Showing 30001 words to 33000 words out of 62424 words

Chapter 11 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2861

dama Baba baya son ya auro wata yaje yaci mutumcin Bilkisu, to yanzu ya lura hankalin ya kwanta kuma Bilkisun bata da wani matsala, yasa ya amince duk da ya lura Rukyn ba mace mai tarbiyya bace, amma tunda ya masa biyayya a baya shima ko zai faranta masa rai ta hanyar aura masa wacce yake so.


Da kansa Baba yaje gidan ya samu ko ina fes, taji daɗi ganin sa ta kawo masa abin sha sannan ta kaishi dinning dan ta bashi abinci, Ya ci sosai, ya ce "Nayi kewan girkin ki ƴata, tunda kika tafi gidan mu ya lalace ba gyara,"

Ta ce "Allah Sarki Babana, nima nayi kewarka, wata rana idan na tuna ka kamar nayi tsuntsuwa naje na ganka"


Falo suka dawo ya kalle ta ya ce "Ya naga baki yi ɗan kiba ba, irin na amare kodai ba matsala ne"


Ta ce "Ba wata matsala Baba komai lafiya"


Ya ce "To sai kiyi haƙuri da abin da zan faɗa miki Umar zai kawo miki ƙanwa"

Dam! Kirjinta ya ce Ta san hakan zai faru kuma kuma ko da suna waya da Umar a gabanta bata jin komai sai gashi yanzu tana jin wani iri a ƙirjinta...



_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/29, 7:10 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 39-40




Ba ya kalle ta ya ce "Yaya Bilkisu ko akwai matsala ne"


Tayi murmushin ƙarfin hali ta ce ", Ba wata matsals komai lafiya lau"


Ya ce "To kiyi haƙuri ko zai sake yin auren ne badan baya son ki ba"

Cikin ranta ta ce "Dama can baya sona dama tsinka auren aka yi da yafi"

Nasiha ya mata sosai sannan ya tafi.

Bai taɓa fada mata maganan auren sa, ita kuma bata tambaye shi ba.


Ana saura kwana uku auren kuwa Ruky ta shigo wannan karon da dogon hijabinta har ƙasa, Bilkisu kan da ta ganta sai da ta waro ido, yaushe Ruky ta koma haka. Tana cikin yin wannan tunani ne Ruky ta ce "Kira min Umar Ke"


Zama Bilkisu tayi ta ce "Yaje a koya masa Sallama tunda daga shi har ke ba ku iya ba, kinga idan ya koyo sai ya koya miki"


Ta ce "Kan buuu ni keke faɗawa haka to bari kiji nan da kwana uku zan kasance a gidan nan daga lokacin kin daina farin ciki har ƙarshen rayuwanki"


Bilkisu ta ce "Baki isa ba, ƙarya kike ki hana ni sakewa a gidan mijina"


Yana tsaka da barci ya jiyo hayaniya ya fito yana tsaki Yana ganin su ya kalli Bilkisu ya ce "Ke menene haka kuma"


Ruky ta matso kamar zata shafi jikinshi ta ce "My dear Dama nazo ne na zaɓi ɗakina ko"


Ya ce "Ɗaki ɗaya ya rage a gidan nan, sai ki shiga tunda kinki ki zauna a wancan gidan, ni gani nayi wannan ɗin ya miki kaɗan"


Ta ce "Ni nafi so ma ka haɗa mu gaskiya"


Ya ce "Ga can ɗakin da ya rage sai ki ɗauke shi, ay ina ga ma ba sai ansa komai ba, saboda akwai komai a ciki sai dai ki shiga ki duba abin da babu sai a siyo a saka"


Ta leƙa ɗakin sannan ta sake leƙa ɗakin Bilkisu ta gata kayan alatu a ciki kuma yafi na wancan ɗakin ta dawo ta ce "My dear ni wancan ɗakin nake so, ka mata magana ta koma wannan din"


Ya ce "To kinji Matar gida ta ce tana son ɗaki ki koma wancan ɗin kawai, zan kira masu aiki su mayar miki kayanki can ɗakin a dawo mata da nata"


Kafin Bilkisu tayi magana Ruky ta ce "No ni kayan ɗakin ma nafi so ay"


Ya ce "To shikenan ba sai an canja ba ma"

Bilkisu ta ce "Duk cikin ba wanda ya isa ya canja min ɗaki balle kayan ɗaki, baka faɗa mata cewa kayan ɗakin nan ba kai ka siya ba, Mommyn Kaduna ta siya min kuma da sunana ta siya, dan haka ɗaki ina zaune a ɗaki ba wanda ya isa ya fidda ni, idan baza ta zauna a wancan ba ta bari"



Ya kalle ta ya ce"Ke... "


Ta ɗakatar dashi ta ce "Saidai ka kashe ni ka fitar da gawata a ɗakin ko kuma ka tsinke igiyar auren ay tana hannun ka, amma ka sani kaya nawa ne bak isa ka raba ni da shi ba"


Ruky ta ce "Ka bincika yarinyar nan anya bata sha wani abu ba"

Ta ce "Abin da kike sha shi nima nasha yau"


Tana tsaye tana girgiza yazo ya riƙe kunnenta ya ce "Ke bakya ji ko"


Ta ce "Wallahi idan ka takura min zan faɗawa Baba"


Hankaɗata yayi ya kalli Ruky ya ce "Baby ki kyale ta ki zauna a can ɗakin kawai keda gidan ma ya kusa ya zama naki ke ɗaya, bari dai ayi auren"

Ta ce "Oho idan ma gida ya koma nata to ay Kaya nawa ne, da su zanyi gaba "


Zata yi magana Bilkisu ta ce "Rufe baki nifa na zama ciwon ido sai haƙuri "


Umar ya ce "Kije gida zanyi maganin ta ay"



Ba musu ta fita ya zauna a kujera ya ce "Kije ki haɗa min lipton zan sha"


Kicin ta shiga ta haɗa masa ta kawo ta miƙa masa yana amsa tayi ɗakin sa.


Alhaji shine wanda ya wakilci Ruky Yayin da Umar kuma wani Abokin Baba ya wakilce shi inda aka ɗaura Auren su. Murna gun Ruky da Mama Amarya ba'a magana haka, ƙawayenta ta gaiyato sukayi partyn su sukayi baɗala da junan su.


Lokacin da za'a kai amarya kuwa har ɗoki take yi ayi-ayi a kaita, inda suka tasa a ɗakinta. Daga cikin masu mata nasiha kuwa tsohuwa ɗaya ne ta mata nasihar arziki.


A haka kowa ya watse aka bar Amarya a ɗakinta sai Uwar gida da take cikin nata ɗakin. Saida kowa ya tafi Ruky ta fito Falon ba kowa sai ƙamshi dake ta tashi a falon, ɗakin Bilkisu ta shiga ta sameta a kan sallaya ta ce "Ashe kina jinmu kika ki fitowa to ay ba kowa sai ki fito ki haɗa min tea zan sha"


Ba ta ce komai ba Ruky kuwa ta na tsaye a kanta, saida Bilkisu ta gama Addu'o'inta sannan ta juyo ta ce "Baki san inda zaki more ni ba sam, da kin haɗa ni da Allah ne da Wallahi ba abin da zai hana ni haɗa miki saboda a halin yanzu ke baƙuwa ce, amma tunda dole zaki sani sai ki sani dolen in gani"




Komawa tayi ta ce "Ay wanda zai saki dole zai shigo kuma sai kinyi"



Kallon ta kunna tana yi Umar ya shigo da sauri ta mike taje ta rungume shi ta kiss a kumatu shima rungumeta yayi da ɗayan hannun ɗayan kuma leda ne manya guda biyu a hannun sa, ta ce "Ko yau ma zaka hana in taɓa ka ne"


Ya ce "A yau kan duk abin da kike so zakiyi saboda ni ɗin naki ne"


Sai ta ce "To ka ɗauke ni ka kaini ɗaki irin na ƴan india"


Ɗaukan ta yayi ga ga ledodin a hannunsa, bai direta ko ina ba sai ɗaki, raba ta ya fara yi da kayan jikin, ita ma tana raba shi da nashi daga nan suka yi bayi wanka suka yi sannan suka fito, shikan saida yayi alola ya fito ya kalleta ya ce "Ki koma kiyi alola sai muyi Sallah raka'a biyu dan nunawa ubangiji godiyar mu"



Turo baki tayi ta ce "Ni gaskiya na gaji bazan iya ba"


Ya ce "To shikenan muci abinci mu kwanta"

Ɗauko ledan yayi ya buɗe musu a cikin ledan sukayu ta ci, Ruky kan tsakanin ta da Allah take ci Bil hakki da gaskiya, Hollandia din kan ma da bakin abin ta ɗauka ta kwankwaɗa, suna gamawa suka kwanta, ita kan tashi tayi ta cire kayan jikin ta haihuwar uwashi ta ce "Saidai shima ya cire nashi, hakan ya biye mata suka shiga bargo suna wasa da junan su, sai dai shi Umar kwata-kwata baiji sha'awanta ba, suran jikin ta ma bata burge shi ba, yana biye mata ne kawai dan kada taji haushi. Gaba ki ɗaya nonuwanta sun kwanta kamar uwar da ta shayar da yara goma, gwara ma wata uwar saboda tana gyarawa, ba wannan yafi bashi haushi ba, sai lokacin da ya shigeta yajita kamar bakin bokiti, saidai ba yadda ya iya haka ya biya mata buƙatarta, dan ba ita ta biya masa ba.


Mikewa yayi zai shiga bayi dan tsarkake jikin sa sai ji tayi ta ruko shi ta ce "Bai ishe ni zo ka ɗan ƙara min mana"


Juyo wa yayi yayi mata wani mungun kallo.


_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/30, 2:39 PM] Mim😘: _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 41-42



Ta sake damƙe shi ta ce "My dear lafiya"


Ya fizge hannunsa Ya ce "Ni ɗan akuya ne kamar ki"


Ya shige bayi yana da na sanin auren ta, a rayuwansa ya tsani macen da ta bada kanta a waje kyamar su yake ji, sai gashi yau yayi taraiya da ita, yau me zai mata ya huce takaici, wai me yasa shi baida sa'ane duk auren da yayi guda biyu duk wasu mazan sun sun riga shi moran jikin matan sa, tir da halin mata tasu irin wannan halin.


Yana fitowa ya samu ta haɗa kai da gwiwa tana kuka yasa kayan sa zai fita ta ce "Nasan abin da yasa kayi fushi dani dan na rasa budurci na ne, hakan da ya faru ba yin kaina bane nima, tsautsayi ne ya faɗa min, shekara biyar kenan da wasu suka sace ni suka min fyaɗe har su uku, dama nayi tunanin wannan rana zata zo min mijina zaiyi baƙin cikin samuna a hakan, kayi haƙuri na ɗauki duk wani hukuncin da zaka min amma kada kayi fushi dani, saboda ni ba mazinaciya ba ce"


Tausayin ta yaji yazo ya dafa ta ya ce "To ya isa haka kiyi haƙuri, ina tare dake "


Rarrashi yayi tayi yana mai jin tausayin ta ita ko Daɗi fal cikin ranta.




Da Sassafe Bilkisu ta kama shirya musu break saida ta gama komai sannan tayi wanka ta fito kenan zata ɗeba ta gansu sun fito Ruky sai kwanciya a jikin sa take, Bilkisu kan ta kawar da kanta gefe guda zata ɗebi abincin Ruky ta ce "Me zaki dashi kuma kije ki girka wani"


Bilkisu ta kalleta ta ce "Uban kuturu yayi kaɗan bare na makaho"


Ta ɗeba yadda zai isheta ta wuce ta gefensu, Ruky zata yi gunta Umar ya jawota ya ce "Kyaleta so take ta ɓata mana wannan rana"


Ta koma suka zauna suka ci abincin su.


Umar dai haka ya manta ma ta yaya ya samu Ruky ko yaushe suna tare yana biya mata buƙata dare da rana safe da yamma ta maida shi ɗan bunsuru, saidai kuma sam yaƙi barinta ta wulaƙanta Bilkisu Aduk lokacin da taso yin hakan takan mata wayo tun bata gane wa har ta gane wayo yake mata, gashi ita kuma sai rashin kunya, abin ya fara isan ta, dan haka tana zuwa gida na farko ta faɗawa Mama Amarya, Mama Amarya ta ce "Lalle kuwa ina ganin da son yarinyar nan a ransa, amma kuwa zanje gun boka zai raba su kuwa"


Ta kuma ware hannunta ta ce "Ya maganan kuɗi fa yana sakar miki kuɗi ko"


Ta ce "Gaskiya baya sakar min komai"


Mama Amarya ta ce "Sha kurumin ki saura kuma idan kin fara samu ki manta da ni"


Ta ce "Haba Mama yaya zan miki haka ay kema kinsan hakan baza ta faru ba"


Hiran su sukayi tayi duk rabin hiran nasu na ta yadda zasu ga bayan Bilkisu ne.


Da yamma kuwa tayi gurin watsewarta dan a cewar ta baza ta iya rayuwa da namiji ɗaya ba, ita ko Mama Amarya gun boka tayi. A gun watsewantan kuwa saida tayi lalata da maza uku, mace ɗaya, dan gurin Maɗigo ma ba'a barta a baya ba, kuma ta samu abin da take so wato kuɗi dan sun cika mata jakarta da kuɗi.

Sai ƙarfe 9:00pm ta dawo ta samu Umar shi ɗaya a falo ta zauna a cinyarsa ta ce "My dear kai ɗaya ne haka"


Ya shafi fuskrta ya ce "Dawa kike son na kasance to ko so kike na kira yarinyar nan"


Ta ce "Da kuwa lahira tayi baƙuwa"


Dariya yayi ya ce "Nayi kewanki My Ruky kin riga kin sabar min da jikin ki, ina zaune a nan ina ta tunanin ki "


Nanko suka faɗa abin da aka saba.


Zaman sa da Ruky tasa ibadan sa ta ragu, yana sallah amma ba'a yin ta akan lokaci ita ma yana sallama zai miƙe ba zancen yin tazbihi wa ubanginsa balle kuma Addu'a.


Yau ƙarfe 10: 45am ya tashi alola yayi yayi Sallahr asuba da haushin Bilkisu yau ya tashi, kwana biyun nan ta raina shi shida matar sa, dan haka yau zai zane ta, fita yayi ya ga ta haɗa musu break kamar yadda ta saba yau, gidan tsab yake a gyare ko ina saidai inda yake kwanciya ne kuma datti har kuɗin cizo sun fara yawo suna cizon sa. Ɗakinta ya shiga ya ganta kwance tana barci ya buga mata duka a cinya da sauri ta tashi tana sosawa, ya nuna mata hannayen sa da jikin sa yana cewa "Dan ubanki kalli jikin, kalli hannayena yadda kuɗin cizo suka cije ni, sai ki gyara ko ina a gidan nan amma baza ki gyara gun kwanciyar mu ni da Mata na ba"


Bilkisu ta ce "Ahhh Lalle ma, ita matar taka bata da hannu ne da baza ta gyara muku ba, kuɗin cizo ku ya shafa ay, ina ruwa na"


Ya ce "Kinga ina kyale ki shine zaki nemi ki raina ni"


Kwanciya tayi ta jawo bargo ya rufe kanta shi kuma ya janye ya kuma ɗaka mata duka a cinya ta kuma ta ce "Allah ya isa mungu kawai"

Bulala ya ɗauka ya ringa zana ta shi tana kuka tana cewa "Allah isana"

Saida ya gaji dan kansa ya ƙyaleta, kuka ya ce "Dole taje ta gyara musu ɗaki"


Fita tayi tana kuka ta shiga ɗakin da tun da aka tare a cikin sa baiga tsintsiya ba, sai tsami da wari yake, zanin gadon kuwa sai wari yake saboda ƙazanta yayi yawa akan sa, haka tana kuka ta gyara ba laifi yayi kyau ɗakin saidai bangon ɗakin ne da ya ɓaci da jinin kuɗin cizo, inda in an gansu ake kashe su a jiki.

Haka take kasancewa da laifi da ba laifi ba kullun a duka, har Ruky ta fara nata ita ma, kai tsaye zata ce tana son mata abu kuma dolen ta ta mata. Idan ba haka ba tasha duka.

Ruky kan yanzu ta gaji da Umar dan zabbin maza take so yanzu, kwata-kwata bata son mu'amala da shi, wannan yasa ta ƙirƙiro tafiya, ta ce zata yi tafiya zata yi sati, ya ce "Ina zaki je ne"


Ta yi masa wani kallo, ta ce "Dallah Malam matsa kuma sai na faɗa maka inda zanje, to bazan faɗa, nidai abin da nake so da kai kuɗi zaka bani"


Ya karyar da kai ya ce "To ba damuwa"




Sassafe ya shirya mata kaya ya bata kuɗi da yawa ta tafi ɗakin Bilkisu ta ce "To Bilkisu zanyi tafiya saura kuma ki fito falo kina masa feleƙe da wannan tsinannun suran naki dan na lura shi ɗin ɗan akuya ne zai iya nemanki"


Bata ce mata komai ba har ta fita, haka ta tafi ba a son ransa ba.


Gidan ya masa wani iri baya jin daɗi dan haka shima da wuri ya fita gurin aikinsa.



Ko da aka tashi ya dawo yaci Abinci ya kuma fita Bilkisu kan ma bata san ya shigo ba, haka ya gama ya fita, sai dare ya dawo ya shiga ɗakin sa ya kwanta sai juyi yake yana tunanin yadda zaiyi da munguwar sha'awar da take damunsa. Ga Ruky ta sabar masa da kanta duk da ba wani daɗinta yake ji ba.



Tunawa yayi da wata matar, ya miƙe da sauri yayi ɗakin ta ya murɗa ya hangota ta baje a kan gado tana ta barcinta. Ciyarta ya zubawa ido daga bisani yakai hannunsa kan cinyar yayin da ita kuma ta buɗe ido jin an taɓa ta...



_Ina masoya Bilkisu ku bata shawara ta yadda da Umar ne ko taƙi shi_

_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/31, 9:39 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐(

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login