ya riga mu aure"


Juyowa tayi ta ɗaga hannu kamar zata mare sai kuma ta sauƙe hannun ya ce "Ya kika fasa "


Juyawa ta kuma yi da niyyar shiga motar sai taga wayam sub tafi ta juya taga ba wata mota sai ta Umar tayi bakin titi yana kiran ta. Tana tsayawa a bakin mota wani ya tsaya ya zuge glass ɗin mota ya ce "Hajiya ina zaki je ne haka"


Ba wani tunani ta buɗe motar ta shiga dan dai kada Umar yazo ya same ta , sannan ta faɗa masa inda zata je yaja mota suka tafi Umar kuwa yabi motar sa kallo, ya ɗauko tasa motar yabi bayan su saida ya ƙara gudu sannan ya iso su suka isa gurin tare.


Ya kalleta ya ce "Zamu iya shiga duk da ba'a gayyace ni ba"



Ta ce "Zaka iya"



Ya fito suka shiga tare Umar ma yabi bayan su, duk wani abin da take yi harda gayya take yin sa kuma a wannan lokacin Umar ya shaƙa yaji haushin ta dan harda rawa ta fito tayi da wannan mutumin. Suna rawan ma yana son ya rike hannunta amma ya lura ita taƙi yadda Saida aka tashi kuwa Sun fita Umar yabi bayan su yaje yaja hannunta ya kaita jikin motarsa ya haɗa bayanta da motar ya ce "Bilkisu Ina son a maida auren dan Allah ki daina min wannan hukuncin yamin tsauri da yawa kinji yadda nake ji kuwa cikin zuciya ta da kikai rawa da wannan mutumin, Ada duk abin da kika min bana jin haushi amma yanzu kin samu abin da zaki tarwatsa min zuciya dashi, dan Allah kiyi haƙuri haka ki bani dama na sake auren ki zaki zama ƴar gata "



Ta ce "Bana son ka Umar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login