Showing 6001 words to 9000 words out of 62424 words

Chapter 3 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2842

fita waje ta fada wa Alhaji cewa Hali ta haihu, ya washe baki ya ce "Me aka haifa? "


Ta ce ay sai sun fito

Suna zazzaune Umma ta fito da Babyn ta miƙawa Alhaji ta ce "Barka Alhaji an samu ƴa mace"

Ya amshe ta yana mata Addu'a, Sannan ya miƙawa Mama Suwaiba ita ma ta amsa tana mata Addu'a sannan ta miƙawa su Abubakar sai murna suke, Tuni aka kira yan uwa da abokan arziki ana shaida musu haihuwa



Saida aka gasa mata jikinta aka yiwa jaririyar wanka ita ma tayi wanka sannan Alhaji ya dauke su tare da Umma suka yi asibiti, aka duba su, da uwar da ƴar duka lafiya.


Sai dai kuma Hali sam taki yarda ta amshi yar wai kunyar ta take ji idan an mika mata ma saidai ta kauda kai ta rufe idonta. Umma tayi tayi amma ko ɗago ido ta kalli ƴar ma taƙi yi, Mama Suwaiba kuwa da tazo bata mata da wasa ba haka ta ɗaga mata riga tasa mata ƴar a cinya ta kama hannun ta ce "Idan baki rike ta kin bata nono ba wallahi baza mu shirya da ke ba, wannan wani irin abu ne "

Haka ta rike tana bata saidai kanta na gefe ko kallon ƴar bata yi. Basu ce mata komai ba sudai burin su ya cika da har ta yadda ta batan.



Bayan kwana biyu kuwa Alhaji ya ce zai raɗa mata suna to dama Mahaifinsu Malam hamza ne mai raɗawa yaransu sunan saidai shi ya rasu dan haka ya samu Hali ya ce "Wani suna za'a sawa ƴar taki"


Ta kwanta ta nutsa kan ta cikin filo a hankali ta ce "A saka mata Sunan Adda Bilki"


Dariya yayi ya fito falo ya amshi yar a hannu Umma ya raɗa mata suna BILKISU, Dama ƴar a gurinsu take sai in zata sha nono ne suke kaita sai kuma bsrci, da daddare kuwa sai ta tashi tayi ta kuka amma Hali haka zata juyar da kanta gefe tana jin ta sai wani daga cikin su ya shigo ya dauketa a mata magana ta bata nonon.


Anyi taron suna inda yarinya taci suna BILKISU, Saidai yarinyar kwata-kwata bata san daɗin uwa ba, saidai Mama Suwaiba ne ke jigila da ɗawainiyarta,


Haka rayuwa ta ci gaba inda Bilkisu tayi girma amma bata san daɗin uwa ba, ko tana kuka saidai yayyenta su lallashe ta ko Umma ko Mama amma da zata kwana tana yi Ummi baza ta ce mata ci kanki ba sadai ta kawar da fuska. ( Nikan na ce ohhh wannan kunyar Fulani na ɗan fari bata yi ba) shekaranta ɗaya aka yayeta Mama Suwaiba ce ta dauke ta ta kwashe kayanta ma daga dakin Hali ta kawo dakinta, a tunanin su zata damu sai suka ga ma hakan da aka yi tafi sake wa.


Gata kuwa tana samu gun yayyen ne ga Umma ga Mama har da Alhaji suna ji da ita, amma banda Hali, ita kan Bilkisu ma ko gurin ta bata zuwa, saidai idan su Abubakar sunje suna barin gurin ita ma zata bar gurin.

Shekaranta biyu suna zaune suna wasa da su Abubakar ita kuma Ummi tana kicin su kuwa su Umma suna Falo suka ji Sallama Suka fito Sarkin Fulani ne tare da wata Mata da yaron ta sa'an Abubakar sai yarinya mace a bayanta, Mama Suwaiba ne ta shigo da su har falo Matar ta kyalla idon ta a kan Bilkisu sai kallonta take, Mama Suwaiba da taga haka sai ta dauke ta ta sata a baya, Mama Suwaiba ta shiga kicin dan ta kawo musu abin sha taga Hali a ciki ta ce "Ki fito munyi baƙi"

Hali ta dauko ruwan yayin da Mama Suwaiba ta tsaya haɗa musu kayan ciye-ciye ta fito da ruwan kenan suna haɗa ido da Matar Hali ta saki abin shan hannunta ta ruga da gudu tana cewa "Addana" suka rungumi juna sai suka saki wani kuka me ban tausayi, Saida sukayi Kukansu sosai ba wanda ya lallashe su sai tausayin da akayi ta ji, Saida suka ci suka sha sannan Sarki ya ce "Halima duk abin da kika ji daga bakin ƴar uwar ki kada ki tada hankalinki ki kwantar da hankalinki haka Allah ya kaddaro muku.




_*Mrs Aliyu ce*_



lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻[5/16, 7:38 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_



_Gaskiya bana ganin Sharhi kuma ya kamata a na yi ɗin_





*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 9&10



Kallonsa duka falon suka yi Umma ne ta ce "To baza ka jira Alhajin ku gaisa ba"

Ya ce "A'a zan tafi kawai"



Yana tafiya Hali ta ce "Adda kinga yadda Allah yayi da mu ko"

Ta fara bata labari daga farko har ƙarshe har irin yadda su Umma ke kula da ita, saidai kwata-kwata bata sa labarin Bilkisu a ciki ba, ko faɗa ma ta haihu bata yi ba. Saida tayi shiru shiru Mama Suwaiba ta ce, "Lallai ma Ummin Yara kin iya fada mata komai amma baki fada mata labarin takwaranta ba"


Ta ce "Hmm "

Umma ta ce "Ay dama na san baza ta faɗa ba, to dai nata faɗa miki maganan haihuwa ba"

Umma ta bata labarin komai da yadda akayi ta fama da ita wajen renon yarinyar karshe ta ce "Tunda Maman yara ta dauke ta har yau ko kallo ba ya haɗa su da ita, na rasa wannan wace irin uwa ce, ace ka haifi ɗa a cikin ka amma ka nuna rashin kulawa."


Adda ta ce "Ni ya kamata nayi wannan rainon wa yara na, tunda ni nasha wahala, dan na taso koda ina buƙatan taimako idan ban samu ba zan mutu mahaifiyar mu ba za ta taɓa taimaka min ba, Sai Baffa shine gata na shine ya raine ne, Amma Inna ko zan mutu ba ruwan ta dani. Amma kin ganni tunda nayi aure na haifi Aliyu naga yadda ƴan binni suke ji da yaran su nima na ɗauka, Aliyu y more ni sosai dan ban kuma haihuwa sai kwana nan yanzu Maryam watan ta bakwai bazan bari su sha wahala ba, ni tunda na shigo naga yar sai naga Fuskar Hali, don abin da tabar Hali tana ƙarama. Hira suka yi sosai kamar sun san juna

Daga baya ne Hali ta ce "Adda me ya faru naji ɗazu sarki yana min wani magana wai inyi haƙuri da abin da zaki faɗa min"


Adda Bilki ta ce "Haka ne Hali Saidai muyi haƙuri da iyayen mu, an samu labarin su a wani riga saidai kuma bukkan su ta kama da wuta sun ƙone gaba dayan su "

Hali ta dafa kirji ta ce "Inna da Baffan? "


Nan fa ta fasa kuka Adda ta rungume ta tana kuka tana bata hakuri sannan taci gaba da fada mata, An kawo wa Sarkin Fulani Shanun na cesa ya ci gaba da mana kiwo"

Alhaji da ya dawo yaji wannan Al'amari ya tausaya musu matuƙa kuma ya kwantar musu da hankali.


Kwanan Adda da yaran ta huɗu a gidan sannan ta koma Kaduna Alhaji kuma ya mata Alƙawarin zai kai mata Hali.

Hakan kuwa aka yi ya kaita din daga baya kuma ita da kanta take zuwa ko ita Addan ta je, ko yaushe Addan nata tana bata baki akan tana kula da ƴarta Bilkisu amma ina ba ma abin da ya dame ta da ita ita ma Bilkisun yanzu bata damu da ita ba.


Idan yayyenta suna gida kullun tana tare da su, wataran ma Idan Umar yazo dashi ake, sun shagwabata sosai, ko abu take so sai tasa kuka, idan ance menene sai ta ce "Ita a bata kaza"

Haka kuma iyayen basa son suji ko da nishi ne, uwar gayyar ko ko oho. Tunda ta gane Umar zuwa yake yi, yasa da zaran ta ganshi sai tasa kuka idan ance menene, sai tace "Ya Umar ya je gidan su "


Abubakar ya kalle shi ya ce ka mata wani abu ko, yakan ce A'a sai ya ce to tafi gidan ku, nan kuma zai fara lallashin ta, ita kuma ta ƙara narkewa, ta jina tana yiwa Umar haka kuma abin da take masa yana bashi haushi dan haka ya sa mata ƙahon zuƙa da zaran ya shigo tana ganin sa kafin ta fara kuka sai ya bubbuge mata baki yace "kuma kika fada sai na ballaki, shegiya zabiya"

Hakan yasa ta fara jin tsoron sa haka zai shigo ya bubbugeta idan anzo anga tana kuka idan aka tambayeta sai tayi shiru su kuma su lallashe ta.


Shekaranta tara Mama Suwaiba ta kwanta ba lafiya koda aka kaita asibiti aka tabbatar tana ɗauke da juna biyu, murna gurin ba'a magana, saidai cikin nata yazo mata da laulayi ƴan gidan suke taimaka mata da komai Musamman Bilkisu duk da yadda take da ƙananun shekaru amma ba'a barta a baya ba, Makaranta take rabata da Maman nata da ta taso saidai ta zauna ɗaki tare da ita, ko ta ce su fito falo, kullun tana jikin ta da yake Allah yasa ita ɗin me son jiki ce.


Har cikin yakai haihuwa tana abu ɗaya ga kumburi da tayi, bata cin gishiri, daban ake mata girkin ta.

Lokacin haihuwan kuwa nayi riƙe ta suka yi asibiti saboda jikin nata, kullun Bilkisu na tare da ita wata ran ma bata zuwa makarantar, koda haihuwan tazo tasha wahala dan saida aka saka mata ruwan naƙuda ta haifi ƴarta mace, tubar kallah da ita, saidai kuma ita ta haɗu da tsinka-tsinka Bilkisu kan kuka ta sa Abubakar ya fita da ita, shi ɗin ma ya daure ne saboda ƙanwar tasa, tana kukan Umar ya shigo yana mata wani kallo duk kuka da take ta gimtse ta kwanta cinyar Abubakar ta rufe Fuskar ta da tafin hannun ta.


A ciki kuwa tana dawo wa hayyacin ta ta kalli Hali dake rike da ƴar Hali ta ce "Kinga abin da kika haifa"


Tasa hannun ta a akan jaririyar ta ce "Allah ya mata Abarka, Allah yasa ta Amfane mu haba ɗaya, "


Umma ta ce "Ɗan rungumeta ki bata Nono"


Ta kaɗa kai ta ce "Ummin yara zan bar miki Amana, ga Bilkisu Amana ce a gurin ki, ina son daga nan har ƙarshen rayuwarki ki kula min da ita, nasan su Umma da yayyen ta zasu bata kulawa, kece baza ta samu ba, amma ina roƙon ki ki cire kunyar nan ki rungumi ƴarki dan Allah. "

Hali dasaurin kuka nan da nan ta fara kuka tana cewa "Ni ki daina wannan magana lafiyarki ake nema yanzu "


Ta ce "Bazan bari ba har sai kin min Alƙawari daga yanzu zaki jata a jiki"


Ta ce "Eh nayi Alƙawari kema kiyi shiru"


Ta ce "Alhamdulillah nagode miki"


Ta kauda kai ta yi kallar shahada daga nan kuma tayi ƙatuwar shaƙuwa sannan rai yayi halinsa.


Suna zaune suka ga Ummi ta fito tana kuka Umma ma nayi Abubakar ya miƙe ita ma ta miƙe ta ce "Umma Mamana ta mutu ko"

Umman ta rungumeta tana kuka tana cewa "Muyi haƙuri Bilkisu "


Kuka tasa me tsuma zuciyar me sauraro, Abubakar ya kamata shima yana zuba hawayen yana bubbuga mata baya alamun rarrashi, Baba Jafaru Mahaifin Umar shi ya maida su gida Alhaji da sauran Al'umma kuma suka taho da gawar. Nan aka mata sitira aka kaita gidanta na gaskiya, (Gidana, Gidanki, Gidanka, Allahu Akbar Allah yasa mu shiga a sa'a)


Bayan anyi bakwai kowa ya watse yarinya dai aka mata huɗuba da suna Khadija Hali take shayar da ita, kuma shayarwa ba irin wanda akayi wa Bilkisu ba, ta bata kulawa sosai ta mata kyakykyawan shayarwa.


Tun bayan rasuwan Bilkisu ta fara ganin abin Mamaki wai Ummi tace take sata a cikin maganar ta har ta ke kiran ta Addana ko ta sata aiki, Amma hakan baisa Bilkisu walwala ba har yanzu tana jin mutuwar Mamanta.

Tun tashin Khadija bata samun kulan da akewa Bilkisu a gidan bata shagwaban da Bilkisu take, ta girma ma amma abu kaɗan saita fara kuka, nan kowa yan gidan zasu zo kanta har Khadija ma da Ummi take ce mata Khadiyo shine kowa ya ɗauka ta gane dane idan abin ya tashi da ita ake lallashi. Umar ne ke taka mata burki idan yazo gidan bata sakewa kwata-kwata, shi kuma hakan ya bashi daman yi mata mugunta yadda ransa ke so idan su biyu ne a gurin.


_Kan labari_








_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/16, 8:11 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*Wannan page ɗin naki ne Juwairiyya Adam (Aunty Juuuu Ƙamshi) kiyi yadda kike so dashi ƴar uwa*




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*






Page 11&12




Bayan sun gama Su Bilkisu su ka kwashe kayan suka je suka wanke da suka dawo ne Khadoyo ta ɗauko jakar ta tayi gun Ya Usman ta ce "Muyi karatu, ita kuwa shagwababbiyar jikin cinyar Abubakar taje ta kwanta Khadiyo ta kalle ta ta ce "Wallahi kamar baki girma ba Aunty"

Ta ce "Barni nayi ay lokacina ne"


Umma ce ta shigo da Sallamarta Bilkisu ta tashi tana cewa "Umma ina kika shiga kika barni ni ɗaya a gidan"

Ta ce "eh da yake Ummin naki naki ba mutum ba ce ko"

Ta ce "Nidai ban faɗa miki haka ba"


Alhaji ne ya shigo fuskarsa da damuwa yana zuwa ya zauna a kan kujera mai zaman mutum ɗaya ya kama kansa Umma tazo ta zauna kusa da shi ta ce "Alhaji lafiya kuwa"

Ya dago kai yaga yadda yaransa suke kallon sa yayi Murmushin ƙarfin hali ya ce "Ku taya ni da Addu'a"

Umma ta ce "Me ya faru"

Ya ce "Akwai wata mace wacce take son aure na, ni kuma ban aminta da tarbiyyan ta ba shine naki ita kuma ta ce ko ta yaya sai na aure ta, na shiga damuwa da jin hakan"

Umma tayi murmushi ta ce "Haba Alhaji wannan ne zai dame ka, kaida kake da Allah zamu yi Addu'a in Allah ya yarda ba yadda za'ayi ka aure Allah ya fita "

Bilkisu ta ce "Abba ni ka faɗa min wacece inje in same ta"


Ya ce "Adda wannan ba hurumin ki bane ke dai ki taya ni da Addu'a kawai"


Bayan Sati ɗaya da yin hakan kuwa Alhaji ya tara iyalensa duka saida suka hallara kowa da kowa ya ce "Abin da yasa na tara ku, shine ina son sanar da ku cewa zanyi aure "

Shiru kowa yayi Umma ce ta yi karfin halin cewa "To Alhaji wa zaka aura kuma"


Ya ce "Ina ga ay kinsan ta, wacce na taba faɗa muku Ummin yara ne bata san zancen ba"


Shiru Umma tayi ta kasa cewa komai Bilkisu ce ta ce "Amma fa Abba kai kace baka amince da tarbiyyan ta ba, kuma ka ce mu taya ka Addu'a akan ta, ay muna maka"

Usman ya ce "Eh haka ne muna yi, To yanzu me yasa zaka aure ta"


Ya ce "Auren wannan mata lada zan samu, kunga tana da ƴa mace, kuma daga ita har yar yawon banza suke, kinga idan na aure ta sai in hana wannan yawon banzan"


Umma ta girgiza kai ta ce, " Lalle baka cikin hayyacin ka Alhaji, da bakin ka ka ke cewa tana yawon banza kuma kake son haɗa zuri'a da ita"


Hali ta ce "Idan kana neman shawaran mu ne Alhaji to zancen gaskiya kada ka aure ta, dama kamilalleya ce mana"


Shiru yayi kamar mai tunani Bilkisu ta ce "Abba ka duba mana, ni dama ka bar maganan wani aure tunda ga su Umma"

Ya ce "Adda bana jin daɗi idan ina ganin su su biyu Ina son wanda zata maye min gurbin Suwaiba ba ne"


Umma ta ce "Aure bamu hana ka ba amma kuma bamu yadda ka auri wannan matar ba"


Ya ce "To na ji, idan na aure ta zan raba muku gida zan ajiye ta a wani gidan daban "


Sai lokacin Khadiyo tayi magana ta ce "Gaskiya Abba kabar zancen nan"

Ita kan Bilkisu kuka ta saka jin kukan Bilkisu yasa ya mike ya koma ɗakin sa ya rufe, kowa ya zuba masa ido cikin mamaki, Bilkisun ma kukan nata ya tsaya cak tana kallon ƙofar, sun san dai ko yaya Bilkisu ta sa kuka to fa duk abin da yake ya daina zai lallashe ta, yau gashi tana kuka ya kyaleta.


Duka gidan sun rasa kansa baya zama a falo a yi hira idan ya shigo gidan to yana ɗakin sa, Idan zai fita kuwa ko Sallama baya yiwa kowa, kowa abin ya dame shi.

Abubakar ya fito kenan sai yaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login