Showing 12001 words to 15000 words out of 62424 words

Chapter 5 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2847

take ji yasa bata tamka mata ba, tayi ɗakin Ummi nan ma komai ya canja sai ji tayi Talatuwa ta ɗuro mata ashar haɗi da cewa "Fita min a ɗakina"


Ummi ce da Khadiyo suka fito Ummi ta kama hannunta suka yi ɗakin da Mama Suwaiba ta zauna ta ce, "Yanzu nan ne ɗakin mu dukan mu, "


Bilkisu ta ce "Amma Ummi... "


Ta ce "Muyi haƙuri bana son wani magana Adda"

Shiru tayi ta cire kayan ta tayi wanka sannan ta shiga kicin ba alaman Abinci ta fito ta dawo ta ce "Ummi yau ba abinci ne a gidan"


Ummi ta ce tana kallon Khadiyo "Akwai mana, da kika ci ina kika kai sauran"


Ta ce "Ay nima naje na duba ba komai a kulan, shine naje ɗakin su Yaya na haɗa Tea na sha"


Ummi ta ce "Shine baki min magana na dafa muku wani ba yaushe tea zai ɗauke ku"


Bilkisu ta ce "Barin dafa mana Indomei sai muyi Abincin saboda idan su Yaya sun dawo su samu"


Ummi ta ce "Abin zai bani Mamaki fa Abincin fa da yawa, mije kicin ɗin in gani"


Suka je kicin ɗin ba komai a kulan dan haka Bilkisu ta dafa musu Indomie ta ajiye a tsakiyan Falo tayi ɗaki dan ta kira Khadiyo su ci tare, suna dawowa tare da Khadiyo suka ga Ruky tasa plate ɗin a gama tana ci.


Bilkisu tazo da sauri ta ɗaga plate ɗin ta ce "Me haka kuma"

Ruky ta kamo plate ɗin Abincin ya zube a ƙasa, haushin haka yasa Ruky ta mari Bilkisu nan aka fara kokawa, Ruky ba Karfi gare ta ba ita ko Bilkisu tasan dabarun kokawa tunda har yanzu yi suke da yayyanta haka ta kaita ƙasa, Ruky kuwa ganin zata cutu yasa ta gantsarwa Bilkisu cizo a damtsen ta, da sauri Bilkisu ta kama gurin ta ce "Kika cije ni"


Tayi kanta Ruky kuwa tayi ɗakin Talatuwa da gudu, Khadiyo ta share gurin Karshe itama Bilkisun zuwa tayi ta haɗa tea a ɗakin su Abubakar saboda duk kayan tea ɗin kicin ɗin babu.


Alhaji yana dawo wa gidan Talatuwa ta fara kuka tana faɗan karya da gaskiya karshe ta ce "Bazan zauna ba gidan mu zan tafi"


Alhaji ya kwala wa Bilkisu kira ta fito, ya ɗauki wayan USB ya ringa zane ta dashi tana kuka Ummi ta fito ta zanye ta, ta ce "Haka ake yi baza ka tambayi ba'a si ba sai ka hau dukan ta"


Finciko Bilkisun yayi ya kuma sake zane ta Ummi ta sake rungumeta ta ce "Ina ji Ina gani baza ka kashe min ƴa ba, saidai ka kashe mu tare"


Wannan kalma da Ummi ta faɗa yafi komai adaɗi a zuciyar Bilkisu, ji tayi bata jin zafin dukan kuma, sai ta juyo ta ƙara rungume mahaifiyarta tana jin ƙaunarta a ranta, cikin ranta kuwa tana tambayar kanta, dama Ummin ta tana son ta.


Alhaji ne ya fara magana da kakkausar Murya, Ruky yayar kice, ta girme ki nesa ba kusa ba, dan haka daga yau kada na ƙara jin wani raini ya shiga tsakanin ku da ita, sannan kuma duk abin da ta saku kuyi shi cikin hanzari" ya Nuna Talatuwa ya ce "Wannan kuma ni na kawo ta gidan nan, uwarku ce, kada na ƙara jin wani ya ƙira sunan ta, daga yau MAMA AMARYA zakuna ce mata, saura Su Abubakar ɗinma zasu dawo su same ni ina dai dai da su"


Bilkisu zata yi magana Ummi ta toshe mata baki da hannunta, Alhaji ya ce "Kyale ta tayi wani magana in karya ta"

Khadiyo kan kukan da take yi kaɗan-kaɗan ne ya kufce mata ta durƙushe a gurin ta ringa ihu kamar wanda aka aiko mata da saƙon mutuwa.


Su Abubakar Suka shigo suka yi kanta suna tambaya, Alhaji ya ce "To ku tsaya kuji"
Suma ya gindaya musu sharuɗan da ya gindaya wa su Bilkisu basu ce komai ba sai ɗaure fuska da suka yi tayi.

Ummi kan jansu tayi duka suka yi ɗakin da Mama Suwaiba ta zauna wanda shine ɗakin su a yanzu.


Abubakar da ya zauna bakin gado ya girgiza kai ya ce "Gaskiya bazai yuyu ba, haka zamu zauna muna kallo, ana ci mata mutunci"


Usman kuwa kallon hannayen Bilkisu yayi ya kama hannunta ɗaya ya ce "Me wannan"


Ɗora kanta tayi akan kafaɗan sa ta fashe da wani sabon kukan cikin kuka ta faɗa masa irin dukan da Abban ya mata.


Abubakar ya matso suka ringa lallashi.


Ummi ce ta ringa lallashin su tana musu nasiha tare da basu haƙuri, sannan ta ce suyi haƙuri su bi Umurnin mahaifinsu.



Sun ɗauki nasihan ta, suma tea suka sha, sannan Ummi da su Bilkisu suka shiga kicin suka haɗa abincin me ɗan sauƙi, suka shiga da nasu cikin ɗaki na su kuma suka bar musu a kicin.


Haka suka ci gaba da zama a gidan suna haƙuri Ummi kuwa kullun tana cikin basu haƙuri da yin Nasiha, lokaci-lokaci sukan ziyartar Umma ita ma nasiha da da basu haƙuri take.


Ummi da Su Bilkisu kullun su suke aikin gidan ita ko gimbiya da ƴarta ba abin da suka ita saidai su ci su koshi su ɓata gurin.


Bilkisu tana zaune ɗakin Ummi Ruky ta shigo da under weres dinta ta watso su sai fuskar Ummi bata damu ba ta ce " gashi ki wanke min yanzun nan"


Bilkisu ta kwasa tayi ɗakin Mama Amarya (Talatuwa) daidai lokacin Ruky ta shiga ɗakin ta watsawa Mama Amarya a Fuska ta ce "Ay uwa bata fi uwa ba"




_*Mrs Aliyu ce*_




lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_



*Sannunku da ƙoƙarin comment*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 19&20




Cafko mata wuya Ruky tayi ta ce "Lalle baki da kunya yarinyar nan, a Maman nawa"


Buge hannun ta tayi ya ce "Ohhh Maman ki ne Uwa ko, ni Ummi na ba Uwa bace, duk gadaran ku sai dai kuyi amma Wallahi ƙarya kuke ku wulaƙanta min uwa in kyale daga ke har Maman naki, Maman kin banza"


Zata juya ta jiyo Mama Amarya ta fizgo ta ta fara duka har da hawa kan ruwan cikin ta, Ummi ne ta fito da taga haka taje gaban ta ta ce "Kiyi haƙuri dan Allah kinga yarinya ce, zan mata faɗa baza ta ƙara ba"


Zaro wa Ummi ido tayi saida hantan cikin Ummi ya kaɗa saboda muni da take dashi, ga kuma jajayen ido yasa a duk lokacin da kuka haɗa ido sai ka tsorata, amma duk da haka Ummi tayi ta maza ta ce "Kiyi haƙurin dai baza ta kuma ba"


Ta ce "Ta ma kuma dan Ubanta"

Ta ɗaga ta Bilkisu tana numfashi da kyar saida taje bakin ƙofar fita ta ce "ba ubana ba"

Ta ruga da gudu sai ɗakin yayyenta ta rufo ƙofa kenan ta hangi mutum kan gado zata hau gadon kenan sai gani Umar tayi da sauri ta sauƙa ta fito da gudu tayi bakin falon tana leƙawa taga ko suna nan, sai ji tayi Alhaji ya ce "Ke kuma fa laɓewan me kike"


Sai ji tayi Mama Amarya daga ciki ta ce "Yauwa tunda Allah ya dawo da kai, dakai zanyi a gidan nan tunda ta zage ni"

Ita kan Ummi ɗaki ta koma, sannan ta ce wa Khadiyo kada ta fita.


Alhaji kuwa shiga yayi ya ce "Me aka yi kuma? "

Ta ce "Wai ni Bilkisu zata zaga har tana cewa ba'a san ubana ba"


Bilkisu ta shigo ta ce "Wallahi Abba ba... "

Ganin ya ɗauki abin duka yasa ta kwasa da gudu ta koma ɗakin ta rufo ƙofa Umar ya daka mata tsawa ya ce "Wai me kike shigowa yi ne"


Ta ce "Dan Allah kayi haƙuri Wallahi Abba zai dake ni ne, kuma idan ya kama ni sai yayi kusan kashe ni"


Ya finciko ta yayi waje da ita ta ƙara komawa, wannan karon bayi ta shiga ta rufe kanta a ciki yayi yayi ta buɗe taƙi, sai ya ce "To ko zan kira shi in nuna masa inda kike"


Kuka ta fara tana cewa "Dan Allah ya Umar kayi haƙuri Wallahi idan ya kamani sai ya kusan kashe ni"


Da yaga baza ta buɗe ba sai kawai yafito ya ga Alhaji da bulala a hannun sa ya ce "Abba lafiya "

Ya ce "Ina Bilkisu? "

Ya ce "Abba me tayi ne"


Ya ce "Zagin Talatuwa take yi bata da mutunci yarinyar nan"


Ya ce "Tana nan a cikin bayi"


Alhaji ya shiga, ita kuwa jin shiru yasa ta buɗe ta je ta zauna a bakin gadon, Alhajin yana shigowa kafin ta ankara har ya kamata ya ringa dukan ta ba, tun tana ihu har ta kasa yi, Umar daga waje ya ringa jiyo kukan ta har ya fara tausaya mata ya shiga ɗakin, ita kuwa tana ganin sa, dama neman me ceto take da sauri tayi bayansa ta cukwikuye shi, shiko ya durƙusa ƙasa yana cewa "Abba dan Allah kayi haƙuri baza ta ƙara ba, ta tuba"


Ganin haka yafita daga ɗakin. Ya shiga ciki "

Tausayinta ya kama Umar ganin yadda jikinta yayi raɗa-raɗa wasu gurin ma saida jini ya fito abin ka da farar fata ya ce "Me yasa kika zage ta"

Cikin sheshsheƙar kuka ta ce "Wallahi ban zage ta ba"


Ya ce "To me kika yi"


Cikin kuka ta faɗa masa komai, Tausayin ta ya kama shi, ya kama hannunta ya miƙar da ita suka fito suka yi falo ya samu ba kowa ya zauna ya ce "Ki kira min Ummi "


Ta shiga tana ɗingisawa ta kira ta ta fito, saida ya gaishe ta ya ce "Ummi A ɗan gasa mata jiki zan siyo mata magani, kuma ki daina bari yana mata wannan duka yayi yawa "


Ta ce "Adda bata jin magana Wallahi gashi ta jawa kanta ay"

Ya ce "komai tayi bai kamata ayi mata wannan dukan ba"


Shiru tayi ta je ta haɗa ruwan zafi shi kuma ya fita, suka je bayi Ummi tana mata Faɗa tana kasa mata jiki da nasiha, daga baya ta ce Tayi wanka.

Daidai lokacin da tasa kaya Umar ya dawo ya bata magungunan sannan shima ya mata nasiha da mata faɗa akan tana yin haƙuri ( Nikan nace Ohhh su Umar harda su Nasiha)


Mamaki fal cikin ranta, kuma taji daɗi sosai.

Koda Su Abubakar suka shigo bata faɗa musu ba, ita dai tasa a ranta zata na yin haƙuri da su baza ta ƙara tamka musu ba duk abin da zasu mata kuwa.



***

Umar kuwa yana komawa gida ya Samu Mama Sauda ya faɗa mata komai, dama tasan da sakin Umma amma bata san me yasa aka sake ta ba, yanzu a labarin da Umar ya bata t gano Talatuwa sheɗaniya ce, Hatsabibiya ce na ƙarshe dan haka dole ta haɗa kai da Ita. Saidai ta nuna wa ɗan nata ta tausaya wa Bilkisu sosai, saidai a ranta ta tsani Bilkisu musamman yadda ƴan gidan gaba ɗaya suka ɗora mata so.



Sun zama bayi a gidan, su suke aikin komai, Ummi har cikin ɗakin Mama Amarya take shiga ta gyara mata ɗaki sannan ta tambayeta ko akwai abin da take so, girki haka zasuyi su zauna su ci, aikin Mama Amarya shine ta kwana da Alhaji a ɗaki, ita kuma Ruky kullun cin kwalliya tasa ƙananan kaya ta fita gun samarinta, duk Bilkisu ta rame ta zama wata iri, tsakaninta da Alhaji sai harara, gwara ma Khadiyo yakan amsa mata a lokacin da ta masa magana.


Mama Sauda kuwa an samu abin da ake so dan ta samu shiga gun Mama Amarya tare suke kulle kullen su.


Tunda Ruky ta ga Umar taji a duniyarta ba namijin ta kasance da shi irin Umar amma shi ba ta tata yake ba ma, dan yana kallon irin shigar ta bata burge shi kwata-kwata.


Basu da wani aiki a gidan sai Addu'a Allah ya juyo musu da kan Alhajin su, Ko yaushe Ummi tasa goshi a ƙasa saidai kayi ta jin ajiyar zuciya alamun kuka da take yiwa ubangijin ta.



Ruky kuwa da taga ta na cusa gun Umar amma yaƙi kula ta sai taje ta yiwa Mamanta magana, ta faɗa mata komai.


Mama Amarya ta ɓata rai ta ce "Shine tuntuni baki faɗa min ba, Umar ɗin banza, da tuni kun daidaita, yanzun ma barin kira uwar sa a waya In ji"


Ta ɗauki waya ta danna number Mama Sauda bugu biyu ta ɗauka bayan sun gaisa ta ce "Kin san menene kuwa, Kamar ɗana da ƴarki sun daidaita kansu"


Mama Sauda ta ce "Ban gane ba"


Mama Amarya ta ce "Ina ganin da Umar da Ruky sun daidaita me zai hana mu haɗa su Aure"


Mama Sauda tayi jim kaɗan, ko kaɗan baza ta so Umar ya kasance da Ruky ba, Yarinyar da bata da kamun kai, yarinyar da uwarta take jigata tabi Maza har ita ce za'a ce sun daidaita kai baza ta saɓu ba.


Jin shirun yasa Mama Amarya ta ce "Ya naji kinyi shiru ko baki aminta bane"

Ta ce "Ba haka bane Gani nayi Bansan zancen ba, kuma shi Umar ɗin bai faɗa min ba".


Murmushi tayi ta ce "Ay bazai faɗa ba, kinsan su da kunya"

Mama Sauda ta ce "Idan nazo za muyi magana"


A hankali Hankalin Alhaji ya fara komawa kan iyalen sa dan yanzu yakan kira Bilkisu ya zaunar da ita suna hira, saidai ta kasa sakin jikin ta dashi.


Yau ta dawo daga makaranta da ƙafa ta gaji ga rana ga yunwa ta shigo gidan da Sallama ta samu Alhaji yana ganin ta ya ce "Adda na tura a ɗauko ki a makaranta ance ba'a ganki na ina kika shiga"


Ta ce "Na taho da ƙafa na ne, saboda Mama Amarya tace da driver din ya daina zuwa, kuma Abba ban san zaka tura ba, da na jira dan nima na gaji da zuwa da dawowa a ƙafa"


Mama Amarya tayi karaf ta ce "Ay ina da dalilin da yasa nace hakan, Yarinyar da ba karatun take ba, ta ƙware a zuwa ɗakin samari, kagan ta nan ba ɗakin ɗan iskan da bata sani ba, "


Ya ce "Adda dama ba karatun kike ba"


Ta ce "Wallahi Abba karatu nake zuwa" ta karashe maganan da fashewa da kuka.


Ya ce "Wa ya faɗa miki hakan ke Talatuwa "


Ta ce "Da idona nake ganin ta, nima nayi shiru ne kada ace na mata sharri dan ba ƴata ba"

Bilkisu ta kuma fashewa da kuka zata yi Magana Ummi ta jawota, ta rungumeta ta ce "Ƴata bata bin maza, nasan halinta nasan wacece ita, dan haka kada ki ƙara jifan ta da mummunan furuci idan ba haka ba... "


Ta nuna ta da yatsa sannan ta yarfar da hannunta.


Mama Amarya ta ɗaga murya ta ce "Ƙarya na mata kenan" nan tayi kanta a lokacin Zuciyar Ummi ta ƙeƙashe, kanta yayi tsauri, komai zata iya yi wa Mama Amarya Zuciyanta na ingizata ta ɗauki makami dan abin nata ya wuce gona da iri, kafin ta ƙaraso Ummi tayi kicin ta ɗauko Wuƙa ta fito tayi kan Mama Amarya da shi gadan-gadan Alhaji ya riƙe ta yayin da Mama Amarya tayi ɗakinta da gudu, Ummi ta fizge a hannun Alhaji ta bita har ɗakin, zuciyarta na ingiza mata yau sai ta ji mata rauni. Shiga tayi ɗakin ta sameta Allah ya ba Alhaji Sa' a ya sake rike ta ya amshi wuƙar ya ce "Baki da hankali ne me kike niyyar yi"


Nan fa Ummi ta fara masifa tana faɗa masa maganganu marassa daɗi, "Tunda ka auro ta ka maida mu bayi a gidan mu muke komai kana kallon ta tana abin da taga dama, to Wallahi idan baza ka yi adalci ba ka ringa ganin masifa da tashin hankali a gidan ka kenan, sai anyi magana kace wanda bazai iya zama da ita ba ya bar maka gidan ka, to baza mu bar gidan ba, kuma mun shirya karban ƴancin mu a gidan nan ni da ƴaƴa na"


Ya ce "Bazan ga tashin hankali ba, dama naga alama shi kike nema, tunda har kika ɗauko Wuka zaki kashe min matata saboda haka kije na Sake ki Saki ɗaya.





_*Mrs Aliyu ce*_





lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_


*Auntu Juuu Ina jin daɗin Comment ɗinki yana sani farin ciki kuma ina godiya*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 21-22


Da gudu Bilkisu ta ƙaraso ta riƙe hannunsa tana cewa Abba dan Allah kada kayi haka ka ce ka janye, Abba dan Allah idan kayi hakan ka tarwatsa farin cikin gidan ka ne Abba"


Fizge hannunsa yayi ya shiga ɗaki yana jin ɗaci a zuciyar sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login