Showing 48001 words to 51000 words out of 62424 words

Chapter 17 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2857

baya suna shiga ya ganta a kan gado ta baje ta rufe rabin jikinta da bargo, wannan barcin da take ke ya nuna masa alamun bata samu na dare ba, gyara mata bargon yayi ya kalli Maisun ya ce "Idan ta tashi kice ina gaidata,"


Ta ce "To"


Sai ƙarfe 11:35am sannan ta tashi bayi ta faɗa tayi wanka ta fito wanka da towel a jikinta ta ɗauki waya taga kiran Aliyu ratata, da saƙonninsa sai buɗewa take tana karantawa tana murmushi, saida ta gama zata ajiye kenan sai ga kiran sa.



Ta ɗaga da Sallamarta a bakin ta, ya amsa sannan ya ce "Da fatan kin tashi lafiya uwar ƴaƴana"


Ta ce "Lafiya lau, "


Hiransu suka yi sannan ya kashe wayar.



Tana cikin shirin ta ne Maryam ta ce "Kina ganin yayanki saboda baki fito kin karya ba shima yaƙi ya karya ya tafi haka "


Ta ce "Da gaske bai karya ba"


Ta ce "Wallahi bai karya ba, ta faɗa mata yadda yayi.


Ya ce "Allah sarki, barin kira shi ya dawo gida ya karya gaskiya. "

Kira tayi yana ɗauka ta ce "Dama baka karya ba ka tafi, gaskiya banji daɗi ba, haka zaka na bar min cikinka da yunwa nikan gaskiya ka dawo gida yanzu"

Kwata-kwata ta manta da Maryam tana gurin sai zuba shagwaɓan ta take yi shi kuma yana biye mata, Maryam kan kallon ta take ta riƙe haɓa, har sai da ta kashe wayar sannan Bilkisu ta kalli Maryam ta ce "Wai dama baki tafi ba"


Ta ce "Taya za'ayi na tafi na tsaya ganin ikon Allah ne"


Ta ce "Kin tsaya gulma dai"



Soyayya ce mai tsabta suke zubawa, basu sanar da iyayen sun ba su suka gane da kansu, dan Aliyu baya jin kunyar faɗa mata abu a gaban su. Sunyi farin cikin hakan musamman Mommy tanajin daɗi idan tagansu tare, sun yanke hukuncin yi musu Aure ita da Alhaji Yusuf amma kuma ya ce a ji ta bakin su tukun saboda haka, Mommy ta kira su duka dama suna tare suka zo.



Alhaji Yusuf ya ce "Na fahimci wani abu game da ku, kamar kuna son junan ku, to na yanke shawara zan haɗa ku aure yaya kuka ce "


Aliyu ya ce "Eh Daddy hakan yayi "


Ya kalli Bilkisu ya ce "kefa Bilkisu me kika ce"



Ta ce "Duk abin da kuka yanke a kan mi daidai ne"


Ya ce "A'a ba wannan nake so naji ba, Zaɓin ki nake son ji, kina son sa ne koko kina da wanda kike so"


Sake Dukar da kanta tayi ƙasa yayin da Aliyu kuma ya zuba mata ido, ta ce "Bani da kowa sai shi"

Ya ce "Masha Allah ku tashi kije, sannan ki faɗawa Mommyn ku abubuwan da kike so a saya miki dan bana son auren ku ya wuce wata biyu.


Aliyu ya ce "Mun gode Daddy Allah ya saka da Alheri Allah ya ƙara girma ba arziki"

Ita kan bata ce komai na, saidai da zaran ka kalli fuskanta zaka san tana farin ciki sosai.





_*Mrs Aliyu ce*_




lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/8, 7:11 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 63-64




Shirye-Shirye ake tayi ba kama hannun yaro, Bilkisu kuwa tuni Mommy ta fara gyara ta saboda jin da tayi Daddy ya ce bazai wuce wata biyu ba. Haka kuma tasa Aliyu ya Mata lefe na gani na faɗa



Alhaji Yusuf ya ce wa Mommy "Kada muyi aiki ba dai-dai ba fa, ya kamata mu sanar da iyayen yarinyar nan kada muyi son kan mu".



Ta ce "Ka kyale su kawai ita kanta Bilkisu bata son ma susan tana tare da ni dani, dan haka ka kyale su, nadai faɗa wa Umman su Abubakar ta ce zata zo bikin."


Ya ce "To shikenan "





*** *** ***



Ganin yana sonta kuma yana jin maganan ta yasa ko da yaushe take masa wa'azi akan abin da yake ba kyau, gashi dai bata da wani ilimi, amma ɗan abin da ta sani da shi take amfani wajen jan hankalin sa.


Harda jahilci ke damun Zalimu, ɗan abin da take faɗa masa yasa ya fara ɗan ragewa, amma kuma ya ce mata bazai iya bari duka ba, saboda dashi yake samu yake ciyar da ƴaƴansa da matansa, ya kwashi yaransa duka ya sasu a makaranta muhammadiyya da ta zamani dan ya ce baya son yaran sa su tashi da jahilci kamar sa.


Idan yana da kuɗi a jikin sa, duk matar da tazo karanta yake ya ce ya daina, amma kuma da zaran yaji baida ko sisi da kansa ke neman matan dan ya musu sihiri su biya shi.


Yanin haka yasa Ummi ta same shi, ta ce "Ka ce kanason ka bari sai dai rashin abin da zaka bamu yasa kake yi, to ga wata yarjejeniya, zanje ƙauye, zan kama shanuna guda biyu na saida zan baka kuɗin kaja jari kayi wata sana'ar, saidai baza ka sake yin bokanci ba ka yadda"



Ya ce "Na yadda wallahi, kuma zan na ajiye ribar har na biya ki duka kuɗin ki"


Girgiza kai tayi ta ce "Idan na baka bana buƙatar ka biya ni kyuta na baka nidai buƙata ta ka daina wannan aikin"


Ya ce "Wallahi na daina, kai daga yau ma na daina Wallahi "




*** ***




Ana saura kwana uku Ɗaurin aure Umma ta sauƙa a Kaduna, Murna gurin Bilkisu ba'a magana Koda suka gaisa da Mommy ta ce "Me kika ce a Alhajinki ya barki kika taho"

Ta ce "Ce masa nayi zanje Biki Kaduna amma baisan bikin waye ba, har ya ce idan nazo na nemi gidan ki in faɗa miki ɓatan takwaranki"



Ta ce "Ayko zanje na same shi na masa jaje Bilkisu kan ta dawo nan sai sun gama shan wahala tukunna ba wulaƙanta suka yi ba"



Umma ta ce "Ayi haƙuri dai Adda a barsu haka ay sun ƙwalu, har yanzu Umar ma tunda ya tafi bai dawo ba, Sauda ko tana ta Bibiyar Jafar akan ya dawo da ita yaƙi"



Bilkisu ta ce "Umma ina labarin su Yayana"


Ta ce "Sunanan suma sun dawo, yayyenki sun zama lauyoyi duka"



Ta ce "Gaskiya Umma ki faɗa musu yanzu yayyen nawa zan yi aure ba wanda ya sani ay ya kamata ko Albarka ne su saka min"


Ta ce "Kada ki damu na komai ay, kuma ko yaushe ina kwantar musu da hankali. Ni Umar ma nake tausayawa, ko ina ya shiga, ko yana mace ko yana raye"


Bilkisu ta ce "Ohonsa can ta matse masa, ina ruwana da shi ya mutu mana"


Dariya suka mata Mommy ta ce "Ay da yana nan shine waliyyinki"


Ta ce "Allah ya sauwaƙa ba gwara ince Ya Aliyun ya ɗauke ni mu gudu wani gari muyi auren ba, daga baya ma dawo "



Dariya suka mata duka.



Rana bata ƙarya saidai uwar ɗiya taji kinya, yau ne aka ɗaura auren Aliyu Yusuf da Bilkisu Ibrahim, kowa cikin Murna yake ɗaurin auren ya tara mutane da yawa.



Alhaji Yusuf da kansa yaje zango ya samo Saniya mai kyau dan a yanka ta koda zai tafi ya ce "Su tura masa da mai fiɗa, Umar ne yaje ya feɗe masa saniyar ganin Umar bai masa ha'incin komaiba ya yi saboda Allah yasa yasa Alhaji ya masa biya mai tsoka sannan ya bashi kai da ƙafafuwan Saniyar, sannan ya ce "Yana gayyatarsa ɗaurin auren yaran sa"


Ranan ɗaurin auren kuwa Umar da Sale sunzo ko da yaji an kira sunan Bilkisu a gurin gaban sa ke faɗuwa, da kyar ya iya cin Abincin ya kalli Sale ya ce "Sale zo mubar gidan nan kaje"


Ya ce "Buje muyi Sallama da Alhajin "

Umar ya ce "Jeka kawai ina jiranka "


Maisun ce tazo ta gabansu Umar ya ganta yaji yayi zuciyarsa ta buga da ƙarfi har saida ta kama gurin ya kama hannunta ya ce "Yarinyar ina zakije cikin wannan jama'a haka "


Cikin tsamin bakinta ta ce " Daddyna nake nema yace yanzu yana zuwa yaƙi zuwa shine na fito neman sa"



Yace "To keɗin a wani gida kike"


Ta nuna gidan ya ce "To ki koma gida zan turo miki Daddyn naki ko, kije ki zauna kusa da Mommyn ki yana zuwa yanzu"


Ta tafi shiko yana kallon ta, ji yayi wani son yarinyar ya shige shi, yanzu yasan idan nashi ɗan yana raye yasa zaikai wannan yarinyar a girma, kai shidai a rayuwansa yana son ƴaƴa mata, Allah yasa shima tasa macen ne, Can kuma ya ce cikin ran sa To idan ma macen ne yanzu ina suke"


Hawaye ne yayi ta zuba masa Sale ya ce "Ka tuna Bilkisu ko, mu tafi kawai yanzu kada ka tara mana jama'a aganka babba da kai kana kuka kuma farin ciki ya kawo kowa nan gurin"


Aliyu ya ce baya buƙatan wani Program dan haka walima kawai ya haɗa musu ita da ƙawayenta.


Da daddare aka zo ɗaukan Amarya ba zanjen yin Kuka ko damuwa zata bar gida, Maryam ta ce "Ko kuka babu"


Ta ce "Wani kuka kuma ina so yana sona"

Nasiha kan tasha shi gun ƴan uwa da abokan arziki.



Maryam da wata ƙawar Bilkisu da suka haɗu a makaranta ta sunan ta Husaina, su suka mata rakiyya.


Nasiha aka kuma mata kowa zai tafi ta ce "Maryam da Husaina amma anan zasu kwana"



Maryam ta ce "Gidan masoyin naki tafiya zamuyi"


Husaina ta ce "Ba ke kika ce, kina so yana so ba, to gaku mun barku ku biyunku"


Idonta ya cicciko da ƙwalla ta ce "Dan Allah mu kwana nikan"


Maryam ta ce "Nabar Maisun mawa kema kinsan bani ba ke kuka zata sa, ga ba ubanta, dama yau sai neman sa take yi"



Tana gani suka tafi ta fara kuka su kuwa Dariya sukayi ta mata Da Maryam taga da gaske ta ke taje ta ce "To a ina zamu kwana"


Ta ce "Anan mana"


Ta ce "To Ya Aliyun fa"



Ta ce "Sai yaje ɗakinsa ma na"


Hasaina ta ce "Baki da hankali kenan mu kinga tafiyar mu, ayi auren yau mu kuma mu ɗale masa gado"


Tana ji tana kallon suka tafi, ba jimawa ta ji muryansa da abokan ango a falo yana cewa "Wallahi ba wanda zai shigar min ɗakin mata, wannan ay iskanci ne, a leƙa min ɗakin mata"



Dariya suka yi ɗaya ya ce "To muje ka raka mu muma"


Ya ce "Saidai inje na kulle ƙofar gida"


Binsu yayi a baya yaje ya kulle gidan sannan ya dawo kai tsaye ya shiga ɗakinta da ledodi guda biyu a hannun sa, ganinta yayi a tsakiyar gado tana kuka, ya ajiye ledan ya hau gadon ya ce "Wai wannan kukan na amare ibada ne, nifa bana so, kinga kin ɓata min kwalliyar yanzu dole sai kin sake min wani, dan ni ina son kwalliya"



Ta ɗago ta ce "Maryam da Husaina ce fa nace su kwana amma suka ƙi"


Ya kalle ta, tabbas har yanzu akwai yarinta akan ta dan haka ya ce "To banda abinki gani wani Maryam da Husaina zaki nema"


Rarrashinta ya ringa yi saida tayi shiru ya ce "To je kiyi alola mu nuna wa ubangijinmu godiya ko Babyna"



Ta mike ta shiga bayi ta ɗauro Alola shima yayi tasa, suka gabayar da Sallah raka'a biyu, sannan ya jima yana musu Addu'a tana amsawa da Ameen saida ya gama ya tambayeta fannin Addinita tana bashi amsa sai yaga ashe da iliminta.


Kicin ya shiga ya ɗauko plate ya saka musu kaza kai ya ringa bata a baki tana ci saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya tsiyaya mata lemo tasha, shima kuma yaci nashi sannan yace "Muje mu kwanta ko"


Ta ce "Barin watsa ruwa, ta shiga bayi, ta fito ta samu baya nan dan haka tayi shirin ta, tare da yin ɓarin turaruka a jikin ta, dan tasan yau Yayan nata zai yaye mata kunya.


Kwanciya tayi lokacin shima ya shigo da kayan barcin sa ya kwanta ya rungumota ya ce "Wannan ƙamshi haka"

Murmushi tayi shigo Yayan nata daga nan ya ringa canja salonsa.



Asuba ta gari Amarya da Ango...







_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/8, 12:58 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 65-66




Washe gari da safe Maryam ce ta kawo musu breakfast ko zama bata yi ba ta koma. Shi da kansa yake bata a baki har sai ta ƙoshi.



Cikin kwana biyu Bilkisu ta koma Bilkisun da, dan shagwaɓa ce ta ƙaru a kan na dan kuwa kullun shawaɓan ƙaruwa yake yi, shi kuma ƙara biye mata yake.

Satinsu biyu Aka kawo Maisun da kayan ta dan ya ce zai sata a makaranta, Islamiyya ya fara saka ta saida tayi wata biyu kuma ya sata a boko, a lokacin ne kuma Bilkisu ta fahimci tana da shigar ciki, dan taji alamomi kuma bataga Al'adanta ba.


Bata yi wata-wata ba ta faɗawa Aliyu ayko murna kamar yasa ruwa a ƙasa yasha. Nan kuma ya kuma ji da ita kamar zai maida ta ciki. A haka taci gaba da karatunta dan tana son ta zama likita ne.




*** *** ***




Tuni Zalimu ya fara Sana'an gwanjo kasuwanni yake bi kuma Alhamdulillah Allah yasa wa abin Albarka, Yana ganin Mutumcin Ummi sosai, idan ya dawo daga kasuwa a ɓoye yake kawo wa Ummi har ɗaki ba tare da sauran matan sun sani ba, Ummi kuwa a rashin sani takan amsa ta masa godiya, tunda ta fahimci hakan sai taƙi yadda ta ce "Yana kawo musu duka dan duk ɗaya suke a gurin sa, "


Maganar tuwo kuwa yanzu babu shi sai lokaci kaɗan-kaɗan idan an ji sha'awan tuwon, duk ƴan gidan sai aka zo ana ganin Mutuncin Ummi sosai, kuma duk abin da ta hana yana hanuwa, duk abin da ta buƙata nan da nan zaka ga ana rige-rigen bata, sirkar tasu ma tana girmama Ummi duk abin da zata yi saidai tayi wa matan gidan amma tana taɓa Ummi tuni ƴaƴanta zasuyi cahhh akanta. Ummi ta zama ƴar gata gidan yanzu tunanin ta ɗaya shine Bilkisu Lalle tayi babban kuskure bata neman Addanta ko rabon ta da ita tun auren Bilkisu lalle yakamata ta nemi ƴar uwarta, maganan Bilkisu kuwa tabar komai a hannun Allah tunda anyi nema har an gaji ko tana raye ko tana mace oho. Amma abin da ta sani yanzu shine dole taje ta duba ƴar uwarta a Kaduna duk da bata san guri ba, zata nemi numberta suna waya.



Koda ta tambayi mijin ya ce "To ba damuwa zai binciko mata number a gun Umman su Abubakar dan anan kawai suka san zata samu, da kansa yaje ya amso number yana dawowa tasa a wayarta ta kira Ringin uku tayi Addan nata ta ɗauka da Sallamartar ta bayan sun gaisa Ummi ta ce "Addana"


Ta ce "Halima ashe zaki neme ni"


Nanfa Ummi ta fara mata kuka a cikin waya, nan fa Addan ta fara rarrashinta kamar suna kusa, abin ka da ƴan uwa tuni Ummi taji zuciyar ta tayi sanyi ta fara bata labarin abinda ke faruwa nan fa Addan nata ta fara faɗa tana cewa yanzu wannan abin ya faru amma Halima ki kasa faɗa min, auren ki ya mutu harda sabon aure, wa kike da shi wanda ya wuce ni"


Ummi ta ce "Kiyi haƙuri Adda zan zo in sake naki haƙuri "


Ta ce "Yanzu ina labarin Bilkisun"

"Har yanzu dai ba labarinta"


Daga ƙarshe dai Addan nata tayi ta rarrashinta.




Zalimu kan yayi mata shiri kaf harda su tsaraba harsaida Ummi ta ce ya isa haka.



Ta shirya kayanta tsab dan gobe ana Sallah asuba zata shiga mota ta tafi, sai jin mummunan Al'amari sukai, Zalimu ne yayi hatsari a hanyar dawowan sa daga kasuwa da suka je cin kasuwa, duk cikin motar shi ɗaya ne yayi rai, saidai shi ɗin ma yana nan ya jigata sosai ya samu karaya a ƙafa, haka hannunsa ma na hagu.


Haka aka kawo shi gida, a lokacin aka masa ɗaurin gida.


Washe gari Zalimu ya ce "Ki faɗawa ɗaya daga cikin ƙannena su kaiki tasha tunda kinga abin da Allah ya aiko min"


Ta girgiza kai ta ce "A'a na fasa zuwa, baka da lafiyan kuma sai na bika, kaima kasa hakan bazai yuyu ba ay"


Ya ce "Ba komai kije kawai"

Ta ce "Ay bazan iya zuwa ko ina ba gwara na zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login